Free chapter · Read without an account

Chapter 8

by MARYAM STAR · ƊAURIN ZUCI

***


𝘿𝘼𝙐𝙍𝙄𝙉 𝙕𝙐𝘾𝙄🔐
         𝘽𝙔
𝙈𝘼𝙍𝙔𝘼𝙈 𝙐𝙈𝘼𝙍 

𝙅𝘼𝙅𝙄𝙍𝙏𝘼𝙏𝙏𝙐 𝙒𝙍𝙄𝙏𝙀𝙍𝙎 𝘼𝙎𝙎𝙊𝘾𝙄𝘼𝙏𝙄𝙊𝙉💪

𝘾𝙝𝙖𝙥𝙩𝙚𝙧 8
Mafaka ne zaune akan kujera wacce aka ƙera da ƙwarangwal ɗin kawunan mutane aka kuma yi mata ado da jan ƙyalle.
    Mutane ne fiye da ashirin wasu cikin jar shiga wasu kuma cikin baƙaƙen kaya, hannayensu riƙe da ƙorai wanda ke ɗauke da jini.
    A tare suka shiga rera waƙa cikin wani yare, yayinda sautin waƙar tasu ya soma tada ƙura me haɗe da iskan guguwa me ƙarfi, suna waƙar ƙarfin guguwar na ƙara ƙaruwa, sannu a hankali wajen ya soma tururin hayaƙi, cikin abin da bai wuce minti ɗaya ba yanayin wajen ya sauya da kukan wasu halittu da ba'a iya ganinsu, yayinda wutar da ke ci a  wajen haskenta ya haskake ko ina.

    Wata mummunar dariya me firgitarwa Mafaka ya saki wacce saboda ƙarfinta sai da wajen ya girgiza da sautin, yana direwa wasu muryoyin suma suka ɗauka fiye da wacce yayi.
    Sai da wajen yayi tsif sannan Mafaka ya miƙe tsaye hannunshi riƙe da wata zabgegiyar sanda wacce ta kere shi a tsawo, fuskarnan tashi ta sake munanewa musamman daya shafa wani baƙin abu a idanuwansu, cike da isa da taƙama ya soma magana.
    "Kamar yanda kuka sani bama hallara a wannan taron musamman a irin wannan lokaci da muke tsaka da more arziƙin mu, sai da babban dalili me ƙarfi to yau ma hakan ce ta kama shiyasa muka aika muku da ɗan saƙo, haƙiƙa ran shugabanku a matuƙar ɓace ya ke dan haka dole ne ke zage wajen ganin kun faranta mani sannan kuma ku taya ni yaƙi akan lamarin da na saka a gaba."
      Yana kaiwa nan ya  dasa aya a zancensa, yayinda wanda ke a kujerae kusa da shi zaune wato shaƙiƙinsa wato Ƙwaro ya cigaba da faɗin.
    "Ƙasarnan tamu ce dole muna buƙatar ƙarfin ikon sarrafata ya dawo hannunmu, hakan ya saka mu da kanmu muke nemo waɗanda suka cancanta da mu lulluɓa a ƙarƙashin inuwarsu mu basu mulki, a shekarun baya komi na tafar mana daidai sai de kuma a yanzh kamurra nason sauyawa, waɗanda muka ƴanta na son bijire mana yayinda mu kuma ba zamu lamunci hakan ba, kamar yanda duniya tasan a yanzu ƙasarmu na ƙarƙashin mulkin Saminaka haka muke son ta shaida mutuwarsa a yanzu kafin nan muna da buƙatar jin kururu da sautin kukan al'umma muna ba  buƙatar ganin jini na gudu kamar yanda ruwa ke gudu ako wace ungu ko wane ƙauye ko wane yanki, daga yau zuwa koda yaushe muna son sauya sabon tsari, yin aiki tuƙuru shi zai bawa ƙungiya damar mallaka muku dukanin abin da zaku buƙata, aikinku a ƙungiya shi zai zama matakin nasarar ku a rayuwa, a je a fara shirin yaƙi, yaƙinda babu tsayawa a  nan kusa da zarar an fara shi hankula zasu gushe rayuwa zata tsananta ga mutanen da basu yi imani da ƙungiya ba, kuje ku nunawa ƙungiyarku irin jarumtakar data baku domin tayi alfahari da  ku, muje zuwa zarafan haziƙan jarumai."
   Ya yi maganar yana ɗaga sandar shi sama cikin basu ƙwarin guiwa.
    Nan da nan jikunansu suka hau tsumama, kowanensu ya ɗaga ƙwaryar jini ya shanye ragiwar kuma suka zuba tun daga kai har ƙasansu sannan suka soma miƙa gaisuwa da martabawa cikin ga shuwaganinsu ta hanyar yin sujjada ɗaya bayan ɗaya suna kuma aje wasu kwalabe da ke a rufe sannan su fice alamar an sallame su.


