Free chapter · Read without an account
THE REVENGE PLAN
*JA DA BAYA...*
*Book 1*
*Page 42* ✍️
***
Haka dai Abbie yakai muhibba asibiti aka dubata, Wanda take gado aka bata sabida ta Sha matukar azaba musammam da ake gyara mata hannun Wanda ta tabbata dai ta karye kas.
Hannun nata kuwa cikin lokaci kadan ya kumbura suntum.
Aikuwa ranar aunty amarya kamar zata hadiye harshen ta Dan jaraba, haka ta dinga fada ta inda ta shiga batanan take fita ba.
Irin alwashin da ta ci akan inarah Allah kadai yasanshi.
Domin tasha alwashin sai tayi Dana sanin zuwan ta cikin family dinnan.
Maganar Ayzaan da abinda ya aikata bai wuce mintuna kaɗan ba, amma tuni labarin ya fara yawo cikin gidan kamar wutar da aka kunna a busasshiyar ciyawa.
Ba a ɗauki lokaci mai tsawo ba labarin ya isa kunnen Uncle Aliyu.
Shikuma dama bamai hayaniya bane Sam hakan yasa baice komai yace akwai abinda ta aikata ne yasa yayi mata hukuncin Kuma baisan zata ji ciwo ba ai" bayan haka kuwa bai sake cewa komai ba.
Uncle Ali ba yanan lokacin da abin ya faru, Wanda se da aunty amarya ta fara dawowa hayyacin ta bayan abinda ya faru yasa ta kira wayar uncle Ali din ta gaya masa bayan ta gama zage zage, a ranar har Abbie bata bari ba.
Ita dama tun can akwai kiyayya tsakanin ta da Ammie da Kuma Abbie gaba daya, ita fa Sam bata sonsu ko miskala zarratin.
Kasantuwar daddy umar da Kuma Abbie sun taso sa'annin juna Kuma daddy Umar dama Yana adawa da Abbie.
Haka Kuma ko da sukayi aure aunty amarya tana matukar adawa da Ammie ganin ta dara ta akomai.
Kiran da aunty amarya tayi masa ya dau wayar tare da karawa a kunnensa, Wanda ko gaisuwa Aunty amarya bata bari sunyi ba ta fara jero masa bayani.
Amma baice komai ba yace Allah ya kyauta gaba, hakan kuwa ya Kara yiwa aunty amarya ciwo kamar hauka.
Daddy Umar kuwa dama Yana cikin dakinsa sedai kasantuwar Yana bedroom a lokacin baisan abinda ma yake faruwa ba.
Karamin yaronsa Mai kimanin shekara goma Sha biyu ne yashiga falon mahaifinsa da gudu cikin tsoron abinda ya gani, da Kuma abinda yaji ana fada.
Aikuwa cikin hakika ya karasa gurin mahaifin nasa yace,
“Daddy” ya fa hakan Yana haki alamar tayi gudu.
Dady Umar ya ɗaga kai ya kalle shi Yana fadin.
“Me ya faru kake wanna. Gudun? Bana hanaka gudu ba ko?”
“Daddy... Yaya Ayzaan ne.”
Take fuskar daddy Umar ta sauya cikin halinsa na hargagi yace.
“Me yayi? Shi sababbe”
“daddy Ya karya hannun Aunty Muhibba bal wlh.” yaron ya fada hakan Yana zaro Ido tare da nunawa da hannunsa.
“Me? Kai banson shirme aiman” daddy Umar ya fada Yana ganin hakan bazai yuwuba, sabida me zai hada muhibba da Ayzaan da har zai karya ta.
Aikuwa yaron cikin so lallai sai mahaifin nasa ya Gane ya cigaba da rantsuwa Yana fadin wlh da gaske ne Abbie ma ya dauke ta zai kaita asibiti ta Suma tun dazu.
“Ya karya hannun Muhibba kace?” ya fada cikin mamaki fuskarsa na sauyawa.
“Eh Daddy wlh da gaske nake”
“Saboda me?”
