Free chapter · Read without an account

20.

by ZainabShehu22 · BARA A KUFAI

*BARA A KUFAI*


20.



*BRIGHT PENS 2026.*

YOTA ID 002



Amma tana cikin yayyanka awara ta ji wayarta tana ruri, ajiye wuƙar ta yi ta zura hannu ta ɗauko a kan window, ganin mai kiran ya sa matsanancin mamaki ya kamata, ta riƙe haɓa tana ƙoƙarin tuna when last da su yi waya sannan ta ɗaga ta kara a kunne bakinta ɗauke da sallama.

"Zahra'u!" Ta ji ya ambata murya a sama maimakon amsa sallamar da ta yi masa, gabanta ne ya faɗi, ta daure ta ce. "Na'am Baban Aliyu lafiya?" 

"Ina fa lafiya kina yi wa ƴarki baƙin hali da hassada, ban da ƙyashi ɗan'uwanki ya biya mata kuɗin karatu amma ki ce ba za ta tafi ba? Ni fa irin waɗannan halayen naki ya saka na ƙaurace miki, gidadancinki ya yi yawa wallahi, mene a cikin tafiya karatu birnin tarayya in ban da ke baƙauyiya ce?" 

Takaici ne ya rufe Amma, ta kalli ƙofar ɗakin Hasina, wato ƙarar ta ta kai gurin ubanta, sai da ta sassauta ɓacin ranta sannan ta ce. "Haka ta faɗa maka ƙyashi nake yi mata?" A harzuƙe ya ce. "To mene idan ba ƙyashin ba? Yarinya ta samu abu na ci gaba kin hana, ki faɗa mini sunan hakan idan ba hassada ba?" Baki ta cize ta ce. "Baffa kenan, ai ka san babu abu makamancin wannan tsakanin mahaifiya da ƴaƴanta, duk wanda zai so ganin rayuwar Hasina ta inganta to a bayana yake, dalilin hakan ne ma ya sa nake tsoron tafiyar tata, gudun abin da zai je ya dawo."

"Malama ba wani abu da zai je ya dawo sai alkhairi, ki bar yarinya ta je ta yi karatunta, umarni nake ba ki ba neman shawara ba, kuma ban da abinki da ta gama fa aiki za ta samu, ke ma za ki mora ai."

"Ka yi haƙuri Baban Aliyu, amma hankalina sam bai kwanta da karatunta a wani gurin ba, ta zauna kawai idan tana da rabo zai samo mata wata a cikin garin nan."

"Ba zan yi haƙurin ba Zahra'u, in ke ba kya so yaran nan su yi karatu su zama wani abu ni ina so, saboda haka dole Hasina ta tafi makarantar nan a gobe, idan kuma ba haka ba a bakin aurenki!" Daga haka ya katse wayar. 

Wani abu Amma ta ji yana yawo tun daga kanta har ƙafafunta, ta sauke wayar jiki a sanyaye ta ajiye, ta ɗauki wuƙa don ci gaba da abin da take, amma hawayen da ya cika mata ido ya sa ta fara gani dishi-dishi, ganin tana yanka awarar ba daidai ba ta haƙura ta miƙe ta share hawayen da ya zubo mata. 

Hasina tana zaune tana ƙara gyara kayanta da ta shirya a cikin box Amma ta ɗaga labulen ɗakin, murya a karye ta ce. "Sai ki zuba ruwa a ƙasa ki sha, hankalinki ya kwanta kin kai ƙara ta gurin mahaifinki ya kira ni ya ci mini mutunci har da barazanar saki, saboda ya san ba ni da inda zan je, ban da gurin da ya fi gidansa, kin yi amfani da son duniya irin nasa kin ƙawata masa karatu da aikin da za ki samu bayan kin gama, shi kuma duk ya ruɗe burinsa kawai ki tafi, to ki je Hasina Allah ya ba da sa'a ya taimaka ya kare ki, amma ki sani babu wanda ya kai ni ƙaunar ki da son ganin rayuwarki ta yi kyau a kaf faɗin duniyar nan, duk abin da na hana ki ba na yi don na cutar da ke ba ne, ko da Aminu bai kai ki makaranta ba ina da wannan burin a raina, jira nake Aliyu ya kammala sai ke ma ki ƙara nema saboda ɗawainiyar kashe kuɗin, zan fi samun sauƙi idan ke kaɗai ce, amma tunda kin nace ga hanya nan, Allah ya sa karatun ya zama alkhairi a gare mu bakiɗaya." 

Baki Hasina ta zunɓura ba ta ce komai ba, wato sai ma ta jira Aliyu ya gama, a komai sai Amma ta nuna banbanci a kansu. 

Ganin ba ta da niyyar tankawa Amma ta ce. "Gobe Zakina za su gama makaranta in sha Allah, kya jira ki je ki taya shi murna kafin ki tafi dai ko?" 

"Ba inda zan je ni." 

"Amma ya ce mini kowa ana zuwar masa, shi sai ya zauna ba kowa kenan?" 

Taɓe baki Hasina ta yi ta ce. "Ni ma da wuri ake son na je makarantar, duk inda bakwai take ma na bar gidan nan." 

Da kallo kawai Amma ta bi ta ba ta sake magana ba, ita kuma ta ci gaba da haɗa kayanta cike da karsashi da farinciki. 

Duk da Amma ba ta son tafiyar amma haka ta fita ta yo mata tsince-tsincen abubuwan amfanin yau da kullum, ta ɗibar mata dakakken yaji da garin ɗanwaken da aka niƙo mata saboda dawowar Aliyu, Hasina kamar ta ce mata ta bar su don abun kunya ne a gan ta da iya wannan kayan sai kuma ta fasa ta karɓa ta adana. 

Ranar bacci rabi da rabi ta yi, asubar fari ta yi wanka ta shirya ta kwashi kayanta ta yi wa Amma sallama ta tafi inda wanda Farha ta turo ya ɗauke ta yake jiran ta, bayan ta yi wa Amma ƙaryar direban gidan Uncle Aminu ne.  Duk da ta ga yadda Amman ta tashi sukuku fuskarta cike da damuwa amma haka ta tsallake ta suka ɗau hanya. Ta waya Farha ta tura mata takardun makarantar ta ce sai sun sauka a birnin tarayya za a ba ta, ta tura mata kuɗaɗe masu kauri na shopping da sauran buƙatu, godiya sosai ta yi mata kamar za ta ari baki, don tsabar farinciki ji take kamar ta yi wa Farha kyautar rai, musamman da ta tura mata hotunan school ɗin ta ga yadda ta haɗu komai nata ya tsaru, irin makarantun da ta daɗe tana mafarkin ganin ta yi.

