Free chapter · Read without an account

DA JININSA NAKE RAYUWA

by Sayyid (Boy) · DA JININSA NAKE RAYUWA

 Wani irin mamaki ne ya ziyarci ƙwaƙwalwarsa wanda ya haifar masa da mutuwar tsaye, wai ta dunƙule hannu kenan dukansa za ta yi? Bai san lokacin da wani murmushi ya suɓuce masa ba, lallai yarinyar nan da sauran ta. 

Jamila da Aisha kam suma mutuwar tsaye suka yi, Jamila a ranta tana ayyana dole kuwa yarinyar nan tabar gidan nan yau, tun da har rashin kunyarta ya kai wannan matakin. Ita kam Aisha ta san Husna zata yi abin da yafi wannna ma, amma bata yi tunanin zata iya yiwa mutum kamar Yaya Ashraf ba, mutum mai girman har haka, cikkaken mutum mai kwarjini, duk irin girman Anty Jamila idan suka jera gani ake ya kereta, amma wai Husna ta ɗaga hannu haka zata dake shi. 

Murmushin da Jamila ta ga ya yi ya ɓata mata rai, cikin salon yaudara ta ce. 
“Rashin arziƙin da kika yi min bai ishe ki ba kenan ko? Sai kin haɗa da shi kenan. Kuma da kika ce yau zaki bar gidan dama wa ya riƙe ki, ɗazu da kika ce zaki tafi wani ya hanaki.” 

Kallon Jamila Husna ta yi, ita bata san me ya sa ba amma haka kawai sai taji bata son biyewa Jamila, mussaman data fuskanci neman rigimata take da ita, ita Husna irin mutanen nan da indai kana son rigima da su a lokacin to baka isa ka yi ba, sai lokacin da ka manta zasu zo maka da nasu jujin kuma duk ƙin da mutum yake wa faɗan to sai fa anyi, shi ya sa bata cika son kula jamila ba. 

Cika ta yi ya sauke hannunsa, itama ta saki nata hannun ta yi cikin ɗaki ko kallonsu bata yi ba, tana shiga ɗaki ta sauko da jakarta daman kaya ɗaya ta sa tun da tazo, daman bata jera sauran a ko ina ba, sai brush da ta ajiye a banɗaki, shima shiga ta yi ta ɗauko. 

Suna tsaye a falo Husna ta fito, Jamila sai sharri take karantawa Ashraf Husna bata ko kallesu ba ta nufi ƙofa za ta fita, Hunsa na fita Jamila ta sauke wata ajiyar zuciya, wani irin sanyi ya ratsa ta kamar ta sauke wani ƙaton dutse da aka ɗaura mata a kanta, sai dai bata gama sauke ajiyar zuciyarba Husna ta sake shigowa. 

“Azo a buɗe min ƙofa.” 

Husna ta faɗa tana turo baki, da yake idan ka fito daga falon wata ƙaramar baranda ce akwai wata ƙofa da ke kusa da ƙofar falon ya zama suna kallon juna, sai kuma ƙofar da zata sadaka da waje, to wannan ƙofar ce a rufe, abin da bata sani ba ƙofar na amfani da remote ne kuma Asharf ya kulle suna tsaye ko Jamila bata kula da lokacin da ya danna remote ɗin ba. 

