Free chapter · Read without an account

19.

by ZainabShehu22 · BARA A KUFAI

*BARA A KUFAI*



*19.*



*BRIGHT PENS 2026*

YOTA ID 002


Ganin yadda bakin Sabira ya bushe ya saka Ahayan miƙewa ta deɓo ruwa a gaggauce ta ɗago kanta ta fara zuba mata a baki, wata irin miƙa ta yi tare da sanƙarewa, ruwan ya dawo ta baki da hancinta, a rikice Ahayan ta yar da kofin hannunta ta fara jijjiga ta tare ambaton. "Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un!" Ruɗewa Umma ta yi ta miƙe ta ɗaura hannu a ka ta fashe da kuka. Wata irin bugawa ƙirjin Ahayan yake yi da sauri da sauri, lokaci ɗaya ta haɗa zufa saboda tashin hankali. A hankali numfashin Sabira ya fara komawa daidai, ta sauke wata irin ƙaƙƙafar ajiyar zuciya mai haɗe da shaƙuwa. 

A tare Umma da Ahayan suka saki doguwar ajiyar zuciya su ma, cike da lura Ahayan ta kwantar da ita cikin farinciki, wani abu da ta ji ya tsaya mata a maƙoshi na fargaba ya fara yayewa, don ta gama saddaƙarwa mutuwa Sabira za ta yi. Tana sassauke numfashi ta dubi Umma ta ce. "Dole fa sai mun je asibiti, zan fita na nemi waya na kira Yaya Saif, ko ba zai zo ba ya turo mana kuɗi, na san in sha Allah zai ba mu." Gyaɗa mata kai kawai Umma ta yi cikin sanyin jiki. Shafa goshin Sabira Raudah da ta idar da Sallah ta yi ta ce. "Zan raka ki Aunty Ahayan, idan Aunty Ummi ta fito daga wanka sai ta taya Umma kula da ita." Miƙewa Ahayan ta yi tana faɗin. "Mu fara zuwa gidan Maman Nasreen, na san ba za ta rasa numbern shi ba tunda suna siyayya a wurinsa." Kallon su Umma Lantana ta yi fuska shaɓe-shaɓe da hawaye ta ce. "Wato ku ta Sabira kawai kuke ba ruwanku da ɓatan Zeenat ko?" Ba su tanka mata suka fice jin Umma tana tausar ta da ba ta baki.


Duk wanda suke tunanin yana da numbern Saif a layin nasu sun je gurinsa ya kira musu shi amma wayar tasa ta ƙi shiga, haka suka dawo jiki a sanyaye, daga yadda Umma ta gan su ta san ba a dace ba, cikin sarewa ta ce. "Mu yi haƙuri kawai mu zuba wa Sarautar Allah ido, idan mai nisan kwana ce za ta warke kamar ba a yi ba da yardar Allah." 


A ranar Inno ta dawo a burkice kamar ba tafiyar daɗi ta yi ba, ta dinga kallon Sabira amma ba ta ce komai ba bare ta yi mata sannu.


***** ******

Buƙatar abubuwan Hasina da Farha ta yi irinsu national ID card da takaddun makarantarta ya saka Hasina zuwa gida, Amma tana ta murna ta ɗauka dawowa ta yi saboda kaɗaici ya ishe ta amma sai ta sanar mata school Uncle Aminu zai samar mata shi ya sa ta zo ɗaukar takardu, addu'ar fatan alkhairi da dacewa Amma ta yi mata, ba ta jima a gidan ba ta yi mata sallama ta tafi bayan ta jidi kayan sawarta. 

Sai da ta biya gidansu Saudat don ta nuna mata irin gidan da take zaune a yanzu tunda ita ba ta da babbar waya bare ta gani a status ɗinta cike da alfahari da jin kai, amma sai ta tarar sai Mama kaɗai a gidan, ta shaida mata Saudat ɗin ta yi tafiya. Ba ta so haka ba, saboda so take kowa ya ga irin daular da take ciki. 

***** *****

Dauriya da juriya da ƙarfin zuciya Aliyu ya tattara ya saka wa ransa, ya ci gaba da rayuwarsa kamar babu wani abu da yake damun shi, ya kuma dage da addu'a da kuma neman tsari daga dukkan sharrin Dr. Dubiya. 

