Free chapter · Read without an account

Fuska biyu angel and Boss

by Miss Nasir · Fuska Biyu: Angel & Boss

CHAPTER 10️⃣

ZAYYAD

Doctor Seef ya gama maganar sa, Zayyad kuwa ya dade zaune shiru kamar wanda aka zuba wa ruwa.

“Aure?” ya maimaita kalmar a hankali.

Doctor Seef ya gyara zaman glasses dinsa yana kallon shi.

“Eh Zayyad. Aure. Saboda idan kana cikin wani hali da baka taba samun kanka a ciki ba, kuma abin yana damunka har ya shafi tunaninka, kana bukatar ka tsaya ka fahimci kanka.”

Zayyad ya sauke kansa.

“Doctor, ban san me yake faruwa da ni ba.”

“Ka san mace daya ce take jefa ka cikin wannan yanayin?”

Shiru.

“Sabreen ce ko?”

A take Zayyad ya dago kansa ya kalli Doctor Seef.

“Yaya ka san?”

Murmushi Doctor Seef yayi.

“Face din ka ya fada min kafin bakinka.”

Zayyad ya kauda kai yana shafa goshinsa.

“Angel…”

Kalmar ta fito daga bakinsa cikin rauni.

Doctor Seef ya kalle shi sosai.

“Then marry your Angel.”

Zayyad ya mike tsaye.

“Amma ba abu ne mai sauki ba.”

“Me yasa?”

“Saboda ita kanta ba ta sauki.”

Doctor Seef yayi dariya.

“Ka samu wacce take maka challenge kenan.”

Zayyad bai yi dariya ba.

“Ba ka gane ba. Sabreen tana boye min abubuwa. Kuma ni ma akwai abubuwan da ban fada mata ba.”

Doctor Seef ya gyara zama.

“Then kafin aure, ka gano gaskiyar abubuwan da kuke boyewa juna.”

Zayyad ya tsaya shiru.

A zuciyarsa sai wata tambaya ta fara yawo.

Shin Sabreen tana son shi kuwa?

Ko kuwa duk abinda yake ji nasa kadai ne?

---

SABREEN

Washegari da safe.

Sabreen ta bude idanu a hankali.

Jikinta har yanzu babu kwari. Ta zauna a kan bed tana kallon wajen da Zayyad ya tsaya daren jiya.

Hawayen da ta rantse ba za ta sake bari su fito ba suka cika mata ido.

“Me yasa ka yi min haka Zayyad?”

Ta furta cikin rauni.

Sai ta tuna kallon da yayi mata kafin ya fita.

Ta rufe fuskarta da hannaye.

“Ya Allah… ka taimake ni.”

Kafin ta gama addu’ar sai aka kwankwasa kofar.

“Boss?”

Muryar Zara ce.

Sabreen ta share hawaye da sauri.

“Shigo.”

Zara ta shiga, amma da zarar ta kalli Sabreen sai ta tsaya.

“Boss… lafiya?”

“I'm fine.”

“Boss, kina da tabbacin?”

Sabreen ta mike.

“Zara na ce miki I'm fine.”

Zara ta yi shiru.

Ta san lokacin da Boss dinta take son a bar ta ita kadai.

“Breakfast yana downstairs.”

“Okay.”

Zara ta juya zata fita sai Sabreen ta kira ta.

“Zara.”

“Yes Boss?”

“Zayyad… ya dawo?”

Zara ta tsaya.

“Ban sani ba Boss.”

Sabreen ta sunkuyar da kanta.

“Okay. Go.”

Zara ta fita tana girgiza kai.

A zuciyarta tace:

“Wannan labarin Boss da Zayyad fa sai ya bani mamaki.”

---

JULIUS BERGER

Zayyad yana zaune a office dinsa, amma yau babu aikin da yake shiga kansa.

File din dake gabansa ya bude.

Ya kalle shi.

Ya rufe.

Ya sake bude shi.

Har ya gaji.

Sai wayarsa ta yi ringing.

BASH CALLING…

Ya daga.

“Hello.”

“Boss ina kake?”

“Office.”

“Na samu wani information.”

Zayyad ya mike tsaye.

“Me ka samu?”

“Bara’u ya fara magana.”

Idon Zayyad ya sauya.

“Continue.”

“Ya ce mutanen da suka yi Black Market a Abuja ba su kadai ba ne. Akwai wasu manyan mutane a ciki.”

“Names?”

“Bai gama bani komai ba. Amma ya ambaci suna daya.”

“Waye?”

Shiru Bash yayi na wasu seconds.

“Alhaji Musty.”

