Free chapter · Read without an account

014

by Kansa'u Bello · MEERAH

*MEERAH*

      *014*


     "Ya Sultan!." Na furta a hankali sosai hawaye na zubo min.

   "Meerah kina jina, ki faɗa mana inda kike yanzu zamu zo mu ɗauke ki." Sultan ya faɗa yana ƙara damƙe wayar. Ajmal dake kusa da shi ya kasa jurewa ya saka hannu ya karɓe wayar ya saka a kunnensa.

   "Ameerahh!! tell me where are you, hope babu abinda ya same ki dai ko?." Ya jero min tambayoyin gaba ɗaya, yana jin zuciyarsa na tsits-stinke wa. Kuka kawai na saka masa ina rintse ido, idanun shima ya rintse yana jin tamkar ya ɓace ya gan shi a kusa da ita.

  Dady dake kallonsa yana kuma sauraren kukan nata ne ya matso yana cewa.

  "Kaga bani wayar Son." Ya faɗa yana miƙa masa hannu, wayar ya cire a kunnensa ya miƙawa Dady ba tare da ya furta komai ba.

   "Mamana kina jina?." Dady ya faɗa cikin kwantar da murya sosai.

   "Eh Dady." Na faɗa a hankali.

   "Ki faɗa mana kina ina ne? Yanzu zamu zo mu tafi dake gida, kinga Momynki ma tana can cikin tashin hankalin rashin sanin inda kike." Ya faɗa cikin rarrashi. Ajiyar zuciya na sauke a hankali sannan nace.

   "Ina asibiti ne Dady, wani ne ya taimake ni ya kawo ni ban san wane asibitin bane ba." Na faɗa cikin sanyin murya.

   "Ina shi wanda ya kawo ki ɗin?." Dady ya tambaya.

   "Baya nan Dady, ban san inda ya tafi ba." Na bashi amsa.

   "Okay, akwai wani a kusa dake ne?." Dady ya yi mata tambayar.

   "Eh Dady." Na faɗa.

       "To ki bashi wayar ya yi min bayani."

    "Okay Dady." Na faɗa ina miƙawa Nurse ɗin dake kula dani wayar, don tun da na farka nake kuka da kiran Momy da Dady ta kira Nawaz ta sanar masa kamar yanda ya buƙata, ce mata ya yi yana nan zuwa yanzu nan.

   Nice da naga tana wayar ne nace ta ara min in kira gidanmu, ce min ta yi ta kira Yayana wanda ya kawo ni yace yana zuwa. Ce mata na yi ta dai ara min ɗin, kamar ba zata bani ba don sai da ta ɗan yi jim kafin ta bani wayar. Shine da na saka lambar Ya Sultan na kira shi.

   Lokacin da ta amshi wayar bayanin asibitin da nake ta yi masa, kashe wayar Dady ya yi yace.

   "Yaya muje tana asibiti ne." Duk miƙewa suka yi suka sanar wa Commissioner cewar zasu wuce asibitin.

   Commissioner yace.

     "Okay Zamu haɗa ku da Inspector Alim ku tafi tare, koda wani abin zai taso." Ba su tsaya gardama ba suka shiga motoci suka wuce, don a matse suke da son ganinta. A hanya Sultan ya kira Momy ya faɗa mata an ga Meerah tana asibiti ne, da wannan suka ɗan samu relief.

   Ai kuwa ajiyar zuciya ta sauke wani abu da ya tokare mata ƙirji yana sauka, ko ba komai ta samu sauƙi kaɗan jin cewar an san inda ƴarta take.

   "Wane asibitin ne, muna nan zuwa yanzu?." Momy ta tambaya. Sanar mata ya yi amma yace kar su taho, su jira tukuna. Ba don ta so ba ta haƙura ɗin, don ta matsu taga halin da yarinyar ta take ciki. Lokacin da suka isa lambar da ta kira su da ita suka kira, Nurse ɗin dake kula da ita ce ta fita ta shigo da su.

******* Ina kwance idanuna a lumshe ina tunanin yanayin da na tsinci kaina a jiya, da ace Allah bai kawo Nawaz ya ƙwace ni daga hannun waɗan can azzaluman ba, da Allah kaɗai ya san wani irin hali nake ciki a yanzu. Duk da cewa ina cikin shekarun ƙuruciya hakan bai sa na kasa gane abinda magan-ganun banzar da suka riƙa yi a kaina suke nufi ba.

    Sallamar su Dady da ta ratsa kunnena ce ta saka ni buɗe ido ina ƙoƙarin miƙewa zaune, bisa kuskure na bige hannuna dake ɗauke da Cannula. Azabar da ta ratsa ni ce ta saka ni runtse ido da ƙarfi, don ba ƙaramar bugewa na yi ba, saukar hannu na ji a kaina hakan ya saka ni buɗe ido ina kallon wanda ya riƙe ni.

   Cikin idanun Ya Ajmal waɗan da suke a birkice, da wani irin yanayin dana kasa fassara wa, nawa idanun suka faɗa. Shi ya fara janye idanunsa ya taimaka min na zauna da kyau, a hankali ya furta.

