Free chapter · Read without an account

DA JININSA NAKE RAYUWA

by Sayyid · DA JININSA NAKE RAYUWA

“Tabbas burinki zai cika Dade, dan ni ba kamar Kubrah nake ba, ita ce ke yaƙi sai ta zama tauraruwa a gaban Alhaji, tauraruwar da shi ya zaɓi abarsa ya kuma nuna ta, ni ce uwar gida yabani duk wata dama, amma ya nuna Bilki ita ce tauraruwarsa, tun daga wannan lokacin na cire rai da Alhaji, abin da nake so ya yi ya gama da duniyar ya bawa yarana su ci dukiyarsu, nafi kowa yawan ‘ya'ya, ina da maza shida mata bakwai, amma da yake Alhaji butulu ne duk bai gani ba, ya zaɓi mai yara uku kacal, namiji ɗaya ne ma, y barni mai sha biyu ya kuma bar mai shida. Dan haka Dade ko yau kika so ki sallama Alhaji ya bar duniya, waɗanan kamfanunuwan duk siyar da su zanyi, yanda kike fatan kar sunan Musa Ɗankaka ya ci gaba da wanzuwa to ni zan taimaka miki.” 
Wata dariyar jindaɗi Dade ta yi, sannan ta ce. 

“Duk cikin matansa idan wata ta ce zata kawo min cikas a kan goge sunansa da nake son yi wallahi sai nabi ta kanta.” 
Dade na kai wa nan ta fice, bata tsaya ko ina ba sai ɓangaren su Al Qaseem, lokacin da taje yana shirin fitowa zaije ɓangaren Mimi, bayan sun gaisa ta ce da shi. 
“Ashe kun sasanta da Husna ko? To abu ɗaya nazo na faɗa ma, duk wani kurari da ihun banza da uwarka zata yi kar ya cire maka abin da ke ranka, Husna ce sai ka aureta dan har mahaifinku ya amince da maganar, kuma ya miƙa ta ga su iyayen yarinyar, idan har sabida wani cika baki na mahaifiyarka ya ja ka zubarwa da mahaifinka mutunci kasan ba zai taɓa yafe ma ba.”

Shiru Al Qaseem ya yi, ya san maganar Dade gaskiyya ne, idan har ya yi abin da zai taɓa mutuncin mahaifinsa to tabbas Daddy ba zai yafe masa ba, shi yanzu ba wannan ba ne ma yake damunsa ba, yanda Ashraf ya raina shi har yake yi masa wani banzan kallo. 

“Ka jini ko baka ji ba, na faɗa maka abin da yake gaskiyya ne.”
“Na sani Dade, kawai abin da yaron nan Ashraf ne rainin da ya yi min ya yi yawa.”
Taɓe baki ta yi, wanda yake al’adarta sannan ta ce.

“Kai ka fara siyawa kanka raini, da ka mutunta kanka a wajen mahaifinka da bai isa ba, daman kuma ba mutunci ba ne da shi ba son ‘yan uwansa yake ba, yana ganin kamar yafi kowa kuɗi a cikinku, idan ka siyowa kanka mutuncu ta hanyar faranta ran mahaifinka, kaima gaba zaka fi ƙarfin raini a wajensa.”
Tana kaiwa nan ta fice, tasan ta sanya masa abu mai nauyi a zuciya wanda zai haifar da babban rikici wanda bata fatan wani abu yazo ya hana wannan rikicin tashi. 

Husna, tun da Dade ta fita itama ta shiga ɗaki, tana zaune ne dai amma hankalinta da nutsuwarta suna tare da Al Qaseem, so kawai take su yi id biyu da shi, su yi magana ko zata sami sauƙi, ba Al Qaseem ya shigo ba sai ƙarfe sha biyu na rana, sabida maganganun da Dade ta faɗa masa sun kashe masa jiki har sai da ya zauna ya yi dogon nazari, sannan ya sami nutsuwar fitowa. 

