Free chapter · Read without an account

018

by Kansa'u Bello · MEERAH

*MEERAH*

     *018*


    *Mamynah.....* Shine sunan da ya gani yana kaɗawa a saman screen ɗin wayar, wanda ya saka shi lumshe ido don ya tabbatar wani rikicin ne zata zo da shi. Idanunsa ya buɗe lokacin da kiran ya yanke, a saiɓance ya miƙa hannu ya ɗauki wayar sannan ya kira ta back.

   Ringing ɗaya ta ɗauka don a matuƙar hasale take da shi, saboda tun da ya saka ƙafa ya tafi Kano ya share wurin zama bai dawo ba. Gashi Jauhar ta iso tun washe garin tafiyarsu, kullum sai rigima take mata a kan idan Ya Jam (Sunan da ƙannensa ke kiransa dashi) ɗin bai dawo ba zata bisa Kanon.

  Bata tsaya amsa sallamar da ya yi ba, bare gaisuwar da ya ɗora da ita ta bal-bale sa da masifa. Cikin fishi da ɓacin rai take cewa.

   "Shin wai Ajmal Laylah ce ta haifa min kai, ko kuma dai nice na haife ka?!." Tayi maganar cike da jin cewar haƙurinta ya kai ƙarshe a wanan gaɓar. Don babu yanda za'a yi ta sha wahala ta haifi ɗanta amma wata da ban tazo ta mallake mata shi, ita sai dai ta zama ƴar rakiya a sabgarsa, sam ba zata lamunci hakan ba.

   Ajmal kuwa cikin kwantar da murya da tsananin biyayya ga Mahaifiyar tasa yace.

   "Me yasa zaki yi wannan tambayar Mamy, bayan a bayyane amsar take cewar kece kika haifeni, sai dai ita ma Momy uwa ce a gareni domin ita ce ta raine ni cike da kulawa da gatan da ko wace uwa take yi wa ɗanta." Ya ƙare maganar cikin kwantar da murya sosai cikin son ta fahimce sa.

  A ɓangaren Mamy duk da cewa maganarsa ta farko ta cewar ya san ita ce ta haife sa ta sakata a farin ciki sosai, domin Allah ya sani tana son Ajmal fiye da soyayyar da take yi wa sauran yaranta. Sai dai kuma dogon sharhin da ya ɗora a kan Laylah wacce take ganin ta shige mata hanci a kan lamarinsa, abin ya sosa mata rai sosai.

  Cikin bayar da umarni tace.

     "To idan har nice na haife ka kuma ka san da hakan to ka bar duk abinda kake yi ka taho gida gobe ina son ganinka." Tana kammala faɗa ta katse kiran ba tare da ta tsaya jin ta bakinsa ba.

  Idanunsa ya lumshe a hankali ya kwantar da kansa a jikin bangon kujerar da yake zaune a kai yana dafe kansa. Gobe ne za'a gabatar da shari'ar Meerah a Kotu kuma shine tsaye a kan case ɗin, ga kuma umarnin da Mamy ta ba shi na tafiya gida.

   Bai ma san wane irin tunani zai yi a halin yanzu ba, don haka kawai ya rufe laptop ɗin ya tashi daga gaban table ɗin ya koma saman gadonsa yana dafe kai. Nocking aka yi a bakin ƙofa ya bada izinin shigowa saboda ya san ba zai wuce Sultan ba.

   Kamar yanda ya yi zato kuwa Sultan ɗin ne ya shigo ya zauna saman Sofa dake fuskantar gadon yana sauke ajiyar zuciya, ɗago ido Ajmal ya yi ya masa kallo ɗaya ya mayar da idon ya lumshe.

   "Kun gama magana da Barrister ɗin kuwa?." Sultan ya faɗa yana miƙewa ya zauna da kyau yana kallon Ajmal ɗin da ya fahimci kamar wani abu yana damunsa. Tashi zaune ya yi shima ya fuskanci Sultan ɗin  ya bashi amsa da cewa.

   "Mun yi magana, ya sanar dani cewar ya gama haɗa duk wasu hujjoji da ake buƙata. Yace a zama ɗaya za'a iya kawo ƙarshen shari'ar nan, saboda komai a bayyane yake." 

   "Masha Allah, Allah ya taimaka. In sha Allah sai an hukunta yaran nan, domin kuwa barin irinsu a cikin al'umma suna aikata abinda suka ga dama ba tare da ana ɗaukar mataki ba Babbar illa ce." Cewar Sultan yana sauke numfashi sannan yaci gaba da cewa.

    "Yanzu da ace wata ƴar talakawa ce waɗan da basu da karfi suka samu suka yi ƙoƙarin cutarwa fa shike nan da babu abinda za'a yi saboda Iyayensu wasu ne a ƙasar. Kai ko dama ace sun ci nasara a kanta wani bai taimake ta ba, shike nan sun cutar da rayuwarta a banza babu abinda za'a iya yi musu!." Ya ƙare maganar yana jin takaicin irin wannan rayuwar da muke ciki a yanzu, ta mai ƙarfi shine a sama ako da yaushe.