Zayyad ya dafe desk.

“Musty?”

“Yes Boss.”

“Amma Musty ya mutu.”

“I know.”

Zayyad ya mike.

“Then how did Bara’u connect him to them?”

“Bara’u ya ce Musty ya san wani secret daga shekaru da suka wuce.”

“Wanne secret?”

“Game da Sheikh Muhammad Kabir.”

Zayyad ya daskare.

Numfashinsa ya tsaya na dan lokaci.

“Bash…”

“Yes Boss?”

“Ka dawo office dina yanzu.”

“Okay Boss.”

Call din ya yanke.

Zayyad ya zauna a hankali.

Sheikh Muhammad Kabir.

Sunan mahaifin Sabreen.

A hankali ya lumshe idanu.

“Angel… me kike boyewa?”

---

ABUJA

A wani wuri da ba kowa ya sani ba, wata mata zaune take tana kallon hoton wani mutum a wayarta.

Hannunta na rawa.

Ta bude wani old file.

A jikin file din an rubuta:

SHEIKH MUHAMMAD KABIR — 17 YEARS AGO.

Ta bude file din.

Hotuna ne.

Takardu ne.

Kuma wani tsohon newspaper.

Ta karanta abin da ke ciki.

Sai hawayenta suka fara zuba.

“Sun fara komawa daya bayan daya…”

Ta furta.

“Musty ya mutu.”

Ta dago kanta.

“Governor ya mutu.”

Sai ta kalli wata takarda.

“Idan suka gano wanda ya fara komai…”

Ta kasa karasa maganar.

A lokacin wayarta ta yi ringing.

UNKNOWN NUMBER.

Ta daga da tsoro.

“Hello?”

Muryar namiji ta fito daga dayan bangaren.

“Kin ga abinda ya faru da Musty?”

Ta yi shiru.

“Eh.”

“Then ki san cewa lokacin ki ya kusa.”

Ta fara rawa.

“Waye kai?”

Dariya aka yi.

“Mutumin da ya san gaskiyar abin da ya faru shekaru goma sha bakwai da suka wuce.”

Call din ya yanke.

Ta zube a kujera.

“Ya Allah…”

---

SABREEN

Sabreen ta sauko downstairs.

Zara tana parlour.

Da zarar ta gan ta sai ta mike.

“Boss.”

“Hmm?”

“Meeting din yau 12:00.”

“Okay.”

Sabreen ta dauki handbag dinta.

“Zara.”

“Yes?”

“Ki shirya min files din governor.”

Zara ta tsaya.

“Governor Muhammad Kabir?”

Sabreen ta kalleta.

“Yes.”

“Boss… why?”

Sabreen tayi murmushi mara dadi.

“Because akwai wani abu da ban gama ba.”

Ta juya zata fita.

Amma a lokacin kofar gida ta bude.

Wani mutum ya shigo.

Sabreen ta tsaya cak.

Zara ma ta daskare.

Mutumin ya cire glasses dinsa.

Ya kalli Sabreen.

“Ke ce Sabreen?”

Sabreen ta kalle shi sosai.

“Who are you?”

Ya yi murmushi.

“Ni ne mutumin da ya san wanda ya kashe mahaifinki.”

Zuciyar Sabreen ta buga da karfi.

Zara ta rike bakinta.

Sabreen ta matso kusa da shi.

“Repeat what you just said.”

Murmushin mutumin ya kara bayyana.

“Na ce…”

Ya kalli gefen kofar.

“Na san wanda ya kashe Sheikh Muhammad Kabir.”

Sabreen ta dafe kirjinta.

“Where is he?”

“Ba wai kawai zan gaya miki ba…”

Ya tsaya.

“Zan gaya miki me yasa aka kashe shi.”

Sabreen ta kafe shi da idanu.

A wannan lokacin wayarta ta yi ringing.

Ta duba screen.

ZAYYAD CALLING…

Ta daga.

“Hello?”

Muryar Zayyad ta fito cikin tsauri.

“Angel, ina kike?”

Sabreen ta kalli mutumin.

“I'm home.”

“Kar ki fita daga gidan.”

Sabreen ta daure fuska.

“Why?”

“Saboda na gano wani abu.”

“Me ka gano?”

Zayyad ya yi shiru na seconds.

Sannan yace:

“Game da mahaifinki.”

Sabreen ta daskare.

Mutumin da ke gabanta kuma ya yi murmushi.

To be continued…

MISS NASIR ❤️✍️

Want the next chapter?

ui.create_a_free_arewapen_account_to_save_progress_unlock_paid_chapters_fol