   "Ki kula." Kai kawai na iya gyaɗa masa na ɗauke idanuna daga kansa na mayar kan Dady, Abby, da Ya Sultan, waɗanda suke kallo na cike da tausaya wa da tsan-tsar soyayyar da suke min.

   "Dady!." Na furta a hankali hawaye na ciko min ido, matsowa Dady ya yi inda nake ya shafa kaina yana cewa.

   "Sannu Mamana, ya ya jikin? Babu dai abinda suka yi maki ko?." Ya yi min tambayar da ta saka ni mamakin yanda aka yi suka san abinda ya faru da ni. Ture mamakin na yi gefe na rungume sa ina sauke ajiyar zuciya, a hankali na bashi amsa da cewa.

   "Da sauƙi Dady, basu yi min komai ba." Na bashi amsa, Abby ma matsowa ya yi kusa ya min yaya jiki, da min fatan samun lafiya. Amsa masa na yi sannan na ɗora da gaishe sa, haɗi da tambayar sa yaushe yazo.

  Matsowa Yaya Sultan ya yi shima yana tambaya ta yanda nake ji, shima amsa masa na yi cike da shagwaɓa ina lafe wa a jikinsa. Kasancewar ya zauna a gefen gadon kusa da ni. Kamar an ce in ɗaga ido na muka ƙara haɗa ido da Ya Ajmal wanda ya kafe ni da ido kawai yana kallo na ƙasa-ƙasa.

  A hankali na buɗe baki na gaishe sa, bai amsa ba sai ido da ya lumshe min ya ƙara buɗe wa. Ita dai Nurse sakin baki ta yi tana kallon ikon Allah, mamaki sosai take yi a kan irin soyayyar da suke nunawa yarinyar tamkar wata jaririya. 

   'koda yake ba abin mamaki bane a wurin masu kuɗin nan.' ta furta a cikin zuciyarta. 

   Gaishe da su Dady Nurse ta yi cike da girmamawa, amsa mata su ka yi da kulawa, haɗi da yi mata godiyar kulawa da ni da tayi.

   "Babu komai ranka ya daɗe aikina nake yi, sannan kuma Yayanta da ya kawo ta nan shine ya bani amanar kulawa da ita." Nurse ta faɗa tana duƙar da kai.

   "Yayanta? Wane Yayan nata bayan gamu nan." Ya Sultan ya faɗa cike da mamaki. Sai a lokacin ne kuma suka tuna da wanda ya taimake ta, may be shi take nufi. Dady ne ya tambayi Nurse cewar.

       "Ina wanda ya kawo ta ɗin?.

   "Yace da ta farka na sanar masa, don haka na sanar masa yana nan zuwa in sha Allah." Ta bashi amsa cikin girmamawa, don kallo ɗaya ka yi musu zaka san cewa ba ƙananan mutane bane.

    Tana rufe baki aka yi nocking ƙofar ɗakin, Nawaz ne ya shigo bakinsa ɗauke da sallama zuciyarsa cike da mamakin securities da ya gani a ƙofar ɗakin.

   Da farko ma dakatar da shi suka yi, sai da ya kira Nurse sannan ta fita ta shigo da shi. Tsayawa ya yi yana kallon mutanen dake cikin ɗakin, cike da natsuwa da ɗabi'arsa ta sanyin yanayi ya ƙarasa ciki. A kan Meerah idanunsa suka sauka wacce ta lafe a jikin wani matashin da kallo ɗaya ya masa ya fahimci cewa ɗan'uwanta ne. Don ga kamanni nan sun bayyana a saman fuskokinsu.

   Tunda ya shigo nima idanuna suka sauka a saman fuskarsa, ƙasa ƙasa nake ƙare masa kallo ina gulmar yanayin sanyin jikinsa a zuciyata. A ɓangaren su Dady suma duk idanun suka zuba masa suna kallonsa, sai da ya shigo ciki sosai kafin ya gaisar da su cike da girmamawar da take ɗabi'arsa ga duk wanda ya girme masa.

   Amsa masa suka yi da kulawa, ya juya suka gaisa da Nurse ya tambaye ta mai jiki. Amsa masa ta yi da cewar.

   "Jiki ya yi sauƙi, idan Doctor ta zo ma zata iya sallamar ta." Godiya Nawaz ya yi mata kafin ya ɗan matsa kusa da gadon a hankali ya sauke idanunsa a kanta. Cikin sa'a nima na ɗago da niyyar satar kallonsa, sai idanuna suka faɗa cikin nasa.

    "Ya ya jikin naki?." Ya furta a hankali sosai wanda ni da Ya Sultan dake kusa da shi ne kawai muka ji me ya faɗa, sauran kuwa motsin laɓɓansa kawai suka iya gani. Amsa na bashi da cewar.

   "Naji sauƙi." 

      "Allah ya ƙara lafiya." Ya kuma furta wa a hankali. Duk abinda suke yi Ajmal yana kallon su ta ƙasan idanu, sai dai bai furta komai ba, hasali ma fuskarsa a haɗe take sosai. Gyaran muryar da Abby ya yi ne ya sa duk muka mayar da hankali gare sa. 

