Free chapter · Read without an account
Chapter 8
by Rukayyat · RIKON KA'KA
RIKON KAKA
Written by
Rukayyat
(Rukyelmuaz)
Book 1
YOTA
Chapter 8
BATSARI LGA
*************
Zaune su ke suna fira cikin nishadi duk farin ciki ya rufe zuciyar Kaka sai ƙara jan Julaibib da doguwar fira ta ke ya na biye ma ta.
Duk da kasancewar ya gaji da surutun amma babu yanda zai yi saboda ba su jima da fara fira ba aka fara ruwan sama dole ya saurare ta ga gajiya ya na ji amma ya san ya na tashi agurin ya ce zai shiga bedroom ɗin shi Kaka za ta fa ra mi ta yanda kasan ya yi kisan kai.
"Kaka kiran sallar Azhur akayi ne????"
"Kinga bani key ɗin ɗakina inje in canja kaya in tafi masallaci."
"Kai lokaci babu wahala kaga har anyi Azahar Allah sarki a haka zakaji wata rana duk muna ƙabari"
"To ai kin sha jar miya ko yanzu kika wu ce ba kuka zamu yi ba"
Julaibib ya kai ƙarshen maganar yana ɗaga ma Kaka gira.
"Yau naga ikon Allah Zuraibib da ma ka ƙosa in mutu ne???"
"To wallahi kayi ka gama sai naga auren ka harda yaranka duk saina gani"
Kaka tayi maganar tana miƙewa zata wuce ta shiga bedroom ta ɗauko mishi makullin ɗakin shi inda ya ke zama in zo garin.
Julaibib na tsaye a tsakiyar falon ko me ya tuna sai ya fara waige_waige.
"Kaka wai ina wannan yarinyar ne naga bata cikin ɗakin nan yanzu?"
Fasa shiga cikin bedroom ɗin tayi ta tsaya itama tana waige_waige.
"Kai Wallahi kaga har na manta ai tana kewaye tun ɗazu ta ce min zata zagaya, bari in kawo ma ka mabuɗin ɗakin naka sai in duba inga me take yi a cikin kewaye tun ɗazu."
"Uhmmmmmmm."
Kawai Julaibib ya ce saboda shi abun ya ɗaure mishi kai ta ya mutum zai shiga kewaye a ce tun ɗazu amma bai fito ba to zaman me ya ke.
Yana tsaye agurin Kaka ta dawo rike da key ɗin ta miƙa mishi ta fita ya biyo ta a baya.
Hanyar kewaye ta nufa kai tsaye.
"Haisu, Haisu, Haisu."
"Kina jina kika yi shiru ko to uwar me kike a kewaye tun ɗazu sai kin ɗauko wa ta cutar kizo kina kwance ni ina zaune muna jinya ko??"
Ciki ta shiga ta duba taga babu kowa ta fito da gudu tana salati.
"La'ilaha'illalhu Muhammad Rasulullah Sallallahu Alaihi Wasallam"
"Kai Zuraibib zo ka duba min cikin shaddar nan muga ko ciki ta faɗa kaga fa babu ita babu labarinta"
Wata dariya ma Kaka ta bashi ya yi dariyar kamar wanda aka ma dole yo taya za'a ce mutum ya faɗa cikin wancan ƙaramin ramin sai ka ce mai ciwon hauka.
Ganin ya raina ma ta wayo ta na magana ya na dariya cikin ɓacin rai ta ce.
"Wai bakaji abinda na ce ba ne kayi tsaye kana kallo na kana dariya saboda ga sabon kamu"
"Yanzu ke Kaka in banda rigima irin ta ki don Allah ta ya mutum zai faɗa cikin wannan ƙara min ramin sai ka ce kiyashi ."
Wani banzan kallo Kaka ta ke watsa mishi zuciyarta na bugawa da sauri duk tsoro ya gama cika zuciyarta sosai amma duk da haka haushi ya ke ba ta ji ta ke kamar ta rufe shi da duka ta ya tana magana akan ƴar gudaliyarta bugun zuciyarta zai ringa saka shirme a maganar ko don ba shine wani abun ya sa ma ba.
"Idan bazaka duba ba in fita in saka kururuwa jama'a su kawomin ɗauki tunda iskanci ne abunka ta ya ina maganar ceton rai ka na sakamin shirme a ci ki."
