Free chapter · Read without an account

The Night Before London

by ZAHRA B MRS · Nuwayrah the foreigner’s passion


Hannayen Nuwayrah na rawa ta miƙa hannu ta karɓi babbar envelope ɗin daga hannun Rayyan. Idanunta suka sauka kan  tambarin  da ke jikin envelopes ɗin Aura & Heritage Couture — London, UK.

Ta yage bakin envelope ɗin a hankali, ta fito da takardun da ke ciki. Tana buɗewa, idanunta suka soma karanta rubutun da ke saman takardar farko OFFER OF CONTRACT EMPLOYMENT —  RESIDENT EMBROIDERER.

A hankali ta riƙa karanta sauran bayanan Shekara ɗaya cif ta kwangila a masaukin fashion house da ke birnin London, masauki mai zaman kansa a unguwar South Kensington, da kuma albashi mai tsoka  

Nuwayrah ta daskare a tsaye, ta sake karanta sunanta da ke rubuce radau a saman takardar ,Nuwayrah Yusuf Modibbo.

Ray... Are you serious? London? Nuwayrah ta faɗa muryarta  na rawa saboda mamaki 

Rayyan ya saki wata 'yar gajeruwar dariya, 

"I told you something big was coming, Big Head! Babban gidan fashion ne a UK. Kuma kin san menene? Tunda na amshi samples ɗinki kusan watanni  da suka wuce na tura musu, suke ta dubawa. Na Kara tura masu Abuja Residency Challenge shi ne ya ƙara abbatar Musu da kwarewar ki ,kin San turawa duk sanin ka dasu basa alfarma idan Ka Samu aiki ko offer to chanchanta ce ta janyo hakan 

Wata irin  farin ciki ya  ziyarci zuciyar Nuwayrah , ta sake duban takardar hannunta, ta kalli Rayyan, ta koma ta kalli takardar. A karon farko cikin watanni biyu, Murmushin gaske bana yake ba  ya bayyana fuskarta har sai da dimples ɗinta biyu suka loba..

"Ray,  na kasa gaskatawa wallahi... London?" ta sake tambaya tana goge  ƙwallah 

Tana tsaka da wannan murnar ne, aka buɗe ƙofar corridor. Mama ce ta fito daga bedroom ɗinta

Mama ta tsaya tana kallonsu da mamaki. "Lafiya dai?  Muryar kice ta tashe ni daga bacci Dana fara .Ina yini mama cewar rayan yana dan ritsunawa ,Lafiya Lou dan Albarka Ina su hajia hadiza ?Kafin rayyan ya amsa 

Nuwayrah ta tashi tsaye cike da excitement, ta ƙarasa wajen Mama da takardun a hannunta. Mama! Kalli! London ne

Mama ta ɗaure fuska kaɗan tare da ƙara matsowa tsakiyar falon. London kuma? Wace irin London? Miko min takardar nan na gani.

Mama ta karɓi letter ta buɗe tana dubawa. Duk da ba ta gama karanta  dogon Turancin ba, amma sunan London, United Kingdom da Aura & Heritage Couture sun fito fili. Nuwayrah ta soma yi mata bayani daki-daki cikin rawar baki 

"Mama, wani fashion house  ne mai zaman kansa a London. Sune suka gani kuma suka zaɓi samples dina da Rayyan ya tura musu tun kafin mu tafi Abuja. Yanzu sun aiko min da contract na shekara ɗaya in je London in riƙa musu aikin embroidery ... Sune za su biya komai da komai 

 Mama ta gama sauraron bayanin farat ɗaya murnar da ke fuskar Mama ta tsaya gaba ɗaya.

London? Ke kaɗai? Mama ta tambaya, muryarta a sanyaye .

Nuwayrah ta ɗan marairaice fuska. Mama, ai tsari ne na aiki  Kuma Rayyan zai taimaka min da duk wani tsari da za a bi wajen shirya takardu da logistics gaba ɗaya.

Mama ta riƙe ƙugunta, ta juyo ta kalli Rayyan sannan ta dawo da dubanta kan Nuwayrah. 

A london din, ina zaki zauna? Waye me  kamfanin? Wa zai kula da ke a can kasar mutane idan wani abu ya same ki? Yaushe tafiyar za ta kasance? Shekara guda  kina mace ke kadai  Mimi ?