“Saboda Aunty Inarah. aunty amarya suka kama aunty Inarah suka mata duka, shine Yana zuwa ya kama hannun Aunty Muhibba ya balla shi bas”
Daddy Umar ya buga hannunsa akan kujera cikin zafin Rai tana fadin,
“Ahaff Na sani!”
Ya miƙe tsaye cikin fushi.
“Na san wannan jarababben yaron zai iya aikata komai!”
“Daddy, amma fa Aunty Muhibba ce ta fara kama gashin aunty Inarah...” yaron yafadawa daddy Umar din hakan.
“Ban ce komai ba akan abin da Muhibba ta yi, kome tayi haihuwarta yayi da har zai karya mata hannu!”
Dadi Umar din ya katse yaron tare da fadin shikenan fita yaje ya cigaba da wasansa.
Aikuwa. Yaron juyawa yayi ya fita adakin, tunda dai ya Riga ya Fadi abinda ya kawosa.
Amma Wani irin tsoron Ayzaan din yaji.
Domin kuwa yadda yaga muhibba ta Fadi ta sume Nan take abin ba karamin tsoro ya bashi ba.
Su dai su hibba sunji dadin hakan. domin kuwa dama muhibba bata da kirki, akwai rashin mutunci.
Hakan yasa hukuncin da Ayzaan yayi mata yayiwa kowa dadi.
Sabida dama ta matsawa inarah danma itama inarah din ba tayar baya bace ta gaba ce.
“daddy Umar kusa shi kadai afalon nasa Yana sake sake a zuciyarsa wacce me cike da tarin takaincin Ayzaan din.
Tambayar kansa yake me yasa zai karya mata hannu? Shin wannan gidan nasa ne? Kokuwa shine yake da ikon yin hukunci akan mutane, lallai seya gyarawa yaron Nan zama”
Ya fara kai-komo a falon acikin falon nas Wanda dama Yana da takaicin abinda Ayzaan din ya aikata agurin meeting.
“Yanzu saboda waccen yarinyar zai iya yin duk abinda yake so? Kuma zi dinga aikata duk rashin mutunci akanta.
Aikuwa yayi alkawari se ya kuntata zuciyar Ayzaan ta hanyar kaskantar da Inarah ta hanya Mafi Muni.
Saiya sa ta tsani kanta gaba daya, wannan alkawari ya daukarwa kansa.
Da wannan dai takaici ranar mutane da yawa suka wuni a wannan gida a wannan ranar..
Ita kuwa wacce abin ya faru sabida ita tuni ma ta tashi.
Kuma hannun nata da sauki.
Amma tsabar fitina irin ta inarah ta shagwabe tace baza ta iya yin komai ba ko abinci kuwa sedai ummee ta bata a Baki.
Shi Kuma dama ya Riga ya fita agidan sabida akwai inda zai je kafin ranar tafiyar tasa.
Wanda Kuma Yana ta shirye shiryen barin kasar.
Akwai abubuwan da yakeson yayi settling kafin ya tafi.
A wanna Rana duk masu jiran Ayzaan tadawo Babu Wanda yasashi a idonsa. domin kuwa bangaren alhaji baba ya tafiyarsa yayi kwanciyar sa bayan ya dawo.
Babu Wanda yasan Yana cikin wannan daki domin dai Babu Wanda yaga shigarsa.
Hasalima tun bayan rasuwar alhaji baba, Babu Wanda yake shiga dakin nasa, daga hajja sai innah sai Kuma shi Ayzaan din.
Wanda kowa yasa Ido yaga me Ayzaan yake aikatawa a wannan dakin.
Kokuma me yake boyewa a wannan daki Amma sun kasa ganewa.
Duk bincikensu basu samu komai ba adakin.
Dayawa suna zargin cewa koma dai menene alhaji baba ya bawa Ayzaan to tabbas Yana cikin wannan daki, to Amma a'ina??????...
Kuyi hakuri yau ba yawa 😩🙏✍️