Yau da safe ya tashi yana ta shiryen-shiryen tafiya exam, ya fito da exam slip ɗinsa da pen da wayarsa da calculator, yana shirin barin ɗakin wayarsa ta yi ƙara, ya duba ya ga baƙuwar number ce, bai ɗaga ba har ta katse aka sake kira, a gaggauce ya ɗaga tare da faɗin. "I'm sorry ina ɗan wani uzuri ne idan na gama zan kira."

"Kana da wani uzuri ne da ya wuce nawa ne da ma?" 

Muryar Dr. Dubiya ta doki dodon kunnensa da faɗin haka, wata irin faɗuwa gabansa ya yi, a take fuskarsa ta sauya ya nemi kuzarinsa ya rasa. 

Jin ya yi shiru ta saki murmushi mai sauti tare da faɗin. "Aliyu kana ɓata wa kanka lokaci ne kawai, amma ba zan taɓa barin ka ba, dole ka yi abin da nake so, ina jiran ka yau bayan Magriba, zan tura maka address ɗin inda za ka zo mu haɗu, ba kuma shawara ba ce umarni ne, saboda idan ka saɓa abin da zai biyo baya sai ka gwammace mutuwarka da shi." Yawu ya haɗiye da ƙyar cikin jarumta ya ce. "Ba zan zo ba Malama Hajara, don Allah ki ƙyale ni, ki fita daga rayuwata, akwai mutane irinki a duniya burjik da za su yi miki abin da kike so, amma ni ba zan iya ba, so don girman Allah ki rabu da ni, ki bar rayuwata ta huta!" 

"Ba zan iya ba Aliyu, kuma ni kai na zaɓa dole kai za ka kashe mini ƙishirwar da ta addabe Ni, don haka idan kana son tsira da rayuwarka ka yi abin da na buƙata kawai."

"Ke ba Allah ba ce, ba kuma ki isa kin yi mini abin da shi bai yi mini ba, don haka ki ɗauki duk matakin da za ki ɗauka, na dogara da Ubangijina na kuma kai ƙarar ki gurinsa." Yana gama faɗar haka ya katse wayar, zuciyarsa ta gama kawowa wuya, wani irin haushi da tsanar ta ne suka cika masa zuciya, yana zaman zamansa cikin rayuwar farinciki ta rikito masa ciki sama ta ka ta hana shi sakar. Jikinsa babu ƙwari ya kwashi tarkacensa ya fice zuciyarsa babu daɗi, duk yadda ya so ya yakice batun Dr. Dubiya ya ci gaba da walwalarsa amma ya kasa, haka ya yi exam ɗin a ƙuntatace ya fito, da ya tuno ta sai ya ji gabansa ya yanke ya faɗi.

A bangaren Dr. Dubiya da kallo ta bi wayar bayan ta zare ta daga kunnenta, sannan ta dubi mutumin da yake gabanta cikin mamaki ta ce. "Ka ji da kunnenka yadda nake fama da yaron nan ko Janwuya?" Baki Janwuya ya taɓe ya ce. "Abin kunya ba, kamar ke amma ki tsaya wani matsiyacin yaro yana wahalar da ke har haka? Ji fa yadda yake yi miki magana cikin raini da wulaƙanci, alhalin idan kika so cikin mintuna ƙalilan za ki gama da shi." Numfashi ta sauke ta ce. "Ka san yadda tsarin ƙungiya yake, a kowanne aiki da za mu yi Ƙanzula ta fi son a aikata bisa son rai saboda zunubin shi ake da buƙata, idan na tsaface shi ya yi mini duk abin da nake so ba riba tunda ba ya cikin hayyacinsa, kuma shi kaɗai ya rage mini a cikon aikina na wannan shekarar, ga shi da ƙyar na samo shi saboda masu irin tauraronsa suna da wuyar samu, shi ya sa nake lallaɓa shi, amma lokaci ya yi da zan haɗa masa tarkon da ba zai taɓa iya tsallakewa ba."

"Ya dai fi miki, ya batun binciken goɗiyar da kike?" 

"Ina nan ina yi, kuma akwai alamun nasara."

