Free chapter · Read without an account
019
by Kansa'u Bello · MEERAH
*MEERAH*
*019*
"Okay to bari na tura maka da address ɗin." Sultan ya faɗa yana katse kiran sannan ya shiga tafa saƙo ya tura masa. Ajiye wayar ya yi ya juyo ya kalli Ajmal da fuskar nan take a matuƙar ɗaure yace.
"Yana zuwa yanzu, may be ma ya riga Barrister ɗin ƙaraso wa."
"Okay." Kawai Ajmal ya faɗa a taƙaice yaci gaba da abinda yake yi a laptop ɗin dake saman cinyarsa. Shima Sultan ɗin bai damu kasancewar ya san halin Ajmal ɗin na rashin yawan magana, yau kuma ya lura ƴan miskilancin suna kusa.
Don haka ya rabu da shi ya zaro wayarsa ya saka kiran budurwarsa mai suna Amani, wacce ƴar abokin Dady ce suka ƙulla soyayya da ita. Yanzu haka akwai alƙawarin aure a tsakaninsu da zarar ta kammala karatunta wanda ta fara yanzu, wanda zai yi dai-dai da kammala master's ɗinsa shima.
Yanda Sultan ɗin ya kwantar da murya yana faman rarrashin Amani, a kan rashin zuwan da bai yi ba ne ya saka Ajmal dakata wa daga abinda yake yi ya zuba masa ido cike da mamaki, jin kaifin idanunsa a kansa ne ya saka shi ɗago wa ya kalle sa haɗi da ɗage masa gira ɗaya irin yaya dai ɗin nan?.
Harara Ajmal ya zuba masa ƙasa-ƙasa ya furta.
"Kaji kunya Sultan, girma ya gama faɗuwa." Ya faɗa yana mayar da kansa ga abinda yake yi. Dariya ce ta kama Sultan ɗin hakan yasa ya bawa Amani uzuri a kan zai kira ta, ya kashe wayar sannan ya fuskanci Ajmal yace.
"Da nayi mezaka ce naji kunya, har da wani girma ya gama faɗuwa?." Harararsa ya yi sannan taɓe baki yace.
"Da ka zauna kana kwantar da murya wa ƴar ƙaramar yarinya da sunan soyayya mana." Ya bashi amsar cikin yanayin rashin damuwa. Dariya Sultan ya ƙyal-ƙyale da ita, sai da yayi mai isar sa sannan yace.
"Man baka san soyayya bane shi yasa, a yanzu kai da bishiyoyi duk ɗaya kuke a wannan fannin. Sai ka shiga ajin sannan zaka gane me ake ji." Sultan ya yi maganar cike da tsokana yana kallonsa.
Ai kuwa Ajmal ya shaƙa don pen ɗin dake saman table ɗin dake gabansa ɗauka ya jefa wa Sultan ɗin, saboda kalmar bishiyoyi da yake tsokanarsa da ita duk lokacin da suke irin wannan hirar.
Kaucewa Sultan ya yi yana dariya don dama yana sane ya ya furta hakan don ya tsokane sa, kiran Nawaz da ya shigo masa ne ya saka shi dakata wa daga dariyar da yake yi ya ɗaga kiran.
*Abuja, B. M. G Mansion....*
*Mamy...*
Tun bayan ficewar ta a ɗakin Abby ta nufi nata bedroom ɗin cike da takaicin da ya shaƙa mata, bakin makeken gadonta ta zauna ta saka kiran ƙanwarta Abida (Mahaifiyar Jauhar wacce suke son haɗa wa aure da Ajmal). Bugu biyu ta ɗauka da sallama.
Gaishe ta Abida ta fara yi, ta amsa mata murya a cunkushe da ɓacin ran da take ciki.
"Yaya Na'imatu lafiya kuwa naji muryarki haka, ga ƴarki ma yanzu ta kirani tana kuka wai Son ɗin yaƙi dawo wa?." Abida da ƴarta Jauhar ke kira da Mimi ta faɗa cikin damuwa. Tsoki Mamy ta saki cike da takaici tace.
"Ki bari kawai Abida, na rasa wannan masifa dame tayi kama. Ka haifi yaro da cikinka amma wata tazo ta mallake shi!." Ta ƙare maganar cikin ɓacin rai.
"Me yake faruwa yanzu kuma, kiyi min bayani yanda zan gane Yaya?." Mimi ta faɗa tana gyara zamanta. Bayanin yanda suka yi da Abby yanzu a kan umarnin zuwan da ta bawa Ajmal tayi mata. Cikin ɓacin rai itama Mimi tace.
"Kina nufin a kan case ɗin yarinyar ya ɗaga tafiyarsa London ɗin kuma Alhaji Bashir ɗin ya zuba masa ido?."
