Free chapter 路 Read without an account
18
馃挄 NUFIN ALLAH 馃挄
By
Anisa Muhammad yahaya
Page 1锔忊儯8锔忊儯
Yau da sassafe suka tashi anata shirin tarbar su daddy, Dan daman tun shekaran jiya suka so zuwa Amman Allah bai nufa ba sai yau,
Suma su aalima sunyi hutu, abinda daman ya hana su zuwa tun last week kenan reedah ake jira suma suyi graduation dinsu suma sai su taho
Bayan sun gama gyara ko ina ne sukayi settling akan dining table zasuyi breakfast
Jalila tace
"Pookie kalla"
Ta nuna ma nabila abu a waya
"Kaiiii muna ina pixie aka Miki wannan hoton gaskiya ban yarda ba am jealous"
Ta fa蓷a tana 蓷an zun gurar kafadar Anisa
"Me ya faru" Anisan tayi maganar tana le茩a wayar hannun Jalila
Dariya ta yi tace
"To an ce muku ni din wasa ce, kuna can gurin su leema da Maryam aka mun"
"Dan rashin amana ko ki kra mu, ai kin kyauta"
"A'a fa na kira ku kuka dinga cewa gakunan zuwa hira ta muku da蓷i nikam ganin zaku 蓳ata mun lokaci ne yasa na share ku"
"Hmm ke dai kika sani yar 蓳akin hali" nabila ta fa蓷a tana hararar ta
"Eh naji din" itama tana harar ta
"Wai me yasa kin raina ni ne yarinyar nan" ta 蓷an dungure mata kai
" Wace yarinyar taki, ai kema kinsan wallahi ba yarinya 蓳ace ni ba ehe" ta fa蓷a tana wani juya ido cike da tsiwa
"To sannu 茩atuwa, wai me ake ta nuna wa ne nima inason gani" Ya Ahmad dake parlourn ya zagayo zuwa dining din Yana tambaya
Daidai nan Ya Umar ya shigo
"Wani hoto ne na status din Anisa fah, ta yaudare mu taje aka mata ita ka蓷ai bata kira mu ba" fadin Jalila tana banka wa Anisa harara
Ita kuma tun shigowar sa ta kasa wani kwakwaran motsi sai ma abinda ya wakana jiya dake mata yawo a kai
Wai duk bayan haka ma ita fa ma ganin shi tayi so relaxed jiyan kamar be san abinda ya aikatawa marainiyar Allah ba, to dai akwai Allah Kuma ya gani kuma zai saka mata, ya ta蓳a haramiyar sa
harda galla mata harara bayan ya gama bata karasa zancen ba tayi saurin kauda zancen tana istigfari zuciyar ta, tace
"Allah sai ya saka mun wallahi"
bata san a fili tayi maganar ba sai da nabila ta ce
"Yadai saka mana, ai da muma munje an yi mana koda kalla 3 ne"
" mugani"fadin Ya Ahmad
"Ni yaya bana Whatsapp yanzu ina IG ka duba a wayanka"
Fa蓷in Jalila
Wayan ya ciro daga aljihu ya shiga Whatsapp din
"Kufa matsalar ku hauka, shi yasa ba son kallon status din ku nike ba kalla wani mahaukacin status jibi fa yawan shi"
"Kaii yaya jiya fa akayi grad din mu to in bamusa status ba me za muyi tunda baka kaimu ko 蓷an park bane bare ka 蓷an kashe mana zuciya"
Jalila tayi maganar tana sakin dariya
"To dai Allah kyauta muku"
Fara going status din yayi
Waensu hotunan su ne gaba 蓷aya class, wani kuma su uku, wani kuma sanda ake basu award, da wa蓷anda aka musu suna parade da kuma rawa,
sai kuma ya fara cikin karo da nata hotunan ita ka蓷ai
Duk Abinda yake yana kallon shi ta 茩asan ido,dan kusa da shi yake zaune, ya wani maze yana danna waya kamar besan me ake ba
kasa jurewa yayi ganin yanda Ahmad ke scrolling hotunan ta fin biyar a kan status din kawai ya amsa wayar yana duba wa
Shidai Ahmad ma kasa mai magana yayi yana ganin ikon Allah
Ganin wani huton ma da kayan da sukai parade Wanda ko isasshen rufe jikin ta batayi yi bane yaji ranshi ya 蓳aci,
yana kara scrolling yaga wanda aka mata suke ta maganar bata jira su ba
Tayi balain yin kyau a hoton duk da da graduation gown 蓷inta ajikin ta, ji yayi kamar ya rotsa wayar, kawai ya cilla ma Ahmad wayar sa ya tashi zai bar gurin
Har ya fara tafiya ya dawo yace ''bani wayar ki''
Duk kallon shi sukayi dan son sanin ma da wayake
茒agowa tayi ta kalle shi, sai kuma ta zaro jikinta na bari ganin yanda jijiyoyin kanshi suka fito, key ta cire ta mi茩a mishi, Kawai yayi gaba
Sudai su Amma dake parlourn da kallo kawai suka bi shi Anty na girgiza kai kawai tana 蓷an dariya dan ita tasan dawar garin tunda Abba ya fa蓷a mata
茒aki ya koma, kan 3 sitern daka 蓷akim ya zauna wayar ri茩e a hannunsa yana juyawa, wayar ya fara bincika wa, sai da ya goge gaba 蓷aya wani hoton da akwai ta a status din nata sannan ya fara bin chat 蓷inta
Yana yi zuciyar sa na mugun tafasa tunda yasan ai ba iya shi bane ya gani,
infact shi da ma sai yanzu ya gani, yasan wasu sun gani kuma har sun yaba,
hannun shi ya dun茩ule da karfi, ji yake kamar ya ga wa蓷anda suka gani ya bisu ya kwa茩ule idanun su
Chat din ta ya fara bi sai yaga wani chat ansa emojin heart da key
Zancen Abba ke dawo mai kar idan tanada wanda take so, dan baza su mata dole ba,
Ji yayi zuciyar shi ta fara dukan uku uku dan bai tunani shifa zai iya yarda ya rasa ta
Yarinyar da tun bata san kanta ba yake 蓷awainiya da soyayyar ta shine za'a ce wai wani take so instead of him Kai noway Bama zai yu bane
A hankali ya danna kan chat din ya shiga dan ganin dawa take magana, har ji yake yana wani jin jiri daga zaunen da yake saboda kishi da fargabar kar dai wani daban take kulawa
______________________
By
Anisa Muhammad yahaya 馃尯