Ta yi maganar tana lumshe ido, siffar Aliyu da yanayinsa na nutsuwa da kamala na yi mata yawo a cikin kai, a hankali ta saki tattausan murmushi ta ce. "Idan na tuna ƙirar yaron nan sai na ji kamar ba zan iya sadaukarwa da ƙungiya shi ba." Tsaki Janwuya ya yi ya ce. "Ana maganar arziƙi kina sako wata daban, ba mun gama maganar yaron nan ba ne wai?" Buɗe idanunta da suka fara sauya kala ta yi ta ce. "Ina jin wani abu a game da shi ne na daban a ƙasan raina, da na so samu ne ya zama yarona kawai na more ƙuruciyarsa." 

"Amma dai kin san aiki irin wannan idan kuka gama abin da za ku yi ransa fansa ne ga ƙungiya ko?"

"Na sani, shi ya sa ma na fara damuwa, saboda na san zan samu abin da nake so a tattare shi, na duba na gani yana da irin halittar da nake matuƙar so a tattare da ɗa namiji."

Taɓe baki Janwuya ya yi ya ce. "Idan kina ganin za ki nemo wani mai irin tauraron nasa fine, da ma shi ne amfanin lecturing ɗin naki ai, ni dai mu yi maganar da ta kawo ni yanzu, idan na tafi sai ki ta tunanin yaron da hukuncin da za ki yanke, ki daina yi mini wannan kallon kuma tunda ba ni ba ne shi." Ƙara narke idanuwanta ta yi ta ce. "Ina jin ka, akan me ma muke magana?"

Tsaki ya ja tare da yi mata wani kallo, ta yi murmushi sannan ta tattara hankalinta suka ci gaba da tattaunawa.


***** ******

Duk wani sharaɗi da Sauban ya gindaya Saudat tana ƙoƙarin kiyayewa iya yin ta, amma duk da haka ba ta tsira daga cin mutuncinsa, hakan ya sa zaman gidan ya ƙara fita daga ranta. 

Yau ma kamar kullum bayan ta yi sallar asuba ta yi azkar ɗinta ta fita don zuwa ta yi aikinta na safe.

A hankali cikin sanyinta ta tura ƙofar part ɗin ta shiga, ta fara gyara parlourn ƙasa da dinning area, ta wanke toilet, ta gyara kitchen ɗin part ɗin, sannan ta haura sama, tattara ledodin abubuwan da ya ci daren jiya ta fara yi ta je ta zubar ta dawo, ta ɗauki wayarsa da system ɗinsa da ya bari akan kujera ta ɗora a kan centre table, bayan ta kaɗe kujerun ta share falon ta goge ta zauna a kan carpet tana hutawa kafin ta shiga bedrooms ta gyara, tana goge gumin fuskarta da ƙasan hijabinta ya buɗo ƙofa ya fito daga bedroom fuska babu walwala. Cikin takunsa na izza mai cike da taƙama ya ƙaraso tsakiyar parlourn, a ƙyamace ya ya yi mata kallon ƙasƙanci ta ya ce. "Ke!" Ta ɗaga kai ta dube shi a hankali.

"Mene ne haka? A falona kike wannan ƙazantar?"

Kallon shi ta yi ta kalli kanta cikin rashin fahimta, tsaki ya ja ya zura hannayensa a cikin aljihun wandonsa ya ce. "Ki fara cire wannan tsumman na jikinki da kika goge ƙazantar guminki da shi, sannan ki sauka ƙasa ki wanke jemammen hannunki, kafin ki taɓa mini bedsheet." 

Rigar da take bacci da ita ce a jikinta ta ɗoro hijabi ta fito saboda kar ta tsaya saka kaya ya zo yana yi mata masifar rashin zuwa akan lokaci, hakan ya sa cikin ladabi ta ce. "Zan sauka na wanke hannun amma ba zan iya cire hijabin ba." 

Wani kallo ya wurga mata yana ƙara tamke fuska ya ce. "Abin da na ce a yi za ki yi ko ra'ayinki za ki bi? Kina aiki a ƙasana har kike da confidence ɗin musa mini?" Shiru ta yi ba ta ce komai ba, tsawa ya daka ta mata, ta miƙe da sauri ta sauka cikin ɗacin rai, ɗakinta ta koma ta canzo hijabi ta dawo, a tsorace ta ce. "Na canza wani." Dogon tsaki ya ja ya ce. "Uban me kike ɓoyewa a duƙulallen jikin naki da dole sai da wannan shirgin abun za ki dinga yi mini aiki? To daga yau kar ki sake zuwar mini da shi, bana son kayan datti a duk inda nake rayuwa." 

