Free chapter · Read without an account

MATAR GIDA PAGE 63

by Maimuna Bala · MATAR GIDA

MATAR GIDA BOOK 2



SHUUKRAN/022



YOTA ASSOCAITION




P63




Kamar yadda muka karanta a baya mahaifin Unaisa Mallam Shu'aibu ɗan asalin garin gombe ne,mahaifiyarta kuma ƴar kasar Nijar  niman arziƙi ya kawo kakan Unaisa mahaifin Mama garin gombe nan aka haifi Mama ta yi girma har Allah ya haɗa ta da mahaifin Unaisa, bayan aurensu Allah ya albarkace su da haihuwar Aisha,tun daga haihuwar Aisha Mama bata sake haihuwa ba,tun rashin haihuwar baya damunta har ya fara damunta hakan yasa suka fara yawon asibiti ita da mahaifin Unaisa duk inda suka je an tabbatar masu Mama ba za ta sake haihuwa ba dalilin mahaifarta ta samu damuwa a lokacin haihuwar Aisha ƙwayar cuta ta shiga mahaifar wanda hakan yasa mahaifar matsewa,Mama ta yi kuka har ta gode Allah haka zalika mahaifin Unaisa ya yi bikin ciki sosai amma ya danna damuwarsa ganin yadda Mama ta ɗaga hankalinta ta dauki sama da watanni biyu bata iya cin abinci yadda ya kamata,sosai mahaifin Unaisa ya dage wajen rarrashin Mama daga karshe Allah ya taimake sa Mama ta wallafawa Allah komai ta cigaba da rayuwa ta mayar da hankali wajen bawa Aisha tarbiyya,bayan Aisha ta ciki shekaru goma sha biyar a duniya Allah ya albarkaci Mama da samun cikin Unaisa murna da farin ciki wajen Mallam Shu'aibu da Mama ba a cewa komai a watar da Mama ta haifi Unaisa a wannan wata Allah ya karɓi rayuwar Mallam Shu'abu,tun daga ranar da aka haifi Unaisa Mama ta dauki son duniya ta daura mata duk wani laifi da Unaisa zata yi Mama bata mata faɗa,ko kaɗan bata son ɓacin ran Unaisa hakan yasa Unaisa ta girma a sangarce kuskure na biyu na Mama ta yi shine bata ja Unaisa jiki ba ta bar Unaisa ta girma a bulayin makwabta ko kwana Unaisa za ta yi makwabta Mama baza mata faɗa ba,wannan dalilin yasa Unaisa ta girma babu hankali babu sanin ya kamata duk abinda tunaninta ya bata shi take aikatawa,wata doguwar ajiyar zuciya Mama ta sauke murya can ƙasa ta furta ''kila na yi kuskure wajen bata tarbiyya kila akwai inda na gaza'' a can wajen Ɗalha kuwa bayan tafiyar Unaisa ya fita parlour cikin shiri da alama fita zai yi kallo ɗaya ya yiwa yara dake kallon TV da Amirah da ta yi jigum tana tunani,kallo ɗaya zaka masa ka tabbatar har sannan ransa a ɓace yake,da ido Amirah ta bisa har ya fita daga parlourn ta so ta yi masa magana amma ganin har sannan ransa a ɓace yasa ta yi shiru bata ce masa komai ba,bayan fitarsa ne ta kashe TV ta tura yara ɗaki lokacin karfe tara saura ƴan mintina,gaba ɗaya bata ji daɗin abinda Ɗalha ya yiwa Unaisa ba a tunaninta bai dace ya korata gida ba,koma menene za su iya sasanta tsakaninsu ba ƙaramin tausayin Unaisa ta ji ba a wannan daren,ko a wani hali Unaisa zata kwana oho,haka Amirah ta daure ta yi duk wani abinda ta saba kafin ta kwanta bayan ta kwanta gaba ɗaya bacci ya yi kaura a idanunta haka ta yi ta juyi a gado,bayan fitar Ɗalha bai tsaya ko ina ba sai gidan Muhsin,kofar gidan ya yi parking yana zaune cikin mota ya kira layin Muhsin wayar tana daf da tsinkewa Muhsin ya amsa kiran bayan Muhsin ya amsa kiran ne Ɗalha ya ce yana jiransa a waje,daga haka ya kashe wayar Muhsin dake zaune cikin ɗaki yana aiki cikin