***** *****

Sai da Raudah ta ci kuka ta ƙoshi sannan ta wanke fuskarta ta zo ta samu Umma ta ce. "Umma don Allah magana nake son mu yi da ke, ina fata kuma za ki fahimce ni ki fuskanci inda na dosa."

"Ina jin ki uwar zance." 
Umma ta faɗa tana gyara wa Sabira kwanciya.

"Akan yawan zuwan Woman leader gidan nan ne, ni jikina bai ba ni saboda Allah ba ne gaskiya, gani nake kamar tana da wata manufar ta daban, ke kuma ga shi Umma ba ki da zurfafa binkice indai sabga ta kuɗi ce, kina ji za ki ba da amanna ɗari bisa ɗari." 

Cikin rashin damuwa Umma ta ce. "Dole ce ta saka Rauda, ni ma wasu abubuwan ba a son raina nake yi ba, to an riga an ƙaƙaba mana talauci da fatara ya zan yi? Ga ku duk mata a gabana, ga ba abinci, ba sutura ba kuɗin makaranta, dubi ɗakinmu fa, window a wangale ba murfi, lokacin zafi sauro ya cika, lokacin sanyi ya yi ta buso mu, lokacin damuna ruwa ya dinga feshi, ga yoyo ta sama, kuma duk babanku yana da hali amma ba zai gyara ba, shi ya sa nake wannan ficiccikar don ganin na inganta rayuwata da taku." Girgiza kai Raudah ta yi ta ce. "Duk da haka dai Umma ki dinga nazari kafin yanke hukunci, da kuma miƙa wa Allah lamura, kina dai ganin abin da ya faru da Aunty Zeenat, kuma irin wannan garajen ne ya janyo haka, ga Umma Lantana nan yanzu kullum sai zaman ɗaki cikin kuka, abinci ma gagarar ta ci yake, ta koma kamar taɓaɓɓiya, to mene amfanin irin wannan? Yanzu wa gari ya waya? Ni gaskiya na ajiye duk abubuwan da nake yi a baya, zan koma miƙa wa Allah lamurana kawai, shi ne mai komai da yin yadda ya so." Shiru Umma ta yi cikin nazari, duk da Raudah yarinya ce amma tana da kaifin basira da hangen nesa, a sanyaye ta sauke numfashi ta ce. "In sha Allah zan kiyaye a gaba, halin mahaifinku ne sai shi, ban da haka ai yana da abin da za mu ci mu yi sutura ya kai ku makaranta, amma....."

"Ke Karima! Yarinyar kika saka a gaba kuna zage mahaifinta da cin namansa?"

Inno da ta fito daga ɗaki kamar an jefo ta ta katse ta da faɗin haka cikin kanbabawa tana tafa hannaye.

A tsorace Umma ta marairaice ta ce. "Wallahi ba zagin shi nake yi ba, hira kawai muke yi." Harara Inno ta zabga mata ta ce. "Bari ya dawo gidan za ki maimaita a gabansa."

Yadda Umma ta yi tsuru-tsuru ne ya ɓata wa Raudah rai, kicin-kicin ta yi da fuska ta miƙe ta koma ɗaki, sai da Inno ta gama ɗiban albarkarta ta koma ɗaki sannan ta dawo ta zauna ta dubi Umma cikin takaici ta ce. "Umma wai don Allah Innon nan mala'ika ce da kike tsoron ta haka? Gaskiya ba ma jin daɗin yadda yake yi miki."

"Ni ma ba daɗin nake ji ba, ban da yadda zan yi ne kawai, auren mahaifinku shi ne gatana da rufin asirina a yanzu." Umma ta faɗa murya a karye kamar za ta fashe da kuka. 

"Ina danginki suke Umma? Ba ki taɓa zuwa da mu ba, wani naki bai taɓa zuwa mun gan shi ba, na san har da hakan ya saka kowa ya mayar da ke bolar zuba shararsa a gidan nan." 

Ɗibibicewa Umma ta yi ta fara kame-kame, don wannan ne karon farko da ƴaƴan nata suka fara yi mata tambaya makamanciyar wannan. 

"Amm.... Ai... Ai... Na sha faɗa muku, mu ba ƴan asalin ƙasar nan ba ne, shi ya sa." 

"To ko ina ne ai za mu iya zuwa Umma."

"E haka ne na sani, akwai shirin da nake za mu je nan kusa in sha Allah, ɗebo mini ruwa na shashshafa wa Sabira a jiki, na ga jikin nata ya yi zafi da yawa." Umma ta faɗi haka don son kawar da waccan maganar, sai rarraba ido take kamar shega a rabon gado ko wanda ya yi wa sarki ƙarya, har wani gumi ta faɗa haɗawa. Raudah ta miƙe tana faɗin. "Batun Aunty Ahayan, idan da hali ya kamata a bi bayansu a ce ta dawo mun haƙura da aikin, hankalina ya ƙi kwanciya wallahi." Duban ta Umma ta yi rai a haɗe ta ce. "Wai Woman leader da alkhairanta ga al'umma ne baƙon abu ko me? Kin san dai ba za ta taɓa siyar da ita ba ko? To ki rabu da ni da wannan maganar." 

"Gaskiya fa ta faɗa Umma, ni kaina yadda Matar nan take shige wa Ahayan a kwanakin nan bai kwanta mini ba." 

Hararar Ummi da ta yi maganar Umma ta yi ta ce. "Ku dai kawai kuna jin haushi don ba ku kuka samu aikin ba ne, amma babu abin da zai faru sai alkhairi in sha Allah." 

Shiru suka yi, don sun san akan sabgar samun kuɗi Umma ta yi nisa ba ta jiran kira, ko me za su ce ba za ta taɓa fahimtar su ba.

Kai wa da komowa kawai Inno take ranta a jagule, fuskarta cike da damuwa ta zare wayarta daga chaji ta bar parlourn saboda kar Husnah da ke bacci a kan kujera ta ji maganar da za ta yi, sai da ta rufu ƙofar uwarɗakinta sannan ta zauna a bakin gado ta lalubo numbern Ramlah ta kira ta, ganin har sau biyu tana kira ba ta ɗaga ba ta shiga Whatsapp da sauri ta danna mata voice.