"Taɓ!" Ta furta a ƙasan leɓenta don abin da ba zai yiwu ba kenan, ita ko a gida da hijabi take yawo bare kuma gidan wasu. 

"Ba kya ji na ne?" Ya faɗa a harzuƙe. 

"Na ji, amma hijabi sutura ne, ba zan iya zama babu shi ba." 

"Ok." Ya faɗa cikin izgili tare da ɗora ƙafa ɗaya kan ɗaya, wayarsa ya ɗauka ya fara latsawa, lokaci ɗaya kamar wanda aka tsikara ya sake ta ta faɗi a ƙasa, kamar wanda ya ga kashi haka ya taɓe fuska ya ce. "Kin taɓa mini waya ne?" Ta ɗaga kai a razane ganin yanayinsa, a fusace ya ce. "What! Na saka ki ne?"

"A'a zan goge kujera ne sai na ɗauke na ajiye a...."

"Shut up! Stupid! Ke waccan irin mahaukaciya ce? Na taɓa abu da hannuna ke ma ki taɓa kuma kina gani na ɗauka ba sai ki faɗa mini kin taɓa ba?" 

"Canza mata guri kawai na yi, ban taɓa maka ciki ba." Saudat ta faɗa don ita ba ta ga abin da ta yi na ba daidai ba da zai yi wannan fusatar. 

Miƙewa ya yi yana yarfe hannu kamar wanda ya taɓa wuta ya ce. "Ko tiles ɗin da kike gogewa kin taɓa gani na taka da ƙafata babu takalmi ko socks?" Ta girgiza masa kai a sanyaye. 

"Kujera da Bed da kike gyarawa duk ba da kaya a jikina nake zama a kansu ba?" Ta gyaɗa masa kai idanunta a ƙasa.

"Amma shi ne don ba ki da hankali abin da nake taɓawa direct za ki saka ƙazamin hannunki ki taɓa ke ma?" 

Shiru ta yi ba ta ce komai ba, a zuciye ya jijjiga kai ya koma ya zauna yana huci, sosai ransa ya ɓaci, ƙyanƙyamin wayar ya cika masa zuciya, sai murza hannunsa yake kamar hakan zai goge taɓa wayarsa da Saudat ta yi, tunanin irin hukuncin da zai yi mata kawai yake, tashi ya yi ya shiga ɗakinsa ya wanke hannunsa yana keɓe fuska ya fito ya saka handkerchief ya ɗauki wayar a ɗarare ya fara latsawa, Saudat dai tana tsaye kawai tana kallon ikon Allah. 

Tsawon mintuna goma suna haka sannan ya ajiye wayar ya miƙe ya dube ta a wulaƙance ya yi mata alama da ta tsugunna da hannu, ba ta musa ba ta risina.

"Fito da hannunki." 

Da sauri ta fito da su, ya nuna mata yadda za ta yi da nasa, ta yi kamar yadda ya ce ta shimfiɗe su a ƙasa, taku ya fara yi a gadarance ya matso daf da ita, numfashi ta ɗauke saboda yadda ƙamshinsa ya cika mata hanci, cike da mugunta ya ɗora ƙafafunsa duka biyun akan hannun nata ya take ya murje su da ƙasan takalminsa. 

"Innalillahi!" Ta faɗa cikin azaba tare da ƙoƙarin janye hannun amma ya ƙi ba ta damar hakan, sai da ya so dan kansa sannan ya ƙyale ta ya zagaye ta ya wuce. Da ƙyar ta iya ɗaga hannun da take jin shi kamar ba nata ba saboda raɗaɗin da yake yi mata, wasu irin hawaye masu zafi ne suka zubo a kan kuncinta, saboda kawai ta ɗauke masa waya ya yi mata wannan izayar? Wacce irin dauɗa ce da ita ta ta cancanci wannan ƙyamar haka? Haka ma jiya tana cikin aiki ya sha lemon kwali ya cilla mata kwalin a jikinta, bola ya mayar da ita ko me? Shi ya yi mata Yayyinsa mata su yi masa, don yanzu Hansai tana jan ta su shiga kitchen tare, to ganin haka duk wanda zai ci abinci a cikin yaran gidan sai ya kira ta ta yi serving ɗinsa, ko su saka ta gyaran kayansu da wasu ayyukan na ƙasƙanci, ga cin mutunci da tozarci, musamman ma Suhaima babbar cikinsu, halinsu ɗaya sak da Sauban. 