A lokacin Husna na kicin tana dafawa Mimi jallop ɗin taliya da ta ce mata tana so, a cewar Mimi indai jallop ne ta abarwa Husna kayarta, taƙware a wannan fannin, ita kuwa Husna sam bata wani iya ba, kawai dai baiwa ce Allah Ya bata ko ba ita take girki ba, in dai ta sa hannu ko juyawa ne ta yi, to sai ɗanɗanon abincin ya yi daban. 
Husna na kicin taji suna gaisawa da Mimi, bayan sun gaisa ne Mimi ta kwaɗa mata kira, tana faɗin.

“Kin gama ne, idan kin gama ki fito ga Al Qaseem.” 
Shiru Husna ta yi Allah yaso ma ta kusa kammalawa, ba afi minti biyar ba ta fito hannu ta riƙe da food plast, sai da ta kaiwa Mimi shi cikin ɗakinta sakamakon bata falon, sannnan ta dawo wajensa. 
Shiru Husna ta yi masa ba tare da ta ce mai komai ba, shi kuma ya ƙura mata ido yana ta faman kallonta, sai can ya ce.

“Baby girl.”
Wannan Baby girl ɗin da ya faɗa ya tayar mata da wani abu, Uncle Dee ne ka ɗai ke kiranta da wannan sunan, yau sai gashi Al Qaseem ma ya kira ta. 
“Ki yi haƙuri, tun jiya da na dawo banda lafiya shi ya sa kika jini shiru.”
“Uhm.”
Kawai Husna ta faɗa ba tare da ta tanka ba, ya sake cewa.
“Haba Baby girl, ki yi haƙuri.”
“Ai ko text message ne sai ka yi min ko.”
“Hakane na manta ne, kuma na faɗa miki da ciwon kai na kwana na tashi, lokacin da kika zo tashi na kenan.”
“Kaje asibiti?”


Ya gyaɗa kai, sannan ya ce.
“Baki ce kin haƙura ba.”
Shiru ta yi dai bata ce komai ba, haka ya yi ta fama yana lallaɓata har ya samu ta sauko, suka hau hirar soyayya. Har ta faɗa masa abin da Daddy ya ce bayan an ɗaura auren zai mai da ita gida, shi dai kawai da ido yake binta, soyayyarta na sake shiga zuciyarsa. 
Idan aka ce an rabashi da Husna shi wai ina zai sanya rayuwarsa? Sai lokacin sallar azzahar sannan ya tashi ya fita, har lokacin kuma Dade bata dawo ba.
Bayan kwana biyu. 
Shirye shirye sun fara nisa, Daddy da kansa ya sake zuwa gida ya sanar da Abba Husna ta tsayar da miji, Abba yaji daɗi mussaman da ya fito daga gidan Alhaji Musa Ɗankaka, ya san ba zai taɓa bawa Husna wanda ba nagari ba. Ya sami ‘yan uwansa da maganar suma suka yi na’am, aka bada kuɗin aure aka sanya kwana goma za ayu ɗaurin auren. 
Hajiya Babba ta shiga ta fita ta karɓi kuɗaɗe wajen Alhaji Musa tana haɗa lefe, cikin kwana biyu ta haɗa lefe na gani na faɗa, wanda ya ƙara mata girma sosai a wajen Alhaji Musa, Hajiya Kubrah bata san ana yi ba sabida itama Dade bata nan ta koma Wudil sabonta aikinta, bata da nutsuwar da zata zauna tasan abin da ake yi a gidan. 


A Ɓangaren Mama kuwa daman tana da ‘yan kayyayakin da take tarawa Husna, waɗanda ta kwashe shekara da shekaru tana tarawa, Abba ya saki Aljihu sai fito da kuɗaɗe yake yi ana ta yiwa Husna siyayya, haka ‘yan uwanta maza duk wanda ya fita haka zai dawo da kaya tumuli wai na Husna, irin su blander, greater, Husna tana da sun fi kala biyar, Set ɗin Food plast kam bazasu irgu ba dan duk wanda ya fita da abin da zai shigo, cikin kwana biyar ɗakin Mama ya cika ya batse da kaya. Su Yaya Abdul duk inda suka ga kayan da suka san za ayi amfani da su a gidan amarya sai sun siya, a rana sai su shigo da abu iri ɗaya kusan dukansu, babu wanda ke gajiya kowa cewa yake bikin ƙanwarsu ɗaya tamkar da da dubu. 

