Free chapter · Read without an account

Chapter 14

by Nanamaryama · KANWAR SHEHU

P14



Ya ce Ni dai na bar ma Allah zaɓi tunda dai wallahi na rasa mafita gaskiya na hakura duk Abinda Allah ya yi mai kyau ne! 

      Don Allah kada kazo ka ƙara min zafi matsa kabani waje' kada ka manta fa gobe ne za'a yi abin ni dai gaskiya guduwa zan yi bazan zauna ba .... 

   A lalle kana ruwa a kore ka a wajen aikin ka, kan ka kai ma asara dai nidai duk abinda Allah yai ina maraba dashi ban san wane irin alheri ne ya kawo ni garin nan ba! 


       Ikon Allah wai na zaune bai ga gari ba, kai yanzu murna kake za'a maka Auren dole? 

     A'a fa ni ba murna nake ba amma wallahi kasan idan har ka gudu aikin ka ka rasa shi? Don haka idan ka ga dama ka zauna idan baka ga dama ba ka tafi kan ka zaka yi ma wa!! 

   **
Aunty Aure fa naji yana magana? Shi bro da bai san mata ƙazamai gashi ya je wannan garin ya zai yi? 

    Hmmm sister idan da "abeed yana jin magana da haka bata faru ba, tun lokacin kafin su gama services ɗin su na bashi shawarar aure har Alhaji yana zai mai Auren dole ashe ko shi za'a masa, muna magana wayar ta mutu ban san ta ina za'a fara ba ma!" 

   Kuka ta fara tare da faɗin Allah sarki Rayuwar mu daga wannan sai wannan kenan, yanzu mainene mafita kenan? Mu ga mu cikin wannan hali shi kuma gashi dokar da aka sa masu...... 

     Kamo ta tai tana bata hakuri, ita kan ta aunty tasan suna cikin yana yi amma ita uwa ce dole ta rinka dan ne wani abin kada ta sa suma su raunana, ta ce sister ba kuka zaki ba addu'a zamu yi kinji in Sha Allah Allah na tare da mu..! 

Haka ne Allah ya ƙara rufa mana asiri Aunty... 

        Zubee yanzu kin yarda kije gidan sa ki wata huɗu kenan? 

To wai idan ban yarda ba ta yazan auri Abeed ɗin? Ya ce dole sai na je an tsuma ni fa, kinga ko dole na yarda da maganin sa sannan aikin zai yi....! 

    Shiru tai alamar tunani take a fili ta ce" zubee ina mai baki shawara da ki canza tunani amma wallahi idan har kika ce zaki dana sani ina faɗa maki ne domin wallahi hmmm!" 

    Ta tashi kamar zata duke ta tare da faɗin bakin ciki dai kike min kada na auri ɗan mai kuɗi ko? Kuma wallahi ta Allah ba taki ba na faɗa maki kawai dai kina so kada naji daɗi yadda kike ji ne nasani..... 

      Mummy ta kama baki ta ce nice nake maki baƙin ciki? 

 Ehhh man idan bashi ba mainene? Taya an ce za'a min yadda zan aure sa ki ce min haka? 

   Okay tunda kin ce haka na kyale ki, ki yi duk abin da kika ga dama kawai ta tashi ta bar mata falon...... Zubee ta ce haba malama ai na gane ki Kuma abeed ne sai na aure sa ta gyara zama tare da kunna kallo!

                **
Gwaggo aka kira aka nuna ma kayan sha tara da arziki sosai tai murna tare da fatan alheri ta ce kace birni zamu? 
           Dariya dai jawahir tai tana rufe idon ta saboda ita kunyar gwaggo take ji sosai, ta ce mudai a taya mu da addu'a idan alheri ne Allah ya tabbatar mana idan ba alheri bane Allah ya canza da mafi alheri...! 

 Amin ya Allah ƴata shiyasa nake san ki wallahi, ta ce ina zaki bar mana jibo kenan? 😅

   Gwaggo ai jibo shi ma Allah zai basa amma nidai gaskiya bazan iya auren jibo ba, dalili da ɗan maye ne kuma bai sallah fa, ina zan iya da wannan abu ai ya yi yawa....! 

   Ita dai Inno tana gefe tana jin su, ta ce bari na shiga duk da baku saka ni ba ai zai shiryo ba sai ki gyara sa ba jawahir? 

La-la-la ta faɗa tare da mike wa gun don yanzu Inno sai ta sa ta kuka, don haka take mata da tai mata laifi sai ta ce sai jibo zata ba ba wani Alhaji da zata ba auren ta....!

         
                         Mai unguwa ya kira su domin ya ji wane hali suke ciki akwai wani bayani ne? Sukai shiru ya ce kenan yanzu ƴan matan garin mu zaku aura dai...? 

           Abeed ya ce" ranka ya dade a kara mana ko da one month ne man?" 

     Yaro faɗa mun da Hausa yadda zan gane mai kake nufi dai... 

         Sosai keya ya yi tare da da faɗin ina nufin wata ɗaya fa! 

   Waro ido ya ce.....

Want the next chapter?

Create a free ArewaPen account to save progress, unlock paid chapters, follow this author, and keep reading across web and the Android app.