Free chapter · Read without an account
2
by Mamuh gummy · AASIYAH
Aasiyah
By
Mamuhgee
2
Qarasa sarewa kafafuwanta sukai daga inda take tsayen tayi qasa gabaki daya jikinta na sakewa idanuwanta na sauyawa zuwa tsananin ja da wani irin boyayyen radadin dayake bayyana a cikinsu mai kaifi da babu misali ta zauna dabas tana rintse ido jikinta na sakewa.
Taku biyu yayi da wani irin lafiyayyan xafi da nasa kakkaifan radadin dayake riqewa ya isa gareta yana tarota gabaki daya a jikinsa tareda fidda wani numfashi mai zafin da radadinsa ya saukar mata hawayen datake riqewa suka ciko idanuwanta sedai bushewan zuciya da idanuwanta bazasu bari su sauko a fuskanta ba saboda sama da shekaru baqin ciki da zafi sun gama busar da hatta ruwan jikinta takeji.
Ahankali hannunta daya ya motsa ta qanqamesa dashi tana jan numfashin kamshin dayake fita daga jikinsa wanda yake asalin kamshin mahaifinsa sak da sak daya sauya niimar dakin gabaki daya tana jin har abada duk jarumta da bushewan zuciya da ruhinta jin 'danta a jikinta da shaqar kamshinsa sune abunda kadai suke karya duk wata garkuwa da kangarewanta tareda karfi da jarumtarta tareda dawo mata da duk wata rauni da jin tana tsananin kewansa da kewan mijinta datake fatan ta bisa ko ruhinta da gangar jikinta zasu samu zama free da kowace rayuwan duniyar nan.
Sake kankameta yayi ahankali a jikinsa yana shaqar nata kamshin da dukkanin daci da baqin ciki tareda zafin da babu misali,zafin dayake tafasa kowace diqo ta jinin dayake yawo a jikinsa daya gama busar da kone zuciyarsa datake a bushen da babu sanyi ko rahama a cikinta,
Sake maimaita ambatar sunanta yayi da kai tsayen kalma mara hayaniya ko rawa
"Mammah"
Girgiza kai tayi hawaye na sake ciko idanuwanta ta saka kanta a kirjinsa ta kwantar ahankali tareda bude baki da sautin da babu wanda zaiji koda kuwa akwai wani a dakin sbd raunin gaske daya dabaibayeta a take hakama bakinta baya wata motsawa sosai tace
"Gobe wata shekarar ta sake zagayowa a cikin shekarun da suka tafi."
Ahankali kalaman suka ratsa kunnuwansa zuwa kirjinsa ya rufe oily idanuwansa da suka sauya wani iri ya budesu yana dan sake qanqameta jikinsa da wata irin zazzafar kauna da so tareda danne radadi ya bude bakinsa da sauti mai kauri da sanyin da ita kadaice kaf take samun wannan sautin daga garesa yace
"Wannan shekarar ce ta karshe kuma,
Hakama Wannan shekarar ce dukkanin wani buri da alkawari zasu cike Mammah"
Numfashi taja ta sauke ahankali mai zafi tana bude nata idanuwan da sukai jajir itama ta sake cewa
"Ko shekara nawa zaa dauka bazan taba gajiya da jira ba,
Na jira shekarun da suka wuce,
Zan jira wannan shekarar,
Hakama zan cigaba da jiran wasu shekarun masu zuwa saboda cika dukkanin wani buri da alkawarin da yake hannunka."
Hannunsa yakai fuskanta ya kama ahankali ya dago daga kirjinsa yana kallanta ya zaro handkerchief black daga aljihun wandonsa ya fara goge fuskanta ahankali yana magana a natse da wani irin yaren da na hausa ne amma sam babu wani abu da duk mai sauraro zai gane itama a natse take maida masa wanda kaf duniya idan ba su biyun ba babu wanda zai taba fahimtar magana ce suke da isarwa da juna cikakken bayanai.
