Free chapter · Read without an account

18. ... tawakkalin da nake so...🖊️

by Noor · RU'UYAA (The dreams we never lived)

                

Da na shiga gidan,daurewa nayi na hana kaina kuka na danne baƙin cikina kuma na hana zuciya ta..tambayoyin da take rattafo min a duk sanda abubuwa suka kasance kamar haka...

Dogon numfashi naja sannan na shige cikin gidan ina kallon tsakar gidan da ba kowa sai na wuce ɗakin Mama

'' Ni babban abinda yafi damuna kuma yake ban tsoro saratu shine idan fa wata rana sukayi ƙoƙarin....'' ɗaga labulen da nayi ya katse Mama daga ƙarasa faɗar abinda take faɗa duka su biyun suka jiyo suna kallona kyakkyawar fuskar Mama dake ɗauke da damuwa tayi saurin canja wa zuwa mai walwala inna sarai take zarar ido...su biyun daka gansu kasan yaya da ƙanwa ne, nayi nadamar ɗaga labulen dama na bari na gama jin abinda zata faɗa amma kuma ata wani fannin Haramun ne laɓe aiko? na sassautawa kaina...

'' Abeedah har kin dawo?" Inji inna sarai da alamun rashin gaskiya jinjina kaina kawai nayi...sai na shigo cikin ɗakin na zauna gefen Mama tareda kwantar da kaina saman cinyarta,ta ɗaura hannun ta saman goshina... '' Mama dan Allah ayi fate yau...''

'' wai fate,na bishi da gudu ba wando...!" Anaam ta hankaɗo labulen tana harara ta

 '' to uwar yan marasa kunya shi za'ayi bari in tashi ma kigani...'' kwantawa wurin Anaam tayi tana birgima ita ala dole baza'ayi fate ba

'' yauwa inna sarai sai dake...'' na faɗa ina dariya da son ƙular da Anaam...

'' ai sai dai in kwana da yunwa wallahi...''

'' cikin ki kona wani? Ke kika sani...'' miƙewa inna sarai tayi ta fita Anaam biye da ita...nikam na raka su da dariya 

'' Ya kike?" Mama ta tambaya da kulawa, mirginawa nayi ta yanda ina kallon fuskarta batareda na tashi daga jikinta ba...ita da Asma'u kamar an tsaga kara duk da Mama ta tsufa idan ka kalleta zaka gane ba ƙaramar kyakkyawar budurwa akayi ba lokacin yarinta

'' dama banda lafiya ne?" Na mayar mata da tambayar tayi murmushi 

'' ba wannan rashin lafiyar nake tambaya ba Abeedah...ina nufin ya kike ji a ranki yanzu?" 

'' oh...'' sautin ya fito daga bakina ya nake ji yanzu? Babu komai bana farin ciki bana baƙin ciki a dai dai wannan lokaci ban san nan da anjima kaɗan ba

 '' babu abinda nake ji'' na mirgina na koma gefe...'' wani abu ya faru a waje?" Tambayar data yi yasa na juyo na kalli fuskar ta...'' na lura da sanda kika shigo...''

'' A'e ce tace wai Fuskata kamar anyi ƙunar baƙin wake...'' murya ba amo maganar ta fita

'' hmm..ke kuma me kika faɗa mata?" 

'' nace ƙila idonta ne bai gani da kyau tunda ido ɗaya ne da ita...kuma na faɗa masu bana son wasan banza tunda sunce wai wasa suke niban iya ɗaukar wasa ba...Mama meyasa mutane basa tunani kafin su faɗi magana ne?" 

'' kowa da yanda yake Abeedah..ba zaki iya sa mutane suyi yanda kike so ba...'' ta fara sai na juyo ina kallon fuskar ta,ta cigaba da faɗin '' amma kina da damar zaɓin yanda zaki tunkari abinda suka faɗa ko sukayi....zaki iya kallon alkhairi ko gaskiyar dake cikin maganar su,sai Kiyi aiki da wannan,Kiyi farin ciki ki cigaba da rayuwar ki...ko ki kalli sharri da ƙaryar dake cikin maganganun su,sai ki bari hakan yayi tasiri a kanki sai ki kasance cikin baƙin ciki da damuwa da rashin karsashi....''

