Free chapter · Read without an account

Chapter 5

by Nanamaryama · KANWAR SHEHU

بسم الله الرحمن الرحيم











Kamar kullum tun ƙarfe 6 na asuba basu koma barci ba sai gyaran gidan ake yi "Inno ta ce Jawahir kinga yanzu an kusa komawa makaranta ko? To abincin kawai zamu rinƙa yi a gida ne ana zuwa sai ki daina tallar kawai kinga ba lokaci to!''

    Inno kuma kina ga za'a zo a siya kada fa mu kwana ciki?

A'a in Sha Allah za'a siya ma ki kwantar da hankalin ki, daga yau zamu fara a cikin gidan in Sha Allah zamu yi nasara haba Dr jawahir ya da sarewa haka a'a Allah na tare damu in Sha Allah...

Allah yasa mu dace ta faɗa, karfe 8 dai-dai suka gama aikin su aka shinfida tabarma domin ƙari tana gamawa kuma suka huta inno ta daura abincin ita kuma kwanon da suka bata ta wanke su...

   Ƙarfe 12 dai-dai inno ta gama abincin inda can kasuwar ana ta jiran "Jawahir" ta kawo abinci amma shiru saboda inno tana gyara kayan ta, ita kuma mai saidawa ga tsafta komi nata tsaf take tafiya dashi, sallama aka fara cikin gidan abada abinci cikin kan kanin lokaci sai gashi har nema ake babu, inno ta ce kinga ni ai yanzu shikenan munyi dabara daga yau a gida zamu rinƙa komi kawai bazan iya wannan tallar ba kullum gaskiya!.. 

    Wallahi kam anyi dubara kinga wanda ya siya yau zai faɗa gobe a gida aka yi ya saya ... 

   Tabbas haka ne mudai Allah ya dafa mana! 

Suna zaune majociyar su ta shigo da sallama a bakin ta, suka gaisa da Inno ta ce don Allah tana san "Jawahir ta raka ta birni saro kaya ita yar ta bata da lafiya ne!''

Inno ta ce har ina zaki je haka? Ashe rabii ba lafiya ubangiji Allah ya bata lafiya to!! 

Amen ya Allah zanje Kano ne in Sha Allah.. 

  Ubangiji Allah ya kai mu lokacin badamuwa! 

Godiya tai mata tare da tafiya.... Sai da ta tafi ne inno ta ce wai lafiya na daina ganin" rabi ne gidan nan?''

Bata rai tai tare da faɗin inno mun bata da ita fa.. 

    Kai innalilahi wa'inna ilahir raji'un shiyasa nadaina ganin ta ashe gidan nan, o Allah na tuba mai zai haɗa ki da ita har kukai wannan lokacin baku magana Jawahir ban san ki da wannan halin ba faɗa min? 

   Inno kan maganar auren ta ne don na bata shawara kan tai yanzu shine take jin haushi na fa ni kuma na kyale ta idan ta sakko zata neman da kan ta... 


     A'a kece baki da gaskiya fa, taya zatayi aure ki ce a'a Saboda me ina ruwan ki? Don kina san karatu ance maki wani ma na so ne miyasa tom laifin ki ne kije ki bata hakuri ku dawo dai-dai kinji mai na ce maki? 

   Ehh inno in Sha Allah zan je amma ba yanzu ba!. 

Ko ma dai yaushe ne sai kin bata hakuri na faɗa maki... 


        *

Ƴan uwa ana ta zuwa ana gaisawa da su "Abeed sai dadi suke ji kamar me jadda ta ce kenan yanzu ban kwana aka zo min? ''

   Eh wallahi saboda bana so na tafi ban kara kallon ki ba " Jadda na ina san ki da yawa ne, sanki ya min over fa! "

     Dariya sukai ta ce" Amma takwara nan za'a barki ko? Tunda dai yanzu kinzo ki zaman ki nan asa ki makaranta nan komi dai nan!''

   Gwalo ido tai kamar mai ta ce"Jadda na zauna nan kuma ita kuma Aunty fa? Wayyo Aunty za'a kwace maki sister din ki kizo ki tafi ni kada a dauke ni fa! ''

   Abeed ya dungure mata kai tare da faɗin yi mana shiru malama.. 

