Free chapter · Read without an account
Chapter 4
by MARYAM STAR · ƊAURIN ZUCI
***
𝐃𝐀𝐔𝐑𝐈𝐍 𝐙𝐔𝐂𝐈
NA MARUBUCIA
𝐌𝐀𝐑𝐘𝐀𝐌 𝐒𝐓𝐀𝐑
💪𝗝𝗔𝗝𝗜𝗥𝗧𝗔𝗧𝗧𝗨 𝗪𝗥𝗜𝗧𝗘𝗥'𝗦 𝗔𝗦𝗦𝗢𝗖𝗜𝗔𝗧𝗜𝗢𝗡💪✍🏻
𝗙𝗥𝗘𝗘 𝗕𝗢𝗢𝗞
𝗖𝗵𝗮𝗽𝘁𝗲𝗿 4
Kallonta kawai Malam ke yi babu ko ƙiftawa, yana ƙoƙarin gane inda kalamanta suka dosa.
Maida kallonta ta yi akan fuskar Muhammad wanda idon shi ke lumshe kamar me barci sai de kuma bata da tabbas akan barcin yake ko akasin hakan.
.
Sai da Malam ya tattaro nutsuwar shi bayan ya gama ƙare musu kallo sannan ya ce yana dubanta.
"Tabbas na gane aƙawai shiryayyar ƙaddara da ke bibiya rayukanku, a kallon farko da nayi muku a gefen hanya na soma gane hakan, sai de kuma ina tsoron tabbatar hasashena."
Da sauri Zunaina ta kai kallonta kan shi, yanayin da suka kasance na dawowa a kwanyarta....
Zaune suke ita da shi a gefen hanya, yayinda duhu ke sake bayyana hasken fitilu na sake haskake su, motoci jifa-jifa na wucewa a hanyar sai de babu wanda ya kula da su.
Tafe ya ke cikin keke napep ba tsoho bane tuguf amma babban mutum ne me cikar kamala, daga ganinsa zaka tabbatar da yana daga cikin mutane masu kamewar addini.
Ta gefen su ya huce bayan ya haske su sai kuma ya dawo da baya a hankali tare da tsayawa a saitinsu.
"Assalamu alaikum bayin Allah lafiya kuwa kuke zaune a nan tun kusan awa ɗaya na barku a wajen nan yanzu kuma na dawo na tadda ku."
Ya faɗa yana ƙare musu kallo.
Kallon shi Zunaina ta yi da soyayyun idanuwanta, kamar ba zata yi magana ba sai kuma ta ce.
"Lafiya ƙalau kawai de taimakon inda zamu zauna muke nema."
Bai ce da ita komi ba yaci gaba da kallon Muhamma da daya kawar da kan shi gefe baice komi ba.
"Wannan ɗin waye?."
Ya jefo mata tambayar yana karantar yanayin da take ciki.
Matse yatsunta ta yi sannan a sanyaye muryarta na kyarma ta ce.
"Mijina ne, kuma ba'a garin nan muke ba yau muka zo."
Bai sake cewa komi ba daga haka ya tada mashin ɗin shi kamar zai tafi sai kuma ya tsaya tare da faɗin.
"To ko zamu bini mu ƙarasa can gidana kafin zuwa gobe yanzu dare ya soma yi bai dace ace mace kamar ke ba na a irin wannan wajen da babu tsaro."
Nan Zunaina ta shiga yi mashi godiga kafin ta matsa kusa da Muhammad ta kama hannuwansa ta miƙar da shi tsaye, sai da ta fara saka shi sannan ta shiga itama tana sauke ajiyar zuciya tare da handala.
Sai da suka daidaita zamansu sannan mutumin ya tada napep ɗin shi suka soma tafiya.