Tana hawaye ta baro part ɗin nasa ta koma ɗakinta ta kwanta tana jin duniyar ta yi mata zafi, ta gaji da zaman gidan nan da cin mutuncin da ake yi mata alhalin tana da gatanta, babban damuwarta rashin zuwa Islamiyyarta, ta tambayi Hansai ko idan ta gama aiki za ta iya zuwa ta dawo tunda a cikin unguwar ne amma ta ce ba za a taɓa barin ta ba, don masu aiki ba su da ƴancin shige da fice a gidan sai da ƙwaƙƙwaran dalili, tana nan kwance tana saƙawa da warwara bacci ya ɗauke ta, cikin baccin ta ji ana buga mata ƙofa, ta miƙe da ƙyar saboda baccin da ke idonta ta je ta buɗe, Asabe ta gani, ta risina ta gaishe ta, bayan ta amsa ta ce. "Ki je Hajiya na kiran ki." Ta amsa sannan ta zura takalmi ta bi bayanta cikin fargaba, tun ranar da aka kawo ta ba ta ƙara ganin ta ba, ko ta shiga babban ɓangaren gidan ƴanmatan kawai take gani, shi ya sa take mamakin wannan kiran da ta aiko a yi mata. 

Har saman ɓangarenta suka hau, suka tarar da ita hakimce a kan kujera, kamar yadda Asabe ta zube a gabanta haka ita ma ta zube ta ce. "Hajiya barka da rana."

"Ke ce mai tsaurin idon ɓata wa Son rai ko?" 
Ta faɗa cikin tsare gida. Ba ta jira amsar Saudat ba ta ci gaba da magana cikin gargaɗi.

"To ki kama kanki, tsakaninki da shi bin duk wani abu da ya gindaya da barin wanda ba ya so ne, kar na sake ji ko ganin kin kuma yin wani abu da zai sosa mini ran yaro, idan kuma ba haka ba za ki yi kuka da kanki."

"In sha Allah zan kiyaye Hajiya."

"Tashi ki ba ni guri! Yara an yi muku gata an tsamo ku daga rayuwar wahala amma sai ku zo ku dinga yi wa mutane iskanci!" 

A hanzarce Saudat ta miƙe ta fice, Asabe ta dinga ba wa Dr. Dubiya haƙuri sannan ta bi bayan Saudat cikin sauri don ta cimmata.

"Ƴar nan ki lallaɓa ku rabu lafiya da Hajiya, saboda ba a taɓa mata Sauban a zauna lafiya." 

"In sha Allah!" Saudat ta faɗa cikin karaya, don ta rasa irin mutanen da Allah ya haɗa ta rayuwa da su waɗanda ba a yi musu gwaninta kuma ba su san darajar Ɗan'Adam ba ko kaɗan. So take ta je gida ta ga Mama ta kuma ɗauko wayarta, amma Hansai ta tabbatar mata ba za a taɓa barin ta ba, kuma masu aiki ba sa riƙe waya a gidan, tagumi ta rafka bayan ta shiga ɗakinta don kamar tana prison haka take jin ta. 

***** *****

Ahayan tana durƙushe a bakin rariya tana wanke wa Inno kwanuka Woman leader ta shigo gidan bakinta ɗauke da sallama. Umma da ke zaune tana yi wa Sabira firfita ta amsa cikin fara'a kamar bakinta zai yage. 

"Sannu da zuwa Hajajju." Ta faɗa tana shimfiɗa mata darduma. 

"Yawwa Maman Ummi, wata mara lafiyar ce a nan?" 

Canza fuska Umma ta yi cikin yanayin damuwa ta ce. "Wallahi ita ce, ai ta kwana biyu ma, amma jikin da sauƙi yanzu."

