Free chapter · Read without an account
Page 08
by Ummu~Fadeela · JUYIN LAMARI
By
*Ummu Fadeela*
*Book One*
*Page 08*
Gabadaya falon ya rikice, Baba ya bude idanu sosai yana kallon Karami.
Amma duk yadda yaso furta kalmar dake yawo kan harshensa ya kasa.
Yaya Abdul ya mike taku uku kawai yayi, ya fita daga falon tsabar saurin da yayi.
Halima ta zaro idanu ta dafe kirjinta da karfi tace.
"Innalillahi wa'inna ilaihiraji'un"
Umma da numfashinta ya kara yankewa, tayi iya kokarinta na ganin ta mike daga inda take, amma ta kasa.
A hankali ta dora hannunta duka biyu ta dafe carpet din sai kuma ta rankwafa ta fara rarrafe tamkar yaro mai koyan tafiya. Ƙofar fita daga falon ta nufa. da wani irin gudu Dubulle ta bita.
"Ummah ta" ta fada da karfi, sai kuma ta tsaya lokacin da Umma ta daga mata hannu. Ta dafe ƙofar falon tana mikewa dakyar ta fita.
Dubulle ta bi bayanta da sauri.
Innani ta koma kan kujera ta zauna dabas wani abu mai kama da sanyin jiki yana sauko mata. Tabbas Ikleema taso Tahir, Tahir yaso Ikleema kamar zasu mutu, amma suka hanasu auren juna.
Muryar Baba ne ya katsewa Innani tunaninta.
"Usmanu Halima yarku ce, gata nan duk hukuncin da ya dace ku dauka a kanta, banda maganar soke makaranta dan gaf take da kammalawa."
Daga haka ya fita daga falon da sassarfa.
A bangaren Mairiga kuwa, Allah ne ya iso da ita bangarensu lafiya. Amma tuni idanunta sun rufe bata ganin gabanta.
Tana isowa kofar daki kuwa wani hajijiya ya kwasheta, tayi baya-baya kafin ta fadi a kasa.
Dai dai isowar Dubulle, tayi ihu tana kiran. "Ummata"
Lokacinda Umma ta bude idanu a kan gadon asibiti ta ganta kwance da karin ruwa a hannunta.
Gefe daya kuma Halima da Baba ne zaune sunyi jugum jugum. A hankali Halima ke share hawayen da suka ki tsayuwa a idanunta.
Baba kuma a kallo daya zaka fahimci tsananin damuwa da tashin hankalin dake tattare dashi.
A hankali cikin muryar marasa lafiya Umma tace.
"Malam"
A tare Baba da Dubulle suka karisa wajanta da sauri.
Dubulle ta kama hannun ta da rawar murya tace, "Ummata"
Umma ta matse hannunta gam.
"Sannu Mairiga, ina ke miki ciwo yanzu"
Baba ya fada yana kallonta cikin tausayawa, dan a take ta fige tayi fayau.
"Malam ba zan iya cigaba da zama ba. Zuciyata tana gaza daukar hakuri yanzu. Zan dauki Dubulle mu koma garinmu can maigatari, duk da iyayena sun rasu amma akwai gidanmu na gado, kuma dakin uwata yana nan".
Da kyar ta kai aya tana sauke numfashi sama-sama.
Baba yace, "Haba Mairiga. Ki tafi ina yanzun nan tsofai-tsofai damu. Ki rufa mini asiri ki bar zancen nan jikin ki babu kwari. Ta lafiyarki muke yi yanzu."
Likitan dake duba Umma ya shigo ya yi yan dube dube yace Baba ya biyosa office.
Koda suka fita Umma ta yafito Dubulle cikin muryar marasa lafiya tace, matso kusa dani, hau nan ki kwanta"
Ta fada tana nuna mata gefenta a kan gadon.
Halima ta hau ta kwanta tana share hawayen idonta.
Umma tana shafa Kan ta tace, "Idan na samu lafiya zamu tattara mu koma maigatari mu bar musu gidansu.
Sai kuma tayi shiru kafin tace. "A jikina nake jin bake bace a hotunan can Dubulle. An hadasu ne dan a ci mana zarafi.
Wani daci ya biyo ta makwogoron Halima, ta hadiye da kyar tace. "Nice Ummata, amma wallahi ki yarda dani ba haka abin ya faru ba. A kwamfuta aka hada"
Tiryan-tiryan ta bawa Umma labarin abinda ya faru ta kare da fadin. "Wallahi Allah ke nan Ummata iya abunda ya faru ke nan. Ba zan taba cin amanar tarbiyyar da kuma yi mini ba.
Baba yaji tamkar ya dora hannu a kansa ya kwala ihu, yayi jarumtar dannewa ya furta. "Lahaula wala quwwata illah billah."