"Wallahi Kaka saboda wannan ƴarinyar bazan shaƙi cuta ba bazan je in ga abinda zai hana ni cin abinci a yinin ranar nan ba ni bazan zauna ta wahalar da ni ba ke dai da zaki iya, go ahead."
Kuka ta saki kamar wata ƙaramar yarinya ta kama saleɓar zaninta tana goge hawayen ta harda face hanci tana tunanin ina Haisu ta shiga tana kukan tana masifa.
"Dama ai ba ƙaunarta kake ba dole zaka ce haka kuma wallahi in dai baka dubamin ba saina haɗaka da ubanka in ji in shine ya ce in na ce kayi abu kamin gardama"
"Yarinya marainiyar Allah in ba'a kula da rayuwarta ba ubanwa kake so ya ku la da ita zaka min iya shege da wata ƙo ɗaɗɗiyar fuskarka ka nunar rana."
Ganin rigimar bazata ƙare ba yasa Julaibib raɓawa ta gefenta ya wuce gurin da ɗakin shi yake ya buɗe ya shiga don in ya biye ma ta tabbas zai rasa jam'i kuma rigimar ta bazata ƙareba don yanzu ba ya riga ya saba da rikicin Kaka don in ma abin ya yi ƙaramari zata iya zube mishi agurin ta na kururuwa.
Agurin ya barta tana mi ta yanda kasan zata aro baki ta ƙara da nata.
Yana shiga ɗakin ya wuce toilet ya ɗaura Alwala ya fito ya buɗe wardrobe ya canja kaya yasa wata black jallabiya ya fesa turare.
Yana matuƙar son kamshi a rayuwar shi baya gajiya da tara perfumes a ɗakin shi haka cikin motar shi wannan ya sa ya ajiye perfumes kala_kala a bedroom ɗin.
Ba wani gayu ya yi ba amma da yake kayan sun sami farar fata sai suka zauna a jikin shi kamar wanda zaije gasar kyau ko yake tallata kayan a jikin shi.
Fitowa ya yi riƙe da Sallaya da niyyar tafiya Masallaci ya ga inda ya bar Kaka nan ya sameta.
"Allah kaka yarinyar nan tana wahalar min da ke sosai ki koma ɗaki tunda kika ga bata nan ai ta fita yawon ta ne kawai amma wannan rigimar taki kema tayi yawa."
"Kai Zuraibib kasan darajar rai kuwa kasan darajar ɗan adam ko da yake ina zaka sani tunda har yau baka da niyyar aure bare tunanin tara iyali."
Kaka ta bashi amsa tana mai binshi da kallon zaka yi baya ni ne duk ta kaici ya gama cika zuciyarta.
"Aini yaro ne kuma ke kaɗai ce matar da nikeso."
Shiru tayi dashi bata ce komi ba sai kallon baka da hankali da take bin shi da shi.
Shi dariya ma ta bashi sosai duk tabi ta ɗaga hankalinta akan wannan ƴar tsakuwar ƴarinyar wadda in da sabo ta saba da halinta ko yaushe zata daina ɗaga mata hankali ta barta ta mori tsufarta amma kullum tada mata hankali take tana neman ɗaura mata hawan jini.
A hankali ya raɓa gefenta ya wuce yana dariya ganin taki ƙara ce mishi komi yasan ya kai ta ƙarshe bazatayi magana ba in ko tayi magana tabbas zata ɓata mishi rai wanda hakan zaisa ran shi ya ɓaci shi ma.
Yana fita Kaka ta koma cikin ɗaki ta ɗauko ƙatuwar fitila mai haske ta shiga kewaye tana haske cikin shaddar ita a dole Haisu take nema.
"Uhmmmmm"
Ganin babu alamar mutum yasa ta sauke ajiyar zuciya ta ce.
"Ohhhh ni Hasatu to inda ace faɗawa ta yi ai da yanzu ta gama sulalewa kuma ai wannan bakin shaddar ya yi ma ta ƙarami, komi nike tunani Oho"
Komawa ta yi cikin ɗaki ta maida fitilar da ta ɗauko ta dawo ta shiga kewaye ta ɗauro Alwala itama ta koma domin tayi sallah.
Jikinsu sharkaf da ruwa ko wannan su hijabin jikin shi ya manne da jikin shi ɗan irgar dangin da suka fara fito musu a ƙirji ya fito raɗam suna tafiya kayan na ɗiga saboda ruwan da ya jika su
fuskar su tayi fari fes alamar ruwa ya wanke ta ga takalman su rike a hannu saboda gurin laka suke takawa suna tsoron su zame.