"Laure Ina kika ajiye wayar ne ina ta kira ba ki ɗaga ba? Ina cikin tashin hankali fa, na je na zabga kuɗina a aiki amma ban ga alamar aikin ya kama yarinyar nan ba? Ga shi na kan tudu ya ƙara tabbatar mini akwai wani babban alkhairi da yake tafe a kan ta, ga Adam ga Saif sun kafa naci a kanta, na yi na yi Saif ya fita harkar yarinyar nan amma ya ƙi, abin nasa ma sai ƙara gaba yake yi, har da faɗa wa mahaifinku shi kuma ya kira ni ɗazu wai na bar yaro ya auri wadda yake so, na ce masa ko mata sun ƙare wallahi Saif ba zai auri Ahayan ba, yarinyar da na tsana wadda ba a san asalinta ba, ga abin da boka ya faɗa mini a kanta na irin illar da da za ta zamo ga cikar babban burina, ni yanzu so nake kawai Yaya ya kore ta daga gidan nan, ta ƙara gaba ta je duk inda za ta, in ma har da uwar ne duk su rankaya, na haƙura da bautar da take yi mini, zan ɗauki mai aiki kawai." 

Ta danna ya tafi, ganin ya yi tik biyu sai ta tsaya ko za ta duba ta ba ta amsa nan take, don a ƙagauce take da neman shawarar yadda za ta yi. Bayan wasu mintuna kiran Ramlah ya shigo, da rawar jiki ta ɗaga ta kara a kunne. 

Ba gaisuwa ba komai Ramlah ta fara magana da faɗin. "Kar ki kore ta daga gidan nan Inno, kin san abin da aka ce mana tun farkon zuwanta gidan, yarinyar nan akwai wani abu a tattare da ita, kuma duk ranar da ta bar gidan ƙullika da dama da muka yi za su warware, kar idonki ya kulle ki manta wannan, ita ɗin garkuwa ce a gare mu."

"Garkuwar uban me? Wace ce ita? Ko aljana ce ai sai haka? Ni na gaji wallahi, ina da plans da yawa a gabana amma yarinya ta zo ta hana ni rawar gaban hantsi, kin san burina akan Adam da aikin da nake yi a kansa, hankalina ba zai taɓa kwanciya ba in ba gani na yi wannan uwar tarin dukiyar tasa ta zama mallakina ba." 

"Na sani Inno, amma duk da haka ki ƙara haƙuri, wallahi na fi ki tsanar yarinyar nan, amma sanin amfanin zamanta a tare da mu ya saka nake daurewa, tunda ba a bakin boka ɗaya ba ba biyu ba duk inda muka je sai an faɗa mana, ina nan zan zo a cikin satin nan, sai mu ƙara tattaunawa." 

Ba don Inno ta so ba ta ce. "Shikenan sai kin zo ɗin, ya jikin sirikin naki?" Ramlah ta ce. "Da sauƙi, ana ta samun ci gaba ai." 

"Allah ya ƙara sauƙi, ki gaishe da Juraij ɗin." Daga haka ta katse wayar ta cillar a kan gado, tunda aka faɗa mata Abba Adam yana da tarin dukiyar da ba su san da ita ba a yawon bin malamanta hankalinta ya tashi, ta ji ba ta da wani buri sama da ta kawar da shi ta mallaki dukiyar ko ta halin ƙaƙa, sama da wasu shekaru tana fama amma har yanzu abu ya ci tura.

A ɓangaren Ramlah ma dafe kai ta yi saboda abubuwa da suke ƙoƙarin jagule mata, wanda suke yi ita da Inno da wanda take yi ita kaɗai akan wani buri nata na sirri.

Fakar idon su Ummi Umma ta yi ta faɗa ɗaki, a firgice ta fara burkita ɗakin ta ƙwaƙulo wata waya a cikin shirgi ta soke a jikin zaninta ta fito daga ɗakin ta shiga banɗaki, jikinta na tsuma na saka wa wayar battery, bayan ta kunnu ta saitu ta danna wata number ta kara a kunnenta, duk da ta saka sakata amma sai waige-waige take, murya na rawa ta fara magana ƙasa-ƙasa. 

"Aikin nan fa kamar ya lalace, yarana sun fara tambayar asalina, duk da ba wannan ne matsalar ba, amma daga haka watarana za su iya tambayar abin da zai fallasa komai." Ta yi shiru na sakanni sannan ta ɗora hannunta ɗaya a kai, damuwa ta bayyana sosai a fuskarta, kamar za ta yi kuka ta ce. "Wallahi ba daga gurina ba ne, na fi tunanin daga gurinku ne." Ta ƙara yin shiru, sannan ta buɗe baki kamar za ta kurma ihu, sai kuma ta yi saurin toshe bakin, ta durƙushe a gurin tana rarraba ido cikin matsanancin tashin hankali. 

Da ƙyar ta iya saita kanta ta cire batirin wayar ta ɓoye su a jikinta ta fito tana bin bango, saboda yunwa da kaɗuwa da suka haifar mata da wani irin jiri, kuka ne yake son ƙwace mata amma ta daure don ba ta san amsar dalilinsa da za ta bayar idan su Raudah suka tambaye ta ba.

***** *****

Yau rana ce ta musamman da farinciki kamar yadda yake ga duk wani ɗalibi da ya kammala karatu, department ɗin su Aliyu gabaɗaya ya ɗume da hidimar graduation, kowa yana cikin farinciki da annashuwa, tun kafin su shiga last paper amma har sun fara hotuna, kasancewar sai 2 suke da exam ɗin ya saka suka sassaka rigunan da suka yi mai ɗauke da sunayensu da na  department. 

Aliyu yana tsaye yana ɗaukar su Auwal hoto fuskarsa cike da walwala, ya yi kyau sosai a cikin kayan, a bayan rigarsa da gaban hular kansa an rubuta ZAKI, taɓa shi ya ji an yi da abu, ya juya ya ga wata yarinya ce Kaltum ƴar class ɗinsu, tana sakar masa murmushi ta miƙa masa makar hannunta ta ce. "Ka yi mini sing out." Kallon ƙasan farar rigarta da take ɗago masa ya yi ya ce. "Kin ga ina yi wa mata ne?" A shagwaɓe ta ce. "Ni dai sai ka mun, Ƙwaro guda idan ba ka mun ba me aka yi kenan?" 

"To ki dai yi haƙuri, idan Mum ta samu labari na yi miki za ta mun bulala." 

Yadda ya yi maganar sai ya ba ta dariya, ta karɓi makar tana faɗin. "Tunda ka sako Mum a zancen na haƙura, amma mu je a yi mana hoto da wayata." Bai musa ba ya je aka yi musu su Auwal suna tsokanar shi, don kowa a class ɗinsu ya san yadda Kaltum take shishshshige masa, shi kuma ganin yanayinta yar masu hannu da shuni ce ya sa yake yin baya-baya da ita, don da ma ba ya shiga sabgar mata, tsakaninsa da su gaisuwa ce kawai sai kuma koya musu karatu. 