Gidan Alhaji Musa. 
Kwata kwata baya gane abin da Hajiya Kubrah ke faɗa masa, ya dai san hayaniya kawai take yi masa a kai, a hankali Alhaji Musa ya ɗaga kai ya kalli Hajjya Kubrah da ke magana ya ce. “Kubrah wai me kike faɗa a kaine.” 
“Bangane ba Alhaji, ina maka magana ne a kan auren da ake so a ƙaƙabawa ɗana, na ce maka bana so, bana so to a barni mana.” 
“To amma ai shi yaron ya ce yana so, kuma shine ya kawo maganar da kan sa, Kubrah dan Allah ki riƙe girmanki, a yanzu haka bikin ya kusa, hatta da kayan lefe Hajiya Babba ta yi da kanta to sai me ya rage? Kawai ki sa masa a albarka a kai.” 

Ficewa ta yi ba tare da  ta ce masa komai ba, tana fita ta yi part ɗin Hajiya ba, ashe abun har ya kai haka, lallai yau sai ta face Hajiya Babba sai ta nuna mata ba tsoronta take ba, kuma wallahi duk sharrinta tafi ta, bata gudu duk wanda yake gudu ma shi ya jiyo. Babu sallama ta shiga cikin ɗakin Hajiya Babba, tana zaune kan gado tana ganin Hajiya Kubrah ta miƙe tana murmushi da faɗin. “Uwar ango, kaga surikar gidan malamai.” 
“Saratu ki fita a lamarina da ‘ya'yana na rantse miki da Allah, idan kuma ba haka ba wallahi zan yi miki abin da baki taɓa tunani ba.”  Murmushin jindaɗI Hajiya Babba ta yi, kafin ta ce. “Duk shirinki Kubrah a bayana kike, na rantse da assamadu sai na kai ki ƙasa.” 

“To zamu gani, ni da ke wanda bai fasa ba Allah Ya tsine masa albarka.”
“Ni kike tsinewa albarka Kubarh.” Hajiya Babba ta faɗa tare da ɗaura hannu aka ta fashe da ihu, kamar daga sama Hajiya Kubrah taji an ce.

"Khadija."

Tana waiga ta ga Alhaji Musa, ya ƙara cewa. "Khadija."

Yanayin da yake tafiya ka ɗai ya isa ya nuna ransa a ɓace yake, cikin fushi ya ce.

"Naji duka abin da kika faɗa, naji komai. Daga yi miki abuj arziƙi shine zaki mayar da shi na tsiya kenan? Kinsan ba a taɓa yin magana biyu a gidana ko? Aurene da yardar ubangiji sai mun ɗaurashi rana irin ta yau sai dai duk abin da zaki yi ki yi. Sannan kuma ina umartarki da ki bawa Hajiya Babba haƙuri anan wajen a yanzu."

Wani irin kallo Hajiya Kubrah ta yi wa Alhaji Musa sannan ta yi wa Hajiya babba, ita zata bawa Hajiya babba haƙuri? Ita da ake shirin cuta wannan ai bazat saɓo ba wallahi. 

"Magana nake miki fa?"

"Ki yi haƙuri."

Hajiya Kubrah ta faɗa, Alhaji Musa ma ya sake cewa.

"Hajiya ki yi haƙuri, ni kika yiwa kuma na gode Allah Ya ƙara girma."

"Amin Alhaji, na gode."

Hajiya Babba ta faɗa tana ci gaba da matsar ƙwalla, ganin haka Hajiya Kubrah ta matsa kusa da ita tana wani irin murmushi ta ce.

