Free chapter · Read without an account

THE NEW CASE✍️

by Meelah Bazata · JA DA BAYA...

JA DA BAYA...
Book 1
Page 39✍️

***

Zaune take adan matsakaincin gidan nata.aikin gida take kamar yadda ta Saba,tsohon cikine ajikinta,ga Kuma yaronta Wanda bazai wuce shekara hudu ba agefe Yana ta wasansa.

Sauri take ta gama aikin domin taje asibiti, kasantuwar yanzu garin ya waye.

Bayan ta gama aikin nata, ta kama yaronta ta yi masa wanka,bayan tagama ta bashi abinci ya ci ta kaishi wajen sirikar ta, tare da mata sallama ta tafi asibitin.

Ta samu layi sosai ba laifi. Bayan ta fito da katin ta zauna ta jira har layi ya zo kanta.
Tana shiga, likita yayi mata wasu tambayoyi game da yadda take ji a jikinta. Bayani tayi masa akan duk yadda takejin jikinta.

Bayan ya gama wasu 'yan rubuce-rubuce, ya dago ya kalle ta.
"Yanzu kina samun ciwon ciki akai-akai ne?"
Ta jinjina kai tare da fadin.
"Eh Doctor. Wani lokacin nakan ji shi sosai, wani lokacin kuma sai ya lafa."
Likitan ya sake kallon bayanan da ya rubuta.
" akwai wasu abubuwa da nake so ki kula da su. Ki rage wahalar aiki, sannan ki samu isasshen hutu,sannan kidena cin abu Mai gishiri,haka karki ci zaki"
Ta sauke numfashi.
"To Doctor, inshallah zan kiyaye"
"Kin taba samun irin wannan yanayin a baya,kokuma wannan cikin shine kika fara fuskantar haka.?"
"A'a, wannan karon ne."
Ya jinjina kai.
"To zan rubuta miki wasu magunguna. Amma kafin nan akwai wasu gwaje-gwaje da za mu yi domin tabbatar da komai yana tafiya yadda ya kamata,sannan Kuma da kinji Wani yanayi Wanda Ba ki saba ji ba,to kiyi gaggawar zuwa asibiti."
Ta kalle shi da ɗan fargaba.
"Gwaje-gwaje Kuma doctor?"
"Eh Kada ki ji tsoro. Abu ne na yau da kullum,zamuyi hakan ne Dan tabbatar da lafiyarki da Kuma babynki"
Ta jinjina kai tana Sasuke numfashi 
"To."
Likitan ya rubuta wasu bayanai a takarda ya mika mata.
"Ki je dakin gwaje-gwaje da wannan. Bayan an gama za ki dawo da sakamakon."
Ta karɓa tare da mikewa tana fadin,
"Nagode Doctor."
"Allah ya baki lafiya."
"Ameen."
Ta mike ta fita daga ɗakin.
Tana fita, ta tsaya a bakin corridor ɗin tana kallon takardar da aka bata.
A hankali ta furta,
"Allah yasa komai lafiya,yasa Muji alkhairi"
Sannan ta nufi wajen gwaje-gwajen.
Bata dauki  wani lokaci a wurin ba ta dawo tana riƙe da sakamakon.
Ta sake komawa wajen likitan.
Bayan ya karɓi takardar ya karanta a hankali,ya yadau Wani Dan lokaci 
Shiru sannan ya sauke numfashi ya dago ya kalle ta.
"Doctor, lafiya?"
Ya ɗago kai ya kalleta.
"Ki kwantar da hankalinki Ba wani abun da zai sa ki damu bane,sedai kamar yadda na fada Miki sekin kula sosai,sannan situation dinki baya bukatar dogon na kuda, Sannan ki kiyaye ka'idojin komai zai tafi normal."
Ta sauke numfashi.
"Alhamdulillah."
Likitan ya sake kallon takardar.
Sannan Ki rika zuwa duba lafiya a lokacin da aka tsara miki."
Ta jinjina kai tace
"Inshallah."tare da mike wa tana so likitan ya duba ta sabida Yana da kirki sannan Yana mutunta ta sosai.
Ta tashi ta fita daga asibitin, farfajiyar asibitin ta saya abinda takeso sannan ta samu mota ta hau ta tafi gida.