Likitan yaci gaba da Magana. "Ku guji bacin ranta, jininta yayi mummunar hawan da bacin rai kadan zai iya janyo mata paralysis."
Likitan ya dan nisa kadan yana kallon fuskar Baba Gadanga ya cigaba da fadin. "Kumburin da zuciyarta ta samu ba mai daga hankali bane. Idan aka dora ta a kan magani komai zai koma dai-dai da Ikon Allah."
Yayi rubutu a kan takarda ya mikawa Baba. "Ga wannan a saya ta fara sha, ko zuwa gobe za a baku sallama."
Bayan kwana biyu Halima tana zaune a gefen Umma, ta ballar mata magani ta mika mata.
Umma ta karba ta hadiya ta kora da ruwa tana bata fuska tace, "Maganin nan babu dadi Dubulle."
"Sannu Ummata, babu dadi amma zakiji dadin jikinki."
Umma ta gyada kai ta kalli Halima da tausayawa irin ta ya da Uwa tace. "Baki da aji ne yau a makarantar "
"Ina dashi Ummata, sai karfe hudu na yamma" Na bata amsa jikina duka a mace, idan na tuna hotunan da iyayena suka gani sai inji zuciyata ta tsinke. Tabbas ba zan taba yafewa duk wanda ya aikata mini wannan lamarin ba. Tun daga wancan ranar har yau Baba baya amsa ko gaisuwa ta balle ya kalleni. Baba bai taba kullatata irin wannan karon ba.
Hawayen da ya gangaro mini na share da bayan hannuna.
Hannuna Umma ta rike cikin kulawa tace "Dubulle, jiya da dare mun yi magana sosai da Malam. Ya kawo mini misalai masu yawa na rayuwa. Sannan ya bani dalilai dayawa na amfanin auren ki da Alhaji Sambo.
Shin Dubulle kina jin zaki iya rayuwa da Alhaji Sambo tsohon mijin yayarki Ikleema a matsayin mijinki?.
Halima tayi shiru zuciyarta tana tseren gudu.
Umma ta kamo hannunta tana shafawa a hankali tace, "Ki fada mini idan kina jin zaki iya zama dashi, koda ace kaso daya ne cikin dari".
Halima ta kasa bude bakinta bare Umma ta saka ran zata samu amsa.
"Kada ki boye mini abunda ke ranki Dubulle Domin ni na haifeki. Ina tare dake a kowanne hali.
Matukar bakya son sa ko jin zaki iya zama dashi, to sai inda karfina ya kare wajan ganin bayan wannan lamarin da Baffanki Karami ya shigo mana dashi."
Halima ta kwantar da kanta bisa kafadar Umma, ta lumshe idanunta tace, "Ummata zuciyata bata mini adalci, ina iyaka kokarina. Amma kamar na gaza.
Ummata soyayyar Yaya Abdul zata yi mini illah. Ki dinga sanya ni cikin addu'arki Ummata...
Halima ta dago da sauri tana bude lumsassun idanunta tace, "Amma zan iya hakura in auri Alhaji Sambo matukar hakan zai sanya Baba ya daina fushi dani Ummata."
Umma tayi shiru na dan lokaci tace. "Ya Allah ga Halima a sassauta mata wannan jarabawar.
Umma ta dan nisa taci gaba da cewa. "sai dai ki sani Dubulle, ban taba ganin soyayyar ki dai dai da kwayar zarra a cikin idanun Abdul ba.
Ina mai bakin cikin watarana yazo da zaki zo nan ki sanar dani Abdul ba soyayyar aure yake yi miki ba ta Yan'uwanta ka ce kawai."
Halima tayi shiru tana jin yadda bugun zuciyarta ke sauyawa. "Tabbas Bata fatan Allah ya gwada mata wannan ranar da Umma ke hasashen zuwansa.
Tashi ki shirya makaranta kada kiyi latti, sannan kiyi taka tsantsan kada ki maimaita abun da Zai janyo mana cin zarafi"
Halima ta gyada kai ta mike jiki a mace ta wuce dakinta. Umma tabi ta da kallo tana jinjina Ikon Allah, ita kuma nata yayan da soyayyar yayan makiyanta aka jarrabcesu.
A gaggauce Halima ta shirya kasancewar karfe biyu ta gota kafin tayi Sallah da sauran uzurinta karfe uku tayi.
Ta fito sanye cikin atamfa dinkin riga da siket hot red ta yafa mayafi dan karami a kanta shima hot red, kasancewar ta mai tsaho bata son dogin takalma.