   "Wannan dalilin ne ya saka na ɗauki alwashin cewar dole sai an hukunta su Sultan. Idan har sun saba taɓa wasu su zauna lafiya, to a wannan karon sun tsallako layin da yafi ƙarfinsu, dama duk wanda suke jin zai tsaya musu. Domin duk wanda ya yi yunƙurin taɓa koda inuwar Meerah ne da sunan cutarwa ba zan taɓa ɗaga masa ƙafa ba har abada!." Ajmal ya ƙare maganar da wani irin sautin dake bayyana gaskiyar abinda ya faɗa ɗin.

    Shi kansa Sultan kallonsa yake yana jin-jina wa irin tsananin kulawa da taka tsan-tsan ɗin ɗan'uwan nasa a kan ƙanwar tasu, wacce take ɗaukar hakan a matsayin takurawa. Ya sani cewar gaba ɗayansu suna tsananin son Meerah, suna nuna mata soyayya da bata kulawa sosai.

   Amma sai dai kalar kulawar da Ajmal ke nuna mata, da irin taka tsan-tsan ɗin da yake da shi a kanta na musamman ne. Wanda ba kowa yake iya fahimtar hakan ba sai shi da yake tare da shi a koda yaushe. 

  Ajiyar zuciya ya sauke yana cewa.

   "Ƙwarai kuwa, in sha Allah daga kan Meerah ba zasu ƙara marmarin aikata makamancin hakan ba koda a kan wata ne kuwa." Sultan ya faɗa sannan ya ɗora da cewa.

   "Kamar akwai abinda ke damunka Man?."

   "No, Nothing, I'm okay." Ya bashi amsa a taƙaice, bai takura masa ba don ya san koma miye da kansa zai sanar da shi idan ya kamata ya sani ɗin. Don basa ɓoye wa juna damuwarsu. Wani zancen suka kama da ban a kan tafiyarsu London da aka ɗaga zuwa wani satin idan komai ya kammala.

*******

  A ɓangaren Mamy kuwa lokacin da ta kammala bawa Ajmal umarni, ta kashe wayar kenan Abby ya fito daga bayi kasancewar tana cikin bedroom ɗinsa ne, zaune a saman gadonsa tana jiran fitowar sa ta kira Ajmal ɗin a waya.

  Bata san cewa yaji maganar da suka yi ba sai da ya zauna a kusa da ita yana binta da kallon mamakin randa zata sauya wannan halin nata da ya kasa sauya ta a kansa.

   Sai da ya gama ƙare mata kallo sannan cikin natsuwa ya buɗe baki yace.

   "Wai don Allah Na'imatu yaushe zaki yi hankali ki san cewar kin girma ne? Yanzu ina amfanin irin wannan maganar da kika faɗawa yaron nan?." Ya ƙare maganar yana tsare ta da ido.

   Haɗe fuska ta yi sosai don ita fa har ga Allah ta fara gajiya da bin umarnin Abby ɗin a kan bar wa wata damar ci gaba da juya rayuwar yaronta, bayan kuma tana raye da lafiyarta a cikin duniya.

   "To yanzu kuma me nayi ne Alhaji, don kawai ina buƙatar ganin ɗana na bashi umarnin zuwa shine zai zama laifi?." Mamy ta faɗa tana sake haɗe rai sosai.

  "Ba laifi bane don kin buƙaci ganin ɗanki, hanyar da kike bi ce wurin son nuna isa da ikonki na Mahaifiya har kike kushe wacce ta raini ɗan naki cike da gata da soyayya ce bata dace ba." Bai bata damar yin magana ba taci gaba da cewa.

   "Bari kiji abinda baki sani ba Na'imatu, idan kika ce zaki riƙa ɓata Laylah a idanun Ajmal ko faɗin magan-ganun da basu dace ba a kanta. Don ki raba shaƙuwa da soyayyar dake tsakaninsu, to fa ki sani ba zaki cinma hakan ba ko kaɗan, domin shi yaron naki yana kallonta da mutunci da ƙima a idanunsa. Maimakon hakan sai dai ya koma yana ƙalubalantar halayenki a ɓoye koda ace ba zai iya bayyana maki ba." Numfashi ya sauke sannan yaci gaba da cewa.

  "Ni banga laifin wanda ya ƙaunaci naka ba, sam Laylah bata can-canci haka a gareki ba. Abu na ƙarshe shine Ajmal ba zai dawo gidan nan ba har sai ya kammala abinda yake yi a can." Yana kammala faɗar haka ya miƙe ya nufi gaban mirrow ya fara shirya wa ya barta da baki buɗe tana bisa da kallo cike da tsan-tsar takaici.

    Ganin bai ƙara bi ta kanta ba ya sa ta tashi fuuu!!! Ta fice daga ɗakin, kai kawai Abby ya gir-giza yana mata fatan shirya a zuciyarsa. Sai da ya kammala shirya wa sannan ya zauna bakin gadonsa ya ɗauki wayar ya saka kiran Ajmal.