Rayyan ya gyara zamansa Mama , ki kwantar da hankalinki. Wannan sanannen gidan fashion ne sosai a can London, kuma 'Suna da masauki na musamman da tsaro da za su ba ta a wata  a tsakiyar garin, kuma komai yana karkashin yarjejeniya 

Nuwayrah ta durƙusa kusa da Maman, ta riƙe hannunta. "Mama, Ba yawon shakatawa zan je yi ba. Aiki ne na kwangila na shekara ɗaya. Zan koyi sabbin abubuwa , zan faɗaɗa sanina na ɗinki, kuma zan gina sunan sana'ata na Nuwayrah’s Stitches a matakin duniya. Ɗan Allah Mama ki tayani Murna ki sa min albarka kawai 

Mama ta saki gajeren numfashi,  Auta, ta yaya zan taya ki murna ta hanyar tura ki ƙasar  waje ke kaɗai? Yau watanki biyu kacal da samun nutsuwa daga tashin hankalin da kika shiga! Yanzu kuma ki tashi ki bar ni ki tafi can inda ban san kowa ba? A'a wallahi, zuciyata ba za ta ɗauka ba. 

A daidai lokacin ne aka tura ƙofar falo, Abba ya shigo riƙe da hularsa a hannu, yana sallama. Seeing the tense atmosphere a falon, da Rayyan zaune da takardu 

Lafiya dai Bilkisu? Me ke faruwa na ganku a haka?" Abba ya tambaya yana dubansu .

Mama ta mika masa takardar hannunta. Abbansu, ka duba kani. Wai kwangilar aiki ce ta fito wa Nuwayrah A London ... Za ta tafi birnin London ita kadai har shekara 

Abba ya zauna a kan kujera, ya sa gilashin idonsa ya karanta  takardun contract ɗin da kyau. Ya bi kowace sakin layi da dukkan sharruɗan da ke rubuce. Bayan 'yan mintuna, ya ɗago kansa ya kalli Rayyan, sannan ya kalli Nuwayrah.

, Wannan babbar dama ce  da Allah Ya kawo mata.

Abbansu! Maimakon ka taya ni nuna mata haɗarin da ke ciki, shine kake maganar babbar dama? 'Yarka mace fa? Ta yaya za mu bar ta ta tafi  London ita kaɗai? 

Ganin mama bata da niyar amincewa ,rayyan ya masu sallama ,yasan dai brothers din Mimi will never fail her dole mama ta sauko .

Bayan tafiyar Rayyan, abba  ya kiraNabil yace yazo gida  Akwai urgent family meeting Bayan isha Kafin nan Sadiq  Shima ya dawo daga office 

Bayan Isha , kowa ya hallara a falon. 

Yaya Nabil ya karɓi kwangilar aikin, ya bi kowace ka'ida ta Aura & Heritage Couture daki-daki . Shi da Yaya Sadiq suka shiga   internet suna Kara  zurfafa bincike kan kamfanin.

Abba, na duba company registration ɗinsu na UK ,Yaya Sadiq ya faɗa yana nuna wa Abba wayarsa.  Gaskiya kamfani ne babba kuma mai daraja a South Kensington London Wannan life time opportunity ne ga Mimi 

Yaya Nabil ya gyada kansa cikin gamsuwa. . Ni a ra'ayina, ya kamata mu ba ta cikakken goyon baya ta tafi sai mu bita da Addua kuma mama ay kin San tarbiyar da kika ba Mimi am very sure bazata watsar dashi ba 

Mubeen da ke sauraronsu ta waya ya tofa albarkacin bakin sa  Wallahi hakane Yaya Nabil! Auta ta cancanci wannan nasarar. Ni kaina a matsayina na lauya na duba sharruɗan kwangilar, da Mimi ta turo min dazu babu wata ka'ida da ta tauye mata 'yancinta ko mutuncinta.

Duk brothers ɗinta gaba ɗaya suka fito fili suka nuna cikakken goyon bayansu ga tafiyar Nuwayrah. Ban da Mama 

Mama da ke zaune ta haɗe ranta, ta kalli mazajen gidan ɗaya bayan ɗaya cikin rashin jin daɗi. "Wato dukanku kun hada Baki kenan ? Magana fa ake Akan yata mace daya tilo 

Ita kaɗai a tsakiyar Turawa a ƙasar waje? Idan wani abu ya same ta a can wa zai taimaka ta wa zai kula min da ita ?mama ta fada cikin daga murya .