"Me ya sa ka saka Zaki maimakon Ƙwaro da kowa ya san ka da shi? Da ƙyar na gano ka fa, saboda ina ta duba bayan rigar mutane ina neman inda zan ga Ƙwaro." 

Murmushi ya yi mata ya ce. "Ƙwaro ai ba sunana ba ne, a nan na tsince shi ana kira na da shi, ni ba ma so nake ba don kaina bai kai na ƙwarin ba, ba yadda zan yi ne kawai tunda kun ƙaƙaba mini, Zaki kuma Mamana ce take kira na da shi, ina jin daɗin sunan kuma sosai da sosai, shi ya sa na saka shi." 

"Kana son Mum da yawa, to ka shirya don na kusa ƙwace maka ita, da ma ni ban da ita, ka ga sai ka bar mini kawai." 

"Ayya, Allah ya gafarta mata." Ya faɗa a sanyaye cikin tausayin ta, don shi ko tunawa ya yi Amma za ta iya mutuwa ta bar shi sai ƙirjinsa ya doka, bare kuma a ce yana rayuwa babu ita ai bai san halin da zai shiga ba duk da komai na Allah ne kuma shi ne mai yin komai a lokacin da ya so, ya san mutuwa dole ce, amma yana fata da addu'ar su rayu tsawon lokaci a tare. 

***** *****

Juraij ne tsaye a gaban DD a office ɗinsa yana sauraren bayanin da yake yi masa akan wani bincike da suke gudanarwa na wata yarinya da aka kama ɗaure da bamabamai. Tsare shi ya yi da ido bayan ya kammala ya ce. "Amma Sir me ya sa aka mayar da case ɗin hannun police bayan mu ya fi dacewa mu gudanar da bincike a kansa?" Da mamaki DD ya ce. "Duk bayanin da na yi ba ka fahimta ba kenan?" 

"Na fahimta, hujjar da suka bayar ce kawai ba ta kwanta mini ba Sir." 

"No AD sun zo da point mai ma'ana da ya cancanci mu bar musu aikin nan, so ka bar batun kawai." 

"Ok Sir." Ya faɗa tare da ɗan sara masa sannan ya fice daga office ɗin, ba don ya bar batun kamar yadda ya buƙata ba, sai don kawai ba ya son Jan maganar. 

Daga nan Family house ɗin su Daddy ya nufa saboda rasuwar wata ƙanwar Daddy da suka wayi gari da ita, ya je an yi jana'iza da shi amma bai zauna ba saboda bin ba'asin wannan case ɗin. Bayan ya yi parking ya fito ya nufi inda tarin mutane ƴan zaman makoki suke, ya zauna ya ƙara yi wa ƙannen Daddy maza gaisuwa, suka amsa ciki-ciki, bai jima ba ya miƙe ya nufi cikin gidan, da sauri su Kawu suka mara masa baya, ɗakin da ya san zai samu Dadah ya wuce direct, tana zaune ta miƙe ƙafafunta ƴar autarta tana shafa mata man zafi, sai da ya ƙarasa har kusa da ita ya zauna sannan ya gaisar da mutanen ɗakin. 

"Sannu Dadah, ya ƙarin haƙuri?" Ya faɗa a taushashe. 

Cikin muryar da take nuna mamallakinta ya ci kuka ya ƙoshi tsohuwar ta ce. "Haƙuri Alhamdulillah, Sa'adatu ta tafi daga yin jinyar kwanaki ƙalilan." Hannunta ya kama ganin tana ƙoƙarin sake fashewa da kuka ya ce. "Allah ya ji ƙan ta ya yi mata rahama, ki yi haƙuri da kukan nan haka, kin san ke ma ba lafiya gare ki ba, kar ciwonki ya tashi."

"Ka damu da ita da lafiyar tata ne?" Kawu Munzali ya faɗa a harzuƙe, ɗaga kai ya yi ya kalle su suna ƙarasowa cikin ɗakin, hakan ya sa matan ciki suka miƙe suka fice, aka bar iya Dadah da ƴaƴanta da Juraij kaɗai.

Dadah tana hawaye ta dube su ta ce. "Mene ne haka? a ranar mutuwar ƴar'uwar taku ma ba za ku yi abin ƙwarai ba? Yaron nan fa jininku ne, babansa Yayanku ne uba ɗaya." 

"Dadah don Allah ki bar mu da shi, ba shi tsegera ba, yana taƙama da dukiyar ubansa yana yi wa mutane gadara da firfita, yaushe rabon shi da gidan nan? Ko da ba ke kika haifi ubansa ba amma ai kin riƙe shi, ya dace ya banzarta da ke haka? Sai yau zai kwaso jiki ya zo mana, To ba ma buƙatar shi, ya tashi ya fice ya bar mana gida." 

Dadah ta ce. "Ni dai bana son wannan maganganun na faɗa muku, da ciwon ubansa da ya ƙi ci ya ƙi ƙarewa zai ji ko da me? Daidai gwargwado yaron nan yana ƙoƙarinsa iya yinsa." A zuciye Kasu Munzali ya ce. "Wanne ƙoƙarin yake yi Dadah? Ya janye ubansa sun koma gefe, dubiya fa idan muka je shegiyar matarsa ba ta bari mu gan shi saboda ya gama hure mata kunne da mummunar huɗuba a kanmu, don yana tunanin asiri aka yi wa ubansa sai ya haɗa har da mu jininsa a zargin? To ba ma buƙatar shi kamar yadda ya nuna ba ya buƙatarmu a lamaransa da ubansa, ka hana mu yin jinyar shi da zuwa dubansa mu ma ka tashi ka ba mu guri!" Ya ƙarashe zancen yana wurga wa Juraij mugun kallo. 

Aunty Rakiya da ita kaɗai ta rage mace a cikinsu yanzu ta ce. "Tsabar rashin muhimmancinmu ai ko gaisuwar da kowa ya zo tun safe shi sai yanzu ya zo, to ba dai a sauya wa tuwo suna, duk abinka mu ne dangin ubanka." 

Juraij dai ko nuna ya san da shi suke bai yi ba, sai ma wayarsa da ya zaro ya shiga latsawa, hakan ya ƙara tunzara su, suka dinga amayar masa da abin da yake ransu, sai da Dadah ta fashe da kuka sannan suka yi shiru, ya miƙe ba tare da ya ce musu ƙala ba ya yi mata sallama ya fice, ta raka shi da addu'a tare da ban haƙuri akan abin da su Kawu suka yi masa. 

