Free chapter · Read without an account
DA JININSA NAKE RAYUWA
Ƙamewa Husna ta yi ta kasa gaba ta kasa baya, har sai Abba ya sake cewa.
“Ki shiga na faɗa miki.”
Juyawa ta yi ciki jiki a sanyaye, Mama na tsaye tana shirin sanya Hijabi tabi bayan Husna taga ta shigo.
“Wallahi Husna sai na saɓa miki, kin fara kaini bango fa.”
Mama ta faɗa ranta duk a ɓace, har cikin ranta ta fara gajiya da halin Husna.
Husna dai ba ta yi magana ba ta shigo, Abba ya biyo bayanta da su Yaya Walid, kallonsu Mama take har Uncle Dee da ya shigo last, Abba ne ya ce.
“Duk ku shiga cikin ɗaki.”
Falon suka nufa gaba ɗayansu har da Husna da ke satar kallon Uncle Dee, duk ya sake ramewa ya zama ɗan firit ne sai kuma wani haske da ya yi, gaba daya suka zauna a ƙasa sai kuma Abba da Mama da suka zauna a sama, Abba ya yi sallama irinta addinin musulunci, sannan ya ce.
“Iliya, ina so ka sa a ranka cewa mu ba mutane ne marasa godiya ba, jinin da ka bayar ka ceto rayuwar 'yarmu Husna, alheri ne babba wanda ba zamu taɓa mantawa da shi ba.
Addininmu ya koyar da mu godewa wanda ya yi mana alheri, kuma mun gode maka sasai. Amma dole mu ware tsakanin halaccin ɗan Adam da kuma dokar Allah (SWT), zan baka hujjoji daga cikin littafinsa mai tsarki, sannan na baka hujoji daga shari'ar mu ta musulunci.”
Abba ya sake gyara zama yana kallon Uncle Dee, ya ce.
“Allah Maɗaukakin Sarki ya faɗa a cikin littafinsa mai tsarki, a cikin Suratul Baqarah aya ta 221.
Kada ku aurar da mata musulmai ga mazaje mushrikai (ko waɗanda ba musulmi ba) har sai sun yi imani. Haƙiƙa bawa mumini ya fi alheri sama da mushriki ko da ya burge ku…
Wannan aya ba shawara ba ce, umarni ne na Allah. Shari'ar Musulunci ta rufe ƙofar auren mace Musulma ga namijin da ba Musulmi ba. Wannan yana nufin ko da mutum shi ne mafi kyawun halaye ko mafi cikar alheri a duniya, muddin babu Musulunci a tsakani, auren ba zai taba yiwuwa ba, idan aka yi shi kuwa, ya zama al'amura na zina a Shari'a.”
Shiru ɗakin ya yi, duk jikinsu ya yi sanyi harda Uncle Dee da ba musulmi ba ai yasan zancen Allah, ya san Al Qur’ani, kuma ya san musulmai basa taɓa ƙetare faɗar Allah, Abba ya sake cewa.
"Haka kuma Allah ya sake jaddadawa a wata ayar ya ce. Idan kuka san su muminai ne, to kada ku mayar da su zuwa ga kafirai. Su (matan) ba halal ba ne gare su, su ma (mazan) ba halal ba ne gare su...' Suratul Mumtahanah aya ta 10.”
Abba ya mayar da kallonsa ga Husna ya ce.
“Husna, kin ji da kunnenki abin da Ubangijin da ya halicce ki ya faɗa? Aure ba tsantsar soyayya ba ne kawai, bautar Allah ne. Ta yaya za ki gina ibada a kan abin da aka rushe tun farko?”
Shiru Husna ta yi, maganar Abba ta soma taɓa ta, amma ai akwai zaɓi ko? Zai iya musulunta me ya sa Abba bai kawo wannan ba? Abba ya maida kallonsa ga Uncle Dee, bayan ya zuba masa idonu ya ce.
"Iliya, a tsarin Musulunci, mijin shi ne shugaban gida kamar yanda Allah ya ce. Ar-Rijalu qawwamuna 'alan-nisa. Addinin Musulunci ya amince namiji Musulmi ya auri macen da take Ahlul Kitab saboda Musulunci ya tilasta masa girmama Annabi Isa (AS) da Littafin Injila.
Amma addininka bai yi imani da Annabi Muhammad (SAW) ba ko Al-Qur'ani. Ta yaya za a danƙa mace Musulma a ƙarƙashin shugabancin namijin da bai yi imani da abin da ta yi imani da shi ba? Wannan zai shafi addininta, da makomar 'ya'yan da za a haifa, sannan ke Husna.”
Abba Ya mai da kallonsa ga Husna da ke kuka ƙasa ƙasa, ya ce.