Ya jima sosai a ciki suna magana kafin suka kammala ya miqe tsaye da ita hannunsa yana kame da nata ya bude kofar dakin wadda tayi daidai da juyowan wainda ke kofar dakin a tsaye daga can gefe.
Ita suka zubawa ido ganin yanda take yagar kanta tana yagar farar fatar jikinsa mai tsananin lafiya da daukan ido a cikin all black kayan dake jikinsa.
Da sauri suka qaraso su biyun a tare suna kamata da kulawa suna danne hannuwanta sbd hatta kanta duk ta jiwa ciwo gashi da alama sam babu sauki ko alamar warkewa a tattare da ita suke gani.
Suna kamata ya saketa a hankali yana kasa kallanta ya dauke kansa yana wucewa gaba take Taj yabi bayansa shima yana kasa iya bin inda ake tafiya da ita da ido sbd yana jiyo yanda take bigewa tan kwacewa.
Kai tsaye inda mota take suka nufa Sir IB na bayansa yana masa bayanin yanayinta sunata kokarin ganin ansamu sauki ko sassauci a duk wannan shekarun amma babu kowace sauki dan hakama an hakura likitan Kwakwalwa ya dena zuwa dubata amma insha Allah zai tabbatarda ansake dawo da treatment dinta.
Duka wannan bayanin da Sir IB din yakeyi baice komaiba kaman yanda bai tsayaba tafiya yakeyi cikin wata irin Aura mai dumi idanuwansa a hanya kawai.
Tin kafin ya isa Taj ya rigasa isa a zafin nama ya bude masa kofar motar ta gaba yana isowa ya dakata cak batareda ya juyoba ya bude baki ya furta kalamai biyu da suka sanya Sir IB dakatawa yana gyada kai a natse da bada girmamawa yace
"Yes Sire"
Shiga motar yayi Taj ya rufe tareda zagayawa ya shiga tareda tada motar wadda ko wata sautin hayaniyar komai batada yaja take suka fice daga prison din wanda suna fita security cameras din koina da aka tsayar ta office din Sir IB suka fara aiki batareda mintinan sun sauya ba sbd tsari da tsaftar yanda ake tsayar dasu a kuma sake su.
Motar na ficewa kaman ko yaushe titi suka hau da wani irin speed take suka bace kaman walkiya batareda sanin ma wace hanyar suka bi ba daga kan titin.
******
BINNAH's GRAND RES
9:47 am
Babban hall maana sitting room din dayake grand din wanda yakeda tsananin girman da yake da bangarorin zama daban daban da tsari irin na asalin grand residents na asalin masu abun duniya da ilimin wayewa sosai da sanin tsarin jin dadi da kwanciyan hankali da cikakkiyar luxurious life,
A cikin babban palon/sitting room din akwai sama da wasu sitting rooms din biyar da bedrooms dinsu sama da bibbiyu hakama akwai hanyar babban dining room din grand din wanda yakeda girman gaske shima dauke da lafiyayyan royal Dining mai girman gaske dayake da kujeru sama da 15,
Baqi da yan uwa ne masu sauka da zama anan banqaren na qasa amma asalin jinin gidan kaf dinsu a sama suke sbd wata lafiyayyar rayuwar da duniyar ce a saman grand din datake da girma da bangarori da kowa yakeda nasa,
Akwai stairs na hawa saman wadda basu cika hawa ba ta can ba sbd akwai elevator da itace suke amfani da ita daga qasa zuwa saman dan kusan komai na grand din da tsarinsa da maaikatansu da tsarin rayuwarsu na rayuwar luxury ce da ita kadai suka sani suka kuma iya.
Sam masu gidan basu cika zama a qasa ba koyaushe suna sama kowa bangarensa yana harkar gabansa kokuma suna tare a palon saman suna hutawa da fira cikin kwanciyan hankali,
Cin abinci ne kadai yafi sauko da dukkaninsu a qasa main dining room nasu sai kuma idan akwai baqi ko yan uwa da suka zo zaa zauna anan ayi fira sai kuma idan sunyi raayi sunso shine zasu kasance a qasa din dukkaninsu suyi zaman fira ko jin dadi kawai haka.