Ƙasa tayi da kanta idonta cikin nawa '' ina so koda yaushe ki kasance mai tunani mai kyau koda baki fahimci abinda ke faruwa ba..Kiyi tawakkali ki fuskanci gaba da ƙwarin guiwa da kuma yarda da cewa Allah ya isar maki abinda yayi shine daidai...'' gyaɗa kaina nayi duk da ban fahimci inda maganar tata ta dosa ba...naso inyi mata magana akan abinda naji suna magana akai itada inna sarai,kafin in tambaye ta naji inna sarai tana ƙwala min kira '' tashi ki tafi...'' 

Tashi nayi na fita daga ɗakin ina jujjuya maganganun ta amma na kasa fahimtar me take nufi...

Anaam na fara gani a tsakiyar gida tana jajjagen kayan miya bakin na yayi tsawo kamar mazurari... Asma'u tana baye inna sarai a kitchen tana fita wuta..duk hayaƙi ya baɗe wurin ... '' xoki kula da wutar bari in wanke tsaki...'' tayi maganar idonta cike da hawaye hanci majina ba shiri na saki dariya '' gaskiya dai bari in wanke tsakin ke kyaji da wuta...'' 

'' ke uwar son banza ko?" Girgiza kaina nayi ina cigaba da dariya na shiga na ɗauki tsakin dake cikin ƙwarya... Ɗakin Mama Asma'u ta wuce bayan ta fito daga baye... ba kamar Abeedah ba nesa da Mama ta zauna tana binta da ido da alamun magana a bakinta

'' ƙaraso nan...'' sai ta tashi ta isa inda Mama take,ta kwantar da kanta saman cinyar ta, zame ɗan kwalin kanta Mama tayi tana shafa gashin ta tace

 '' akwai abinda zaki faɗamin ne?" Asma'u tayi shiru na lokaci dan batasan inda zata fara ba kuma bata san me zata ce ba

 '' zaki iya faɗamin ko meye ne...ni Maman kice...'' mama ta ƙarfafa mata guiwa

'' ina son Khalil...'' shiru ne ya biyo bayan maganarta hannun Mama dake motsi saman gashinta ya tsaya cak... hawaye Masu ɗumi suka silalo daga idon Asma'u...kafin kuka mai ƙarfi ya biyo baya jikin Mama yayi sanyi.haɗiye damuwarta tayi da taushin murya tace 

'' meyasa kike kuka?" Tashi zaune Asma'u tayi ta riƙo hannun Mama ta ɗaura saitin zuciyarta '' duk da yanda zuciya ta ke kiranshi...shiɗin burine da bazai taɓa kasancewa ba Mama...na tabbatar yana da masoya da yawa..kuma daga ƙarshe niɗin yarince kawai daga cikin wa'yannan ɗinbi jama'ar... I'm Just a girl part of the crowd...'' rasa abin faɗa Mama tayi kawai sai ta jawo Asma'u ta rungume ta tana shafa bayanta...'' akwai Allah Asma'u...ki cigaba da addu'a...'' 

*****
Bayan Isha'i dukan mu zaune muke saman baranda yau ma ba wuta sai fitilar da muka kunna daga gefe, akwai iska mai sanyi da taurari kaɗan kuma akwai hadari ,cikin wani ƙaton tire inna sarai ta zubo faten da cokula kowa ɗaya ɗaya muka zauna a cycle nida Asma'u gefe da gefen Mama..inna sarai da Anaam gefe ɗaya,ƙamshin faten mai sa yawun mutum su tsinke amma dai a ganina yayi yawa... '' kai wannan fate yayi mana yawa inna sarai...'' Asma'u ta rigani faɗa taɓe baki inna sarai tayi '' munanan daku wannan mai cikin zanen saita nemi ƙari shine yasa na ciko faranti....'' dukan mu muka yi dariya harda Mama

 tana harare harare tace'' ai dai lafiya ke ci.yanzu idan mutum baida lafiya ko kaza aka ajiye gaban shi sai dai yayi ta lasar baki..ku barni inci abinci na dan Allah...'' 

'' Ina bayan ki Sha'awanatu...'' Mama ta goyi bayanta,ajiye cokalin Anaam tayi taje ta wanko hannu ta dawo ta tsunbula ciki,kowa nashan fate da cokali ita da hannu take sha harda wani ' zuruf zuruf 'take...inna sarai ba abinda take sai aika mata harara faten yayi daɗi sosai bayan mun gama muka zauna a wurin Anaam tana bamu labarin garinsu mun sha dariya ba kaɗan ba...'' akwai wata yarinya mai suna Salame kusa da gidan mu suke wai ɗan ƙaramin bunsuru take goyawa a baya a matsayin jaririnta ko bari batayi ya taka ƙasa...ɗan bunsuru ko ya kafa tsuwa musamman idan tasa zane ta goye shi....''