A daidai wani ƙaramin gida ginin ƙasa ya tsaya tare da kashe mashin ɗin, tun kafin ya fito ƙananun yara maza da matasa suka baibaye shi suna yi mashi sannu, yayinda ya fito da wata leda me ɗan girma ya soma rabawa yaran abin da ke ciki.
A bakinsu ne Zunaina ta ji ana kiran shi da malam.
Bayan ya sallami yaran yayin mata nuni da su fito, babban abin da ya bata mamaki bayan fitowarsu sai gani ta yi Muhammad ya nufi wani waje da aka aje buta da randar ruwa.
Mamaki fal ranta take kallon yanda yake alwala a nutse kamar ba shi ba, bayan ya gama ya nufi tabarmar da wasu maza suke a zaune ya kabbara sallah a nutse.
Murmushi kawai Malam ya yi tare da nuna mata hanyar shiga gidan.
Kamar ba zata shiga ba sai kuma ta shiga bisa jagorancin wani yaro.
Da sallama suka shiga gidan wanda yake ɗan ƙarami me ɗauke da ɗakuna guda huɗu.
Hasken jan kwan lantarki ne ya haske ko ina na tsakar gidan da yake a share ƙwal, daga can ciki wata mata ce zaune tana girki a murhun gawayi.
"Huwaila ga baƙuwa inji malam ya ce a bata wajen zama kuma a bata ruwa ta yi sallah yana shigowa." Cewar yaron yana juyawa tare da fita bayan ya faɗi saƙon.
Da fara'a a fuskar wacce aka kira da Huwaila ta yiwa Zunaina nuni da kujera tana faɗin.
"Sannunki da zuwa naƙuwa ɗan zauna anan bani minti biyu in gama kwashe girkina."
Busashe murmushi Zunaina tayi tare da zama tana ƙarewa ko ina na gidan kallo a ranta tana mamakin dama akwai gida irin haka da mutum zai rayu, sai de kuma ta yaba da tsabtar matar gidan dan bata ga alamar datti ko ƙazanta ba.
Bayan ta gama kwashin ta ɗauki buta ta cika ta taf da ruwa sannan ta ce.
"Yauwa baƙuwa ga ruwan ga can banɗaki idan za ki zaga."
Tana faɗin hakan ta shiga wani ɗaki.
Bayan Zunaina ta gama alwala Huwaila ta shigar da ita wani ɗaki inda ta nuna mata alƙibla, sallar magrib ta soma yi sannan ta yi isha'i, tana sallamewa ko addu'a bata yi ba fice waje, kai tsaye wajen da Muhammad ke zaune shi kaɗai ta nufa.
"Mohan mi kake yi a nan kai kaɗai mi yasa baka shigo gidanba?."
Ta tambaye shi tana kallon shi da wani yanayi akan fuskarta.
Ko arziƙin kallo bata samu ba daga gare shi ba kuma dan bai jita ba kawai dai baiga damar amsata bane.
"Kinga na tsaya fira da maƙota ban san sanda ya gama sallar ba, ku zo mu koma ciki ko."
Cewar Malam.
Riƙe da hanun Muhammad suka shiga cikin gidan.
Bayani Malam yayiwa Huwaila akan zasu kwana a nan ta gyara mudu ɗaki ɗaya, ta kuma gabatar musu da abinci....
*****
Nannauyar ajiyar zuciya ta sauke sannan ta kalli Malam tace.
"Ina jin wani abu me girma na gab da faruwa a rayuwata, jikina na bani akwai abin da ke tunkaro rayuwata, bansani ko miye wannan abin ba, kamar yanda ban san minene musababbin abin da ya shigowa da shi cikin rayuwata ba, ban kuma san dalilina na zaɓar shi a matsayin mijina ba bayab inada tabbacin shi kan shi baisan ko waye shi ba."
Sake gyara zama Malam ya yi yana fuskantar ta da kyau tare da soma yiwa kalamanta filla-filla yana ƙoƙarin gane abin da take faɗa.