Flat shoes dinta kalar gyalen ta sanya, sai fashion dankunne da abun hannu da agogo ta fito tana ta baza kamshi. Kasancewarta fara sol, sai shigar ta amsheta sosai
Halima akwai gayu bata yiwa fuskarta kwalliya ko kadan, Amma ta iya ado na sutura da idan ka kalleta sau daya sai ka kara kallonta saboda kyanta mai fizga ne.
"Allah ya tsare", Umma ta fada tana fitar da dari biyar daga jakarta ta bawa Dubulle.
Ina ta addu'ar kar Allah yasa in hadu da Yaya Abdul a compound. Amma addu'a ta bata karbu ba. Ina fitowa daga sashenmu shi na fara arba dashi tsaye jikin dalleliyar motarsa yaci gayu.
Ya dago kai muka hada idanu, da sauri na matsar da kaina ina kara saurin tafiyata kamar zan kifa da kasa.
"Halima"
Ya kira da murya mai kaushin da ya tilastawa mata tsayawa ba tare da ta shiryawa hakan ba.
"Zo nan"
Ya kuma fada cikin bada umarni.
Duk yadda gangar jikinta yaso kin bin umarninsa, amma zuciyarta taki amincewar da hakan.
A hankali ta taka zuwa gabanshi ta tsaya. Kallon sakan biyar ya mata yace yana sassauta murya, "tun dazu nake dakon jiranki a nan, shine kika bawa banza ajiyata zaki wuce?"
Halima bata ce komai ba.
Abdul ya karkata kai gefe yace, "shiga in sauke ki a makarantar"
*LAGOS*
A fusace ya mike yana dafe babban teburin dake gabansa. Cikin tsananin fushi yace.
"You are fired!"
Ya cire hannayensa da ya dafe table din dasu yana nuna kofa ya kuma fadin.
"Now get out of my office"
Jiki yana rawa P.A din nasa ya tsugunna a kan guiwarsa, ya hade hannayensa waje daya yace, "I am sorry Boss, nayi maka alkawarin ba zan kuma maimaita kuskure irin wann...."
Bai kai aya ba, boss din ya kuma katsa mishi wani tsawan da ya mike ba tare da ya sani ba.
"Get out, kada in kuma ganin fuskarka a ma'aikatan nan"
Tab dake hannunsa ya ajiye gaban teburin boss din, ya juya ya fita.
Yaraf ya koma saman office chair dinsa ya zauna yana dafe goshinsa dake sarawa sakamakon maganar da yayi da karfi sosai.
Landline dake gefen table din ta dama ya daga yana karawa a kunne.
"My office"
Kawai ya fada ya kife wayar yana relaxing kansa saman headrest na kujerar, lokaci daya ya lumshe kyawawan idanunsa masu dauke da Zara Zaran lashes tamkar mace.
Ya kamo lips nasa na kasa yana dan taunewa kadan kadan. Hadadden office ne sosai da a kallo daya zaka fahimci ofishin CEO na babban kamfani ne.
Bangon dake bayansa shelf ne akayi design mai kyau mai daukar hankali. Cike yake taf da award award masu yawan gaske da daukar hankali.
Daga gefe can akwai wajan hutu daya kawatu da duk kayan da Ake samu a falo.
Sai babban teburin sa mai dauke da takardu kwamfuta da sauran abubuwa office, daga gaban teburin akwai CEO desk name, An rubuta sunansa da gold lettering ALEX MALABU. CEO REAL ESTATE AND HOLDINGS COMPANY.
Ƙofar ofishin aka bude. Wata mata da bazata haura shekaru 35 ba ta shigo. Hannayenta ta hade a kan cikinta, ta dan rusuna kadan alamar girmamawa tace. "Ian here Boss".
Alex ya dan dago kadan yana tabe fuska yace.
"Mrs Hannah, kamar yadda kike gani, position na P.A dina is empty, so ina bukatar sabon PA."
Yana gama maganar ya koma ya yi resting kansa.
A rikice Mrs Hannah ta dago, muryarta tana rawa tace, "Yes sir"
Ta juya ta fita. A ranta take fadin "Again Boss, wannan PA din fa ko 2months bai yi ba, sai yaushe zai daina canza PA da korar staff kamar yadda yake canza Riga?."
*****
A harabar makaranta Abdul ya yi parking, ya juyo ya kalli Halima da tayi nisa a tunanin da take yi. Bisa dukkan alamu bata San sun iso ba.
Yatsunsa biyu a buga a saitin fuskarta.
"Yaya Abdul ka bani tsoro fa". Ta fada tana turo baki gaba.
Serious ya yi da fuska, fushin fuskarsa yana bayyana sosai yace, "A ina aka samo hotunan can, meye alakarki da gayen? And meyasa inata kiranki bakya amsa wayata".
Zuciyar Halima ta tsinke, bata son tunawa da maganar hotunan nan ko kadan. A take hawaye ya balle Mata ta fara kuka.