"Subhanallahi! A hakan? Kuma shi ne na gan ku a gida? Ko kun je asibiti ne?" 

Umma ta ce. "A'a, magungunan Hausa dai nake ba ta." Fatan samun sauƙi Woman leader ta yi wa Sabira, sai da Ahayan ta gama wanke-wanken saboda gudun faɗan Inno sannan ta zo ta gaishe da Woman leader, ta amsa cikin sakin fuska. Inno da ta ji shigowar baƙuwa ta fito daga ɗakinta, tana bin su da wani shegen kallo ta ce. "Karima wace ce wannan kuma? Mene haɗin ki da ita?" Kafin Umma ta ba ta amsa suka ga Ummi da Rauda sun fito suna jan wani kwanon roba, kowa na son ya ƙwace daga hannun ɗan'uwansa, Ummi tana ta zunduma ashar Raudah kuma tana kuka. 

"Mene ne haka?" Umma ta faɗa a tsawace. 

Cikin kuka Rauda ta ce. "Garin da muka kwaɗanta ne, ta fi ni ci amma wai ba za ta bar mini ragowar ba." A kufule Ummi ta ce. "Inji uban wa? Kina ta zabga laumar zaki ce na fi ki ci? Wallahi Umm..." Kifewar da guntun garin ya yi a ƙasa ya saka ta kasa ƙarasa maganar tata, cikin takaici Umma ta ce. "Ga shi nan kun zubar kun ji daɗi ai, sai ku wuce ku ba mu guri." Kuka Rauda ta saka ta ce. "Wallahi Allah ya isana." A fusace Ummi ta kai mata duka, tsaki Inno ta ja ta ce. "To sarakan ci gayyar yunwa, kowacce ta nemi guri ta nutsu ta zauna, iyayen zalama akan wannan shegen garin kuke danbe sai ka ce rainon mahaukata." Tsit suka yi, Ummi ta koma ɗaki tana huci, Raudah kuma ta zauna tana matsar hawaye, don ba ƙaramar yunwa take ji ba, da ta sake kallon garin da ya baje a cikin ƙasa sai ta fashe da kukan baƙinciki mara sauti. 

"Haka kuke fama?" Woman leader ta faɗa tana kama haɓa. Umma dai ba ta ce komai ba saboda ganin Inno a tsaye, Ahayan dai tana zaune a gefe ta rafka tagumi ga kunya da ta lulluɓe ta, a kullum abubuwa ƙara taɓarɓarewa suke a gidan, rashin abinci ya ƙara tsananta, an koro su Ummi daga Islamiyya, kullum suna gida yunwa tana saka su masifa da dambe, ga ciwon Sabira da yake tafiyar kura, watarana kamar kafin a matsa a dawo za ta cika, wani lokacin kuma ya yi sauƙi kamar yau, sai da Inno ta koma ɗaki sannan Umma ta iya zagewa suka yi hira da Woman leader ta faɗa mata irin halin da suke ciki. 

"Gaskiya kuna cikin yanayi Maman Ummi, ai ban san abin har ya yi tsananin haka ba, amma in sha Allah zan san abin yi, akwai wani aiki na rabon magani da ake yi duk bayan watanni, ana samun alkhairi sosai a cikinsa, za ki ga ƴanmata suna ta yi." Cikin tarar numfashi Umma ta ce. "Na san shi kuwa, don Zeenat ɗin Lantana da ta yiyyi, wanda ake bi gida-gida ana rabawa ko?" Woman leader ta ce. "Ƙwarai kuwa shi ne, zan samowa su Ahayan in sha Allah, don yau ma ana can ana yin training ɗin wani da za a fara wani satin, duk da lokaci ya ƙure amma za mu je da Ahayan yanzu sai a saka ta a list tunda duk mutanenmu ne a gurin, su kuma ragowar wani yin in sha Allah sai na saka su." Umma ta ce. "Kai amma na gode sosai da sosai, Woman leader ba abin da zan ce miki na irin taimakon da kike yi mini, wannan aiki an ce ana samu sosai a cikinsa, idan yaran nan suka samu dukansu ai mun warke." Woman leader ta ce. "Haba sai ka ce wani abu, babu komai ai, muka samowa wanda ba mu sani ba ma bare ku da ake tare, ni da na san haka ne ma tun yaushe da ba sun daɗe da farawa ba." Cikin murmushi Ahayan ta ce. "Mun gode sosai Aunty." Don ta san irin aikin, ta daɗe tana son yi da ta ga yaran maƙotansu da Zeenat suna yi, har samo mata Yaya Saif ya yi niyyar yi amma Inno ta hana shi. 