Yana fita ta share hawaye ta ce. "Na rasa sau nawa zan faɗa muku ku daina yi wa yaron nan haka amma kun ƙi, shi fa yaƙi ɗan zanba ne, amma sai ku yi ta abu kamar gidadawan ƙauye." 

"Dada abin ne yake damun mu da ci mana rai, yaron nan mugun taƙadiri ne, ya yi kane-kane ya tokare duk wata kafa da za mu ci dukiyar ubansa." 

A ƙule Kawu Falalu ya ce. "Shege kamar ya san shirinmu, ya bar mu mun yi jinyar shi ma ya ƙi, ya gwammace shi da matarsa su yi ta fama su kaɗai, da yana hannunmu da ba tuni mun gama wawusar abin da za mu wawasa ba." Cikin ƙasa da murya Dadah ta ce. "To idan ba za ku iya lamarin nan cikin makirci ba ku bar mini komai a hannuna, saboda wannan abubuwan da kuke yi ne ya sa yake ƙara jan baya da mu, ga shi ni ba ƙafa ba bare na dinga zuwa gidan nasu, duk abinsa dai ai bai isa ya hana ni ganin uban nasa ba." Miƙewa Kawu Munzali ya yi ya ce. "Abun ne da takaici, shi ya sa idan muka gan shi ba ma iya dannewa." Dadah ta ce. "To ku koma gurin zaman makokin dai yanzu kar hankali ya dawo kanmu, daga baya ma ƙarasa tattaunawa, ina fama da damuwar rashin ƴata kun zo kun saka ni magana, saura kuma in kun fita kun gan shi ku ƙara yi masa wata maganar mara ɗaɗi."



***** *****


A motar Women leader Ahayan ta yi shiru tana tunanin rayuwarta ta baya, har suka ƙarasa inda za su je ba ta sani ba, sai da ta taɓa ta sannan ta sauke numfashi ta dube ta.

"Tunanin me kike yi haka Ahayan? Kar ki bari tun kina ƴar ƙaramarki ki ɓaci da zurfafa tunani, don yana da illa sosai hakan." 

Jinjina mata kai ta yi saboda wani iri take jin ta, kamar wadda ƙwai ya fashewa a ciki haka ta buɗe murfin motar ta fita ta fara bin harabar gurin da kallo, a nan ta gane asibiti ne.

Gefe Woman leader ta koma ta yi wa Gaye message, bayan ya yi mata reply ta dawo ta damƙi hannun Ahayan cikin dokawar ƙirji, don ita kanta a tsoarace take da abin da za su aikata, tana murmushin yaƙe ta ce. "Kin san sabgar rabon maganin duk ta asibiti ce,  shi ya sa ake training ɗin a nan, mu ƙarasa gurin kar su tashi, duk da yanzu muka yi chat suka sanar mini ba su tashi ba amma sun kusa." Ahayan ta ce. "To Aunty, na gode sosai da sosai Allah ya saka da alkhairi." Yaƙe kawai Woman leader ta yi suka fara tafiya, duk da rana ce amma asibitin da mutane saboda na gwamnati ne, sun yi tafiya mai ɗan nisa sannan suka tsaya, Women leader ta yi wayar da Ahayan ba ta ji me ta ce ba sannan ta ƙara jan hannunta suka shiga wani corridor bayan ta saka baƙin facemaks a fuskarta ta janyo rolling ɗin kanta ya rufe har girarta, idanunta ne kawai a waje, su ma suna cikin baƙin glasses.

"Akwai wani a gurin nan da bana son ya gane ni ne, takura mini zai yi saboda na yi masa alƙawarin wani aiki." Woman leader ta faɗa saboda kawar da zargi daga zuciyar Ahayan.


A bakin barandar gurin mata ne a zazzaune suna hira, wata ƙofa suka nufa wani security ya tare su ya hana su shiga, sai a lokacin Women leader ta saki hannun Ahayan, ta janyo ta gabaɗaya ta dawo gabanta, ba tare da ta bi ta kan security da yake yi musu magana ba ta danna wani abu da yake saƙale a hannunta kamar agogo, wata ƙara ta bayyana, ba zato kawai sai ganin wasu zaratan maza su Ahayan suka yi suna shishshigowa, fuskokinsu a rufe hannayensu ɗauke da bindigu sun zagaye gurin. 


Saurin juyawa Ahayan ta yi idanunta duka a waje kamar za su faɗo ƙasa amma Women leader ta tura ta cikin ɗakin ta ƙarfin tsiya, bayan ɗaya daga cikin mutanen ya harɓi security ɗin a ƙafa. A firgice nurses ɗin da suke cikin nursery ɗin suka dubi ƙofa, wata da take ba wa wani jariri allura ta kusa yar da shi saboda kaɗuwa. 


Bango wata farar Nurse ta fara bi kamar za ta shige cikinsa, jikinta na rawa ta ce. "Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un! Mun shiga uku! Su waye ku? Me za ku yi...." Bindigar da aka shuna mata ya sa ta yin shiru ta sunkuyar da kanta ƙasa, ilahirin jikinta na rawa cikin matuƙar firgici. 


"Ki bi duk cikin infant incubators ɗin nan ki ɗauko jariran ciki ɗaya bayan ɗaya ki ba wa mutanen nan, idan ba haka ba wallahi za su kashe ki."
Women leader ta raɗa wa Ahayan haka a hankali wadda ta yi suman tsaye.


Ba ta ko motsa ba sai bin gurin kawai take da idanunta da suka yo waje kamar za su faɗo ƙasa, wata irin rawa jikinta yake kamar an jona mata shocking, sautin harbin da ya sake tashi ne ya ƙara firgita ta, ta runtse ido wani lokaci da ya shuɗe yana dawo mata cikin kai, daga inda Woman leader take tana jiyo sautin bugun zuciyarta. Ganin tana ɓata musu lokaci Woman leader ta ƙarasa ta fara ɗauko jariran, nurses ɗin da aka yi pointing ɗinsu da bindiga suna kallon ta cikin kyarmar jiki har ta yi ta gama ta tisa ƙeyar Ahayan suka fice daga nursery ɗin. Gabaɗaya gurin ya turniƙe da wani irin hayaƙi da mutanen Gaye suka saki, a wata mota daban da ke bakin gurin aka cusa su, direban ya ja ta da mugun gudu suka bar asibitin, har lokacin ƙarar sautin harbe-harbe bai daina tashi ba, gabaɗaya mutanen asibitin sun ruɗe, sai iface-iface da guje-guje kawai ake, ga masu bindigar suna da uban yawa sai ƙara tururuwar ficewa suke. 