"A kansa mana, ke sai kin ga yanda suka ɗaga hankalinsu da aka kira ba'a ga yarinyar ba, sai kace wanda aka ce musu an ɗauke Fatima!." Mamy ta faɗa tana jan ƙwafa.
"Maganar gaskiya Yaya sai kin tashi tsaye kin ƙwaci Yaronki tun kafin wuri ya ƙure maki, don ni a zamanin nan banga a inda ake kyautar ɗa sukutum da guda ba sai a wurin Alhaji Bashir. Yaron ma kuma irin Ajmal." Mimi ta faɗa cikin son ƙara tunzura ta, don ta lura cewar matuƙar Ajmal ɗin bai dawo ƙarƙashin kulawar Yayar tata ba, zai yi wuya mutanen can su bar shi ya auri ƴarta Jauhar dake haukar son sa.
Maganar Mamy ce ta dawo da ita daga tunanin da ta tafi inda take cewa.
"Ya zan yi ne Abida? Kina ganin duk wani yunƙuri da zan yi sai Abby ɗinsu ya daƙile sa, yanzu fa umarni na bawa Ajmal a kan ya taho gida amma mutumin nan ya kira sa yace ya zauna ya kammala abinda yake yi sannan. Sai kace in baya nan shari'ar ba zata yiwu ba!." Ta ƙare maganar cikin tsananin ɓacin rai.
Murɗa ƙofar da aka yi aka shigo da sallama ne ya saka ta katse wayar ba tare da ta kammala sauraron amsar da Abida ke bata ba, ta dai ce mata zata kira ta daga baya. Ƙara haɗe rai ta yi sosai saboda ganin Abby ne mai shigowar, don har yanzu bata huce daga abinda ya yi mata ba.
Abby da ya san halin kayarsa sai bai damu ba don ya san bata taɓa iya fushi da shi, ko da tayi da kanta take hucewa ta neme sa su shirya. Taka wa yaci gaba da yi cikin ɗakin yana kallon yanda ta ɗauke kai ta juya masa baya, shi abin ma sai yaso bashi dariya. Don ya tuna masa da lokacin ƙuruciya, don haka take masa in tana fushi da shi.
Yana zuwa ya ranƙwafa ya rungume ta ta bayan yana cewa.
"Ayi haƙuri a huce haka, bawan Allah tafiya zai yi addu'a yake buƙata a yanzu." Ya ƙare maganar yana ƙara rungumeta da kyau. Ajiyar zuciya ta sauke ta juyo ta rungume sa back. Ɓoyayyen murmushi Abby ya saki yana jin-jina wa soyayyar da Na'imatu ke yi masa, wacce tasa bata taɓa iya dogon fushi da shi.
Allah ya sani shima yana matuƙar sonta, sai dai hakan ba zai sa ya zuba mata ido yana kallo tana yin abinda bai dace ba.
"Yanzu kuma sai yaushe zaka dawo?." Muryarta ta dawo da shi daga tunanin da ya tafi. Ajiyar zuciya ya sauke sannan yace.
"1 week zan yi na dawo in sha Allah."
"To Allah ya tsare, Allah ya dawo min da kai lafiya." Ta faɗa tana miƙe wa tsaye ta amshi ƙaramar jakar dake hannunsa suka fita don yi masa rakiya.
"Ameen." Ya amsaata da ita sannan suka ci gaba da tafiya.
Har Compound ta raka sa ya shiga mota driver yaja suka tafi sannan ta koma cike tana jin kewar sa na kamata.
A Palo ta zauna saman ɗaya daga cikin Couches ɗin dake wurin ta ƙwala kiran Fatima, ba'a jima ba matashiyar budurwa wacce zata iya kaiwa 17 ta sauko daga sama.
"Gani Mamy." Ta faɗa tana zama kusa da ita.
"Kije ki kira min Jauhar a ɗakinta." Mamy ta faɗa tana kallonta.
"Okay Mamy." Fatima ta faɗa tana miƙewa ta haura saman. Ba'a jima ba suka sauko tare da Jauhar ɗin, matashiyar budurwa ce da zata iya kaiwa 22 years.
Tana da kyau dai-dai gwargwado musamman da ya haɗu da gyara da yanayin sukunin rayuwa da take ciki.
Tana zuwa ta kwanta jikin Mamy ta fashe da kukan da kana ganinsa ka san na tsan-tsar taɓara ne. Rungumeta Mamy tayi a jikinta tana rarrashinta da tambayar ta abinda ya saka ta kukan.
Cikin muryar kukan tace.
"Mamy ba Yaya Jam bane yaƙi dawo wa, kuma ina ta kiransa baya picking calls ɗina!." Ta ƙare maganar tana jin tamkar tayi tsutsuwa taje ta isko shi a inda yake.