BINNAH's shine sunan familyn nasu wanda yake riqe da power ta bangarori daban daban wanda kuma suke da hadin kai da zafi tareda karfi da wani irin tsari na kasa yadda da faduwa komai kankantarta sbd kowace step na rayuwarsu suna takasa ne bisa lissafi da wani irin tsaro da zallan kiyayewa da wata irin kakkarfan kididdigar da babu gurin kuskuren da zai bada kowace matsala ko illa bare faduwa a rayuwansu dan hakanne suke da iko mai karfi a hannunsu bayan dukiya da duniyar da suka tara.
Tin daga babban harabar BINNAH's grand din dayake jere da motoci kala kala wainda kusan suna cikin masu hawa irin wannan motocin kadai a qasar,
Asalin luxury cars ne da suke siya in dollars ba irin regular cars da kowa ke hawa ba,
A bangare daya na harabar gidan akwai 2 Ferraris daya fara daya black da suke a rufe daya daga cikin ahalin gidan ne wanda ya kasance baya fita koina baima taba fita ba koina tin shekaru masu dan yawa dan haka suka kasance a nasu bangaren daban sabanin sauran tarin motocin da ake fita dasu akai akai ana sauyawa.
Tsit ne koina ba hayaniya sbd ko securities na gidan professionals ne da suka san aikinsu kuma suke yinsa ba wasa dan haka suna gurin aikinsu,
Masu kula da tsaftar gidan da sauran ayyukan da suka shafi haraba da zagayen gidan suma suna nasu bangaren sbd kusan kowa tinda safe suke fara aikinsu su kammala batareda kaida kawo da hayaniyar da zata damu nutsuwar grand din ba da masu shi dan haka kusan kaf masu aikin gidan suma a cikin nutsuwa da kwanciyan hankali suke sbd tsarin rayuwar grand din.
Acan cikin gidan ma koina shiru sbd safiya ce lokacin fitowan basu gidan bai qarasa yi ba,
Iya masu aiki ne na can ciki suke ayyukansu cikin nutsuwa da qware tareda sabo,
Babban palon na kasa shine aka gama aikin gyaransa fes sanyi da kamshi ne mai sanyi da nutsuwa yake tashi koina sai kuma dining da shima kusan masu aiki uku ne suke aikin shiryasa da jere abincin breakfast dinda kusan kowa da raayinsa na breakfast din dan haka abincin yake kaloli sama da uku ma dan kuwa kowa da abinda yafi buqatan ci da safiyarsa.
Suna kammala shirya dining din suna kokarin fitowa daga dakin dining din elevator din dake kusa da hanyar dining room din ta bude take Hajiyar gidan babba ta bayyana wadda suka dan sauke kansu kasa cikin girmamawa da kulawa sosai tareda sabo Asmau ta bude baki tace
"Barka da saukowa Ummah,ina kwana?"
Fitowa Umman tayi tana takawa da yar sakewa a yanayinta da sabon datai dasu itama na shekarun aiki a da sukai a gidan tace
"Lafiya kalau Mama Asmah,kin kuwa duba aikin danace Safina ta qarasa na Jiya??
"Eh na duba komai kafin akai mata ana jiran su tashi ne idan sun fito sai a sake hadawa akai musu"
Gaba Umman tayi tana cewa
"Yawwa hakan yayi dan Allah a tabbatarda baa tsallakewa ana kai masu koyaushe akan lokaci kafin tafiyarsu honeymoon ta kammala"
Safina dake gefen Mama Asmah din bin bayan Umman tayi tana gaidata itama da kuma qarasa cikin dakin cin abincin dan itace zatai serving nasu kafin Mamah Asmah ta iso da sauran abubuwan buqatan a dining din.
#MAMUH
#AASIYAH
#THE BINNAHS
#THE LOVE
#THE GAME
#THE TRAP
#SAM BINNAH
***
***