Free chapter · Read without an account

Chapter 16

by Umma mustapha · WA ZAI FUSKANCE NI??

WA ZAI FUSKANCE NI??

‎BOOK 1

‎Umma Mustapha

‎Wattpad: Umma Mustapha

‎PAGE 16

‎Mafari...

‎Wata rana, ranar Alhamis, da misalin ƙarfe biyar na yamma, Jabir ne a ƙofar gidan su Nihla yana jiran Fatima. Jabir shi ne saurayin da Fatima ta yi, kuma a lokacin suna kan ganiyar soyayya da juna.

‎Shekarun Jabir ba za su wuce talatin da uku zuwa talatin da huɗu ba. Da alama bai samu damar yin karatu tun da wuri ba, sai yanzu. Shi ma Level 1 yake, ma'ana abokin karatun su Fatima ne, amma course ɗinsu ba ɗaya ba ne. A ɓangaren shekaru kuwa, ya fi su girma sosai, domin Fatima da Nihla ba za su wuce shekara ashirin da ɗaya ba.

‎ Fatima ta fito daga cikin gidan ta tsaya a kofar gida, sai ta Kalli gurin da JABIR yake tsayawa idan yazo, Amma ga mamaki baya wajen.

‎dan waige waige ta fara, ko zata hangoshi a Wani wuri.

‎Sai kawai ta ji ƙarar horn mota tayi gefenta.

‎Ta juya da sauri.

‎Wata mota ce a tsaye a gefe nesa da ita kadan.

‎Mamakine ya kama Fatima.

‎Ita dai ta san Jabir ba shi da mota. Ko da yana da ita, ba ya zuwa makaranta da ita.

‎Ta tsaya tana kallon motar sosai.

‎Sai wani abu ya ɗauki hankalinta.

‎Motar ta yi kama da waccan baƙar motar da ta taɓa binsu kwanakin baya.

‎Babu abin da ya bambanta su sai dai launi. Waccan motar baƙa ce, amma wannan ash color ce mai haske.

‎Idonta ya sauka kan number ɗin motar.

‎Waccan motar da ta taɓa binsu ba ta da number ko kaɗan a jikinta, amma wannan tana da number a bayyane.

‎Fatima ta ɗan daɗe tana nazarin motar, fitowar Jabir daga cikin motar ne katse mata tunanin.

‎murmushi ne ya bayyana a fuskarta.

‎Kallon fuskokinsu kawai za ka yi, ka fahimci cewa masoya ne.

‎Jabir ya matso kusa da ita yana murmushi.

‎"Ki zo muje ku gaisa, tare nake da abokina Kuma Dan uwana. "

‎Fatima ba ta yi masa musu ba. Suka juya suka nufi motar.

‎Wanda yake zaune a kujerar gaba ta gefen direba ya buɗe ƙofar ya fito. Yana yi wa Fatima murmushi.

‎Cikin girmamawa Fatima ta risina ta gaida shi.

‎"ina wuni ?"

"Lafiya lau"

‎Ya amsa mata cikin fara'a.

‎Fatima ta kalli Jabir.

‎"Ba ka faɗa min sunan abokin naka ba."

‎Kafin Jabir ya amsa, mutumin ya yi murmushi.

‎"Ba sai ya gabatar miki da ni ba. Ni zan gabatar da kaina."

‎"Sunana Irfan. Ɗan uwa ne kuma abokin Jabir. Daga yanzu na zama Yaya a gareki. Duk wani laifi da Jabir ya miki, za ki iya kawo min ƙara. Shi kuma zai karɓi hukunci."

‎Gaba ɗayansu suka saka dariya.

‎ Jabir ya Kalli Fatima Yana murmushi, sannan ya ce:

‎"To, ina ta hannun damata kuwa?"

‎Jabir ya tambaya yana kallon Fatima.

‎Fuskar Fatima ta ɗan sauya.

‎"Wallahi tana ciki. Ba ta jin daɗi."

‎Nan take zuciyar Irfan ta buga da wani irin ƙarfi.

‎Fuskarsa ta ɗan sauya, amma ya yi saurin ɓoye hakan.

‎Babu wanda ya lura, saboda Irfan mutum ne mai iya tsare gida da kuma sarrafa abin da yake nunawa a fuskarsa.

‎Jabir kuwa ya saci kallonsa, sannan ya mayar da hankalinsa kan Fatima.

‎"Subhanallahi! Me ya same ta?"

‎"Wallahi, santsin tayils ne ya kwashe ta ta faɗi." "Ba ta ji ciwo ba?" suka faɗa kusan lokaci guda.

‎Fatima ta kallesu cikin mamaki.

‎Ganin irin kallon da ta yi musu ya sa Jabir ya yi saurin cewa:

‎"Kin san irin wannan faɗuwar tana iya sa mutum ya karye ko ƙashi ya goce."

‎"Eh, to, ba ta samu matsala a ƙafarta ba. Amma dai ta bugu a gefen kirjinta, kuma ta ce yana mata ciwo sosai. Na kira Yaya Nasir, amma ban same shi ba. Ina jiran shi, idan ya zo sai mu san abin da za mu yi."

‎Irfan ya kasa ɓoye damuwarsa.

‎"kinga je ki kamo ta. Mu kaita asibiti a duba lafiyarta."

‎Fatima ta girgiza kai.