Tafiya suke hankali su kwance garin babu jama'a sosai saboda ruwan saman da aka gama ba kowa ya fito ba wani dogon salati Haisu ta sa ki tare da dafe ɗan ƙirjinta ita a dole babbar mace tana wani zaro ido.
"Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un"
A zabure Mairo ta kalleta sai kuma ta waiga ta kalli gefe bata ga komi ba na cutarwa kallon tuhuma take bin ta da shi kallon meke damunki da hankalin ko babu.
"Wayyo Allah na shiga ukku Mairo na manta basamude ya zo kuma ya ce kar in fita ko ina yanzu ga shi na fita na shiga ukku wallahi mugu ne."
Kafin Mairo ta bata amsa ta zuba da gudu ji kake "temmmmmmmmmmm"
Ta faɗi ƙasa cikin laka fuskarta ta shiga cikin ƙasar bata tsaya duba a wani hali ta ke ba ƙoƙarin ɗagowa kawai ta ke don hankalinta ya riga ya tashi Mairo ta taho a hankali zata ɗaga ta amma kafin tazo gurin ta miƙe ta sake zubawa da gudu ko waige batayi harda naɗe doguwar rigarta saboda jin da tayi tana harɗe ta.
Kallon ta kawai Mairo ke yi har ta ɓace ma ganinta tana mamakin wani irin tsoron Julaibib Haisu ta keyi yau.
Wani tunani Mairo tayi ita ma da hanzari ta ƙara saurin tafiyarta ta ƙara gyara farantin gyaɗarta.
Isowarta ƙofar gida da gudu zata shiga ya yi dai_dai da dawowar shi daga masallaci kamar an jefo ta ko kallon gabanta batayi burin ta kawai ta shiga gida ta ganta a ɗakin Kaka ji kake "Tauuuuuu". sunyi karo da shi lakar dake fuskarta ta shafi baƙar jallabiyar da ke jikin shi.
Baya ta yi alamar zata faɗi ya yi saurin riƙe hannunta ya dawo da ita dai_dai a razane ta kwace hannunta ta shiga gida da gudu bayan ta yabi shima ya shiga gidan.
Da gudu ta shiga ɗaki har tana ƙoƙarin sake faɗuwa kamar wacce taga dodo sautin haki Kaka taji tana zaune ta juya baya akan sallaya tana rike da casbaha tana addu'a.
Bata tsaya gurin Kaka ba tayi cikin uwar ɗaki da gudu.
Ganin halin da take ciki ita ma Kaka ta rufa ma ta baya ta na shigowa ta ganta tayi tsaye a tsakiyar ɗaki ta na haki kamar wacce ta dawo daga wasan tsere sai zare ido take tana raba su kamar wacce tayi ma sarki ƙarya.
"Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un"
"La'ilaha Illallahu Muhammad Rasulullah Sallallahu Alaihi Wasallama"
"Haisu dambe kika yi a cikin ruwa? Ko wani ne ya danna kanki a taɓo ni dama nasan mutanen garin nan ba ƙaunar ki suke ba yanzu don Allah me kika yi musu da zasu danna kanki a cikin taɓo wannan ɗaukar alhaki ne."
Kaka ta kai karshen maganar tana kallon Haisu cikin tausayi da kulawa gani take an cutar ma ta da jika sai ƙare mata kallo ta ke cikin ƙaguwa da zaƙuwar jin abinda ya faru da ita, don ita bama ta ruwan da ya jiƙa ta take ba so take taji waye ya dan na kanta cikin taɓo.
"Nifa babu wanda yamin komi wanka nayi cikin ruwa shine na tuna da wannan basamuden yana gari shine shine shine."
Taƙi idasa maganar tana murza ido da hannu biyu tana turo baki gaba duk jikinta ya yi sanyi tsoro ya gama cika ma ta zuciya sai ƙara raba ido take yi gabas da yamma lungu da saƙo na ɗakin.
"Shine me don uban ki kiyi min maganar da zan ga ne kina magana kina cemin shine shine shine me?" "Zaki gayamin gaskiyar abinda ya faru ko kuwa yau ni da ke ne a cikin gidan nan in baki faɗamin wanda ya cuce ki ba wa zaki faɗawa,
"Inajin ki shine me?????
