Free chapter · Read without an account

4

by Bilkisu Ibrahim Musa · SANTSI




........A yanzu dai shekarun Ummul-khair goma cif, amma idan kuka ga yanda take ɗaukar ƙaton turen talla sai kusha mamaki. Yanda kowa yake a gidansu haka take, bambancinta da su kawai tana matuƙar son karatu, sai dai batada damar yi saboda kai-kawon talla.     
        Amma hakan baya hanata zare jiki zuwa makarantar firamare ta anguwarsu ta gwamnati. Tun ana korarta har wani malami yaji tausayinta ya sakata, sai dai yazo gidansu yayi magana da su Ummanta domin neman amincewar su kawai da tabbatar musu zai dinga biyan komai da za'a iya buƙata. 
       Umma bata nuna hakan ya dameta ba, ita dai kawai ta tabbatar masa tallatar sana'arta dole Ummul-khair tayi. Shi kuma yace babu matsala. Idan ta ɗora mata tallar safen ta taho da ita makarantar, zata dinga karatu kuma zata dinga sayarwa. Wannan shine mafarin fara karatunta ta firamare.
          Da safe dama Umman su awara take yi, dan haka suyar farko ita ake zubawa a botiki fari dai-dai ƙarfinta, zata saka Uniform ta ɗauka ta tafi, idan taje makaranta zata fara siyarwa kafin a gama shiga aji, idan ta ƙare shike nan, idan tai saura zata kai staffroom wajen Malam Awwal ta ajiye ta shiga aji sai anyi break ta je ta ɗakko ta ƙarasa sayarwa. Yanda take komawa Umma da kuɗin cur-da-cur kuma ta sayar yasa take jin daɗi sosai bata hanata zuwa makarantar. Amma fa babu batun hutu a gareta, dan tana cire Uniform zata ɗauki wata tallar ne kuma zuwa bakin layi inda matasa da masu sana'o'in yau da kullum ke taruwa. Anan ma bata haƙura ba, idan taga yara na tafiya islamiyya sai suyita bata sha'awa, dan haka zatayi duk ƙoƙarin da zatayi taga ta sayar da abincinta taje jikin islamiyyar Malam Baba ta maƙale tana sauraren karatun yara.
         Malam Baba bai taɓa korarta ba shi kam. Sai ma zaunar da ita da yayi ya tambayeta ko tana son tayi karatun ne? Cikin farin ciki tace e. Yace taje ta faɗa a gida azo a sakata. A take yanayinta ya canja, tace ai babanta baya nan. Umma kuma kota gaya mata bazata sakata ba. Baice komai ba akan hakan, sai dai yace taje to gobe ta dawo. Bata san yaya akai ba sai yace ta fara zuwa. Tun daga ranar ta fara zuwa nan ma, sai dai ta fara samun matsala da Umma, dan da lokacin makaranta yayi ko bata sayar da abinci ba zata tafi ne. Sai take koma mata da kwantai, wani lokacin wanda sukaci basu bada kuɗi ba kuma su gudu bata amsa ba. Tun tana mata faɗa harta fara kamata ta doka, koma tace sai ta biya ta. Haka zatai ta raragefe da tsoron shiga gida har dare, sai idan ALLAH ya taimaketa cikin yayunta sun dawo daga tasu tallar su bata kuɗin ta bama Umman sannan. 
         Tun ba'a san inda take zuwa ba har aka sani. Maimakon Umma taji daɗi sai ma ta kamata ta doka duka bana wasa ba. Ta kuma hanata zuwa har bokon ma. Da gaske Ummul-khair tana son karatu, dan haka dukan Ummah da hanawarta baisa ta daina zuwa duka ba har islamiyyar ma. Tunma tana tsoron dukan nata harta saba da shi. Sai dai ta canja taku, takan yi ƙoƙarin ganin ta sayar mata da kayan sana'arta kafin. A haka sai ta fara samun sassauci. Yanzu haka dai sunyi jarabawar fita daga firamare, hakama islamiyya duk da tana mata asha ruwan tsuntsaye tana zuwa, dan watarana bata samun damar zuwa itama dai tana samun ilimin gwargwado, kuma duk sanda ta samu dama tana zuwan.
         Malam Baba yasan matsalarta baya hanata, ba kuma ya cewa ta kawo kuɗin makaranta. To yau gashi ta ɗingimo aiki, Umma ta saka mata tallar rana kamar yanda aka saba, taje bisa tsautsayi ta zubda mata da mai, kuma tace sai ta biya. Bata san inda zata dosa ba, bata san ina zata samo kuɗin biyanta ba, ba kuma ta san yanda zata yi da abincinta da babu mai ba balle ta sayar....