kamputa ya shiga juya waya bayan Ɗalha ya kashe kiran,can dai ya tashi ya fita kofar gida bayan fitar sa ganin motar Ɗalha ya yi kofar gida hakan yasa ya buɗe kofar gaba ya shiga motar bakin sa dauke da sallama, bayan shigar sa ganin Ɗalha ya yi zaune yana tunani da alama ya yi nisa cikin tunani gyarar murya Muhsin ya yi yana duban Ɗalha,wata doguwar ajiyar zuciya Ɗalha ya sauke kafin murya can ƙasa ya amsa sallamar da Muhsin ya yi,''ya aka yi Mallam tunanin me ka ke haka?" wani abun ne ya faru?" shiru Ɗalha ya yi bai ce komai ba shi dai Muhsin sai binsa yake da ido,bayan wasu ƴan sakanni Ɗalha ya buɗe baki a hankali ya ce ''ina ganin zan rabu da yarinyar nan kafin ta kashe ni'' cike da mamaki Muhsin ya ce ''wa fa?" Ɗalha bai tanka sa ba sai rintsa idanunsa da ya yi ya tura kujerar da yake zaune a kai baya ƙadan tare da kwantar da bayansa jikin kujerar ''ban san inda ta samo mota ba kawai na fita zan je masallaci sallar magrib sai ganinta na yi da mota tana parking'' fuskar Muhsin dauke da mamaki sosai ya ce ''mota kuma wa ya ɓata ina ta samo?" har sannan idanun Ɗalha rufe murya can ƙasa ya ce ''ban sani ba yanzu haka kai na ya kulle tun safe nake tunanin inda take zuwa da sunan islamiyya na uni tunanin yadda zan ɓullawa lamarin rashin zuwanta islamiyya ban gama da wannan ba kawai ta zo da mota'' shiru ya yi na wasu ƴan sakanni kafin ya ce ''na korata gidansu bazan iya cigaba da zama da ita ba gaskiya ina bukatar hutu tun sanda na aureta ban huta ba'' numfasawa Muhsin ya yi kafin ya ce ''ban fahimta ka korata gida ba?" ya ƙare magana yana kallon Ɗalha cike da mamaki shi dai Ɗalha bai ce masa komai ba,can ya ce ''l think za ku iya sasanta ba sai ka korata gida ba and maganar rashin zuwanta islamiyya shima za ka iya tambayarta ƙilah ta faɗa maka gaskiya'' numfasawa kawai Ɗalha ya yi ya ce ''fatana Allah yasa ba wani abun take a ɓoye ba,Allah yasa ba wani ne..Muhsin bai bari ya kareshi zancen ba ya yi saurin rufe masa baki ya ce ''kar ka fara..kar ɓacin rai yasa ka haramta zamanku,a sanin da na yiwa Unaisa baza ta aikita haka ba,dan Allah ka yi gaggawar cire wannan tunanin a zuciyarka,insha Allah komai zai yi dai dai'' shiru kawai Ɗalha ya yi yana istigfari a zuciyarsa,Muhsin ya dauki sama da mintina talatin yana kwantarwa Ɗalha hankali kafin daga bisani Ɗalha ya sallame sa tare da yi masa godiya,karfe sha ɗaya dai dai Ɗalha ya bar kofar gidan Muhsin bayan komawarsa gida ɗakin Amirah ya wuce kai tsaye,bayan shigarsa rage kayan jikinsa ya yi kafin ya dauki Fauziyya dake bacci gefen Amirah ya kwantar da ita can karshen gado inda ya dauki pillow ya tareta gefe da gefe,daga haka ya hau gado ya kwanta tare da janyo Amirah jikinsa ya riƙeta gam kama za a kwace masa ita ya cusa kansa a wuyanta yana sauke numfashi,tun sanda ya shigo gidan Amirah ta farka amma sai ta yi shiru kamar tana bacci a hankali ta juyo tana fuskantar sa,hannu ta kai ta ɗaga fuskarsa da ya cusa kirjinta kamar zai shiga cikin jikinta,ta zubawa fuskarsa ido tana kallonsa idanunsa rufe ya kai hannu ƙugunta ya ƙara haɗeta da jikinsa tare da rungumeta murya can ƙasa ya ce ''just sleep is midnigth already'' shiru kawai Amirah ta yi ta rintsa idanunta a haka bacci ya dauke su