Komawarta gida ta tarar da ɗan yaron nata Wanda bazai wuce shekara hudu zuwa da rabi ba,yana wasansa kusa da kakar tasa Wanda ta shimfida tabarma tana Shan hantsi.

yana hango ta kuwa,da gudu ya nufe ta 
"Yana fadin Mama,oyoyo!"
sunkuya wa tayi  rungume shi,tana fadin na dawo hibban,babah hutawa ake ne tacewa sirikar tata wacce take mata sannu da dawowa  da Kuma tambayar ya jikanta?
Amsawa tayi da alhmdlh tare da daukar hibban ta shiga daki.

Wata irin damuwa takeji a zuciyarta wanda
Ba ta san dalilin da ya sa ba.

"A zuciyarta take fadin Allah ya sa ko ma menene yazo min da sauki."

Ta shiga ɗakin tare da Hibban a hannunta. Kwantar da shi tayi saman gadon, yayin da shi kuma ya fara wasa da matashin kai.
Ita kuma ta zauna gefen gadon tana kallonsa. Duk da murmushin da yake yi, zuciyarta bata samu sukuni ba,haka kawai takejin kamar akwai abinda zai sameshi
Ta buɗe jakarta ta ciro takardar da aka bata a asibiti. Kallon ta tayi na ɗan lokaci, sannan ta sake mayar da ita cikin jakar.
"Hibban, ka ga abinda mama ta kawo maka?"
Da sauri ya dago kansa yace,
"Mama, me?"
Murmushi tayi ta ɗauko wani abu daga cikin ledar da ta siya a hanya tace,
"Zo ka gani."
Da gudu ya taso ya nufe ta.
"Na'am mama!"
Ta buɗe ledar ta bashi abin da ta saya. Da farin ciki ya karɓa.
"Nagode mama."
Ta shafa kansa cikin Jin dadi sabida ta Riga ta koyar da yaron duk abinda akayi masa yayi godiya komai kankantar sa.
"Allah ya raya min kai."
Hibban ya koma gefen gadon yana wasa da abin da ta bashi.
Ita kuma ta kwanta tana kallon silin.
Abin da likitan ya fada ne yake sake dawo mata a rai.
"Ki kula da kanki sosai."
Ta lumshe idanu,Amma akan wa Nan cikin na jikinta tanajin fargaba sosai,haka kawai se taji kamar bazata haifi cikin ba,gaba daya tunda cikin yayi girma take cikin fargaba,numfashi ta sauke Mai karfi tare da fadin.
"Allah ya sa komai ya tafi lafiya."
wayarta dataji ta fara ringing.
Hannunta ta kai cikin jakarta ta ɗauko wayar tare da duba screen din wayar.

Mijinta ne yake kiranta,hakan yasa ta daga wayar tare da fadin,
"Hello."
Muryarsa ce ta fito daga ɗayan ɓangaren Yana fadin.
"Kin je asibitin?"
"Eh."shine abinda ta amsa a gajarce.
"Yaya jikin naki?"
Ta yi shiru na ɗan lokaci kafin ta amsa.
"Alhamdulillah. Likita yace in kula da kaina kawai,Amma ni inajin kamar akwai matsala."
"To ki kula sosai. Bana son ki wahalar da kanki da aikin gida,sannan da kinji Wani yanayi Wanda Baki Saba ba kije asibiti."
Murmushi tayi sannan tace.
"To."
"Ya babah da hibban,banji duriyar sa ba yau?"
"Gashinan, yana wasa,komai lafiya."
"To shikenan. Zan kira ku daga baya."
"To, Allah ya kiyaye,adawo lafiya."
"Ameen."
Kiran ya yanke.
Ta ajiye wayar a gefenta.
Hibban ya dago ya kalle ta yace.
"Mama, babana ne?"
"Eh,babanka ne,Amma ai kana kanaji bakayi masa magana ba."
"Yaushe zai dawo?"
Ta yi murmushi tace.
"Da wuri inshallah."
"To."
Ya koma ya cigaba dawasansa.
Ita kuma ta sake lumshe idanu.
Amma wannan karon, tunanin nata bai tsaya kan cikin da ke jikinta ba.
Wata magana ce kawai ta tsaya mata a rai.
"Allah ya sa komai ya tafi lafiya."
Domin ita kanta bata san dalilin da ya sa take jin wani irin fargaba ba.

********************

Abbie ne zaune acikin office dinsa Yana duba wasu files sabida Wani case da yake kokarin settling.