   "Yaya sunanka Yaro?." Abby ya tambaye sa. Amsa masa ya yi da cewa.

   "Sunana Nawaz Baffa."

      "Masha Allah." Abby ya faɗa sannan ya ci gaba da yi masa bayani.

   "Sunana Alhaji Bashir Mamman Gwangwazo, wannan kuma ɗan'uwana ne Hon. Abbas Mamman Gwangwazo. Mune Iyayen Meerah yarinyar da ka taimaka ka kawo ta nan, waɗan nan kuma ƴan'uwanta ne. Mun gode sosai da ƙoƙarin da ka yi mana, Allah ya saka maka da alkairi." Abby ya ƙare maganar yana kallon Dady da tunda yaron ya shigo ya kafe sa da ido.

   "Babu komai ranka ya daɗe, nayi abinda ya dace ne." Nawaz ya faɗa. Dady kuwa ganin kallon da Abby ke masa ne ya saka shi sauke ajiyar zuciya yace.

   "Sannu da ƙoƙari, mun gode da abinda ka yi.

    "Babu komai ranka ya daɗe." Nawaz ya faɗa yana duƙar da kai ƙasa, saboda kallon da ya ga mutumin na masa duk sai yaji ya tsargu. Sultan ma godiya ya yi masa a kan abinda ya yi. Juyo wa Nawaz ya yi ya kalli Ajmal dake tsaye kawai fuskar nan a haɗe babu alamar fara'a, kamar an ce ya ɗago suka haɗa ido.

   Da sauri Nawaz ya duƙar da kansa ƙasa, don har ga Allah wani irin kwarjini Ajmal ɗin ya yi masa. A ba zata ya tsinci muryarsa ya furta.

   "Thanks." A taƙaice. Kasa cewa komai Nawaz ya yi sai murmushi da ya ƙaƙalo, Abby na ƙoƙarin sake yin magana Doctor ta shigo da sallama. Ba ta yi mamakin manyan mutanen da ta gani a ɗakin ba, saboda tun a ƙofa ita ma taga security. Gaishe su ta yi sannan ta ƙaraso inda nake tace.

   "My patient ya ya jikin?." Ɗagowa na yi daga jikin Ya Sultan nace.

   "Naji sauƙi Doctor, Dady mu tafi gida." Nayi maganar ina mayar da kallona ga Dady.

   "Okay Mamana yanzu zamu tafi." Cewar Dady, kansa ya mayar kan Doctor dake duba Meerah yace.

   "Muna son wucewa gida idan babu matsala Doctor." Cike da girmamawa Doctor tace.

   "Babu matsala zaku iya tafiya, sai dai akwai maganin da zan rubuta wanda zata yi amfani da shi." Doctor ta faɗa sannan ta kara yi musu bayani sosai a kan ciwon nata, wanda kunya ta saka na kasa motsin kirki a inda nake. 

   Godiya Dady ya yi wa Doctor yana miƙewa yace ma Ya Sultan ya kama ni mu mu fita.

   "Okay Dady. Ya Sultan ya faɗa yana tashi tsaye. Hannuna ya kama ya miƙar da ni tsaye. Kuɗi masu yawa Ya Ajmal ya ajiye wa Doctor kamar yanda Dady ya bashi umarni.

    "Sultan ka amshi lambar yaron nan." Dady ya faɗa a dake sannan ya fice a ɗakin. A hankali na fara takawa zuwa inda yake tsaye ya na kallona.

   "Thank you for saving me." Na furta a hankali ina kallonsa, tattausan murmushi ya sakar min a hankali ya bani amsa da cewa.

   "Kar ki damu." Murmushin nima na yi masa sannan na fara takawa a hankali, ji kawai nayi an kama min hannuna. Ɗagowa na yi na sauke idanuna a kan Ya Ajmal da ya riƙe ni muka shiga takawa a hankali  muka bar ɗakin. Da kallo Nawaz ya bi bayansu har suka kammala ficewa sannan ya ɗauke idanunsa a bakin ƙofar.

  Ajiyar zuciya ya sauke yana juyowa suka haɗa ido da Sultan dake bin sa da kallo, kunya yaji ta kama sa ganin Sultan ɗin ya kama sa yana kalle masa ƙanwa. Murmushi Sultan ya saki sannan ya miƙa masa wayarsa yace.

   "Ka bani Contact dinka." 

      "Okay." Nawaz ya faɗa yana amsar wayar ya saka masa lambar sannan ya miƙa masa, saving ya yi sannan ya fice shima bayan yace.

   "Zan kira ka." 

     "Okay." Kawai ya iya amsa wa da shi, daga haka Sultan ɗin ya fice shima. Kallo ya bi bayansa da shi har ya fice, sannan ya sauke ajiyar zuciya. Yana juyowa suka haɗa ido da Doctor wacce ke bin sa da kallo.......

  
   (Barkanmu da dare da fatan anyi hutun weekend lafiya.)


   Oum Fatima 
      ***

Want the next chapter?

Create a free ArewaPen account to save progress, unlock paid chapters, follow this author, and keep reading across web and the Android app.