"Haba Hajiya Babba kukan ya isa haka, nagane kuskurena kuka na baki haƙuri, tabbas ke ce babba kuma duk abin da kika yi girman ki ne, na gane na yi laifi maimakon na gode miki sai na kushe, kawai ina mamakin yanda kika yi babban aiki irin wannan ba tare da kinsanr da ni ba. 

Amma Hajiya Babba alherinki ai bazai lissafu a wajenmu ba, ki yi haƙuri dan Allah."

Hajiya Kubrah ta ƙarasa maganar tana durƙusa a gaba Hajiya Babba, wacce mamaki ya kusa dakatar mata da numfashi, tarasa wane irin makirci Hajiya Kubrah take ji da shi a duniya,  Alhaji Musa ne ya katse mata mamakin ta hanyar cewa.

"Haba Kubrah au ta haƙura, ki miƙe tsaye komai ya wuce Allah ya ci gaba da haɗa kanku."

"Amin Alhaji, ai duk abin da muke yi a wajenka muka gani, ka haɗemu ka mayar da mu tsintsitya guda, kuma Hajiya babba tana ƙoƙarin bin irin wanna tsarin da kake yi, tabbas tun kafin aje ko ina na yi danasani, na yi na damar biyewa son rai na yi mata rashin mutunci. 

Hajiya Babba kamar uwa take a wajena, ki yi haƙuri dan Allah."

Hajiya Kubrah ta faɗa tana fashew da wani irin kuka mai cin rai, jiki a sanyaye Hajiya Babba ta tallafota tana faɗin.

"Babu komai ya wuce, ya wuce. Nima na san ba halinki ba ne hakan, na yi miki laifi ta hanyar haɗa kayan ba tare da na yi ko shawara da ke ba a matsayinki na mahaifiyarsa, tabbas abun da ciwo amma ki yi haƙuri."

"Ya wuce Hajiya."

Hajiya Kubrah ta faɗa tana rungumo Hajiya Babba, ganin haka ya sa Alhaji Musa juyawa, daman tun da Hajiya Kubrah ta fita yaji bai kamata ya zauna ba, shine ya tashi yaje part ɗinta bai same ta ba shine ya yo nan, a lokacin da ya shigo kuma Hajiya Babba taga shigowarsa tun da ita ce ke kallon ƙofa, shi ya sa ta canja abin da ta yi niyar faɗa ta hanyar cewa Me kike nufi. 

Yana fita Hajiya Kubrah ta cika Hajiya Babba, ta yi mata wani irin murmushi, sannan ta yi magana cikin raɗa raɗa. 

"Idan juranki sammako wajen makirci, to ni a tafe na kwana. Kaina baya taɓa kullewa Saratu, ni  khadija Kubrah, ba kanwar lasa ba ce."

Tana kaiwa nan ta fice ta bar Hajiya Babba baki a sake, lallaimw Kubrah, ta nuna mata ita ba ƙaramar katanga ba ce, dole sai ta miƙe tsaye dan ganin auren nan ya tabbatu tun da itama a jikinta take jin idan auren ya tabbatu kamar lokacin barin Kubrah gidan ne ya yi, sannan kuma lokacin mutuwar Alhaji ne ya yi. 

Ita bambancinta da Hajiya Kubrah shine, ita 'ya'yanta take so kawai da dukiya ko yanzu Alhaji Musa ya mutu takama gabanta ta siyar da komai tun da tafi kowa yawan 'ya'ya maza da mata tasan tabbas zata sami rabi na dukiyar alhaji koma fin haka, ita kuwa Hajiya Kubrah so take ta zama tauraruwa a wajen Alhaji Musa, ya zama ita ke jiyawa shi sannan 'ya'yanta kuma ke juya dukiyar, wannan shine bambancinsu, ita so take ma Alhajin ya mutu, ita kuma tana so ya rayu, to Allah Ya bawa mai rabo sa'a. 

*******

Hajiya Kubrah tana komawq part ɗinta ta ɗaura hannu akai ta fashe da wani irin ihu mai zafi, ta rasa abin da ke yi mata daɗi, wallahi wallahi ba zata bari Al Qaseem ya auri waccan yarinyar ba, ko da kuwa zata yi yawo tsirara ne, gashi Alhaji yana magana a kan auren saura sati ɗaya, wannan abune da ba zai saɓo ba, wankan kuturu da sabulo. 