Sai da kowa ya fice ya rage saura mutane biyu sai kuna Ƙwaro da Makafa sannan suja nufi wani ɗaki me girman gaske wanda babu komi a cikinsa sai mutane guda biyu kwance mace da namiji da akama basa cikin hayyacinsu.

     Duƙawa Mafaka yayi a saitin fuskar Muhammad wani mugun murmushi na bayyana akan fuskarsa ya shafi kan idon shi da ke a rufe yana faɗi cikin buɗaɗɗiyar muryar shi.
    "Ina alfahari da jininki Rimsha saboda ke da jinin ki kune cikar burukana."
    Hannu ya ɗaga nan Ƙwaro ya miƙa ma shi wani abu siriri, tare da nuna sandar hannun shi nan take haske ya bayyana tare da haske fuskar Muhammad.
   Buɗe idanuwansa ya yi da alama baya cikin hayyacinsa, da wannan damar Mafaka yayi amfani wajen ciro wani abu me kama da yana ya saka a cikin farin ƙyalle, yana gamawa udanuwan suke kulle kansu.
     Sai kuma ya buɗe ƙirjin Muhammad ɗin ya ɗauki wani abu tare da kwalba ya daka a saitin zuciyar shi, a nan kam sai da ya saki wata ƙaƙƙarfar ajiyar zuciya sai kuma ya koma yanda ya ke, bai saki abin ba sai da ya kai wata fara tas ɗin ƙwalba a daidai saitin yana ɗagawa ya saka a kwalbar ɗaya daga cikin mutanen wajen ya yi saurin amsa ya rufe tare da nufar saitin wani shuri ya aje kwalbar, nan take wani haske ya baibaye kwalbar tare da zagayeta, yayinda wannan abun me kama da zuciya ya soma harbawa kamar yanda zuciya ke harbawa.
    Zunainama  haka suka yi mata yayin da suka kai tata kwalbar a kusa da ta Muhammad suka aje sannan ya kalli ɗayan mutumin wanda yake da ƙira da jiki kamar basamude ya ce cike da gargaɗi.

    "Rayuwa me inganci, babu alaƙa a tsakani babu haɗuwar ruhi banda sakaki."
    Kai mutumin ya shiga gyaɗawa cije da ladabi sannan ya  soma tura abin da suke kwance a kai ya nufi hanyar fita ɗayan na take ma shi baya.

Bayan sun fice Mafaka ya kalli Ƙwaro suka saki murmushin da su kaɗai suja san manufar shi sannan suka nufi wata ƙaramar ƙofa suka ɓace ta jikinta.

Mafari kuma somin taɓi kenan yanzu zamu shiga ciki ainahin labarin Ɗaurin Zuci.

********************
Saka hannayensa ya yi tare da tare hasken ranar da ya dallare idanuwan shi a sanda fuskar shi ta biyo gangar jikin shi a yayin da ya ke saukowa daga matattakalar jirgi.
    A nutsu cike da mazantaka ya ke tako yana ƙara kare idanuwan shi daga hasken ranar.
    Sai da wata par ƙura ta tashi a sanda ya diro da ƙafarshi zuwa ƙasa, daga nan yaci gaba da takawa yana tafiya bayan ya saki sauke hannun shi ƙasa sai de still kan shi na ƙallon ƙasar da yake takawa.
    Tafiya yake yi yana ƙallon ƙasar da ta zama cikin kan shi, wacce bai taɓa mantawa da ita ba daidai da minti ɗaya, ƙasar da ta bani farinciki kuma ta bashi bain ciki du a lokaci ɗaya, ƙasar da yake yiwa kallo biyu a cikin idanuwan shi.
   Bai yi tunanin zai sake taka ta ba gaba ɗaya a rayuwar shi, yayi tunanin kamar yanda ya barta ya barta kenan har gaba da abada, sai de abin da bai saniba daga ranar da ya fita daga cikinta a ranar ne ta soma yi ma shi kiranye ta hanyar sigogin da ba zai iya jura ba, yayinda ƙaddara ta riga da ta rubuta sunan shi cikin jerin waɗanda zaman ƙasar ya zama ƙaddararsu shi yasa koda ya tafi ɗin sai da ya dawo, bai kuma san abin da ta tanadar ma shi ba a wannan zuwa.