   Ajmal dake zaune shida Sultan suna hira kiran Abby ya shigo masa, ɗauka ya yi da sallama ya ɗora da gaishe sa. Da kulawa sosai Abby ya amsa masa haɗi da tambayarsa mutanen gidan.

   "Alhamdulillah Abby kowa yana lafiya." Ajmal ya bashi amsa.

  "Kana jina ko?." Abby ya faɗa muryarsa na komawa serious.

   "Eh Abby." Ya faɗa yana gyara zama haɗi da natsuwa sosai tamkar yana gaban Abby ɗin.

   "Maganar da kuka yi kai da Mahaifiyarka na tahowa gobe na soke ta, ka zauna ka natsu ka kammala abinda ka fara kafin ka dawo. Nima ba don tafiyar gaggawar nan da ta same ni ba da zan zo gobe ayi shari'ar a gabana. To amma ka ganni yanzu na kammala shiri zan wuce airport, ina so kayi abinda ya dace kaji ko, sannan Uncle's ɗinku suna nan idan wani abin ya taso, Baba Alhaji ma yana nan." Abby ya faɗa yana kallon agogon hannunsa.

  "In sha Allah Abby za'a yi yanda kace." Ajmal ya faɗa sannan ya ɗora da yi masa addu'ar sauka lafiya da samun nasara a kan abinda zai je nema. Daga haka suka yi sallama ya ajiye wayar ƙaƙƙarfar ajiyar zuciya na ƙwace masa. Dama tun ɗazu tunanin dake ta kai-kawo a ransa kenan na yanda zai yi da umarnin da Mamy ta bashi wanda ba zai iya tsallake wa ba.


*Nawaz.......*

   Kwance yake a ɗakinsa dake cikin gidan nasu idanunsa a buɗe suna kallon rufin ɗakin nasa, yayinda zuciyarsa ta lula duniyar tunani. Hoton fuskarta ne ke haska wa a cikin idanunsa yana jin wani abu mai kama da kewa na mintsininsa.

   A can ƙasan zuciyarsa yake fatan samun kira daga ɗan'uwanta, ba don komai ba kuma sai don ya samu damar ƙara ganinta koda sau ɗaya ne. Kamar an mintsine sa ya miƙe ya isa gaban drower ɗinsa ya buɗe ya ɗauko wannan ribbom ɗin nata.

   Saman katifarsa ya koma ya zauna yana tsira wa ribbom ɗin idanu tamkar ita ce ya samu, yana cikin wannan yanayin ne wayarsa ta yi ƙara wanda har sai da ya ɗan firgita saboda nisan da ya yi a tunani.

  Baƙuwar Number ya gani don haka ya share kamar ba zai ɗauka ba, zuwa can kuma wani tunanin ya faɗo masa na cewar zai iya yiwu wa ko kiran da yake jira ɗin ne. Don haka ya ɗauka tana gab da katse wa.

  Sallama aka yi masa daga can ɓangaren, amsa wa ya yi a mutunce sannan ya yi shiru alamar yana saurare. 

  "Sunana Sultan Abbas Mamman Gwangwazo, Yayan Meerah yarinyar da ka taimaka. Nine wanda na amsa contact ɗinka a asibiti." Sultan wanda ya kira sa ya faɗa daga can ɓangaren. Allah ya sani sai da zuciyarsa ta yi wani irin tsalle lokacin da yaji an ambaci sunanta.

   "Are you there?." Sultan ya faɗa daga can ɓangaren jin ya yi shiru bai ce komai ba. Ajiyar zuciya Nawaz ya sauke yana kama kansa yace.

  "Eh na fahimta, yaya jikin nata? Ina fatan dai ta warke?." Ya jero masa tambayoyin cike da son jin amsoshinsu, wanda har sai da Sultan ya ɗan yi jim saboda jin yanda ya yi maganar. Share wa ya yi ba bashi amsa da cewar.

   "Alhamdulillah, ta war-ware." Nam ma ajiyar zuciya ce ta ƙwace wa Nawaz wanda ya ƙara saka Sultan a mamaki. Sai dai yanzu ma bai ce komai ya sako masa bayanin da ya saka ya kira sa tun farko.

   "Dama idan babu damuwa ina son mu haɗu ne, ko zaka iya zuwa gida ka same ni?." Sultan ya faɗa yana kallon Ajmal wanda ya haɗe rai sosai tamkar wanda aka aiko wa da saƙon mutuwa. Nawaz kuwa cikin sauri yace.

   "Okay ba matsala zan iya zuwa." Ya faɗa yana jin wani irin farin ciki na taso wa daga ƙasan zuciyarsa.

   "Okay to bari na tura maka da address ɗin" Sultan ya faɗa yana katse kiran sannan ya shiga tapa saƙo ya tura masa.......


   Barkanmu da dare da fatan mun yi hutun weekend lafiya.

   *Oum Fatima*
       ***

Want the next chapter?

ui.create_a_free_arewapen_account_to_save_progress_unlock_paid_chapters_fol