"Yarinya zan iya sanin wani abu koda ƙanƙani ne dangane da rayuwarki, sannan zan iya sanin asalin alaƙar ki da wannan bawan Allahn?."
Ya yi magar tunanuka daban-daban na yawo a kawanyar shi.
"Ƙwarai kuwa zaka ji abubuwa masu muhimmanci danganr da rayuwata, amma kafin nan bari imfara baka labarin haɗuwata da shi, da kuma abubuwan da suka faru."
Gyaɗa kai yayi alamar yana saurarenta.
*****
Bansan dalilina na tunkarar inda yake ba, kawai de na ji kamar bani ba kuma kamar ana sarrafa tunani da zuciyata, daga sanda na tsayu a gaban shi daga nan shafukan cuɗanyuwar ƙaddarorinmu suka soma, ban san cewa wannan tsayuwar da nayi a gaban shi ita ce hanyar ta farko da zata soma ruguje ginin rayuwata ba.
Wani irin sanyi ne ya soma ratsa can cikin gaɓoɓin jikina yayinda idanuwa suka sarƙafe a cikin na shi ido wanda nike iya hango wuta me ci a cikin su.
A kuma lokacine na soma tsinkayar sauyi daga zuciyata, bazan iya cewa ga ainahin abin da ya faru ba kamar yanda ban san sanda Afnan ta isa gida ta faɗawa Daddy abin da ke faruwa ba, kawai de naji sautin murya daga bayana ana faɗin.
"Zunaina mi kike yi a nan."
A razane na juya jin muryar Daddy a ɗan daburce na soma kame-kame sai de kuma na tsaya cak sanda na ji wani sauti da ban taɓa jin irinsa ba ya maimaita sunana.
"Zunaina."
Shine abin da ya ce yana kallona cikin ido, har sannan jikinshi na ɗigar ruwan da yayi ma shi duka.
"Waye wannan
?."
Daddy ta jefo min tambayar, a ɗan daburce na ce.
"Babu kowa Daddy, nima ban san waye shi ba."
Gyaɗa kai ya yi tare da faɗin.
"Okay shige muje to." ya faɗi yana nuna min hanya.
A saɓule na shiga gaba muna tafiya, sai de kuma du tako ɗaya da zanyi ina yinshi da wani irin tashin hankali, ina ji a jikina kamar ina yin nisa da rayuwata ne.
Ko bayan da muka koma gida ban iya yin koda motsi ba bayan na shiga ɗakina kwanciya na yi ina jin kaina kamar ba ni ba....
Can cikin barcina kamar a mafarki na soma jin kamar ana hayaniya, kuma muryar Daddy ce, hakan ya saka na farka a firgice jikina na rawa na buɗe ƙofar ɗakina na leƙa, jin hayaniyar a down stairs ya saka ni saukowa a hanzarce, turus na yi lokacin da naga Daddy na kokowar mayar da shi amma ya tsaya ƙyam kamar dutse ko motsi baya yi, wani ƙarin abin tsoro idanuwansa suka sake kaɗawa da launin jah kamar rushin wuta.
A sanda muka haɗa ido da shi ban san sanda na soma takawa zuwa inda suke ba, wannan rawar da jikina ya soma yi ta ɗauke kamar ɗaukewar lantarki, nan take nutsuwar da na rasa a wunin ranar ta dawo gare ni.
A lokacin bana iya jin komi duniyata ta yi shiru babu wani sauti da kunena ke saurare face na bugun zuciyata, du jijjigar da Mommah ke yi min sam bana jinta na rigada nayi nitso a wata duniyar wacce ta mantar da ni komi da kowa.