'' Haahaa! kai.wai mutum da goyon bunsuru ina Lafiya..'' inji Mama...

'' wallahi ko..ranar an ɗaura sanwa saman wuta,bunsuru garin kwaɗayi ya toye baki yana ta tsala ihu '' Inna sarai tayi maganar wurin dariya har saida ciki na yayi ciwo...kuma naji daɗin kasancewar mu tare a wannan lokacin..hakan ya rage min girman damuwa ta ba kaɗan ba....


Washegari da muka tafi makaranta,na iske Jay d da Diyaam har sun iso sannan ajin shiru,kusan kowa ya mayar da hankali yana rubutu akan wata farar paper wurin zaman mu muka isa nida Anaam muka gaishe da wa'yanda ke kusa kusa,farar paper nima ta miƙo min.. Diyaam kuma taba Anaam... '' me zan yi dashi?" Dakatawa tayi da rubutun ta '' ai dole sai da wannan su xasuyi amfani dashi wurin cika bayanan ki,suna, ranar da aka haife ki,me kike so ki zama da sauran su...''


'' oh...'' na furta a hankali...na dawo da idona kan paper,me nake so in zama? Ban taɓa tunani akan wannan ba tsawon rayuwa ta ban taɓa ganin wani abun daya birge ni ba naji ina so in zama sunana na rubuta da sauran abubuwan da aka buƙata na ajiye biron batareda na cika inda aka tambayi me muke so mu zama ba''.na gani...'' Diyaam ta ɗauki paper tana dubawa kafin ta ajiye tana nuna min

 '' nan baki sa komai ba...'' ɗagowa Jay d tayi

 '' baki fahimci bayanin da na maki bane?" Ɗage kafaɗuna nayi '' ban san me nake so in zama ba ban taɓa tunani akai ba...''

Suka kalli juna kamar na faɗi wani gagarumin abu'' nima ban san abinda nake so in zama ba...'' Jameelah dake zaune daga gaban mu ta juyo...

Wasu ma daga cikin yan ajin mu sukace basu san abinda suke so su zama ba.. wasu kuma kawai suna rubutawa ne badan abinda suka rubuta ɗin shine burin suba...wasu kuma daga gida aka zaɓar masu abinda zasu zama...

'' kuna buƙatar career counseling...'' Jay d ta furta tana kallon mu... Ta sake fita ta tsaya gaban allo ta shiga rubuta sunan abubuwan abinda mutum zai iya zama.. tana bayani akai... 

Daga nan waya'nda suka fahimta ko suka ji abin yayi musu sai su zaɓa...nidai har lokacin ban sani ba...bana son in shiga abinda bana ra'ayi...

Wata yarinya daga can gefe...kowa na rubutu banda ita,ta mayarda kanta tana kallon waje..'' Amina kefa? Bazaki yi rubutun ba?" Hameeda ta tambayi yarinyar kowa ya mayar da hankali akanta ta sauke numfashi sannan tace '' idan akwai abinda nake so in zama ina so in zama ƙwararriya a fannin soyayya...wannan shine kawai...'' 


'' Oh abinda kaɗai ke ranki kenan?"

'' aure kike so ko meye?...''

'' awwn...kamar saliha...''

Sai zolayar ta ake ita dai murmushi ne nata tafa hannayen ta Jay d tayi kowa ya mayar da hankalin shi wurin ta '' eh...akwai...zaki iya zama love coach..mai bawa mutane shawara fanin soyayya..amma meyasa kike so ki zama wannan?" 
Jay d ta tambaya... murmushin yarinyar ya ƙara faɗaɗa...'' saboda idan nayi aure in sace zuciyar mijina ni kaɗai bazai kalli wata mace ba.. kamar yanda yake faruwa a littafi.. yarinyar da suke so ita kaɗai suke gani...''


'' ayyiriririri!!!!!ohhhhhh!" Yan aji suka ɗauka
Ameena ta rufe fuskarta da hijabin ta 

'' amma dai kin san wannan soyayyar sai a littafi ko?" wata yarinya ta miƙe saman wurin zamanta tana riƙe ƙugu


 '' yo dama fa? Mazan yanzu ko suna tafiya tare da matar su wata tazo wucewa sai sun bita dana mujiya na rasa uban me suke kallo...'' wata daban ta faɗa...

