Free chapter · Read without an account
Chapter 15
Bakwai saura na dare su amare suka isa gdn Alhaji Muhammad Gamawa, 'yan'uwansu Sulaiman wa'enda ke nan kusa yawancinsu sun samu zuwa tarban amarya duk kuwa da cewa akurarren lokaci ne aka sanar dasu, amma sai sukayi kokarin goyawa dan'uwan nasu baya! babu abunda kake ji na tashi sai sautittinka gud'a daya karade gidan, abangaren Gwaggo akai wa baki masauki, kuma Khadeejah ta cika alk'awarin zuwa, Sumaiyya hadda rungumeta tana kukan murna tare da zuba mata godiya na taimkonta da tayi tasa baki har Baba Sheikh ya amince ta karashe makarantarta! ,Zaune take abakin kafcecen gadon dakin da aka saukesu, kanta lullube cikin katoton mayafi sai sharban kuka take ganin su yayyunta da yafendunta Farida duk sunyi haramar tafiya dan sun kafe akan bazasu kwana anan ba sai agdn yaya Basira! ,hannu takai ta damko hannun Khadeeja dake zaune kusa da ita tace cikin yin kasa da murya"Khadeeja dan girman Allah karki tafi, keda Yafendu ku kwana tunda su sun k'iya "wa ? aikam baza'ayi hakan dani ba, kafata! kafarsu ! " ....."Ni zan kwanan miki in kinaso, kai inma kinason in miki 'yar zaman daki ne zanyi kin ga ko ba komai duk safiya dai inna tashi zan dunga had'a ido da madarar zuciyata inji sanyi, kin min kwacensa amma babu yadda na iya dake, wannan gatan ne kawai nakeson kimin wato ki bari in zauna agidanki ...." babu wanda be dara ba da wannan shirme na Beebah ba, ita da hankali sunyi hannun riga ne kawai, irin shigar da tayi kadai ma zaisa kasan hankalin bai wani wadace ba, sai ta wani togalo dankwali gaba ga sharb'a sharb'an lebunan nan nata da suka sha jan fenti sai walkiya suke kamar tsuliyar biri, dariyar da suke mata ne ya kufular da ita don hatta Sumayyar ita kanta sai da wani munafikin murmushi ya kufce mata, "meye abun dariya donna fadi iya gaskiyata ? " aharzuk'e Khadeeja tace"ban tabbatar da cewa ke din baki da hankali ba sai yau, kai maganganun da ma kike yi ya nuna kwata kwata baki da saiti, just imagine the moron having a crush on her sister's hus......" Wani irin wawan mari ne ya hanata ida abunda tayi niyyar fad'a..
Yaya Asiya ce da wannna danyen aikin wacce tun farko ranta bai so ta biyosu ba don dai kawai babu yadda ta iya ne kasancewar Baba Sheik jan ido yayi mata shiyasa, karin takaicinta ma ya dad'u ne sanda ta tabbatar da cewa gdn maiko ne suka kawo Sumaiyyar! ,yar yatsa ta shiga karkadawa Khadeejar da tayi Sumar zaune tana fadin"yarinya ahir dinki! Karki kuskura kiyi gangancin tura kanki cikin ramin da bazaki iya fitowa ba in har ba kinsan abunda kika taka bane, Habibar ta miki kalar shashasha ne da har zaki dubeta ki zageta ?, ai gaskiya ta fada shigar sauri aka mata, Sulaiman Habiba yakeso shine Badi'atou tayi shige shige har ta dauke hankalinsa zuwa ga 'yarta wacce ta gama rarrabar da mutuncin kanta akan hanya, jakar titi abin hutawar garadai gata nan ku kalleta dakyau... " ai basai kin tsaya batar da lokacinki wajen zayyane ko ita d'in wacece ba, da hankalina da kuma sauran numfashina bazan tab'a yin gangancin had'a Zuri'a da Fasik'a ba, Allah na gode maka daka bayyana gaskiya tun kafin nayi kukan dana sani akurarren lokaci don wallahi bazan jira ma har sai an wayi gari ba, kafarku kafarta in har na isa da mijin nata! in kuma ya nuna mun cewa ban isa dashi ba to ai na isa da mahaifinsa kuma ya zama dole ayi abunda nakeso" ...da sauri suka waiga suka sauke kallonsu akan Gwaggo wacce ke tsaye abakin kofa da shigowarta kenan, Sumaiyya bata san sanda ta yaye mayafin kanta ta mik'e da gudu tayi wajenta gami da fashewa da kuka ba, adaidai lokacin Yafendu Farida ta fito daga toilet don dama can sauri take ta fito taci mutuncin Asiya sai ga