Dole ma ta yi ihu dole ta yi kuka ko zata sami mafita, dole ta ɗauki babban matakin da zai zama gargaɗi na ƙarshe ga Al Qaseem wanda daga shi sai ƙoli, ko takan Dade ba zata bi wajen aiwatar da wannan hukuncin, dole ta nunawa Hajiya Babba ita ce ya haifi Al Qaseem kuma ita ke da iko a kan sa, yau ba sai gobe ba. 

Waya ta ɗauka ta dannawa lambar Al Qaseem kira, Al Qaseem da ke zaune a compound ɗin Mimi shi da Husna suna hira, duk wani nauyi da ke zuciyar yana raguwa a hankali a hankali idan yana tare da Husna, duk wata magana idan ta yi tana cire masa raɗaɗin da ke damunsa, tana sanye da riga da skirt na atamfa, Al Qaseem zai iya rantewa yaune na farko da ya ganta da riga da skirt, ita kullum cikin doguwar rigar atamfa ko abaya, kowani ɗinki da take yawan yi, material ne ake mata doguwar riga da shi sai a ratsa mata ado da gunguwar atamfa, sai ta yi ɗankwali da atamfar, yana lissafe tana da su sunfi kala 20. 

Ƙarar wayarsa ya katse masa maganar da yake shirin yi, ya ɗan dakata ya ɗauki wayar. Ganin sunan Hajiya Babba ya sa shi mayar da ita cikin aljihu tare da faɗin. 

"Allah dagaske nake miki baby girl, kwata kwata kayanan basu yi fitting jikinki ba, sai kika yi daban daban."

Husa bata bashi amsar tambayar da ya yi mata ba, sai ta ce.

"Wake kiranka?"

"A wajen aiki ne."

Ya bata amsa yana kallon fuskarta, Husna a rayuwarta bata son taga an kira mutum bai ɗauka ba, hakan yana matuƙar ɓata mata rai yasa mata tunanin itama idan ta kira ba za a ɗauka ba kenan. 

"To ka ɗauka mana."

"Me ya sa? Bana son abin da zai janye min hankali daga sauraron muryarki."

Ƙasa ta yi da kanta, ta rasa me ya sa take jin kunyarsa idan ya yi mata irin waɗanan kalaman, saɓanin Uncle Dee da ita da kanta ke yi masa irin waɗanann. 

"Kin yi ƙasa da kai."

Ɗagowa ta yi ta sakar masa murmushi, sai kuma ta ce.

"Bakomai, kawai ina tunanin yanda abubuwa suka sauya ne, haɗuwarmu da kai alheri ce gashi zaka zama silar komawa ta gidanmu."

Yaji daɗin kalaman Husna sosai da sosai, ya kuma fahimci yanda take matuƙar kewar gidansu da mahaifiyarta, shi kuma ya yi alƙwarin dauwamar mata da farin ciki. 

"Allah Ya tsara hakan ne, shi ya sa muka haɗu a wannan ranar dama sauran ranaku. Ke ɗin haske ce a gareni Husna, ina matuƙar ƙaunarki."

"Nima haka."

Ta faɗa a ƙasan zuciyarta kuma tana mamakin wace irin zuciya Allah Ya bata haka, da har ta iya amsar soyayyar wani ba Uncle Dee ba, wanda a sanadin son sa tabar gidansu ta tsinci kanta a wannan a duniyar, idan ta yi tunani kenan shi Uncle Dee kawai ya zama tsani ne na haɗa ta da wanda ƙaddara ta zaɓa mata, lallai Allah mai hikima ne. 

Ganin kiran Hajiya Kubrah ba zai ƙare ba yasa Al Qaseem ƙarƙare hirar tasu ya tafi, Husna na shiga ciki ta kira lambar Said Kibiya ta sanar da ita gobe za a kawo kayan lefenta, sannan kuma auren sauran sati ɗaya ya za ayi a sanar da 'yan munjibir, sai da Said Kibiya ta sha dariya sannan ta ce.