Doguwar ajiyar zuciya Women leader ta sauke bayan sun bar area ɗin gabaɗaya, ita kanta ba ta san mutanen da Gaye ya ce mata za a turo su yi aikin tare za su kai yawan haka ba, zufar da ta tarar mata a fuska ta goge ta saki numfashin da ya maƙale mata saboda tsoro, ba ta taɓa aikata wani abu irin wannan ba duk taƙadirancinta shi ya sa duk ta firgice. Taɓa Ahayan ta yi ganin tunda suka hau motar kanta yake duƙe, sai ta ga ta faɗa gefe sharaf, jikinta ya shika kamar babu numfashi a jikinta.



***** *****


Ƙarfe biyu da mintuna su Aliyu suka shiga ɗakin jarrabawa, bayan an rarraba su an ba su question paper da booklet sun fara answering Dr. Dubiya ta shigo hall ɗin, yana can ya duƙufa rubutu bai sani ba sai da ya ɗago saboda wani abokinsa da ya taɓo shi da ƙafarsa sannan ya gan ta tana bin students tana invigilating, gabansa ne ya yanke ya faɗi, saurin mayar da kansa ƙasa ya yi yana ambaton sunan Allah, kasa ci gaba da rubutun ya yi, ya tsaya kawai yana kallon papern hannunsa, tana ƙarasowa inda yake bugun zuciyarsa ya sauya, jikinsa ya fara ƴar rawa amma bai yarda ya ɗago ya kalle ta ba, yadda ta yi wa kowa haka ta yi masa, ta ɗan bubbuɗe booklet ɗinsa ta duba. 

A hankali ya ga ta ware hannunta, wata ƴar takarda ƙarama mai ɗauke da mitsi-mitsin rubutu ta bayyana a kan tafinta, kamar mai duba abu haka ta ranƙwafo daidai saitin kunnensa ta fara magana yadda shi kaɗai zai ji ta.

"Ka amince da buƙatata a yanzu ko kuma na tara maka Malaman can na sanar musu a cikin answer sheet ɗinka na samu wannan, ka san ko za ka haɗiyi alƙur'ani ba za ka taɓa fita ba, kuma ka fi ni sanin hukuncin malpractice." 

Idanunsa ya zuba mata, a raunane ya ce. "Ki ji tsoron Allah, kar ki yi sanadiyyar ɓata shekarun da na shafe a banza da asarar kuɗin da mahaifiyata ta kashe mini a wannan karatun."

"Ba iya asarar kuɗin za ku yi kawai ba, har da rasa juna kai da mahaifiyar taka." 

Da mamaki ya dube ta, ta kanne masa ido sannan ta zaro wani ɗan abu mai kamar shape ɗin waya a jakarta ta saita masa a ido, hoton hannunta ne da wannan papern a jiki, sai kuma na gurin da ya rubuta reg. Number ɗinsa, ta danna wani guri a jikin abun, videon shi gabaɗaya a yanzu da na hannunta da papern ya sake bayyana. Janye abun ta yi daga fuskarsa ta ce. "Evidence, saboda za ka iya nuna ka amince mini a yanzu bayan kun gama exam ɗin kuma ka bujire, ka ga ni kuma a lokacin sai na kai wannan gurin Malaman department ɗinku, hukuncin kora ya tabbata a kanka, don haka kafin result ɗinku ya fito ka zo mu yi komai mu gama, idan kuma ka shirya asarar kwalinka ne to ƙofa a buɗe take." 

Kasancewar tsilla-tsilla aka raba su suna nesa da juna shi ya sa babu wanda ya san abin da suke cewa, invigilators kuma ganin ta a wurin sai suka tafi wasu guraren suka tsaitsaya. 

Bai san lokacin da biron hannunsa ya zame ba sai jin ƙarar faɗuwar shi ya yi a ƙasa, ya zura mata ido kawai cikin maɗaukakin tashin hankali amma ko motsi ya kasa yi, wata irin juyawa kansa yake yi masa, wani abu kamar yaji ya ji yana zagayawa a ƙirjinsa, a yadda lecturers suke da zafafawa da jiran ƙiris a kama exam malpractice ya san ya gama shiga tarkon Dr. Dubiya, don tana nuna wannan videon ko bayan sun fita daga exam ɗin ne indai result bai fito ba sai an kore shi, tunda ga shaida nan ƙuru-kuru kuma bai san me ta kitsa faɗa musu ba. 

Bai gama fita daga wannan ruɗin ba ta ƙara haska masa abin ɗazu, ya kalla na wasu sakanni, a gigice ya murza idanunsa saboda abin da ya yi tozali da shi, amma abin da ya gani still shi yake bayyanar masa, Amma! Fuskar Amma ce ya fara gani, sai kuma videon ya fara ƙanƙancewa kamar ana yin baya da shi, gabaɗayanta ta bayyana a wani guri da bai san ina ba ne, an ɗaure ta, kamar ba ta cikin hayyacinta don kanta ya karye gefe. Wani murmushin mugunta Dr. Dubiya ta sakar masa bayan ta janye abun ta damƙe shi a cikin hannunta ta ce. "Rayuwar mahaifiyarka ko yin abin da nake so." 

"Noooo!" Aliyu ya faɗa cikin ƙaraji tare da buga desk ɗin gabansa a haukace, hakan ya janyo hankulan gabaɗaya mutanen cikin hall ɗin kansu.



***** *****


Hasina tana ta baza idon ganin sun isa airport amma ta ga sai tafiya suke yi kamar za su bar garin, ta yi zuru ita kaɗai a bayan mota tana kallon ikon Allah, a haka bacci ya ɗauke ta ba ta sani ba, sai farkawa ta yi ta ga rana ta yi sosai amma still suna ci gaba da tafiya. Kallon direban ta yi da mamaki ta ce. "Bawan Allah ka san inda za ka kai ni kuwa? Ya na gan mu kamar a daji kuma har yanzu tafiya muke?" Ta yi maganar gabanta na faɗuwa tana bin inda suke da kallo. 

"E Hajiya ai su a bayan gari inda suke hawa jirgi in za su yi tafiya yake, private jet ne, a cikin shi za ki je birnin tarayyar." 

Ajiyar zuciya ta sauke ta ɗauki wayarta a jaka ta kira Farha, sai dai babu network a gurin wayar ba ta shiga ba. 