wata sabuwa kuma, hakan yasa ta yanke bahayarta babu shiri ta fito! ,Sumaiyya ta zube agabanta gami da rirriko kafafunta tace"dan girman Allah hajiya karki dauki abunda ta fad'a da mahimmanci Wallahi ba gaskiya bane sharri akemin, ni ba fasika bace, ban tab'a aikatawa ba amma kuskurena daya na tab'a kusantar inda yake..." da azama Yafendu Farida ta karaso wurinta tasa hannu tana dan jijjigata tace"ke Sumaiyya ki dawo hayyacinki, baki tab'a kusantarsa ba kuma insha Allahu Allah bazai sa mu ga wannan ranar da zaki koma amshin wannan sunar ba, hajiya abinda kika ji ki yadda dani ba gaskiya bane....." Gwaggo ce tayi saurin taran numfashinta"Na shiga ban dauka ba baya fidda barawo, yarinyar ma da kanta kinji abunda ta fad'a, ta tab'a kusantarsa, kenan ba wai ta zama shahararriya bane aharkan kawai sau daya tak! Arayuwarta ta tab'a aikatawa ! kuma sannan ni ba zancen dana ji wannan tana fad'i bane ya daga hankalina ba " ta furta tana nuna Asiya da 'yar yatsa gami da girgiza kai kan tacigaba"a'a ina zaune na ne na sami labari da zafi zafinsa, abunda ma yafi dauremun kai da wannan al'amarin shine.....shine...." kasa karasa maganarta tayi sakamakon kukan daya ci karfinta, Cike da kunar Zuciya tace"wallahi Muhammadu ka cucemu daka aurawa danka Shahararriyar karuwa, kuma ayanzun nan zan nuna maka cewa Nima na isa da gidana! " juyawa tayi ta fita daga bayanta tana kwalawa Zainab kanwar Sulaiman k'ira, Su Yafendu kuma suka mara mata baya suna rok'o.... "Ke Zainab kiramin Ubanki awaya kice dashi maza maza ina son ganinsa yanzun nan ".......amsawa tayi da"Tou" amma tasan babu lafiya...
****
Asma'u ce kwance saman Alhaji Madugu tsirara haihuwar uwarsu suna aikata sabon Allah abun dai sam babu kyan gani, tun sha biyun rana take gdnsa sunata abu daddaya har zuwa wannan lokacin da ake neman takwas d'in dare, ita ko kadan bata tunanin komawa gida kasancewar Sulaiman ya sanar da ita baze dawo da wuri ba zai iya kai goman dare shiyasa ta saki ranta take cin duniyarta da tsinke! ,kirrrrr wayarta ya hau burari, hannunta akan kaciyar dan katuwar tana mulmulawa tasa dayan hannun ta jawo wayar ta kara akunne"hello! banza ya zaki katse mana sweet moment ne haka ey ?, muna tsaka da jiyar da juna dad'i sai ga kiranki " daga daya bangaren Hafsat tace"ke malama da kin san abunda nake shirin gayamiki da baki gayamun wannan maganar ba, yanzu nake samun wani mummunar labari wai Sulaiman d'inki ya kara aure yau dinnan ma aka kai masa amarya can gidan iyayensa nan Bauchi... " wani irin hantsilowa tayi kasa da wayar akunne wanda ba karamin tsoratar da Alhaji Madugu yayi ba, tace"Hafsa What ??? Sulaiman yayi aure fa kika ce ?, ke ina kika samo wannan labarin ? " tab'e baki Hafsat tayi kan tace"ina cousin d'ina dinnan Firdausi da nake yawan baki labarinta ? " dasauri tace"eh eh na ganeta " to ai kawar kanwarsa Zainab ce, wallahi ita ta kirani take sanar dani wai ashe tun last week aka daura auran amma ayau aka kai masa amaryan, ni abun ma takaicin ayadda take gayamun wai karuwa ce, ranar aurenta saurayin yace ya fasa shine aka likawa mijinki..." Fashewa da kuka tayi tana furta kalmar Innalillahi wa'inna ilaihi rajiun, cike da hauka tace"Ni Sulaiman zai wulakanta yayiwa kishiya ?, kishiyar ma karuwa ? Salon yaje ya kwaso cuta ajikinta sannan nima yazo ya manna mun ?" Girgiza kai Hafsat tayi tana fadin"Kibar son kanki da yawa Asma'u, gwara dashi aurenta yayi ke kuma fa ba shek'e ayarki kike zuwa yi da aurensa akanki ba ?, ke baki tsoron ki kwaso muku cuta amma don ya miki kishiya shiyasa kike tsoron kar shi ya kwaso hakane ?, baki son kishiya amma shi kika masa ?, lallai Asma'u baki da kan gado, gaba kika bawa iskanci ba baya ba...."