"Tashi ki kintsa mu je gurin training ɗin kar su tashi, don idan ba ki yi training ba aiki ba zai yiwu ba." Woman leader ta faɗa tana miƙewa.

Umma ta ce. "Ai ba shirin da za ta yi, hijabi kawai za ta saka ku tafi, ba abin da ake tafiya da shi ko?" Woman leader ta ce. "Babu komai." Umma ta ce. "Yawwa, bari ta fito ku tafi." Duk ta gigice saboda ta ji batun samun kuɗi.

Soro Woman leader ta koma ta lalubo wayarta ta danna ta kara a kunne, cikin ƙasa da murya ta ce. "Gaye na yi sara akan gaɓa fa, ina shiga gidan na tarar suna gaɓar tsananin buƙatuwa, na samu na yi musu ƙaryar cewa zan samar mata aikin rabon maganin nan da ake yi, za mu taho yanzu, sai ku fito kuma, don Allah ku zo da wuri, don duk a firgice nake, burina kawai na ga an yi aikin nan an gama na tsira...." Hango Ahayan ya sa ta yi saurin canza maganar da take. Bayan ta kashe wayar ta sakar mata murmushi, tare da kama hannunta ta yi wa Umma sallama wadda ta biyo su har soron tana ƙara yi mata godiya da jera mata addu'oi, sai da suka fice sannan ta koma cikin farincikin za su samu kuɗin da za su toshe wata kafar. 

Ummi da ta fito za ta shiga banɗaki ta dube ta cikin hassada ta ce. "Wai komai ita matar nan sai dai ta ce Ahayan Ahayan? Ke ma kuma maimakon ki ce a tafi da ni na fara aikin sai kika yi shiru, wallahi suna biyan kuɗi sosai, su Mero ƙawata duk yi suna yi, da ma ina son na siya ankon Hadiza, kin ga da tuni sai na siya idan aka biya mu." Umma ta ce. "Ki yi haƙuri, ta ce kuma za ta samo muku ai, kuma kuɗin Ahayan na kowa ne kin sani, biyar ba za ta ɗauka ba idan aka ba su haka za ta ba ni." Baki Ummi ta taɓe ta ce. "To a wanne account ma za a saka mata kuɗin ita da ba account ba?" Umma ta ce. "Na san duk Woman leader za ta ji da wannan in sha Allah." Ummi dai ba haka ta so ba, ta so a ce ita ta samu wannan damar.


***** ******



Farha ta tura an ɗauki Hasina an kai ta inda za a yi mata duk wani shirye-shirye na tafiya, an kammala komai ta tabbatar mata a cikin satin nan za su tafi, cike da murna da farinciki Hasina ta haɗa kayanta, da ma a ranar Uncle Aminu zai yi tafiya, za su bar ƙasar saboda batun kwangilar da za su yi, Laila ta tama yi mata korar kare sai ta ga ta yi shirin tafiya don radin kanta, kuɗi masu kauri Uncle Aminu ya ba ta, ta yi musu sallama ta tafi. 

Yadda Amma ta ga ta dawo cikin walwala da farinciki sai ta ɗauka ta fara hankali ne, don a tunaninta duk ranar da Hasina za ta dawo da ƙunci za ta zo mata amma sai ta ga saɓanin haka. 

Sai da Hasina ta kira duka numbobin Uncle Aminu ta ji ba sa shiga alamun ya bar ƙasar sannan ta tunkari da Amma batun tafiya makarantarta ana i gobe tafiyar. Cikin mamaki Amma ta ce. "Da wurwuri haka? Wacce makarantar ya samar miki?" Da zumuɗi Hasina ta ce. "Wata private university ce mai kyau a birnin tarayya." Kwanon da Amma take wankewa ta ajiye ta taso ta dawo kusa da Hasina ta ce. "Birnin tarayya kuma? Ba ma a nan garin ba ne? Kuma da ya kira ni ya ce mini zai yi tafiya bai sanar da ni wannan batun ba sam." 