"Wai A sheshe ke ce kike cewa a sanar da aurenki da wani ba Uncle Dee namu ba."

"To ya za ayi."

Husna ta faɗa, dariya Said Kibiya ta yi sannan ta ce.

"An jima zan sanya ƙanina ya yi min kati sai na tura kowa, muce anko kuma baƙar abaya duk suzo da ita."

Girgiza kai Husna ta yi, sannan ta ce.

"A'a fa, ba zasu sanya min abaya ba, kawai kowacce ta ƙure adakatar, sannan a gayyatomin Aisha Sharif, tasan yayan mijin yayarta na aura ni ba saar yinta ba ce."

Dariya Said Kibiya ta kwashe da ita, sannnan ta ce.

"An barta mata Uncle Dee taje ta ƙarata, yanzu ya za ayi kisa Mama ko Mimi ɗin ta kira Mamansu Ali Kaita, kinga sai sunfi barin tazo."

"Ai yanzu zan sanar da Mimi ta kirata, chaɓ."

Husna ta faɗa tana miƙewa, kai tsaye ɗakin Mimi taje ta sanar da ita Mimi ta karɓi lambar wayar Maman Ali Kaita ta kirata, bayan sun gaisa ta sanar da ita komai, Mama ta ce in sha Allah zata zo ai Husna 'yar ta ce. Daga haka su Husna suka ci gaba da shirye shiryensu na baki.

A daren Said Kibiya ta tura da Iv group ɗin 'yan ajinsu, ta ce duk waɗanda ke kano da kusa da kano suna gayyatarsu, da yake mutane sun san labarin soyayyarsu da Uncle Dee aka yi ta magana a group ɗin, sai da Ali Kaita ta fito ta yi musu bayanin cewa Uncle Dee fa ba musulmi ba ne, babu aure a tsakaninsu. Ai kamar sun sami abun magana har washe gari haka aka dinga maimaita zancen, wasu suna basu taɓa ganinsa a massallaci ba, wasu suce har warin kafurci yake yi, wasu su ce suna ganinsa da cros, ƙarshe sai da aka yi babu daɗi da Aisha Sharif har ta fita daga group ɗin sai da aka sasanta aka dawo da ita, dayawa sunci burin zuwa bikin Abubakar Sheshe daman har yanzu ana kewar juna. 

Al Qaseem tun da ya shiga part ɗin Hajiya Kubrah take faman zazzaga mai masifa, kansa yana ƙasa ya kasa ɗagowa ya yi ido biyu da ita, cikin tsawa ta ce.

"Tun da ka shigo ina maka magana ka yi kunnen uwar shegu da ni, ba zaka yi abin da na ce maka ba kenan?"

Girgiza kai ya yi, hawaye na zuba a fuskarsa ya ce.

"Haba Hajiya, tayaya zan watsawa mahaifina ƙasa a ido, yau fara saura sati guda ɗaurin auren..."

"Kai dallah shashasha ka rufe min baki, dan yau saura sati guda sai aka yi mene? Ko ranar ɗaurin auren ai zaka iya cewa kafasa, kai ko an ɗaura ma zaka iya cewa kafasa ka danƙaramata saki sai kuma mene? Ina mai baka umarni kaje ka ce da mahaifinka kafasa."

"Ki yi haƙuri Hajiya."

Wani mugun kallo ta watsa masa, wai ta yi haƙuri ba zai yi abin da take so ba kenan shine zai hau bata haƙuri to wallahi yaci ƙarya ya kwana da yunwa. 

Zama ta yi a kan kujera da ke kusa da shi, sannan taa ce.

"Al Qaseem."

"Na'am."

Ya faɗa ba tare da ya ɗago ba, bayajin zai iya yi mata abin da take so.

"Kai da Ashraf waye babba?"

"Ni."