Jauhar na matuƙar son Ajmal sosai tun ma kafin ta ƙarasa sanin kanta ta tsinci kanta a cikin soyayyar sa, shine kalar mijin da take so take fatan ta mallaka a rayuwa. Don ya haɗa komai da ake buƙata a wurin Namiji, tun daga kyau, nasaba kuɗi, kwarjini da wani irin Class da yake da shi.
Wannan dalilin yasa kai tsaye ta sanar da Mahaifiyarta cewar tana son sa, itama bata jira komai ba ta faɗa wa ƴar'uwata wacce ta yi mata alƙawarin cewar Ajmal bashi da mata sai Jauhar in sha Allah. To tun daga nan fa Jauhar ta addabi rayuwar Ajamal ta zama mayyarsa.
Duk lokacin da ta buƙaci ganinsa ita take wanko ƙafa tazo gidan su, daga ƙarshe ma tare wa tayi a gidan aka bata ɗakinta. Sai ya tafi Kano ne ita ma take tafiya nasu gidan.
Wannan kenan.
Rarrashinta sosai Mamy ta yi haɗi da yi mata alƙawarin cewar ya kusa dawowa da zarar ya kammala abinda ya kai sa Kano ɗin zai dawo, da wannan ta samu ta lallaɓa ta ta haƙura saboda Jauhar ɗin rigimammiyar yarinya ce da Iyayenta suka sakaltata kasancewar ita kaɗai Allah ya basu.
*Kano.....*
A can Kano kuwa Nawaz ya zo kamar yanda Sultan ya buƙata, koda ya iso ƙofar gidan tsayawa ya yi ya kira Sultan ɗin ya sanar masa isowar tasa. Shine ya kira securities ɗin bakin ƙofa ya basu umarnin shigowa da shi inda suke.
Har cikin rumfar da suke zaune ɗaya daga cikin securities ɗin ya rako Nawaz, wurin zama Sultan ya nuna masa fuskarsa ɗauke da murmushi. Hannu ya bashi suka yi musabiha cike da mutuntawa, satar kallon Ajmal Nawaz ya yi wanda kansa yake saman laptop ɗinsa yana faman danna wa.
Bai ko ɗago ba bare ya nuna ya san da zuwan sa wurin ba, wanda ya saka Nawaz ɗin kama kansa sosai. Sultan na lure da satar kallon Ajmal ɗin da Nawaz keyi don haka ya yi murmushi yana jin-jinawa miskilancin ɗan'uwan nasa kuma Amininsa. Ajmal ɗin ya kalla ya yi gyaran murya yace.
"Man ga Nawaz ya ƙaraso." Sai da ya mula don kansa sannan ya ɗago ya yi wa Nawaz ɗin kallo ɗaya ya ɗauke kai yana cewa.
"Barka da zuwa." Amsa wa Nawaz ya yi haɗi da gaishe sa, don ko ba komai Ajmal ɗin ya girme sa, uwa Uba kuma shine kwarjinin da yake yi masa duk lokacin da suka haɗa ido da shi.
Waya Sultan ya ɗauka ya kira Momy yace a bawa Meerah ruwa ta kawo musu suna garden, ɗagowa Ajmal ya yi ya kafe Sultan ɗin da ido jin yace wai a bawa Meerah ruwa ta kawo, bayan duk masu aikin da suke a gidan. Kamar zai yi magana sai kuma ya fasa ya mayar da kansa ga abinda yake yi.
Sultan kuwa ya san kallon da yake masa sarai don tun ba yau ba in friends ɗinsu suka zo gidan baya barin Meerah tana zuwa wurin, ko wani abu suke buƙata sai dai ya saka ɗaya daga cikin su Aryan ya yi musu.
Shima ya yi hakan ne saboda tazo su gaisa da Nawaz ɗin don ko ba komai shi ɗin wanda ya ceci rayuwarta ne daga cutarwar da aka so yi mata.
**** A ɓangaren Nawaz shima tunda aka ambaci sunanta zuciyarsa take doka tsalle da ɗokin murnar ganinta, sai dai ya yi iya yinsa wurin ganin ya danne hakan a cikin zuciyarsa ba tare da ya bayyana ba. Ko don wan nan Sadaukin Yayan nata da ya cika wurin da kwarjininsa.
Yana cikin wannan yanayin ne siririyar muryarta tayi sallama, kasa jurewa ya yi sai da ya juya ya kalli inda take tahowa. Idanu suka haɗa ya sakar mata tattausan murmushi, ita ma murmushin ta sakar masa tana ƙaraso wa inda suke.
Juyowar da Nawaz zai yi da nufin gyara zamansa, sai idanunsa a cikin na Ajmal da ya bar abinda yake yi ya tsare sa da kakkaifan kallon da ya saka shi duƙar da kai ƙasa babu shiri......
*Oum Fatima*
***