Abba ya kalle ta cikin lallashi Bilkisu, Allah shi zai kula da Nuwayrah ,hanya ta alheri ce ta bude mata bayan jarrabawar da ta fuskanta, bai dace mu zama katanga a gare ta ba. Za mu bi ta addu'a kuma abu na zamani na waya kullum zaku dinga waya  Kamar yaune zakiga har an shekara Dayan ta  dawo cikin nasara inshallah haka duk suka saka mama a gaba da magjiya da rarrashi , dole ta sauko ganin ba ta da wani zaɓin da ya wuce ta amince. Ta maida dubanta ga Nuwayrah Shikenan, tunda Abbanku  da yayyanki sun ce haka, Allah Ya tabbatar da alheri. Amma wallahi idan kika je can ko a waya waya naga sauyin tarbiyar a Wajan ki sai kin dawo gida ko kin gama contract din ko biki gama ba .

Rungume Mama Nuwayrah ta yi cikin farin ciki, tana hamdala ga Allah da Ya sa Mama ta amince.rayyan tayi wa text Akan cewa mama ta amince 

Daga ranar, shirye-shirye suka ƙankama gadan-gadan

Rayyan shi ne ya ɗauki alhakin  zaryar kaita Embassy a Abuja domin karɓar visa da gudanar da biometrics, gami da haɗa duk wasu takardu (documentation) da suka dace. Rayyan ya tsaya mata matuƙa , bai huta ba har sai da visa ta fito .taje Bauchi da Zaria dangin abba da mama yi masu sallama duk da yawanci basu nuna Jin dadin su ba ita dai ta fita hakkinsu 

A gefe guda kuwa, Nuwayrah tana ta shiri Akwatina biyu ta ware  gabadaya Kayan tana ne  gida atamfofi ,hijabai,mayafi sai daya Akwatin abaya shoes turaren kabbasa and sauran abubuwan bukata ,rayyan ya kawo mata coats 🧥 din masu kyau dan yasan sanyin London tunda yana zuwa time to time 

Gobe da safe zata daga London Nuwayrah tana zaune a bakin gado sanye da riga da wando na barci,  tana kallon kowane lungu na ɗakin da ta yi shekaru tana rayuwa a ciki. Ganin  keken ɗinkinta da ke  gefe ya sa ta jin wani irin shauƙi.

Mama ta tura ƙofa ta shigo . Ta zauna kusa da Nuwayrah, hannun yartata ta rike ,Mimi Ki tuna 'yar wace ce . Addu'a da karatun Al-Ƙur'ani ki Kara rike su hannu biyu , ki kiyaye mutuncinki da mutuncin iyayenki kar ki bamu kunya Mimi ba ruwanki da koyan al’Adar turawa .

Hawaye suka  shiga wanke fuskar Nuwayrah. "InshaAllah Mama, za ki sameni mai biyayya da kiyaye dokokin Allah a koda yaushe ,ta rungume maman suna kukan rabuwa da juna.

 Tare Yaya Sadiq da Yaya Nabil suka shigo ɗakin. Yaya Sadiq ya zauna kan keke . Mimi, gobe zaki zama International Ambassador. Za mu missing dinki da girkin ki mai dadi  muna alfahari da ke. Duk abinda kike bukata just call me Mimi idan ma Akwai damuwa duk Kankantar ki kirani cewar Nabil,haka suka rashe Ana ta hira ,abba ma yayi joining dinsu daga baya ,sai Wajan 10:30pm nabil yayi masu sallama ya bar gidan .text rayyan ya mata Akan ta shirya dan shi zai kaita train station na rigasa Wanda zasu wuce abuja daga abujan zata hau flight din London na karfe 12 rana .yayyenta sun so kaita abujan rayyan yace su kyaleta ta fara abubuwa da kanta 

A wannan daren, Nuwayrah ta daɗe tana juyi a kan gadonta. 

A hankali barci mai daɗi ya ƙwashe ta, tana jiran wayewar garin da za ta canza rayuwarta har abada.

Want the next chapter?

Create a free ArewaPen account to save progress, unlock paid chapters, follow this author, and keep reading across web and the Android app.