'' kuma sai ayi ta zuzuta kyaun jaruman abu zar takaici..kai mutum gaka ga kamar ka..ana ƙarasa mutum najin ɗaci...''

Nake sauraren su ina tankaɗe da rairaya akan kowane bayani da suke faɗi abu ya zama muhawara kowa yana bada nashi fahimta akan soyayya wasu na ganin irin soyayyar da ake yi a littafi har abada baza'a taɓa irin ta a rayuwar gaske ba...wasu kuma suna ganin zai yiwu

Hafsah tace '' ban sani ba koda gaske irin wannan soyayyar tana faruwa..amma ni...zan so in yarda da cewa,zata iya faruwa...tunda akwai Allah...kuma ina fatan samun irin wannan soyayyar ko fiye da haka...'' 

gungu mu kayi suna cigaba da hirar su akan soyayya nidai ina saurare amma a raina ba tun yau ba,nima ina fatan samun irin wannan soyayyar Jay d da Diyaam suma sun tofa albarkacin bakinsu...abu yayi ƙamari da har yan wani aji suna shigowa ajin mu dan ayi muhawarar dasu...wasu daga cikin masu zuwa littafan soyayya makaranta harda musaya suke...wannan yaba wancan wancan yaba wannan...nima na samu wani littafi Mai suna ' DA AKWAI CIWO CIKIN ZUCIYA TA...' Jay d ma ta ƙara min da wani na turanci tace '' tunda kin fara fahimtar turanci,karatun littafan turanci zai taimaka maki ki ƙara iyawa...'' duba littafin nayi... zanen cover wani namiji saye da baƙaƙen kaya irin na turawa da wata farar mata saye da baƙin gyale kamar hijabi ya riƙe fuskarta yana sumbatar goshinta sunan littafin ' HER SHIELD ' 

Shi kuma dizain ɗin littafin Hausar wata yarinya dafe da ƙirjinta da hawaye a fuskar ta...kamar ta karye fiye da yanda za'a iya gyarawa(broken beyond repair)

Jefa su nayi cikin jakar leda ta,hirar yan ajin namu na man daɗi sosai kowa sai kare abinda ya yarda dashi yake... suna kawo hujjoji masu wahalar sharewa...amma dai na zaɓi in yarda da cewa,wannan soyayyar zata iya faruwa a gaskiya kuma daga wannan lokacin na ƙudiri aniyar nemo tawa...


Sanda ake koyar damu lesson bayan an tashi,na mayar da hankali na ina ƙoƙarin fahimta,duk da ba duka na fahimta ba na fahimta to some extent...

🍁🍁: Naji su Abeedahtuwo kamar anyi turanci?

Eh mana turanci nayi...baki ji nace yanzu ina fahimtar karatun ba kamar daba? ai kawai ku shirya daga yanzu ina magana ina haɗowa da turanci dan in ƙara ƙwarewa kuma a san na iya ehe...


🍁🍁:🤭

Sanda muka koma gida,muna gama cin abinci Kasancewar babu wani aiki da zanyi na shiga karatun littafan dana samo na fara dana turanci ina da saurin karatu sosai duk da wasu kalaman sai dai in tsallake dan ba iya karanta su nake ba,wani abun ma ban ganewa haushin daya cika ni yasa na ajiye na turanci na dawo karatun Hausa inda nafi ƙaimi...rayuwar jarumar abun tausayi wato ita ɗin kamar babu ta, babu wanda ke lura da ita,babu wanda ke ganin ta..ba wai dan ita fatalwa bace sai dai saboda kamar ita ɗin bata da muhimmanci baga iyalanta ba.baga sauran mutane ba ko ƙawaye bata da babu wanda ke son magana ko mu'amala da ita...

Idan da ace rayuwa ta zata koma kamar haka? Allah ya raba ƙila mutuwa zanyi ya zanji idan zan wayi gari ace su Mama sun dena kulani babu Jay d a tare dani?



