Free chapter · Read without an account
Chapter 9
by Nanamaryama · KANWAR SHEHU
بسم الله الرحمن الرحي
Ta ce" wankan magani kuma?''
Ehh wankan magani ya ce, saboda ki mallake shi da ƙyau shi ne amfani wankan maganin....!
ta buga tagumi saboda taji an kira mata abin da ya fi ƙarfin ta..
*
Yau take Monday Kuma yau ne tafiyar su Abeed ƙauyen nan ya kammala komi farar tishat yasa da baƙin wando yai matuƙar kyau sosai" Haroon " ne ya kira sa ya fito ya shirya bai so su kai dare a hanya fa!!
Ya ce'' dalla kada ka damu mutane malam mutum zai yi kewar gida amma yana maganar a fito da wuri? Kai har ka shirya ne?''
Ehh man!
Haroon
Uhmm nidai futo mu tafi, saboda mu yi yamma a can ya sa mai dariya ya kashe wayar, shi ba abin da yake tunani irin ya tafi ya bar "aunty a wannan halin ya zata kasance ba mai kula da ita, balle ya ɗebe mata kewa ta hanyar raha? Shi dai yana cikin damuwa sosai kam!''
Abeed ya ce" aunty yanzu tafiya zanyi na barki kenan?"
A'a ka kwantar da hankalin ka kaji, idan Allah yasa muna da rayuwa ai zaka dawo ka same mu in sha Allah, nidai Fata na da buri na ku mai da hankali kai da haroon ɗin kaji ko banda wasa a aikin ku?!
In sha "Aunty yanzu dai bari mu tafi sai Allah ya mana dawowa, addu'a ta masa sosai ita sister tana makaranta tun 7am ta shiga school....!
*
Kawu Nura ne zaune kusa da gwaggo ya ce" kinsan matar can munafuka ce kam wallahi, yanzu kinji mai ta ce faɗa ne?''
A'a malam ita fa ba munafunci tai ba an yi maganar an ba jawahir "jibo" ita kuma ta ce ba haka ba kaga ko ai ba munafunci bane ko?
Ke dakata idan ba munafunci bane? Mai nene a ciki? Na me zata ce za'a bata ɗan daba mai shan taba, wannan daidai ne komi? Wallahi matar nan tun da nace na fita harkar ta ta kuka da kan ta, don na daina mata komi a hidimar ta kuma auren yarta zai zo ina ce zata sameni?
Yanzu dai malam kayi hakuri don Allah komi ya wuce kawai.......wallahi bazai wuce ba sai ta gani a ƙwayar shanta!.
Karfe huɗu aka kawo mata wayar ta, rabii ce taje ta amso mata waya ce karama keypad mai kyau, a kwali ita kanta da ta gani tayi murna sosai, harda sim aka sa mata ga kati ciki enough {su Fatima anyi waya fa congratulations 🤪 fan's ɗin jawahir} Inno ta ce Masha Allah waya tayi ƙyau sosai, alhamdulilah aje a nuna ma "mama ko ita ma tasa albarka!"
tashi sukai tare ita da Rabi'ah suna tafi, ba abinda yafi burge Rabi'ah irin complete Qur'an da aka sa mata ciki da yake akwai M card ciki ta ce'' kawata sai ki kira shi ko kafin shi ya kira ki masa godiya ko? Tunda naga akwai kati ciki kawai ma!''
Kallon mara hankali tai mata ta ce ni zan kira sa Saboda ya kawo min wannan wayar haba nidai gaskiya a'a bazan iya ba? kawai idan ya kira na ɗaga bawai na kira sa ba ai shine...
Okay bari na tura masa text message kawai na godiya!
Ke dai kika sani da gulmarki kuma ba da miyau na ba ai kin ji mai nace suka ida sa shiga cikin gidan ko sallama babu, mama ta ce kuma yau lafiya aka shigo kamar ba gidan musulmai ba..?
Au mun manta "Mama" wallahi ita ce ta ɗauke mun hankali ai da tuni munyi ta faɗa tana murmushi....!