Washe gari da ƙyar Anty Aisha ta samu ta tada Unaisa ta yi sallar asuba bayan ta idar da sallah ta koma ta kwanta,ita ko Anty Aisha fita ta yi tsakar gida ta shiga rumfar girki inda ta kunna gawaye ta daura ɗumamen tuwo,karfe takwas da wasu mintina Mama ce zaune  kofar ɗaki tana cin ɗumamen tuwo da Anty Aisha ta sa mata daga gefenta kuma kofin kuno ne me zafi wanda Anty Aisha ta dama,Anty Aisha na can kofar rumfar girki tana juye ruwan zafi cikin botiki,Unaisa ce ta fito daga ɗaki tana goge ido sanye da dogon hijab kasancewar garin da sanyi,Mama da Anty Aisha suka kalleta, zama ta yi kan shimfiɗa da Mama ke zaune ta kai hannu tana matse goshi,ciwo kanta kai mata amma ba sosai ba,tunawa ta yi da maganinta na gida hakan yasa ta ja wani guntun tsaki can ta mayar da dubanta ga Mama ta ce ''barka da safiya Mama'' Mama ta amsa tana kallonta ta ce ''kin tashi lafiya?" Unaisa ta ce ''lafiya ƙlau alhamdulillah'' ta mayar da dubanta ga Anty Aisha ta ce ''barka da safiya Anty'' Anty Aisha ta amsa mata a takaice kafin ta dauki botiki da ta zuba ruwan wanka ciki ta wuce bayi,tamabaya Unaisa ta yiwa Mama inda ta ce ''Mama ina Auwal so nake ya siyo min maganin ciwon kai'' Mama ta ajiye kofin kunu dake hannuta ta ce ''ya je makaranta'' shiru Mama ta yi kafin ta ce ''wane maganin ki ke sha?" Unaisa ta bawa Mama amsa a takaice ta ce ''panado'' shiru Mama ta yi na wasu ƴan sakanni kafin ta ce ''kin fara zuwa awo ne'' cike da rashin fahimtar maganar Mama Unaisa ta ce ''awo kuma? na me?" Mama ta yi shiru bata sake cewa komai ba ta cigaba da cin abincinta Unaisa na nan zaune gefen Mama wani yaron makwabta ya shigo gida,cike da girmamawa ya gaida Mama,Mama ta amsa masa kafin ya gaida Unaisa ta amsa nan yaro ya mayar da dubansa ga Mama ya ce ''Mamata ce ta aiko ni wai dan Allah idan an  kunna wuta a ɗiba mata garwashi'' Mama ta masa nuni da rumfar girki ta ce ''je ka ɗiba'' bayan ya ɗiba wuta yana daf da fita daga gidan Unaisa ta ce ''in ka kai wutar ka dawo zan aike ka'' da to ya amsa kafin ya fita daga gidan bayan fitarsa Unaisa ta mayar da dubanta ga Mama ta ce ''Mama wai har yanzu ana siyar da ƙosai bakin kwalta?" Mama ta ƙara kallon Unaisa sosai kafin ta ce ''eh ana siyarwa'' daga haka Unaisa bata sake cewa komai ba,bayan fitar Anty Aisha daga wanka shirya kanta ta yi cikin wasu riga da zani atamfa,babu laifi atamfar ta sha ruwa sosai,zama ta yi gefen Unaisa hannuta riƙa da wata kwana dauke da tuwo da miya,ɓata fuska Unaisa ta yi tana kallon miyar gaba ɗaya wari miyar ke mata,sosai warin miyar ya cika mata hanci hakan yasa ta tashi ta shiga ɗaki ta kwanta tare da ɗaukar waya shiru ta yi tana juya waya bata kunna wayar ba,abinda ya faru jiya ya dawo mata nan take ta ji damuwar da ta kwana da ita ta dawo sabuwa nan take ta ji zuciyarta babu daɗi,kamar yadda Anty Aisha ta faɗa kungiyar matan gida sun raba ta da dangi yanzu kuma kungiyar zasu kashe mata aure tabbas haka ne sanin kanta ne Ɗalha ba zai ji dadi ba in ya san tana cikin kungiyar amma bata da yadda zata yi baza ta iya barin kungiyar ba,ba za kuma ta iya rabuwa da Ɗalha ba,wata doguwar ajiyar zuciya ta sauke,tana nan kwance yaron da ta ce zata aika ya dawo gidan,da ƙyar ta yunƙura ta tashi zaune kafin ta fita daga ɗaki mayar da dubanta ta yi ga Mama ta ce ''Mama in kina da canji dan Allah ki bashi ya siyo min ƙosai a bakin kwalta'' Mama bata ce komai ba ta dauki karamar pos ɗinta dake gefe ta zaro gudar ɗari biyar ta miƙawa yaron ta ce ''ungo jika bakin kwalta ka karɓo mata ƙosai ka ce a baka na ɗari biyu da hamsin'' karɓar kuɗin yaron ya yi yana faɗin to daga haka ya fita daga gidan,ɗaki Unaisa ta koma ta cire hijab ɗin jikinta ta daura kan gado daga haka ta fita daga ɗakin,buta ta dauko ta zaga bayi,da kashin kaji Unaisa ta fara cin karo a hanyar bayi kasancewar a hanyar shiga bayi kejin kaji yake,babu wani datti cikin bayin kasancewar siminti ce shimfiɗe,kusan kullum Anty Aisha ke wanke bayin amma gaba ɗaya Unaisa ta ji hankalinta ya tashi da ƙyar ta iya rusuna cike da ƙyanƙyame ta yi abinda zata yi ta fito,can magudana inda suke wanke wanke Unaisa ta je ta kukura baki ta wanke fuska daga haka ta koma ɗaki tana mayar da numfashi kamar wacce ta yi babban aiki












SHUUKRAN

Want the next chapter?

Create a free ArewaPen account to save progress, unlock paid chapters, follow this author, and keep reading across web and the Android app.