Waya ya dauka yayi waya Wanda yadau lokaci suna tattaunawa akan maganar kafin ya aje wayar ya cigaba da dube duben takardun.

Mikewa yayi ya tafi zuwa chamber din domin akwai Wanda yake bukatar gani acikin lauyoyin.

A harabar kotun Bai karasa inda yakeson zuwa ba ya hango wata yarinya ta hada Kai da gwiwa se kuka take.

Tsayawa yayi Yana kallon yarinyar cike da mamaki.
Me akai mata take kuka anan? Me ya kawota kotu ma?"shine tambayar dayake yiwa kansa.

Karasawa yayi kusa da ita yace"yarinya me yafaru?"da sauri ta dago kanta tana kallonsa ganinsa sanye da kayan lauyoyi yasa ta sake rushewar da kuka tace"baba Dan Allah kataimaka mana" ta Fadi hakan tana taga hannen ta sama alamar roko.

Abbie kuwa kallon ta yake Yana ganin kankantar ta kamar diyarsa.
Bude Baki yayi cikin sigar rarrashi yace"Dena kuka yarinyata Maza Yi shiru ki gayamin me ya faru?

Aikuwa take yarinyar ta goge hawayen ta da hijab din nata Wanda daga gani kasan ya kwana biyu.

“Ke yarinya, lafiya?”meyake damunki kikazo Nan kina kuka? Abbie ya tambaya yarinyar cikin tausayawa.
Yarinyar ta share hawayenta kafin ta Bude Baki tace.
“baba... ina neman lauya ne Wanda zai tsayawa mahaifina.”ta fada tana share hawayen dayake Kara zubo mata
Abbie ya kalli file ɗin dake hannunta yadda duk suka jike da ruwan hawaye sannan yace cikin mamaki,
“kare mahaifinki Kuma?to me ya faru da mahaifin naki?”
Ta kasa magana seda ta Kara kuka  na ɗan lokaci sannan tace.

“An kama mahaifina... Ba tare ta ya aikata komai ba Amma kuma an yi masa sharri,akan yayi kisan Kai,Kuma wlh Bai aikataba,babana baisan komai ba kawai anyi amfani dashi ne,yanzu nasan kasheshi zasuyi.”

Abbie ya ɗan daure fuska tare da kallon yarinyar aranshi Yana tinanin Anya kuwa tana da cikakkiyar lafiya ma?Amma haka ya daure ya Bude Baki yace,
“Wane irin sharri kuma?”
Yarinyar ta ɗaga file ɗin hannunta ta Mikawa Abbie tace.
“Ana zargin shi da laifin da bai aikata ba. Kowa ya ƙi saurarona. Na zo neman lauya tun safe, amma babu wanda yake son ɗaukar case ɗin,baba Dan Allah kataimakeni kamar yadda Allah yataimakeka ka wanke mahaifiyana shine bangonmu bayanshi bamu da Wani sauran gata arayuwa.” yarinyar ta karasa maganar tana rushewa da kuka sosai.
Abbie ya zauna a kujerar da ke kusa da ita Yana nazarin ta sosai kafin ya Kara kefa mata wata tamabayar.
“Ina mahaifiyarki?”
“Ba zata iya zuwa ba,sabida bata da lafiya tana gida tana jinya,aikin da baba yakeyi dashi muke mata magani muke cin abinci.”

Abbie ya kalli file ɗin yace.
“An kawo case ɗin kotu ne?”
Tace“Eh.”
Tamabayar ta yayi akan“An riga an fara shari'ar?”
Yarinyar ta girgiza kai sannan tace.
“An fara sauraron karar... Shi Kuma baba Yana gurinsu atsare sun Hana kowa ganinshi sun Hana kowa yayi magana dashi ,sunce wai ya kashe wata yarinya.

"Menene sunanki " shine abinda Abbie ya tambayi yarinyar ganin zallar kuruciya agun yarinyar.

Maryam "ta bashi amsa tana Kara goge idanunta.

Hannu ya Mika mata ya ce,
“Bani file ɗin.”
Yarinyar ta  Mika masa da sauri.
Abbie ya buɗe file ɗin ya fara karanta duk bayanan da suke ciki,ya dau dogon lokaci Yana nazarin abunda yake cikin file din ,haryazo Wani guri da ya Tsaya yayi Jim Yana Kara dubawa dakyau, numfashi ya sauke Yana Kara kallon yarinyar wacce itama kallonsa takeyi tun bayan fara nazarin file din hannunta.