Ai nasani jawahir da dai ita ce, zan ce zata ai kata..... Wayar aka miƙa mata tare da faɗin mama wannan a ka aiko ɗin fa.
Farin ciki fal fuskar ta ce alhamdulilah alhamdulilah waya tayi kyau sosai da sosai ubangiji Allah ya tsare, sai a kiyaye banda ruwa kinji ko ƴata?
Gyada mata kan ta tai tare da faɗin in Sha Allah mama!.
**
Motar haya suka shiga sai dai Haroon ya kalli Abeed yasa mashi dariya, duk dai yana kallon sa bai ce masa komi ba saboda shi abinda yake tunani ya baro fa "Aunty Cikin wani hali, gashi zasu dade basu dawo ba'' ya ce don Allah haroon ka rage wannan shirmen Please cikin jama'a fa muke!
Uhmm kai dai ka ce ka fara missing " Aunty tunda dai baka da wadda zaka ce kayi missing idan ba ita ba, hey idan munje can ma ka ga kayi mata kawai Allah! ''
Innalilahi wa'inna ilahir raji'un ya furta a hankali ya ce'' kamar ni Abeed zan buge da auren yar ƙauye haba malam? Ka fita a idona na rufe ma wallahi kadai na min maganar nan?!''
Jawahir ce zaune kan dadduma ta tasa wayar tana kallo sai ta tuna alƙawarin da "Shehu" ya mata na idan sukai aure zata ci-gaba da karatu har ta zama likita, kuma ya sai mata babbar waya irin ta ƴan birni Allah sarki ko ina ya shiga? ƙwalla ce ta zubo mata saboda idan Shehu na gari da yake manemin kuɗi ne bai zama gari sai idan ya dawo, to da ya dawo kuma suna tare, a fili ta furta Allah ya sa kana cikin aminci Yaya na kanwar ka tana cikin kewar ka.....!
Inno da shigowar ta kenan ɗakin sai taji duk ta bata tausai, ta ce Jawahir har yanzu ba'a gama sallar ba ne?
A'a nagama yanzu!
To a roki Allah ya mana budi na alheri dai kada a manta...
*
Sister ki tashi mu yi break fast ko?
Wallahi "Aunty nagaji da yawa kamar wadda akai ma duka fa, jiki na duk ciwo yake mun ta idasa maganar kamar zatayi kuka! ''
Aunty ta ce uhmm ƴar shagwaba kenan tashi dai muyi, ai da bro din ki na nan da kin kwanta ɗin nagani...
Dariya tasa tare da faɗin har na fara kewa fa 😭 saboda da shi ne ko ina so ko bana so da tuni an sauke ni kasa....!
Nima to bari na fara daga yau..... A'a Aunty muje minti uku zan fito ma!
Okay sai na ganki..
*
Boka na zaune ya ce'' wannan ita ce za'a fara ma wankan maganin kenan?''
Ita dai tana gefe saboda duk bin malaman ta bata taɓa ganin wanda ya ce zai mata wanka ba sai kan sa, mummy ta ce" Eh ita ce zubaida ɗin da na faɗa maka!''
Cikin zuciyarsa ya ce a lalle ko zubaida taji kaya sosai zan kwashi daɗi nayi amfani da kanwa kuma nayi da yarta, ubanda ya kawo ku ya anshe ku...... A fili ya furta kada ki damu kinji da nace za'ayi wankan maganin na kwana uku to yanzu gaskiya na sati guda za'a maki Yadda zaki mallake sa sosai, kada ki damu aikin mu bai da wuya sai aiki ai kin gani ma gidan yayar ki ma!
Eh nagani, ina so na mallaki yaron ne saboda wallahi ina san sa, shi kuma yanzu ba tani yake ba a karkato min da hankalin sa nan kaji?
Baki da damuwa yanzu dai ga wannan man ki shafa yanzu, saboda yau za'a fara wannan wankan sai kin shafa sa sannan sai a bi da maganin....
Amsa tai jiki na rawa da yake "mummy tasan ya man yake ta taimaka mata suka shafa, ya ce ta shiga ciki nan yana zuwa yanzu!"