Sai bayan Azhar suka ƙarasa cikin gari mai ɗauke da manyan gidaje, amma gurin tsit kamar babu halittu masu rayuwa a cikinsa, a ƙofar wani ƙaton gida mai hawa-hawa ya tsaya, ya sauka ya buɗe get ɗin sannan ya dawo ya shigar da motar ya ƙara fitowa ya rufe, da kansa ya buɗe wa Hasina ƙofa yana faɗin. "Madam za ki huta a nan gidan kafin anjima mu ƙarasa inda za ki hau jet ɗin." Cikin al'ajabi Hasina ta ce. "Me ya sa sai anjima? Ni da wannan doguwar tafiyar ai da birnin tarayyar ma ka kai ni a motar kawai." Cikin girmama ya ce. "Muna cikin garinmu fa, ba wani nisa ba ne daga nan zuwa gida, kawai titi ne ba kyau shi ya sa muka daɗe." A gajiye Hasina ta fito ta ƙara kiran layin Farha, yana shiga ta ɗaga, a shagwaɓe ta fara yi mata ƙorafi, rarrashin ta Farha ta yi ta ce mata an samu matsala da Flight ɗin tafiyarsu ne, amma anjima zai ɗauke ta ya kai ta inda za su tafi, ita kaɗai ma ba cikin cunkuso ba. Kanta ne ya ƙara fasuwa, ta fara tafiya cikin yanga shi kuma ya biyo ta janye da trolly ɗinta. Sai da suka zo entrance na gidan ne ya koma gaba ta bi shi a baya, wani dogon corridor mai ɗauke da ɗakuna suka wuce, ya sa key ya buɗe wata ƙofa suka shiga wani ƙaton parlour.

"Wow!" Hasinah ta faɗa a bayyane tana bin ko'ina da kallo. 

Bedroom ya nuna mata ya ce. "Madam ga ɗaki nan ki shiga ki huta a buɗe yake." 

"Ok." Ta faɗa a yanƙwane. 

Bayan ta shiga ta ajiye mayafi da wayarta ta yi alwala ta fito ta daidaici gabas ta yi Sallah, kafin ta idar ya kawo mata abinci, ko lazimi ba ta yi ba ta janyo abincin ta fara zaƙa saboda azababbiyar yunwar da take ji. Sai da ta cika cikinta sannan ta ajiye ragowar ta sha ruwa. Sai a lokacin ta fara bin ɗakin da kallo, daga gani an kwana biyu ba a shige shi ba, don ya yi ƴar ƙura amma babu datti sosai. Gado ta karkaɗe ta hau ta kishingiɗa tana latsa waya, ta yi mamakin rashin ganin missed call ɗin Amma, amma ita ba ta yi tunanin kiran ta ba ta ci gaba da chat ɗinta.

Ba zato ta ji an buɗe ƙofa an shigo, ta ɗaga kai tare da ƙoƙarin tashi bayan ta ajiye wayarta, wani ƙaƙƙarfar mutum ta gani ba wanda ya kawo ta ba, ido ta zura masa tare da buɗe baki za ta yi magana, ya yi saurin katse ta ta hanyar saita mata bindiga. Zaro ido ta yi a ɗimauce ta ce. "Wayyo Allah Na shiga uku! Wayyo Ammata! Wane ne k...."

"Shiiiiii" Ya katse ta yana ɗora yatsansa a bakinsa. 

Ja baya ta fara yi cikin kakkarwar jiki har ta sadu da bango ta jingina tana ɗaga hannunta sama, biyo ta ya yi, hakan ya sa ta ji cikinta ya yi muguwar kaɗawa, fitsarin da ba ta san da shi ba ya fara zuba daga jikinta. 

"Don..do.. gir...man....Al... Allah ka..yi.. haƙuri...kar....ka....kashe...Ni!" Ta faɗa bakinta na wata irin kamar harshenta zai faɗo ƙasa.

"Ba abin da zan yi miki, amma idan kin bi duk abin da na umarce ki." Ya yi maganar yana ɗora mata bakin bindigar a goshinta.

***** *****

Da wani irin sukuku Saudat ta tashi yau kamar me cuta, a haka ta yi gyaran part ɗin Sauban na safe ta dawo ɗaki ta kwanta, ko kitchen ba ta je ta taya Hansai aiki ba, Sallah ce kawai ta tayar da ita. 

Da rana ta je yi masa gyaran rana ta tarar da shi tare da wani da ta fahimci abokinsa ne, suna zaune a parlour sun baje su choculate da cake suna ci, ga wani abu a kwalba da ya yi mata kamar giya suna sha, amma ba ta ga alamar buguwa a tattare da su ba kwata-kwata. 

Ranta babu daɗi ta cire hijabin jikinta ta ajiye a bakin ƙofa, tana kallon yadda abokin Sauban yake ta bin ta da ido duk da riga biyu ta haɗa a jikinta. Siririn tsaki ta ja ta shiga toilet ɗin parlourn ta kunce ɗankwalinta ta yafa ya rufe mata wuya da saman ƙirjinta, sai da ta wanke hannu kamar yadda ƙa'idarsa take sannan ta fito. Zuciyarta a jagule saboda mayen kallo da abokin yake yi mata ta gyara parlourn ta shiga bedroom, da ma ba wani datti a part ɗin, tsurfa ce kawai irin tasa sai an yi masa gyara sau uku a rana. 

"Mutumina ina ka samo wannan me uban body ɗin?"

Tsaki Sauban ya ja ya ce. "Ban sani ba, maye kawai." 

Abokin ya yi dariya ya ce. "Ba zancen maita, wallahi ta yi mini ne, raina ya biya kuma sai na mayar da yawuna." Wani mugun kallo Sauban ya yi masa ya ce. "Wannan bunkusar? Mene abin so a gurinta? Ga manyan bebs can za ka tsaya kana shirme a nan." Ya ƙara jan tsaki don bai san me ya sa ba kwai ya ji ransa ya ɓaci. Abokin ya ci gaba da koɗa Saudat da yabon ta, bai san lokacin da ya buga masa tsawa ba da faɗin. "Shut up! Ka ishe ni, ka rabu da ni da zancen nan Please bana so."

"Ba za ka gane ba ne, amma wallahi irinsu ba ƙaramin amfana ake ba, ni ka san jiki kawai nake dubawa a gurin mace, ba ruwana da muninta ko talaucinta." 

Miƙewa Sauban ya yi a hasale ya ce. "Bari na bar maka parlourn sai ka nemi da wanda za ka yi."

"Ko dai kana kwasar rabonka ne kai ma shi ya sa ba ka son na..." 

