Free chapter · Read without an account

Chapter 18

by Umma mustapha · WA ZAI FUSKANCE NI??

WA ZAI FUSKANCE NI??

BOOK 1

Umma Mustapha

Wattpad: Umma Mustapha

PAGE 18

Hanyar Hadeja...

Dare ya riga ya yi, titin da suke bi kuma ya yi shiru fiye da yadda Fatima ta saba gani. Fitilun motar ne kawai suke haska ɗan ɓangaren hanyar da suke bi, yayin da duhun dare ya lullube sauran wuraren.

Irfan yana tuƙi ba tare da ya rage gudun motar ba. Hannuwansa sun yi ƙarfi a kan sitiyarin, idanunsa a kan hanya, amma duk da haka hankalinsa bai cika kan tuƙin ba.

A duk lokacin da ya ji motsin Nihla daga kujerar baya, sai ya ɗan ɗaga idanunsa zuwa madubin motar.

Nihla tana kwance a kan cinyar Fatima, idanunta a rufe. Zazzabin da ya kama ta yana ƙara tsananta.

Fatima kuwa sai sannu take mata. Ta ɗora hannunta a goshin Nihla.

"Subhanallahi... Nihla, haka jikin naki ya ƙara zafi."

Nihla ta buɗe idanunta a hankali.

"Fatima..."

"Na'am?"

"Ina jin sanyi."

Nan take Fatima ta ƙara gyara mata mayafinta.

"Ki yi haƙuri, mun kusa isa. Ki ɗan daure."

Irfan da ya ji maganar sai zuciyarsa ta ƙara cunkushewa. Ya yi shiru na wasu daƙiƙu, sannan ya tambaya ba tare da ya juya ba:

"Har yanzu tana jin sanyi?"

Fatima ta ɗago kai ta kalle shi.

"Eh. Zazzabin ma yana ƙaruwa."

Irfan ya matse sitiyarin sosai.

"Jabir..."

"Na'am?"

"Ka kashe A/C ɗin nan gaba ɗaya. Sannan ka duba ko akwai wani pharmacy a gaba. Mu tsaya mu siya mata maganin zazzabi kafin mu ƙarasa."

Jabir ya kalli Irfan na ɗan lokaci, sannan ya ce:

"To, zan duba."

Ya kashe A/C ɗin.

Amma kafin su kai ga wani pharmacy, Nihla ta sake buɗe idanunta.

Fatima kuwa, a cikin zuciyarta, mamakin Irfan take yi. Irin kulawa da damuwar da yake nunawa a kan Nihla sun fara ɗaukar hankalinta.

"Me hakan ke nufi?"

Ta kalli Irfan na ɗan lokaci, sannan ta mayar da kallonta kan Nihla.

Nihla kuwa ta sake lumshe idanunta. Motsawa ta yi kaɗan, tana ƙoƙarin gyara kwanciyarta.

Irfan ya ɗan ɗaga idanunsa zuwa madubin motar, yana son ya tabbatar da halin da Nihla take ciki. Amma saboda duhun da ke cikin motar, bai iya ganin fuskarta sosai ba. Sai dai ya iya gane cewa tana kwance cikin rashin kuzari.

Ya sauke idanunsa daga madubin, ya ci gaba da kallon hanya, zuciyarsa cike da fargaba.

A gefe guda kuma, Fatima ta ci gaba da nazarin Irfan. Ta fara lura da wasu abubuwa da ba za ta iya bayyana su da kalmomi ba.

Ta kalli Irfan.

Sai ta kalli Jabir.

Jabir ya lura da irin kallon da take musu, amma bai ce komai ba.

Ba su samu pharmacy ba har suka shiga cikin garin Hadeja.

Da misalin ƙarfe tara na dare suka isa cikin garin. Gaban wani private hospital mai kyau suka tsaya.

Irfan ya faka motar.

Suka fito.

Fatima ta buɗe ƙofar baya domin ta taimaka wa Nihla ta fito. Amma kafin ta samu damar riƙe ta sosai, sai jiri ya ɗauki Nihla.

Ta yi ƙoƙarin kamo ta.

"NIHLA!"

Amma ƙarfinta bai isa ba.

Nihla ta sulale, ita da Fatima suka faɗi a wajen.

"Ya Allah!"

Jabir da Irfan suka juya da sauri.

Irfan ya ruga zuwa gare su. Da ya ga Nihla ba ta motsi, bai tsaya tunani ba.

Ya sunkuya, ya ɗaga ta cikin hannuwansa, sannan ya miƙe da ita.

"Ku buɗe hanya!"

Muryarsa cike take da tashin hankali.

Ya shiga cikin asibitin da Nihla a hannunsa, yayin da Jabir da Fatima suka mara masa baya.

Fatima tana binsa da sauri, zuciyarta na bugawa da ƙarfi.

Ita kuwa Nihla, ko da yake ba ta cikin hayyacinta sosai, jikinta ya kasa yin wani motsi.

A rayuwarta, babu wani namiji da ba ɗan uwanta ba da ya taɓa kusantar jikinta ba. Koda rike hannunta wani namiji da ba shi da alaƙa da ita bai taɓa rikewaba.

Amma yau...

Ga shi wani mutum ya ɗauke ta gaba ɗaya a hannunsa, yana neman ceto mata rayuwa ba tare da ya damu da komai ba.

Wani sabon yanayi ne da Nihla ba ta taɓa fuskanta ba.

Kuma ba ta san cewa wannan daren ne farkon wani sabon babi a rayuwarta ba.

Umsar ✍️ 
***

Want the next chapter?

ui.create_a_free_arewapen_account_to_save_progress_unlock_paid_chapters_fol