Har dare ina abu guda kwanakin da suka biyo baya na ƙara tsoma kaina cikin labarin..dan an fara kawo wa wurin daɗi sannan a makaranta ina iyakar bakin ƙoƙari na kuma a duk sanda na samu lokaci ina cigaba da neman aiki na har yanzu bamu faɗi a gida ba kuɗin da ake nema mu biya a makaranta Jay d tana ƙara taimaka min itama a nata fannin rayuwa ta cigaba da tafiya..ina jin sauyi tattare dani kullum ina Cikin murmushi idan na tuna irin soyayyar da ake zubawa a cikin littafin da kuma yanda nake ƙudurin samo tawa soyayyar kowa dake tareda ni ya fahimci nishaɗi na...ko aiki nake nakan tsinci kaina da hasashen faɗawa soyayya da nawa namijin novel...

A haka kwanaki suka cigaba da tafiya..har ranar da zamu fara mock ta iso...nayi karatu sosai a gida,a makaranta ma munyi tare da Jay d da Diyaam wasu kam sai ƙoƙarin shiga suke da littafi da pepopin da aka rubuta amsa akai tsaye muke a gaban block ɗin ajujuwan mu mu yan SS 3,sunaye aka fara kira daga A-Z aka bamu lambobi Nice lamba 25 a ajin farko Jay d lamba 113,a aji na biyu Diyaam lamba 305 a ajin kusa dana ƙarshe Anaam lamba 205 ajin su ɗaya da Diyaam Asma'u lamba 101 ajin su ɗaya da Jay d...

Ana kiran mutum zai shige kowa da seat ɗinshi...mun sha gargaɗi har kunnen mu yayi ciwo malamai kuma sai zagaye mu suke..duk dai irin abubuwan nan da ake idan za'a rubuta jarabawa dan tabbatar da cewa ɗalibai basu samu damar satar amsa ba shi ake mana yanzu... Paper farko English ne....yawu na haɗiye ganin tambayoyin da suke hararata jikina yayi sanyi naji hankalina ya fara tashi..na ɗaga kaina naga kowa na rubutu banda ni

'' ki tuna kada ki tsoro ta kija dogon numfashi idan baki fahimci tambayar ba ki tsallake ki amsa na gaba kada ki ɓata lokaci akan wanda baki sani ba...'' kalaman Jay d suka dawo min kamar lokacin take yinsu badan na yarda dacewa jan numfashin zaiyi wani abu ba naja ɗin na ɗauki biro na shiga rubutu...

Wanda ban sani ba in tsallake nayi mamaki dana ga cewa ina amsa tambayoyin da sauƙi... to da yake dai nayi karatu..na ɗago kenan naga wasu suna fito da littafi daga cikin hijabin su.. wai suna duba amsa taɓe baki nayi dan Jay d tace babu amsa a cikin littafi na mayarda hankali na akan paper ta bada daɗewa ba mukaji ance '' KAI KU TASHI!!!" 

Sai da naji hanjina sun kaɗa da sauri na ɗago naga ashe waya'nda suka fito da littafi ne aka kama taɓ ɗi jam sun wulaƙanta gaskiya Da ƙarfe sha biyu muka gama jarabawar ko kaɗan bana son yanda aka wani zauna ana faɗar amsar da ba daidai ba da wacce ke daidai hakan na tayar min da hankali '' ya jarabawar?" Diyaam ta tambaya '' jarabawa da godiya Allah yasa munci...''

''.haha..kada ki damu wannan ba itace mai muhimmancin ba gwaji ne kawai'' na gyaɗa kaina muka zauna ƙarƙashin bishiya bada daɗewa ba su Jay suka ƙaraso'' ya jarabawar?" Murmushi tayi min ta zauna kusa dani 

'' dama wannan jarabawa ce?'' tayi maganar da dariya nayi murmushi..itafa na manta...ashe yar baiwa ce....


Mutane da yawa suka taru a ƙarƙashin bishiyar muna hira,dayawa daga cikin mu sun damu da idan abinda suka rubuta daidai ne .. wa'yanda basu damu da sakamakon suba,suna burgeni cewa sukeyi abu mai muhimmanci da kansu suka rubuta sannan kuma sun yi iya ƙoƙarin su,sun barwa Allah saura irin wannan tawakkali shine zuciya ta take mutuwar son samu amma na kasa a koda yaushe Nasan da cewa akwai mutane da yawa da yanayin su yafi nawa ɓaci amma kullum suna rayuwa da murmushi da gode Allah..meyasa nima baxan zama kamar suba? 