A taƙaice dai wannan ranar a nan gidanmu Muhammad ya kwana ba barci yayi ba kawai ya zauna ne a saitin inda nike ya duƙar da kai bai sake ɗagawa ba sai da asubahi lokacin da aka soma kiran sallah, wani abun ɗaure kai a tattare da shi da kan shi yayi alwala ya tada sallah, kuma a nitse cike da kamewa ya gabatar da sallar shi a nan falo, kafin ya gama na sulale zuwa ɗakina na kulle da key na bar key ɗin jiki na shiga nayi wanka ko zanji ƙarfi a jikina.
Bayan gari ya soma haske bansan taya aka yi ba kawai na ji kamar mutum a kaina, sanda na tashi Muhammad na gani jingine da bango yayi yana kallon saitin ƙofa, dubana na kai wajen naga su Daddy ne tsaye rayukansu a ɓace ga kuma ƙofa nan aje a ƙasa da alama ɓallawa aka yi.
A ranar na fuskanci fushin Daddy dan du yanda yaso Muhammad ya fita ko kallo bai ishe shi ba, kuma du inda na yi yana biye da ni baya umm baya umm-umm.
In taƙaice maka dai har da jami'ai Daddy ya kira don kawai su fitar da shi amma ko gezau hasalima babu wanda ke iya tunkarar shi kai tsaye kowa baya-baya yake da shi, ganin haka ran Daddy ya kuma ɓaci sai ya kore ni ya ce inje da shi waje kar insake in dawo dashi gidan.
Ina kuka ina roƙon Daddy amma fafur yaƙi, daga ƙarshe dole na fita Muhammad na biye da ni kamar bindi.
Har ga Allah raina ya kwanta da shi ban taɓa kallon shi a me cutarwa ba, hasalima tsananin tausayi yake bani, sannan ina jin kwanciyar hankali a tarrayyata da shi.
A ƙalla mun kwashe awanni uku a waje ni ban tashi na tafi ba shima kuma bai motsa ba, Daddy na leƙowa a kai a kai dan ganin ko na taso amma ban yi hakan ba hakan ya ƙara ƙular da shi, lokacin da azahar ta gabato sai na kalle shi cikin ɗarɗar na ce.
"Bawan Allah dan Allah ka yi haƙuri ka zauna a nan ni gidanmu zan tafi."
Na faɗa kamar zanyi kuka, bai ce dani komi ba ganin haka sai kawai na yanke hukuncin tafiya.
Ba tare da na saniba ashe wannan tafiyar tawa ita ce sanadin afkuwar ƙaddarar farko bayan ƙaddarar haɗuwa, na tafi ne da iyakar gangar jikina amma ruhi da zuciyata na a wajen shi na barsu.
Tun da na saka ƙafata a cikin gida ban sake sanin inda kaina yake ba, ba kuma fita nayi a hayyacina ba a'ah kawai zuciyata ta rigada da ta ɗaure tare da ruhina, abisa rashin sani ba baro su a wajen.
Gani da rai amma tamkar gawa gani da gangar jiki sai de bana iya amfanin komi, ina jin magana amma bansan abin da ake faɗa ba, ina da baki sai de bana iya furta koda kalma ɗaya ba, ina gani da idanuwa sai de ba ainahin mutane nike gani ba ina ganin wasu halittu daban masu ban tsoro da firgitarwa sannan kuma fuskar Muhammad na yi min gizo.
Du yanda zan misalta ba zaka gane yanayin da na tsinci kaina ba.....✍🏻
Tofa labari na neman kaimu wani bigire na daban, domin kuwa kaina ya soma caji akan labarin nan.
Shin wai wannan Muhammad lin wayene shi?
Sannan kuma waye MAFAKA da matarshi Rimsha da muka karanta a shafin baya??
Wacece Zunainah???
Mike faruwa da rayuwarta???.
Ku biyo ni domin mu warware zaren da ke sarƙafe da wannan labari, karku manta har yanzu shimfiɗa muke bamu shiga ainahin labarin ba, ku kasance tare da ni take me son ganin farincikin ku
MARYAM STAR ƳAR BAIWAR JAJIRTATTU⭐💪.