"Dallah malama ki rufemun baki inji da abunda ke damuna, wannan irin rayuwar dana tsinci kaina aciki wanene sila ?, kin manta kece kika bani muguwar shawara ?, Hafsa ki sani kema kin bada naki gudummawar wajen lalacewar rayuwata...." saurin taran numfashinta tayi"dana baki shawarar cewa nayi lallai sai kinyi aiki dashi ?, in banda dama can kema 'yar iskan kanki d'in ce, Asma'u kibi asannu fa karki bari asoma tone tone..." bani da lokacinki yanzu, bari in gama da abunda ke gabana sannan in dawo gareki musa wando kafa daddaya..." kit ta kaste wayar tana firda huci gami da rushewa da kuka tana fadin"Sulaiman ka cuceni !wallahi bazan bari ta zauna ba don ba'a haifi wata d'iya macen dazan bari mu raba soyayyarka da ita ba, wallahi never!!" Ji tayi ana shasshafa bayanta, ko bata juya ba tasan ko waye, ahalin yanzu haushinsa kawai take ji, Alhaji Madugu yace"haba baby ki manta da damuwarki mu cigaba da farantawa juna rai, shifa namiji da kike gani rigar kaya ne muddin kika sakashi kin shiga uku, ina tausayawa duk macen data dauki son duniya ta dorawa d'a namiji don kuwa tana iya kukan dana sani agaba, tunda kina dani banga wani abun damuwa ba, naga dai abun nan ina baki ita dakyau yadda ya kamata har sai kince kin koshi, to menene na wani damuwa akan wani ragon namiji can wanda ya rako maza duniya ?, haba baby ki manta dashi gani nan ki Moreni iya yadda kikeso sannan kici arzikinki babu me hanaki.." surutansa kawai yake tayi amma bata tankashi ba, ta hau saka kaya, tana gamawa ta dauki jakarta ko sallamarsa batayi ba ta fice, Fitowa wanka yayi kawai yaga dakin wayam babu ita! Tsaki yaja abunsa yace"can ta matse miki! bari in shirya inje inyi maneji dana Sa'ade don ba koshi nayi ba" yana nufin matarsa...
***
"Muhammadu wallahi ba'a tab'amun abunda ya tab'a zuciyata ba kamar auren daka daurawa Manu da wannan yarinyar !" Gefen zaninta tasa tana share hawayenta kan ta cigaba"wallahi ko mahaifinka Audullahi har ya koma ga mahalliccinsa bai tab'a bakanta raina kamar kai ba " cike da mamaki Abba yace"Gwaggo wai menene ke faruwa ?, wani laifi na aikata da har yasaki zubda hawaye ? " ashe yarinyar nan karuwa ce kuma kasan da hakan shine ka aurawa danka ?, to wallahi bari kaji sai ya saketa don gwaramun irin Asma'u dubunta akan wannan yarinyar, yanzu Umarni nake baka ka kirashi awaya kaima ka masa umarnin ya sawwake mata in ba haka ba duk zaku gamu da fushina ..." Innalillahi wainna ilaihi rajiun shine abunda Abba da Mama ke furtawa, Abba shine hadda cire hular kansa yana firfita dashi duk kuwa da sanyin Ac daya ratsa falon amma zufa yake na fitar hankali, cikin in ina yace"Gwaggo...ina ina kika samu wannan labarin ?, wallahi ba gaskiya bane sharri ake yiwa yarinyar nan ..." bai ida maganarsa ba ta daukeshi da mari akaron farko na rayuwarta abunda bata taba masa ba kenan da girmansa da tsufansa, sosai ta shayar dashi madarar mamaki hatta da matar tasa Haj.Hindatou, Zatai magana Gwaggo tayi saurin daga mata hannu tace"Kul karki saka mana baki, wannan magana ce tsakanina da d'ana in bazaki iya kallo kiyi shiru ba to maza tashi ki fita ki bamu wuri!" Maida kallonta tayi akansa tace"Madu ba cewa nayi ka nuna mun yadda ake firfita da hula ba, kuma sanin inda na samo wannan labarin ba damuwarka