Duk jikin Kaka ya yi sanyi jira kawai ta ke taji sai me ya faru.
Haisu tayi narai_narai da manyan idanunta kamar zata yi kuka ai dukan ya yi ma ta yawa ga faduwa ga kuma faɗan Kaka da in ta fara kamar wacce zata aro baki daga makwabta ƙara turo baki tayi gaba gaba kamar zata zunguri Kaka dashi sannan ta yi magana. "Shine na faɗi ƙasa ina gudu saboda kada in zo basamude ya dake ni"
Cikin ɗaga murya kaka ta fara faɗa kamar zata kai ma Haisu duka don ta tsani wasan ruwan da take yi yarinya ba ƴar ruwa ba amma ko yau she cikin son sanyi ta ke yanda kasan wata macijiya.
"Yanzu Haisu don Allah dole sai kinsa hankalin ubanki ya tashi ne in ba iskanci ba kinsan ko zazzabi aka ce kinayi bayada kwanciyar hankali, ya dunga kira na wannan TV kola ɗin ta wazof (WhatsApp Video Call) "amma shine kika shiga ruwa har ɗiga kike yi to kin kyauta kije ki cire kayan jikinki ki ɗaura zanin wanka bari in juyo miki ruwan zafi a kitchen kiyi wanka ko ƙyaji dumi a jikin na ki."
Kaka ta shiga toilet ɗin ɗakin ta ɗauko bokitin wanka ta fita ta barta a tsaye.
Turo baki tayi gaba ta kallon bayan Kaka da ta fita da bokiti ta ke cire hijabin jikinta ta yi sannan ta cire rigar baki ɗaya ta wuce ta nemi zanin da zata ɗaura.
Julaibib yana shigowa gidan ɗakin shi ya wuce ya cire rigar da Haisu ta ɓata mishi da ƙasa sannan ya canja yasa( T Shirt White) mai dogon hannu yasa wando Jeans blue sannan ya fito ya shiga ɗakin Kaka ganin babu kowa a falon yasa ya shiga cikin uwar ɗaki kai tsaye yana shiga ya iske ta a tsakiyar ɗaki tayi ɗaurin gaba tana ɗago kai suka haɗa ido tayi ƙasa da kai, cikin tsoro ɗakin ya shige ya zauna a kan gado ya kalle ta yanda ta ke sadda kai ƙasa kamar ba ita bace mara kunyar yarinyar nan mai tsiwar tsiya kamar ba ita bace yarinyar da in ka faɗi ɗaya saita mayar maka ba kallon yanda duk ta tsora ta ya yi sai ya ji hukuncin da ya yi niyyar yi ma ta ya fasa don yanda yaga ta tsorta duk ta bashi tausayi amma dole ya tauna tsakuwa don aya taji tsoro murya ƙasa_ ƙasa ya ce.
"Zo nan" ta ɗago ta kalle shi shima ita ya ke kallo ta fa ra takowa a hankali cikin tsoro da sanɗa kamar wacce za'a ce takkk ta ruga da gudu tafiyar da batafi tayi tako biyar ba taje inda yake sai jan ƙafa take tana tafiya cikin sanɗa da jan ƙafa.
"Bakida jini ne a jikin ki in taso in taimaka miki don naga tafiyar tana baki wahala ko?"
Da hanzari ta ƙarasa gun da ya ke ko idasawa bai bari ta yi ba ya ɗan taso ƙaɗan ya kama kunnanta ya murɗe ya na rankwashin kanta yanda zataji zafi sosai durkusawa tayi a ƙasa tana riƙe hannun shi ta na ƙoƙarin kwace kanka.
"Au dama kinada ƙarfi bansaniba". Bata ce komi ba sai ƙara ƙoƙarin kwace kunnanta takeyi ganin bazata iyaba yasa ta saki wa ta uwar ƙara yanda kasan an yanki fatar jikinta ya ɗago kanta zai sake rankwashi ta sake sakin wa ta ƙara wacce tafi ta farko da tayi Kaka da ta shigo rike da bokiti saida ta razana cikin kiɗima ta na mishi kallo mai cike da tambayoyi.
" Kai Zuraibib me kayi ma ta haka take wannan ihun kamar zata ciremin dodon kunne?"
Baice komi ba ya saki kunnanta ya ture ta gefe ta faɗi ƙasa ta buge mirror dake bayanta ƙarar faɗuwarta jikin mirror ɗin kawai kake ji.