Cak ya tsaya ba tare da ya ji ƙarshen zancen ba, ya yamutsa fuska kamar ya ga kashi ya ce. "Wannan abar ɗin? Ko mata sun ƙare ko kallo ba za ta ishe ni ba bare na haɗa jikina da ita." Miƙewa abokin ya yi ya ce. "To ni ta mun, ka bar ni mu gana ba ruwanka." 

"Ba za ka zubar mini da mutunci ba wallahi, don haka tun wuri ka san inda za ka kai jarabarka, amma ba a gidan nan ba."

"E na ji, ma haɗu a wani gurin, bari na karɓi numbernta."

Daidai lokacin Saudat ta fito da moffer a hannunta, ta gan su a tsaye cirko-cirko, za ta wuce abokin ya sha gabanta yana yi mata wani kallon iskanci, haɗe rai ta yi ta sauya hanya ya ƙara shan gabanta. 

Sakin moffer hannunta ta yi cikin rawar murya ta ce. "Malam lafiya?" 

Kafin ya yi magana Sauban ya riga shi cikin fusata. "Safwan kai wanne irin maye ne wai? Ka ba ta hanya ta wuce idiot kawai."

"Ba zan ba ta ba ɗin, ina ruwanka ne?" Ya faɗa shi ma a harzuƙe. Sannan ya juya ya kamo hannun Saudat, wani irin ɓacin rai Sauban ya ji ya cika masa zuciya, da hanzari ya ƙarasa ya hankaɗe Safwan tare da dukan ƙirjinsa, cikin fusatar da shi kansa bai san dalilin ta ba, Saudat tana tsaye sai gani ta yi sun fara dambe, Safwan yana ta zagin Sauban yana ce masa sai dai in son Saudat yake, in ba haka ba akan me zai hana shi kula ta? Shi kuma sai huci yake yana ɗaukar ko me ya samu yana maka masa.

Ƙaramin abu sai ta ga ya zama babba don bugun juna suke yi sosai, gabaɗaya sai ta ruɗe don ba ta ƙaunar tashin hankali ko kaɗan, ta fara roƙon su akan su bari ganin Safwan ya yi nasarar kayar da Sauban yana ta naushin cikinsa. 

"Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un! Don girman Allah ku bari, kar ku yi wa kanku illa! Na shiga uku!" Ta faɗa cikin kuka tana ƙara matsawa kusa da su, ɗaga Sauban Safwan ya yi yana huci da haki ya zare rigar jikinsa ya cillar ya kama hannunta ya fara jan ta yana faɗin. "Kuma a gabanka zan yi duk abin da na so da ita, in ya so ka haɗiyi zuciya ka mutu." Ƙoƙarin turjewa ta fara tare da sakin kuka a gigice. Ba ta san ya aka yi ba, ta san dai ta ji ƙarar fashewar abu a ƙasa, ta ga Sauban da ba ta san lokacin da ya tashi ba ya nufo su, sai ji kawai ta yi hannunsa ya zame daga nata da ya damƙe, ya faɗi ta baya bayan ya dafe cikinsa tare da ƙwallara ƙara. Hakan ya ba ta damar ganin kwalba a maƙale a jikinsa a daidai saitin cikinsa, jini na fita ta gurin. Gigitacciyar ƙara ta saki ta yi kansa ta zare masa ƙwalba cikin rawar jiki, a daidai lokacin Suhaima da Hansai da Asabe da wasu maza ma'aikatan gidan suka shigo parlourn a ruɗe. 

"Ta kashe shi! Kisa kika yi mana a cikin gida?" Cewar Suhaima tana duban Saudat da ta ƙame ƙam a durƙushe da kwalba a hannunta, idanunta a kan Safwan da babu alamar numfashi a jikinsa. 


***** ******


Marka tana zaune a parlour a ƙasa tana kallo a TV Ramlah ta fito daga bedroom ɗinta, tana sanye da hijabi har ƙasa amma sai baza ƙamshi take, duban Marka ta yi a raine ta ce. "Samun guri, wato har kallo ma kike yi kamar da kuɗinki aka haɗa aka siya TVn?" Miƙewa Marka ta yi tana faɗin. "Na ga ba aiki ne na gama shi ne na zauna na ɗan ɗebe kewa." Baki Ramlah ta taɓe ta ce. "To ɗan fita waje, anjima kya dawo, saboda duk kin ɗumame parlon." Girgiza kai kawai Marka ta yi cikin takaici ta fita ta samu guri ta raɓe, duk da gurin inuwa ne amma hucin rana da zafinta suna ɗan buso mata. 

Upstairs Ramlah ta haura ta nufi ɗakin Daddy ta tura ƙofar ta mayar ta rufe ta jingina da ƙofar tana kallon shi. A hankali ya yaye bedsheet ɗin da yake lulluɓe a jikinsa, ya tashi zaune yana sakin ajiyar zuciya haɗe da gwauron numfashi, taku ta fara yi cikin wani irin salo, sai da ta ajiye key ɗin hannunta sannan ta ce. "Ka rame fa Dattijona kamar mai ciwon gaske." Hannunta ya kamo ya sumbata ya ce. "Ba dole ba, zama guri ɗaya kwanciyar guri ɗaya, sai idan ɗana ba ya nan ne fa nake samu na tashi na wasa jinina a jikinki na ɗan tattaka." Zama ta yi a daf da shi tare da zare hijabin jikinta ta ce. "Na manta yau ban tittilar da tawadar nan ba, kar ya dawo mu haura da shi, ka san kullum ba dare ba rana sai ya yi ta nanata mini na ba ka maganinka akan kari, ko waya muka yi da chat yana gurin aiki sai ya ƙara nanata mini." Janyo ta Daddy ya yi jikinsa ya fara ware igiyar rigar jikinta, yana jifan ta da wani irin kallo ya ce. "Kamar kuwa ya san ke ce babban maganin nawa ba." Fari ta yi masa da ido ta taya shi ƙarasa abin da ya fara, yana ƙara jan ta jikinsa ya ce. "Na yi kewar ki sosai, yau kin bar ni ba ki zo da wuri ba, ga shi ni ba abin na sauko ba, duk na bi na damu." Ba ta ba shi amsa ba sai akalar al'amarin da za ta sauya zuwa abin da yake kewar a kansa.



*Alhamdulillah! Ƙarshen BARA A KUFAI book 1 kenan wanda shi ne free, book 2 paid ne akan 1k ta wannan account ɗin. *** Opay account Zainab Abdullahi Shehu.*




*#Zeey Kumurya*
*#****

Want the next chapter?

ui.create_a_free_arewapen_account_to_save_progress_unlock_paid_chapters_fol