"To ai Amma kin san halin Uncle ba ya son ya yi alkhairi ya faɗa, da na ce ya faɗa miki tun a lokacin da aka fara neman makarantar cewa ya yi idan an kammala komai sai na sanar miki."  A sanyaye Amma ta ce. "Gaskiya da ya sanar mini tun a fari ba za ki je har birnin tarayya karatu ba, yanzun ma zan kira shi na ce a sauya miki makaranta ya samo miki a nan garin, don hankalina ba zai taɓa kwanciya kina can wata uwa duniya ni ina nan ba." Zunɓura baki Hasina ta yi ta ce. "Gaskiya Amma ni dai sai na je, zan je na haɗu da ƴan gayu na yi rayuwa da ƴaƴan masu kuɗi kuma sai ki ce a'a, ya fa gama kashe kuɗaɗensa don makarantar mai tsada ce, yanzu kawai ki kira ki ce masa ba zan je ba yaya kike zaton zai ji? Shi yana ganin ya yi gwaninta ke kuma sai ki sace masa gwiwa?"


"Ba gwasale shi zan yi ba, saboda tun da kika zo mini da batun na ji daɗi sosai na yi farinciki, don kin san burina kenan ku yi karatu, amma birnin tarayya dai ba za ki je shi ba gaskiya, musamman da ba wani ne da mu a garin ba, ba mu san kowa ba kuma." 

Kamar Hasina za ta yi kuka ta ce. "A gidan abokinsa fa zan zauna, shi ya san mutane sosai a garin tunda daga can suka dawo nan, ni dai Amma ki bar ni na tafi kawai." Amma ta ce. "Duk da haka ban yarda ba, bari ma na kira shi yanzu mu yi magana, ya yi haƙuri ya samar wata a nan." Bubbuga ƙafa Hasina ta fara yi cikin ƙunƙuni, a ranta ta ƙudurce ko sama da ƙasa za su haɗe sai ta yi tafiyar nan, shi ya sa take faɗa rashin wayewa bai yi ba su Saudat suke ganin laifinta, yanzu da Amma wayayyiya ce ai zuwanta karatu birnin tarayya ba zai dame ta ba sai dai ma ya zama abin alfahari a gurinta. 

Tana kallo Amma ta yi ta kiran Uncle Aminu ba ta same shi ba, sai ta kira Aliyu ta labarta masa komai, shi ma ya ce bai goyi bayan Hasina ta tafi ba ko don saboda halinta na san ƙawar duniya, tana nan ma ya aka cika bare kuma ta je birnin tarayya ta yi gogayya da masu hannu da shuni. Ihu Hasina ta fasa kamar wadda aka yi wa wani mugun abun, ta dinga zagin Aliyu tana kiran shi da ɗan buƙulu da ma ta san shi ne mazigin Amma, sai da Amma ta kwaɗe ta ganin za ta tara mata mutane sannan ta yi shiru ta koma ɗaki ta kwanta tana tunanin hanyar da za ta bi don ganin ba ta fasa tafiyar nan a gobe ba, saboda ta gama cin buri, har hoton makarantar Farha ta tura mata, ga jirgi da za ta hau, idan ta rasa wannan babbar damar gani take kamar ta rasa komai a duniya. Wani tunani da ta yi ne ya saka ta doka tsalle tare da sakin murmushi. A fili ta furta. "Amma sai dai ki yi haƙuri, amma tafiya babu fashi, na riga na samo mafita."



*Littafin BARA A KUFAI na kuɗi ne akan 1k ta wannan account ɗin, ****
*Opay*
*Zainab Abdullahi Shehu*


*Few pages suka rage mu kammala book 1 wanda shi ne zai zo a free, book 2 kuma na kuɗi ne, wanda a nan asalin labarin da danbarwar suke, akwai wata ƙaddara da take jan Ahayan da Saudat da Aliyu da Hasina da Juraij mai wuyar warwarewa, don haka ku hanzarta siyan tikitin wannan tafiyar kar a yi babu ku. Na gode!*



*#Zeey Kumurya*
*#****

Want the next chapter?

ui.create_a_free_arewapen_account_to_save_progress_unlock_paid_chapters_fol