‎"Ta sha maganin rage zafi. Haka kuma Shukura ta ba ta wani mai ta shafa a wurin. Yanzu dai Yaya Nasir muke jira."

‎Wani irin takaici ya rufe zuciyar Irfan.

‎Idanunsa suka sauya saboda tashin hankali, amma ya yi iya ƙoƙarinsa ya ɓoye abin da yake ji.

‎Sai ya watsawa Jabir wani kallo.

‎Kallo ne da ba kowa zai fahimci ma'anarsa ba.

‎Amma Jabir ya fahimta.

‎Ya san abokinsa.

‎Jabir ya gyara tsayuwarsa sannan ya kalli Fatima.

‎"Fatima, wannan ba hujja ba ce. Yaushe za ki ce za ku zauna kuna jiran mutumin da ba ku same shi a waya ba? Kina da tabbacin zai buɗe wayarsa da wuri? Ba ki san inda yake ba. Wataƙila meeting suka shiga, ko kuma ya tafi wani uzuri."

‎Ya ɗan dakata, sannan ya ƙara da cewa:

‎"Yanzu idan ba a kaita ta samu taimakon gaggawa ba, wa ya san abin da zai iya faruwa da ita?"

‎Jikin Fatima ya yi sanyi.

‎A hankali maganganun Jabir suka fara shiga cikin zuciyarta.

‎Tsoro ya fara kama ta, domin ita ma ba ta son wani abu ya samu Nihla.

‎Ta kalli ƙofar gidan.

‎sannan ta kalli Irfan da jabir, wanda har yanzu fuskokinsu ke dauke da alhini da damuwa.

‎Babu wani zaɓi a gabanta.

‎Ta juya ta shiga cikin gidan.

‎Bayan Fatima ta juya, Irfan ya sauke wata ajiyar zuciya mai ƙarfi, kamar wanda ya daɗe yana riƙe da numfashinsa.

‎Jabir ya kalleshi ya yi murmushi kaɗan.

‎"Ka kusa kwafsawa fa."

‎Irfan bai ce komai ba.

‎Jabir ya ƙara da cewa:

‎"Domin Fatima da kake gani, tafi Nihla wayo sosai. Tana da saurin gano abu."

‎Irfan dai ya yi shiru Dan hankalinsa ba'a wajen JABIR yake ba.

‎Idonsa yana kan ƙofar gidan da Fatima ta shiga.

Ji yake kamar ya shiga cikin Gidan ya fito da ita.

Fatima kuwa, da ta shiga cikin gidan, kai tsaye ta nufi ɗakin da Nihla take.

Ta tarar da ita zaune, hannunta ɗaya a kan gefen kirjinta, fuskarta ɗauke da alamun rashin jin daɗi.

"Nihla Ki tashi, Mu tafi asibiti."

Nihla ta ɗago kai tana kallonta cikin mamaki.

"Asibiti kuma?"

"Eh. Kada ki damu, za mu je a duba ki kawai. Ba na son mu ci gaba da jira."

Nihla ta yi ƙoƙarin miƙewa, amma sai ta ɗan dafe wurin da yake mata ciwo.

Fatima ta ƙarasa wajenta ta riƙe ta.

" sannu. Ki tashi a hankali."

Da taimakon Fatima, Nihla ta shirya cikin ɗan lokaci. Fatima ta ɗauki A T M dinta, sannan suka fito daga gidan a hankali.

Jabir da Irfan suna tsaye a wajen motar suna jiran su.

Irfan yana ganin Nihla, hankalinsa ya tsaya gaba ɗaya a kanta. Ya lura da yadda take tafiya a hankali, Fatima kuma tana riƙe da ita.

Ba tare da ɓata lokaci ba, ya ƙarasa ya buɗe musu ƙofar baya.

"Ku shiga a hankali." Irfan ya fada tare da jerawa NIHLA sannu.

Fatima ta taimaka wa Nihla ta shiga. Nihla ta zauna, amma saboda ciwon da take ji, sai ta zame ta kwanta a kan cinyar Fatima.

Irfan ya tsaya na ɗan lokaci yana kallonta.

Wani irin tausayinta ya ji ya mamaye zuciyarsa.

Bai san dalilin da ya sa baya son ganin Nihla cikin wannan hali yake damunsa fiye da komai a rayuwarsa ba.

Ya rufe ƙofar motar, sannan ya zagaya ya shiga gaban motar.

Jabir ne ya zauna a kujerar direba, yayin da Irfan yake gefensa.

"Mu tafi," Irfan ya faɗa cikin sanyin murya.

Jabir ya kunna motar ya ja a hankali.

A cikin motar kuwa, Fatima tana ta lallashin Nihla tare da Yi mata sannu Akai Akai.

Nihla dai Ta lumshe idanunta tana ƙoƙarin jure ciwon.

Irfan ya saci kallonta ta madubin motar.

Sai ya ga Fatima tana gyara mata mayafi.

Ya mayar da idanunsa gaba, amma hankalinsa har yanzu yana kan ta.

Jabir wanda yake tuƙi ya lura da yadda abokinsa yake yawan kallon baya.

Ya yi murmushi kaɗan, amma bai ce komai ba.

A haka suka nufi General Hospital da ke cikin garin kafin hausa, yayin da kowa a cikin motar yake cikin wani irin yanayi na damuwa.

Umsar ✍️ 
***

Want the next chapter?

ui.create_a_free_arewapen_account_to_save_progress_unlock_paid_chapters_fol