“A tsarin addininsa akwai abincin da yake halal ne a gare shi, kamar naman alade, giya, ko naman dabban da ba a yanka ta da sunan Allah ba. Idan kuka zauna a gida ɗaya a matsayin mata da miji, a matsayinsa na shugaba a gida kina ƙarƙashin ikonsa, zai iya buƙatar ki dafa masa waɗannan abincin. A Musulunci kuwa, mutumin da ya dafa giya, ya matsa ta, ko ya taimaka wajen sarrafa abin da Allah ya haramta, la'anar Allah da ta Manzonsa tana kansa.
Ta yaya za mu gina rayuwar 'yarmu a gidan da kowace rana za ta iya aikata abin da zai janyo mata la'ana?
Bama wannan kaɗai ba, Idan safiya ta yi, Husna kina buƙatar tashi ki yi Sallah, ki sa hijabi ki fuskanci Alƙibla. Shi kuma mijinki yana shirin tafiya Coci ko gudanar da ibadar da ta saɓa wa kaɗaituwar Allah. Idan 'ya'ya suka taso a wannan gidan, wane ne za su bi? Mahaifinsu da ke tafiya Coci ko mahaifiyarsu da ke gudanar da Sallah? Wannan shi ne babban gurɓataccen yanayin da zai watsa imaninsu baki ɗaya.
Sannan Idan aka samu saɓani na aure wanda ya kai ga saki ko rabuwa, matakin da na san bakya so azo, to dole sai na faɗa miki. A Shari'ar Musulunci kina da haƙƙin Idda, da samun haƙƙin ki ta hanyar Hukuncin Alƙali. Amma muddin mijinki ba Musulmi ba ne, babu Shari'ar Musulunci da za ta haɗa ku ko ta tilasta masa ba ki haƙƙinki. Ba zai amince da hukuncin Alƙalin Musulunci ba, sakamakon haka haƙƙin ki na mace Musulma zai murƙushe kuma ki zama babu kariya.
Idan baku rabu ba har rai ya yi halinsa, a Shari'ar Musulunci, rabon gado dokar Ubangiji ce ta gindayayya. Manzon Allah (SAW) ya faɗa cewa 'Musulmi ba ya gadon kafiri, shi ma kafiri ba ya gadon Musulmi.' Idan ɗaya daga cikinku ya rasu, babu haƙƙin gado a tsakaninku ta fuskar addini.
Husna ba za ki gaje shi ba, shi ma ba zai gaje ki ba, kuma 'ya'yan da kuka haifa za su shiga tsakani na rashin samun gado. To duk a kan me zaki tura rayuwar ki a wannan wahalal? Idan kika yi duba da waɗannan hujjojin, ina sake tabbatar muku cewa auren mace Musulma da namijin da ba Musulmi ba kuskure ne guda ɗaya mai gina jerin saɓa wa dokokin Ubangiji. Saboda haka, wannan al'amari ya ƙare a nan! Babu aure tsakaninku har abada."
Abba ya miƙe tsaye, ya dubi Uncle Dee cikin girmamawa duk da ya rufe fuskarsa bai bar wata kafa ta tausayawa ba, hakan ya sanya masa kwarjini sosai da sosai, ya ce.
"Iliya, muna godiya ta musamman gare ka da halaccin jinin da ka bayar wajen ceto rayuwar Husna, da kuma nuna kulawa da ka yi. Muna maka fatan alheri a rayuwarka. Amma dangantakarmu da kai ta tsaya ne a kan wannan alherin kawai, babu wata alaƙa ta aure da za ta haɗa mu.”
Iliya ya ji duk abin da aka ce, amma shi dai bai gane ko abu ɗaya ba, ji dai ya ji amma fahimta babu abin da ya fahimta, jikinsa ya yi wani irin sanyi, a hankali ya miƙe kamar mai koyan tafiya ya fita.
Bayan Uncle Dee ya fita Abba ya kalli Husna da ke durƙushe tana kuka, muryarsa a kausashe ya ce.
"Husna! Ki saurare ni da kyau! Na rantsa da Allah wanda ya halicci ni ba za ki taɓa auren Iliya ba! Ko da shi kaɗai ne namijin da ya rage a doron ƙasa, wannan auren ba zai yiwu ba!
Daga yau, na haramta miki ambaton sunansa, na haramta miki sake sanya ƙafarki a makarantarsu, kuma babu ke ba sake magana da shi! Idan na samu labarin kina ƙoƙarin nemansa a ɓoye, wallahi kashinki ya bushe! Daga yau kowanne motsinki yana ƙarƙashin idon 'yan uwanki!”