Kamar ta ce mata ai ƙofar a buɗe take, sai dai kuma bata so ta zaƙe ya ce ya hana Husna tafiyar, shi kam bai tanka musu ba ma ya yi ciki, ta sake cewa.
“Azo a buɗe min.”
Sai da Jamila ta tabbatar ya shiga ɗaki sannan ta ce.
“Dalla malama tura ƙofar zaki yi.”
Wani kallon banza Husna ta watsa ma Jamila sannan ta ce.
“Ke me ya hana ki zuwa ki tura, tun da an ce miki ban iya turawa ba.”
Wani haushi ya tokare Jamila, zata so ta buɗe mata ta tafi, amma kuma bata son ta ƙasƙantar da kanta a wajenta, tsaki taja ta bi bayan mijinta, Husna kam ta koma wajen ƙofar tana bugawa, tun tana bugawa a hankali har ta fara da ƙarfi ko zai zo ya buɗe mata, har kuma ƙarfinta ya ƙare ta dawo bugun a hankali.
A can kuwa Jamila na shiga ɗaki ta ce.
“Sannu da zuwa Honey.”
Ya ɗaga mata kai na tare da ya yi magana ba, jikinta ne ya yi sanyi ta sami waje ta zauna tana kallonsa, duk abin da take yi a kan sa ne. Son sa ne ya ja mata komai, shi ya jefata a wannan halin ya cire mata nutsuwar zuciya, Allah Ya gani tana son mijinta kuma bata ƙaunar ganin shi kusa da kowacce mace. 
“Honey.”
Ta kira sunansa, kai ya ɗaga ya kalleta baya son yin magana kwata kwata, sabida zafi yake ji a cikin ransa yana mamakin me ya sa Jamila take haka ne, ‘yar wannan yarinyar ta gagara zama da ita, zama na ɗan lokacin na ‘yan kwanaki amma sai nemanta take da masifa, yasan halin yarinyar nan sarai zataje ta kwashe komai ta faɗawa Mimi ko Dade, su daman ba son Jamilan suke ba haka zasu zo su yi ta kusheta, amma gaba ɗaya ita bata ganewa. 
“Jamila.”

Ya kira sunanta cikin sanyin muryarshi, mai haɗe da izzah da taƙama. Haka yake magana a hankali amma kana ji kasan akwai zallan izzah a cikin maganar. Shi kawai baya son magana ne, magana na damun sa. Shi ya sa ya zaɓi yawaita shiru a kan magana, amma shi kansa ya san muryarsa na da wani irin amo mai daɗi, Jamila bata ƙi ya kwana yana mata magana ba ko da kuwa faɗa ne zai yi mata to ita ya yi mata, muryarsa tana haifar mata da wata annashuwa, amma gaba ɗaya maganarsa batafi a ƙirga ba. 

“Na,am Honey.”
“Me ya sa bazaki iya haƙurin zama da yarinyar nan ba, just for 1week.”
“Honey rashin kunya take yi min fa.”
“Na sani bata da kunya, amma ai gani nake ko mahaukaci idan ba a kula shi ba bazai yi hauka ba.”

Shiru ta yi, tasan yana cikin fushi ne kuma ya bayyana a cikin muryarsa. 

“Ka yi haƙuri Honey, bazan sake ba.”

“Allah Ya sa.”
Ya faɗa tare da tashi ya shiga wanka, yana shiga itama ta tashi ta fita, saboda Ashraf irin mazajen nan ne masu kunya matuƙa, yana matuƙar jin kunyar jikinsa, shi ka ɗai ba ya iya tsayawa dole sai ya ɗaura towel, bare kuma da wani. Ba yanda Jamila ba ta yi ba mussaman farkon aurensu a kan su dinga wanka tare, amma ya ce shi ba zai iya ba, tun da suke da ita bata taɓa ganinsa a wani yanayi ba idan ba da kaya cikakku ba, idan ma ta ganshi babu riga baifi a ƙirga ba, yana ganin mutuncin kansa sosai, shi ya sa ko itama baya taɓa bari ta fito daga toilet a gabansa. 

Abun yana matuƙar ciwa Jamila tuwo a ƙwarya, ko yanzu da ta fito sai da ta yi ƙwafa, ita macece mai matuƙar ƙaunar soyayya da kulawar namiji, bata ƙi su yini tun safe har dare tana manne da shi ba, amma shi gaba ɗaya ba haka yake ba. 

Lokacin da ta fito Husna na tsaye a falon, Aisha kuma na zaune kan kujera hannunta wayar Jamila ce tana dannawa, Jamila na fitowa Aisha ta ce.
“Anty, ga Amrah ta kira ki.”
Tsaki Jamila taja, sannna ta ce.
“Ƙyalen ‘yar mitsiyata.”
Wani ƙululin takaici ya tsayawa Husna a rai, wai su me suke ɗaukan kansu ne, kowa talaka kowa mitsiyaci, Allah Ya kyauta. 