             ★________________★
                   ««KADUNA»»

       “Wai dan ALLAH baki bar kukan nan ba Deenah? Baƙya ma tsoron kanki yazo yana ciwo. Ya kamata kiyi haƙuri haka nan, ga abincin kici sai muyi magana a nutse”.
       Cikin jan shashsheka da share hawaye wadda aka kira Deenah ta girgiza kanta. “Bazan iya cin komai ba wlhy Siyama. A yanzu babu wani abu dake birgeni, jima nake kamar na kashe kaina...”
       “A'uzubillahi! Wace irin magana ce wannan? Haba Deenah da hankalinki kike tunanin kashe kanki akan wani ƙarin auren mijinki da bazai cutar dake da komai ba idan kika kwantar da hankalinki.”
        “Ya zaki ce ba zan cutu ba Siyama? Kishiya fa! Wata ce fa zata shigo cikin rayuwata da mijina da ƴaƴana. Zamu raba duk wani abu nashi da ita. Wlhy bazan iya ba Siyama, bazan iya rayuwa da Farouk tare da wata ba.”
      “Humm Deenah kenan, idan baki iyaba yaya zaki yi kenan? Kin san dai bazai fasa ba tunda har ya iya tunkararki ya faɗa miki ko? ALLAH da nice ke zan kwantar da hankalina, zanyi haƙuri kuma. Musamman ata sigar da yazo miki da zancen. Ya lallasheki, ya kuma gaya miki gaskiya. Baki san yana neman aure ba amma bai taɓa canja miki ba har zuwa yau daya furta da kansa. Maza nawa ne daga sanda suka fara neman aure gidan su ke rikicewa saboda rashin adalcin su. Amma Abban Amnah baiyi haka ba, sai ma sake ninka ƙyautata miki da yayi. Ki duba ƙaton shagon da yake shirin buɗe miki, ya baki danƙareren gida mallakin ki, ya ɗaukeki kuka fita yawo ƙasashe har uku tsawon lokaci. Sannan ya miki bayani cikin nuna girmamawa da alƙawarin bazai taɓa wulaƙantaki ba. Mi kike so bayan hakan Deenah? Miyasa bazaki karɓi uzirinsa ba. Idan muka duba ta wata fuskar fa kema harda laifinki. Kin dage akan bazaki ƙara haihuwa ba daga yara uku, shi kuma ya nuna miki yana buƙatar yara tunda ALLAH ya hore masa abinda zai ɗauki nauyin su. Sannan wasu ɗabi'unki ya nuna miki baya so baya buƙata. Kalleki fa Deenah sai kace ɗiyan da bana musulunci ba. A saman kanki gashin doki ne da aka haramta mana, farcenki kin ƙara babu ko burgewa, giran ido, har fa wushirya kika je akai miki, haba Deenah, wannan ya kamata uwa kamar ki ace ta damu da shi a hanlin yanzu ko maida hankali akan tarbiyyar yaranta?. A yanzu haka fa Amnah tana shekara ta goma ne, js 1 zata tafi Secondary, baƙya tunanin tana buƙatar tsayayyar MAHAIFIYA-UWA a wannan gaɓar?........”✍🏼

Want the next chapter?

ui.create_a_free_arewapen_account_to_save_progress_unlock_paid_chapters_fol