Husna ta rushe da wani irin kuka mai ban tausayi, jikinta ya shiga ɓari saboda tsananin kukan da take, numfashinta ya fara sama sama, sai kuma ya tsaya cak, ta zube ƙasa sumammiya.
Hankali a tashe Mama ta yi kanta tana kiran sunanta, su Yaya Abdul ma suka hau kiran sunanta amma bata numfashi ko kaɗan.
Basu kai ga miƙata asibiti ba, aka gane suma ta yi, bayan an yayyafa mata ruwa ta farfaɗo, kallo ɗaya ta yi musu ta fashe da kuka, tana kuka tana faɗin.
“Wallahi ni sai na aure shi, shi nake so shi zan aura. Da jininsa fa nake rayuwa haba sai ka ce ban san hallaci ba.”
Bazan suka yi da ita suka barta tana ta faman kuka, babu wanda ya ce mata sannu har dare, bacci ma ɓarawo ne ya ɗauketa ranar sabida kukan da take yi bata da niyar kwanciya.
Washe gari da safe wayar Mama da take yi da Mimi ce ta tashi Husna, a ranta ta ce. ‘Ita Mama komai sai ta sanar da Mimi.’ haka kawai take jin ma ta tsani kowa a gidan nasu, ko breakfast a ranar Husna ƙinyi ta yi, tun suna banza da ita har suka fara mata magana, amma ta ce ita ba za ta yi ba.
Sai da Abba ya zaunar da ita ya yi mata nasiha mai ratsa jiki fiye da wadda ya yi mata jiya, sannan ya sanar da ita babu ita babu auren Uncle Dee ko da kowa ya musulunta, sabida idan har ya musulunta sabida yana so ya aureta, to musuluncinsa yana gareta ne kawai ba shi da wani lada wajen Allah, sabida ba dan Allah Ya musulunta ba, bare kuma shi da har a wannan matakin ma bai yi zancen musulunta ba, hakan ya nuna cewar yana nan a kan bakansa na addininsa.
Tun da Abba ya sa ƙafa ya fita Husna take ta rusa kuka, tun Mama tana banza da ita har ta yi mata magana.
“Ke wai wace irin banzar yarinya ce da ba ta san ciwon kanta ba, Husna?!"
*Cigaban labari*
Kukan ta ci gaba da yi, maganar Alhaji na dawo cikin kunnenta, mussaman da ya ce zai roƙi Allah Ya ɗauki ransa kafin lokacin da zata auri Uncle Dee, cikin kuka take faɗin.
“Wai ni shikenan dole sai na haƙura da wanda nake so? Da wane ido zan kalli rayuwa idan babu wanda nake so? Wallahi ba zan taɓa son wani ba sai Uncle Dee.”
Haka ta yi ta surutai cikin kukan nata, har aka yi magariba aka yi isha tana kwance, Mama ce ta shigo ɗakin daga bakin ƙofa ta ce.
“Husna ba zaki tashi ki yi sallah ba? Ko kin bi addinin nasa ne?”
Wata nannauyar ajiyar zuciya ta sauke, kanta ne yake wanin irin sarawa kamar da gatari ake sara mata ƙwaƙwalwa, a hankali ta miƙe tsaye tana dafa bango ta fito ta nufi toilet, tsaki Mama taja a fili ta ce.
“Kina zaune a kan soyayya zaki halaka rayuwarki, wai Husna ma nawa take da har za ta yi wannan nisan a kan soyayya?”
Tsaki ta sake ja ta koma ɗaki ta ci gaba da lazimin da take yi, Husna kam ko a cikin banɗaki ta kwashe kusan mintuna 20 sannan ta kammala alwalar ta fito, adaddafe ta yi sallar magariba da isha’a tana idarwa ta kwanta a kan kafet ɗin, lokacin Mama ta shiga haɗawa Abba abinci sabida ya kusa shigowa, kuma indai ta tashi yanzu zata ɗauki kusan minti 30 kafin ta gama tun da har sai ya ci abincin zata dawo falon.
Wayarta da ke kan kujera Husna ta ɗauka, tana fargaba take rubuta lambar wayar Uncle Dee da ta haddace ta a kan ta, tashi ta yi ta shige ɗakinta tana shiga ta danna kira, sai dai har wayar ta tsinke ba a ɗauka ba, ƙara danna kiran ta yi shima har ya ƙare ba a ɗauka ba, tana shirin danna na ukun sai ta ji ƙarar shigowa saƙo, da sauri ta shiga wajen saƙon taga daga lambarsa aka turo.
“Ki yi haƙuri Husna, kalaman Abba sun shiga zuciyata fiye da yadda kike tunani, ina tunanin wannan soyayyar kawai mu barta hakan nan.”
Legendspen
***