"Timmmm" Ko kallon ta baiyi ba ya gyara kwanciyar shi akan gado.
Ta na shirin miƙewa suka haɗa ido da Kaka tayi saurin komawa ta zauna Kaka da ta ke tsaye riƙe da bokitin ruwa tana son taga taji rauni ko lafiya ta ke don wannan faɗuwar ta kayar mata da gaba kallon ta kawai take tana jiran ta tashi.
"Wayyo Allah shikenan ya kashe ni ya cire min ƙashin baya na, "Nadaina moruwa Kaka kizo ki ɗaga ni muga zan iya tsayuwa shikenan za'a koma turani a keken guragu ana rakani bara bakin tasha ko kasuwa.
Sai a lokacin ya waigo ya kalleta don ya ga wani hali take ciki suna haɗa ido tayi ƙasa da idonta tana yarfa hannu alamar zafi har wani jan numfashi ta ke, ta na ɗaga kai sama tana ajewa ƙasa alamar zafi take ji juyowa ya yi kamar zai sauko da ƙafar shi ƙasa don shi bazai iya jure wannan rakin na ta ba gwara ya koma ɗaki ya huta ya yi bacci da sauri ta miƙe tsaye har zanin jikinta na shirin kwancewa ta ƙara rike shi don karya kwance ganin ta miƙe tsaye yasa ya koma ya gyara kwanciyar shi.
" Kaka shigar min da ruwan kewaye naga ashe bai karyamin bayan ba zan iya tashi ina ga tsami ya yi kuma da na watsa ruwan zafi zai dawo dai_dai."
Tana gama faɗin haka tayi saurin shigewa toilet ko kallon inda yake bata sake yi ba.
Babu musu Kaka ta bi bayan ta da bokitin ruwan don dama don ita ta ɗauko ruwan ba don kowa ba tana aje mata ruwan ta fito ta barta ta koma falo saman sallaya ta zauna.
Kallon mamaki yake binta da shi tana cikin toilet ɗin tana taɓa ruwan da Kaka ta kawo mata don taji zafin shi ta bar ƙofar toilet ɗin a buɗe tana riƙe da ƙofar don tana tsoron duhu sosai don bacin ta gan shi a ɗaki da bazata rufe ƙofar ba kallon ta ya ke a zuciyarshi yana jinjina girman maƙirci na ƙaramar yarinya kamar wannan wani murmushi ya subuce mishi wanda baisan ma ya yi ba maganar da tayi yanzu yake tunawa da yanda take ɗa ga murya kamar da gaske ya ƙarya ma ta ƙashin bayan kamar yanda ta faɗa.
Ta ɗauki lokaci sosai kafin ta gama wankan ta fito yana kwance a gadon ya rufe idon shi kamar mai bacci. Ta fito ɗaure da zanin atamfa tayi ɗaurin gaba gurin wani ƙaramin wardrobe ta wuce ta ɗauki riga doguwa ta saka rigar brown ce anyi mata design da White flowers, tana gama shiryawa ta koma falo ta zauna kusada kafar Kaka ta ɗaura kanta saman ƙafar Kaka.
"Kinyi sallah." Shine tambayar da Kaka ta yi ma ta turo baki tayi gaba " Yunwa nikeji Kaka." ta faɗa tana juya manyan idanunta. "Shikenan kiyi sallah akwai abinci a kitchen ki zuba ki ci.
"To shikenan Kaka."
Miƙewa tayi ta koma cikin bedroom ɗin tayi alwala ta zo ta kabbara sallah tana gamawa ta ci abinci wani bacci ne ɗauketa tana kwance kan ƙafar Kaka tana bacci cikin kwanciyar hankali. Fitowa ya yi zai koma bedroom ɗin shi ya isketa kwance tana bacci ga Kaka ta jingina da kujera tana bacci ita ma durkusa ya yi ya ɗauki Haisu ya wuce uwar ɗaki ya aje ta saman gado ya fito ya koma bedroom ɗin shi ya kwanta yunwa yake ji amma ba ya son tashin Kaka a bacci wayar shi ta ke ƙara alamar ana kiran shi duba mai kiran ya yi lokaci ɗaya fuskan shi ta sauya gaba ɗaya bai ɗauki kiran ba har wayar ta yanke.
Rukyelmuaz
***