'' kai dan Rabbi kuzo muyi wasa...'' Hameeda ta miƙe tsaye tana gyara rigarta...'' wace wasa zamuyi?" Wata daban ta tambaya

'' kacha (catcher) ni zanyi...'' Hameeda ta amsa mata...da yawa muka yarda.. muka shigo cikin wasar...tayi daɗi kamar kada mu dena amma lokaci yayi saurin tafiya. da ƙarfe ɗaya muka baro makaranta Diyaam ta tafi motarsu tana mana bye bye mu kuma muka bi Jay D a tata motar...gidan su zamu saboda lesson ɗin data ce zata dinga koya min...


Lokacin da muka iso Anaam bakinta ya kasa rufuwa sai santin girma da kyau'n gidan take itama Asma'u ta yaba...

Da muka shiga ciki Anaam harda yin luuu kamar zata faɗi tsabar ita yar drama ce

 '' ashe Aljannar duniya kike rayuwa a ciki Jadeedah?" Inji Anaam tana kallon ko ina ido waje da alamu ba ƙaramin burgeta gidan yayi ba samun innarsu mukayi zaune a parlor dukan mu muka gaishe ta da girmamawa ta amsa mana da fara'a da sakin fuska... '' Umma karatu zamuyi kin san mun fara jarabawa...ina Deen?" 

'' Deen bai dawo ba su kuma ki sama masu abinci kafin ku fara...'' godiya muka yi mata Jay d taja mu zuwa ɗakinta Anaam ta ƙara ruɗewa da ganin kyaun ɗakin... Asma'u take kallon ko ina amma bata taɓa komai ba,ba kamar Anaam ba...hijabin mu muka cire, ɗaya bayan ɗaya mukayo alwala mukayi salla muka sake komawa ƙasa har kitchen ta jawo mu ta buɗe fridge akwai abinci daban daban tace kowa ya zaɓi abinda zaici Anaam ita tafi kowo ɗaukar kaso mai yawa.ta bamu kunya ba kaɗan ba bayan mun gama duk wannan nida Anaam muka zauna Jay d na koyar damu ita kuma Asma'u take kallo a ƙatuwar TV'n su Jay d tunda ita bata buƙatar a koyar da ita. Study session ɗin yayi min daɗi sai da aka kawo wurin math naji raina ya fara ɓaci..amma Alhmadulillah sauran subjects ɗin na fahimta...sai bayan la'asar muka koma gida ...


Ranakun da suka biyo baya cike suke da wahala a wurina...kullum idan an tashi muke biyo Jay d gida don study session ɗin mu,bayan mun gama idan mun koma gida da wuri zan shirya in tafi neman aiki har sabon gari kasuwar kwari..da sauran wuraren da nake tsammanin zan samu aiki amma babu wani cigaba...ga jarabawar mu ta mock yanzu na fara jin wahalar ta har naga nawar mu gama...

A gefe ɗaya kuma ina cigaba da karatun littafai na...ina ɗan ƙara iya turancin..duk kalmar da ban san ma'anar taba,nakan rubuta idan na haɗu da Jay d sai in tambayeta ma'anar kalmar... A duk sanda na tuna kuɗin da ake tsammanin mu biya sai naji hankalina ya tashi gabana ya faɗi...ban san inda zamu samu wa'yannan maƙodan kuɗaɗen ba...duk sanda nake tunanin na fara samun sararin shan iska daga matsalolina sai wata ƙatuwar matsala ta kunno kai ta sake tayarda wayan'can na bayan da nake tunanin ba zasu sake damu na ba...


Zaune muke a parlon su Jay d muna kallon wani fim ɗin Hausa..dukan mu mun mayarda hankali ko ƙiftawa bama san yi...

Takun da mukaji a matattakala yasa muka juyo ba shiri dan dai mun san mu kaɗai ne a gidan,Maman su Jay d ta fita mamaki ya hanani motsi ganin wanda ke wurin shima yayi tsaye yana min murmushi..saye da baƙin wandon Gucci da farar riga da slippers...


'' Name sa...'' kafin ya iyar Anaam data sheƙo da gudu daga ɗakin Jay d tayo cikin shi ta bangaje shi dama ya kawo ƙarshen stairs ɗin faɗuwa yayi Itama garin ƙoƙarin taimaka mashi ta biyo shi suka faɗi tare ita a sama

'' Ahhh!!!"miƙewa mukayi muka isa wurin su muna musu sannu Abeed yayi kwance fuskarshi a yamutse alamun 

Want the next chapter?

ui.create_a_free_arewapen_account_to_save_progress_unlock_paid_chapters_fol