Sai da ya shafe kusan mintu talatin sannan ya fito daga ɗakin, har lokacin Husna na tsaye inda take, Jamila kuma ta shiga ɗaki ta sake shiryawa, yana fitowa ya nufi wajen dinning yana faɗin. 
“Jamsyna, na gama.”
Tasowa ta yi itama, ranta fari sol ta san ya huce daga fushin da yake, daman bai da dogon fushi shi, yana shirin zamane ya yi ido biyu da Husna, a take ya haɗe rai sannnan ya ce. 
“Zaki shiga ki mayar da wannan koɗaɗɗiyar jakar ko sai na yi tamole da ke.”
Turo baki Husna ta yi gaba, tana gunguni ta ce.
“Koɗaɗɗiyar amma tafi zuciyarka kyan gani.”
Ɗauka ta yi zata shiga ɗakin, ya ce. 
“Saura sai na ce miki ki fito.” 
Banza ta yi da shi ta shige ɗaki, ita a kan abinci ma sai an ce mata ta fito ta ci, ashe ma ba dan ta ci take rayuwa ba, ita yanzu tana da wani abu ma da ya wuce ta ci abinci ta kwanta, ai yanzu abinci ne burinta a rayuwa. 

Tana ajiyewa ta ɗauki hijab ta sanya ta fito, amma kafin ta fito duk sun zauna a kan dinning ɗin har da Aisha ma sun fara cin abincin, taɓe baki Husna ta yi daga inda take, a hankali ta tako kamar wata ta Allah, bayan ta zauna ma ta ce. 
“Anty Jamila ina yini? Aisha ya kike, Yaya Ashraf an dawo lafiya?”
Dukkansu wani irin kallo suka yi mata, shi Ashraf kallon anya baki da aljanu yake mata, ita kuwa Jamila kallon wannan wane irin rainin hankali ne take mata, ita kuwa Aisha kallon kin ɗebu aljanu a munjibir take mata. 

Ganin duk sun bita da ido ne ya sa ta ce.
“Zan sami abincin Anty?”

“Ki zuba da kanki mana.”
Jamila ta faɗa tana hararata, Husna kam ta zuba abincin hankalinta kwance ta fara ci, sai da ta ci wanda ya isheta sannan ta miƙe tsaye ta bar wajen ta yi cikin ɗaki, so ta yi ta musu aljanun ƙarya ko zata sami dama ta yi wa Ashraf ɗan iskan duka ko zata wuce takaicin abin da ya yi mata, sai dai kuma gaba ɗaya bata jindaɗin jikinta, sabida faɗan da ta sha. 

Allah Yaso ta yi sallah, sai kawai ta kwanta abunta, a can kuwa bayan sun gama cin abincin Aisha ta kwashe su zuwa kicin, sannan itama ta tafi ɗakin Jamila ta kwanta, Jamila kuma tabi mijinta ɗakinsa, kamar ko yaushe hasken ɗakinsa a kashe yake, haka ta shiga ranta a ɓace. 

Tun daga wannan ranar Jamila ko Aisha babu wanda ya sake tanka Husna, itama kuma babu wanda take tankawa tana rayuwarta daban suma suna tasu daban, amma duk da haka Jamila a wuya take da ita, a tsakanin Husna da Ashraf kam basa haɗuwa sai wajen cin abinci, daman magana bata haɗa su sai wani abu ya faru, to zaman lafiya take da kowa ma cikin gidan babu abin da ya haɗa bare ya mata magana, ta manta da shi gaba ɗaya shima haka. 

Husna dai tun da tazo gidan kaya ɗaya take sawa gashi har yau kwananta huɗu duk bata canja ba, tun da ita dai ba datti suke yi ba daga ɗaki sai ɗaki, tana dai canja na ciki wando da bra amma na saman dai ta ce ba zata canja ba dan ita ba ahalili mubazzarina ba ce. 