Ita maYarinyar ta kalleshi cikin fargaba,duk azatonta zaice bazai taimake ta ba kamar sauran hakan yasa tace,
“Sir... Kaima bazaka Tsaya mana ba ko?”
Abbie bai ɗago kai ba Yana cigaba da duba file din kafin yace.
“Wannan statement ɗin na waye?”
Ta ce,
“Na wanda ya kai ƙarar mahaifina se Kuma na yan sanda.”
Abbie ya sake kallon takardar.
Sai ya rufe file ɗin a hankali.
“Kin ce mahaifinki bai aikata wannan laifin ba? Ta ya kike da hujjar cewa Bai aikataba?

“Wallahi bai aikata ba baba,baba na Yana da tausayi ko dabba baya iya kashewa bare Kuma mutun aranar da abin zaifaru kamar bazai fita ba,se ya samu Wani Sako daga gurin aikinsa ana nemansa ,shine yacemin bari yaje ya dawo bazai Dade ba in Sha Allah,to shikenan tunda ya tafi Bai dawo ba,sun kamashi yan sanda since yayi kisan kai.”

Abbie ya kalleta sosai ganin yanayin ta da alama tana da surutu yace,
“To me yasa kika zo neman lauya ke kadai ba? Baku da yan uwa manya Wanda zasu zo ke ke karamar yarinya?”
Hawayene suka sake cika idanunta tace.
“ ni banida kowa daga baba se mama suka ragemin a duniya.
Yaya ga da Kani na duk sun rasu mota ce ta takesu da gangan Wani Dan me kudi yabi ta kansu da mota,Amma se akace karyane karshe Babu Wanda yabi ta kan maganar.
Tundaga Nan mama tafara rashin lafiya sosai komai bata iyawa.
Yanzu Kuma ga abinda ya faru da baba,bansan me yasa abubuwa marasa kyau suke faruwa da rayuwata ba kodai baba da gaske ne bani da kyakykyawar sa'a... Bata bari ya bata amsa ba tacigaba" idan ba wanda ya tsaya masa ba... za a ɗauke shi a matsayin mai laifi alhali ba shi ba.”
Abbie ya yi shiru Yana ta kallon yarinyar da tausayawa.
Ya ɗaga kansa ya kalli hanyar courtroom sannan ya sake kallon yarinyar yace.

“Menene sunan mahaifinki?”
*Sunanshi malam Musa".
“Za ka tsaya mana?zaka wanke baba na daga sharrin da akayi masa?”shine tambayar da yarinyar ta jefawa Abbie.
Abbie ya rufe file ɗin,tare da mikewa yace,
“Zan fara bincika komai tukuna. Idan gaskiya tana gefen mahaifinki, ba zan bar ta ta nutse saboda babu wanda yake son tsayawa akan ta ba,Amma idan mahaifinki bashi da gaskiya bazan iya tsaya masa ba.”shine abinda Abbie yace, sannan ya Kalli agogon hannunsa yace,
“Zo mu je.”
Yarinyar ta miƙe da sauri tana share hawayenta tare da bin bayansa.

"Wani irin aiki mahaifinki yakeyi?"shine tambayar da Abbie ya jefowa yarinyar.

"Yana aikin gadi ne agidan ALHAJI MAMMAN GWARZO,Kuma a gidanne abun ya faru.

"ALHAJI MAMMAN GWARZO?????" Shine abinda Abbie ya sake maimaita WA cikin mamaki tare da Jan birki ya Tsaya.

(To jama'a ko Wani irin case ne Kuma yazo gurin Abbie 🤔zaiman amsa case din ko kuwa🤔ya batun alakar alhaji mamman gwarzo da Kuma estate na Mai rabo?shin kunsan ma Wani irin rikitaccen case ne Kuma wannan karon yazo ga Abbie 😳🤔 muje zuwa dai jama'a yanzu ne komai zai fara bayyana💥🔥)

Se kunamin uzuri kwana biyu sabida inayin short update,afwan Ina lallabawane sabida wasu uzuri👌🙏

Want the next chapter?

Create a free ArewaPen account to save progress, unlock paid chapters, follow this author, and keep reading across web and the Android app.