        Alhaji ga abincin nan bari na shiga ciki wanka zanyi....! 

Maimakon wankan nazo ayi dani zaki tafi ke ɗaya haka ake yi? 

Uhmm Alhaji kenan ban minti 30 kawai dai yanzu nadawo' minti 30 din da zai canza mata rayuwa minti 30 din da zai sa bugawar zuciyarta ya canza da ana canza ƙaddara da Aunty ta canza ta ta ƙaddarar, Alhaji ya fara cin abinci ba tare da yayi bismillah ba bai taɓa jin daɗin abincin ba irin na yau ya rasa wane irin daɗi abincin ya mashi har kunnen sa ke motsi.....! 

diguwar riga ta barci tasa ta fito da murnar ta ta ce" Alhaji har ka gama cin abincin ne?'' ya mata banza kamar bai san abinda take faɗa ba, ta kara magana wai lafiya?!

Please don Allah kada kidaman ki tafi kiban waje...!  
        iKon Allah ta faɗa ta ce" Alhaji yanzu kake fa lafiya lau amma ka canza min don Allah kayi hakuri idan wani Abu na maka kayafe mun!''

  Magangan nun da take masa ne suka ƙara tun zurusa ya ce" tunda bazaki Shirin ba na bar maki wajen, abincin da ya rage ne tai Bismillah ta fara ci baiwar Allah tana ci tana kwalla, wayar tace tai ring sunan dake kan screen din ya bayyana a jiki son, ɗauka tai tare da sallama!''

Daga can bangaren ya ce "Aunty " I miss you wallahi gaskiya today am come back to home in sha Allah!.

Jadda ta ce iKon Allah wai yanzu nan idan na ce na rike ku to ya zaku yi ne? Allah ya shirya mun ku dai, ta amshi wayar suka gaisa ta mata addua tare da sa albarka, indai zasu yi waya da ita to a haka take sai an sa albarka sosai kam...!

  Aje wayar tai tare da gyara wajen ta wanke kayan da aka bata ɗin daman "zubee" ta wanke wanda ta ɓata mata ƙarfe goma na dare tana jiran Alhaji yazo shiru ta shiga part ɗin sa taga lafiya kuwa, zaune yake shi da mummy suna ta fira abin su ana shan dariya!

      ta ce Alhaji barka da wannan lokaci...

     Mummy tana kallon emoji ɗin sa tana murmushin mugunta, ta ce Alhaji kana ji ana maka magana fa?!

       Ohh ance maki bana ji ne, na faɗa mata tun a can don Allah kada ta daman amma ta kuma biyo ni nan mai zan mata yanzu? Ya idasa maganar da faɗa..

    Kamo hannun sa tai tare da faɗin kwantar da hankalin ka mijina yanzu zata tafi, ita kam sakin baki tai tana kallon iKon Allah ta rasa mai zata ce masa Alhaji da yake lallaɓa ta amma shine yau yake mata wannan abu lalle kam dole ta da ge da addua don tasan ba banza ba!. 


      Jawahir ce ta tafi gidan su rabii domin bata haƙurin da inno ta ce mata gidan ta shiga da sallama a bakinta lokacin mama bata nan ta rabii ta amsa mata fuska sake, tare da faɗin kawata yau ke ce a gidan kin gama fushin dani kenan?

  Uhmm kawai dai komi ya wuce yanzu ya jikin?fatan da sauki tunda naganki kina aiki ma ai kin wartsake..!

  Ehh alhamdulilah.

  Daga nan suka cigaba da fira abin su daman kuma su mutane ne mara rikon abu a zuciyar su, rabii ta ce naji mama ta ce gobe tare zaku tafi ko siyan kaya?

 Ehh tare zamu jiya tai ma "inno" magana ta yarda..!

   Ƙarfe hudu na yamma ta koma gida tana shiga taga "matar kawu Nura" mace mai mutinci da sanin ya kamata suka gaisa da ita ta ce amaryar jibo tamu...!

dariya aka sa duka ta ce'' ai wallahi gwaggo da na aure sa gwanda na zauna ba aure fa"


Inno ta ce......

Want the next chapter?

ui.create_a_free_arewapen_account_to_save_progress_unlock_paid_chapters_fol