"Amma me ya sa yafika duk wani ci gaba? Baka ganin matar da yake aure 'yar gidan minister ce? Baka ganin yanda yake ƙoƙarin gina kansa, kai baka jin kishi a cikin a ranka? Baka jin me ya sa yafi ka? Baka jin damuwa a cikin ranka?"

"Hajiya ai ɗan uwana ne."

Ya faɗa duk da a ransa yaji babu daɗi, amma shi wannan ai ba wani abu ba ne tun da hakan bai da alaƙa da Ashraf ɗin, shi Husna yake so ba wata 'yar gidan minister ba, sannan kuma shima ai ba ƙarƙashin mahaifinsa yake ba, koƙarin gina kansa yake sai kuma me? Ya san akwai tarin matsaltsalo tsakaninsa da Ashraf amma wannan ai ba zai shafi soyayyarsu da Husna ba.

Ita kam Hajiya Kubrah kallon wane irin asarrraen ɗa ta haifa take yi masa dan bata taɓa ganin mara zuciya ko rashin sanin ciwon kansa ba irin Al Qaseem, ta kawo masa waɗannan points ɗin da zasu tunzura shi amma da yake sauna kira mana sakaraine idan kaga shashasha kira shi ku taho tare. Ko a jikinsa bai ji komai ba? Dole fa sai ta yi zazzafan gargaɗi zata sami abin da take so, amma bari ta fara da zuga shi ko za ayi dace.

"Kana ganin sabida Allah Bilki ta haɗa aurenku da yarinyar wajenta? Ta haɗa ne sabida ta dakushe karka zama wani, ni nan na shirya nema ma aure a gidan sarkin katsina, sabida ina so ka yi aure na kece raini, kaima kaje matsayin da Ashraf yake har ma ka wuce shi, kaje matsayin da bai isa ya yi maka kallon banza ba, ni nan na yi alƙwarin sai ka zama sama da kowa a cikin gidanan, kamar yanda zan zama tauraruwa a wajen Alhaji, haka kaima zaka zama tauraron da ke haskaka gidan, ita kuma Hajiya Bilki baƙin ciki ne zai kaita lahira ita da Hajiya Babba."

Shiru Al Qaseem ya yi, maganganunta kamar gaskiyya ne, amma zuciyarsa taƙi gasgata abin da take faɗa masa, sabida yana son Husna sosai har cikin zuciyarsa, yana son kawo mata farin ciki a rayuwa kamar yadda ya san itama zata kawo masa farin ciki a rayuwarsa, tun da yana sonta itama tana sonsa, shi bai ga amfanin auren wata 'yar sarkin katsina ba, ai ba lallai ba ne ya yi ya sota ko itama ta so shi, amma Husna ai ta shiga can ƙasan zuciyarsa ta zauna, cire ta sai dubu ta taro. 

"Kana ji ko Al Qaseem, a yanzu ina so ka tashi kaje ka sanar da Alhaji kafasa auren yarinyar nan, idan har ka yi haka ni kuma na yi maka alƙwarin nan da kwana uku sai ka zama tauraro a gidan nan, sai na nema ma aure a gidan arziƙi, sai na sa mahaifinka ya damƙa babban reshe a kasuwanci wanda zaka zama kafi kowa cikin gidan nan."

"Hajiya, yanda Alhaji ya shiryawa auren nan da zarar na faɗa masa haka to zai yi fushi da ni ne." 

Girgiza kai Hajiya Kubrah ta yi, kafin ta ce.

"Wallahi ba isa ba, ɗana yafi ƙarfin ayi fushi da shi, kaje ka sanar da shi ni kuma na ce ko ya yi fushin ba zai kwana ɗaya yana fushin ba, katashi kaje ka nuna musu nice uwarka, ni na haifeka na kuma isa da kai, ni kuma zan nuna maka kai ɗan nane, zan nuna maka nice tauraruwa a wajen Alhaji Musa Ɗankaka. 

Legendspen-Sayyid. 
***

Want the next chapter?

Create a free ArewaPen account to save progress, unlock paid chapters, follow this author, and keep reading across web and the Android app.