Jamila duk da babu ruwanta da Husna, amma ta kula da kayan jikinta bata canja su, duk sai ya haifar mata da ƙyanƙyami, gaba ɗaya da taga Husna sai ta fara tashin zuciya, duk abun ya isheta. Duk da bata wari ko tashi da alama tana wanka kawai kayan ne ba zata canja ba. Jamila ta so ta yi banza da ita amma abun ya tsaya mata a rai, ita wannan ƙazantar har ina, gaskiyya bada ita ba wallahi. 

Daren ranar suna zaune a dinning suna ci abincin dare, Jamila ta ce.
“Ni kam Husna dan Allah ki samu ki canja waɗanann kayan, tun da kika zo fa su ne a jikinki, idan ma kin canja ina ga sau ɗaya ne.”
Wani irin abu Ashraf ya ji, wanne wace irin ƙazanta ce haka Husna ke yi, kaya kala ɗaya shi kwata kwata bai kula ba tun da ba wai ganinta yake yi ba, amma tun da Jamila ta faɗa haka ne, tura baki Husna ta yi gaba, sannan ta ce.

“Su kaɗai gareni.”

“Su ka ɗai kuma? Gaskiyya bazan ɗauki wannna ƙazantar ba, kina min amfani da kayana da ƙazanta a jikinki, wallahi da na ganki zuciyata zata fara tashi, kina shiga haƙƙina.”

Jamila ta faɗa ranta idan ya yi dubu ya ɓaci, Husna kam ko a jikinta, wallahi babu wanda zai sanya ta ta yi asara kayanta, kaya kwata kwata basa datti ita kuma sai ta cire su, wallahi a’a, tun da ba a kanta take zaune ba idan taso ta kalleta, idan bata so ba ta ɗauki ido. 
“Na ce miki su kaɗai gareni.”
Husna ta sake faɗa, ɗaga idanu ya yi ya kalleta yanda take wani hura hanci, a cikin ransa ya ce. 
“Wannan yarinyar ta zama annoba.”
A fili kuma shiru ya yi yana ci gaba da abin da yake, Jamila ta ce.
“Honey, please ka mata magana ni dai ta daina zamar min da dauɗa.”
Kafin ya yi magana Husna ta ce.
“Wai da dauɗa kike gani na? Ko kin ji ina tashi ne, kayane su kaɗai gareni, idan kuma naki zaki ban sai ki ban.”

“Tun da ta ce ba zata canja ba sai ki barta, yarinyar da bata yi karatu ba me za ta sani mai kyau da mara kyau.”

Ashraf ya faɗa ransa yana ɓaci da tunawar da ya yi bata karatu amma iyayenta suka barta, tashi Jamila ta yi ya shiga cikin ɗakinta, ‘yan mintuna kaɗan sai gata ta fito da kaya a hannunta wajenta set uku, tana zuwa ta watsawa Husna a jikinta, rai a ɓace ta ce.
“Tun da baki da su ga su nan, amma wallahi duk jahilcin ki bazaki zauna min da dauɗa ba.”

“Jahici.” Husna ta maimaita, ta kalli Asharf da ya mayar da hankali a kan abincinsa kamar bai san me ake ba, Aisha ma hankalinta na kan abinci.
‘Zaki ga Jahilci.’ 
Husna ta faɗa tana tattare kayan, sai da ta gama tattare kayan gaba ɗaya waje ɗaya ta kawo su tsakiyar falon kan kafet, ta yi wani banzan murmushi ta yi cikin kicin, sai gata ta fito da lighter da suke kunna gas da ita irin doguwar nan, ba wata wata ta kunna ta ɗaɗona ɗaya daga cikin atamfofin, sai ga wuta ta fara ci bal bal bal, kamar anzuba wani abu a ciki. 

“What!” 

Legendspen-Sayyid
***

Want the next chapter?

ui.create_a_free_arewapen_account_to_save_progress_unlock_paid_chapters_fol