bane, abunda kawai na sani shine ku din baku isa ku mun wayau ku cuceni ba, Madu har nawa kake da zaka sakani akwana ?, wato wani yaki yarinyar shine kai kuma uban 'yan tausayi me d'a sai ka karba masa aurenta salon azo nan gaba acikamun gida da ya'yan waje ko ? Yo! kana kallona ko bakasan ita karuwa ko bayan aure cigaba take da bibiyar wasu mazan awaje ba ? Wallahi sai dai idan sauyawa tayi amma ni kam wannan dai ba zama zatayi ba, ka kirashi awaya, kai nama ga kana batamin lokaci, ke Hindatou ungo waya ki nemomin Manun awaya "
Adaidai wannan lokacin kuma Sulaiman na can na rigima da Asma'u, babu shiri ya taso office don bata bari ya dawo ba ta nemeshi awaya da batun, abunda ma yafi daga hankalinsa bai wuci yadda take danganta ita Sumaiyyar da karuwanci ba, abunda yafi tsana ga d'iya mace kenan! ,shako wuyarsa tayi tana fadin"wallahi Sulaiman sai dai ka zab'a koni ko karuwarka don bazan zauna ka kwaso mun ciwo ba..." bai san sanda ya dauketa da mari ba, shima abunda bai tab'a yi ba kenan, tureta gefe yayi tayi tagal tagal zata fad'i kasa ba yace"Asma'u kibi ahankali in ba haka ba zan bar miki tab'on da zaki baiwa ya'yanki labari in ma kina da rabon haihuwar kenan, Sumaiyya ba karuwa bace nasan zafin kishi ne yasa kike dangantata da hakan, ki sani zuciyata na tafarfasa in kina fadin hakan, ki kiyaye kar ki kaini bango, kinga dalilin dayasa ma nake ta tsoron gaya miki aurenta da nayi kenan don nasan baki da hankali.." Kuka ta fashe dashi me daga hankali tana fadin"au yanzu gorin haihuwa zakamun Sulaiman akan Wannan karuwar ?, ai kai din ne baka cika d'a namiji ba abarka bata aiki yadda yakamata shiyasa ban dauki cikin ba...." oh my God wallahi Asma'u kibar kiran Sumaiyya da karuwa in ba haka ba zan kasheki..." ya furta da iya karfinsa gami da rike kansa ransa na suya, idanunsa aruntse gam! , shan jinin jikinta tayi ganin halin dayake ciki don bata tab'a ganinsa acikin irin wannan yanayi ba, wayarsa ce ta dauki kara, ahankali ya zaro daga aljihunsa yana dubawa... *KAKUS* shine sunan daya gani yana yawo akan allon wayar ! ,murmushi yayi don yasan ahalin yanzu ita kadai ce zata iya sanyaya masa zuciya diba da yadda take tsananin son auren daya kara d'in....."hello kakuletina wallahi dama inaso inna huta ne sai in kiraki, amma sai nazo na tarar da rigima agida, mutuniyarki ta samu labarin auren har kazafi takewa 'yar mutane wai karuwa ce don dai kawai in saketa ke kinji fa ..." yana wannan maganar ne bayan yabar gaban Asma'u, amaimakon ya sami goyon bayan Gwaggo sai ji yayi tace"ai gaskiya ta fad'a karuwar ce mahaifinka ya aura maka! ai Muhammadu ya cucemu..." ta fashe da kukan bakin cikin, wasu zafafun hawaye ne ya zubo masa, bai san sanda ya karya gwiwowinsa zuwa kasa ba yana fad'in"gwag..gwaggo da gaske kike Sumaiyya karuwa ce?, anya gwaggo gaskiya ne kuwa ?, d'iyar Sheikh Mukhtar Azare ce fa ?, kuma rainonsa, haba kakata taya kike..... "dakata! ko diyar wacece ba abunda ya dami salame ba kenan! an dai tabbatar min da lallai ita karuwar ce kuma ina mai baka umarni in har ka daukeni da mahimmanci amatsayin wacce ta haifi ubanka to maza ka sawwake mata ina jiranka, yanzu ma zan kai mata wayar ka gaya mata taji da kunnenta..................
Comment &
Share Fisabilillah
H/C✍️