     Ba tare da ya ankare ba ya ji an kai mashi zazzafan hug unexpected, ɗan jimmm yayi sai kuma ya saki smile tare da janyo wanda ya rungume shi zuwa gaban shi.
    Wata beauty baby ce wacce ba zata wuce 15 years ba, da fara'a a fuskarta ta ce.
   "Welcome back my lovely Brother."
   Rage tsayinsa ya yi tare da bata sumba a goshi yace cikin tattausan sautin shi.
   "Marhaba biki yah Habibty."

   Zagaye shi sauran mutanen suka yi kowanen su fara'a bayyane akan fuskar shi suka soma gaggaisawa da shi.
   Wani matashi me matsakaicin haske ne ya kalle shi da murmushi akan fuskar shi ya ce.

   "Farin balarabe zo muce, naga sai wani kakkare fuska kake kai a dole rana, to wallahi idan ma zaka saki jiki kara ka saki dan nan Nigeria ce ƙasar baƙaƙen fata bata larabawa ba, kana dai ganin yanda sama take a wawake babu rufi, dole ma ka saba da rana Malam."
    Me bi mashi ne ya cafe da faɗin.
    "Kai fa baka da kirki wallahi Uncle to can ɗinma amfaɗa maka rufu gare su ina ce itama saman a buɗe ta ke, kuma dama ta ina zaka haɗa ranar Dubai data nan, karka wani takura ma shi bayan kasan sai da muka haɗa da ƙiyamul laili sannan Allah ya karkato mana da shi ko hucewa daga jijjigar  jirgi bai yi ba zaka wani zo ka takura ma sa."
   Wanda aka kira da  Uncle ne ya ce.
    "Ai wallahi bai isa yace zai koma ba tun da har ya sako ƙafarshi ƙasar nan to wallahi ya dawo gida kenan dan aure zamu yi ma shi kowama ya huta, kuma idan muka tashi baƙa ƙirin zamu nemo ma shi wacce a kallon farko zai gane yana tare da ƴar 9ja."
     Nan suka soma faɗi in faɗa a tsakaninsu yayin da Uncle ke tsokanar shi, ɗayan na tare ma shi.
    Kallon su kawai yake yana murmushi, ba zai ce baya yin kewarsu ba, domin kuwa rana ba zata fito ta faɗi ba bai tuna da su ko wani abu daya dangance su ba musamman wannan gardamar da a kullum bata ƙarewa a tsakanin su, sauƙin kansu ke sake damfarar da ƙaunarsu a zuciyarsa.
     Tiredly ya ce da su.
   "Sai kun taho."
 Ya wuce wajen jibgegiyar motar da suka zo da ita, kai tsaye ya buɗe front sit ya zauna yana shaƙar ƙamshin freshner da sanyin AC daya gauraye cikin motar, ta cikin glashin motar ya ke kallon yanda suka taho, daga ganin yanayin su yasan gardamar da suka saba yi ce suke yi, ilai kuwa sanda Uncle ya buɗe murfin driver sit ya ji yana faɗin.
    "Ba ƙaramin aikina bane in tattaraka in watsaka can kaima."
    Shigowa matashin yayi bayan ya zaunar da wannan baby girl ɗin yana  faɗin.
    "Ai wallahi baka isa ba Uncle ni da 9ja mutu ka raba takalmin dajaja inmaka tasu Big bro."
   Ya faɗa yana kallon fuskar shi ta mirro, haɗa ido suka yi ya watsa ma shi hararar wasa bai ce komi ba.

   Baby girl ɗin ce ta ce.
   Ya Junaid yau muna tare da kai ko, kuma a room ɗinka zan dawo."
     Juyawa yayi tare da shafa baby face ɗinta, cike da kulawa ya ce.
   "Muna tare princess."
    Daga haka firar ta koma kan yarinyar nan ya samu damae ƙarewa wajajen da suke gittawa kallo yana tariyo sanin da yayiwa wajajen a baya da kuma irin sauye-sauyen da aka samu.

     Sai da ya rintse idon shi lokacin da motar ta shiga tabkeken main get ɗin shiga SAMINAKA ESTATE yana jin yanda zuciyar shi ke ɗaurewa da tunanika iri-iri musamman na abubuwan da suka faru a shekarun da suka gabata kafin ƙaddara ta sauya komi....

Da bisimilla ya soma taka ƙafafuwan shi yana shiga cikin gidan, sam baya fahimtar maganar da ake yi ma shi abin da ya saka gaba kawai ya ke yi, a daidai ƙofar da zata sada shi da ɗakin da zuciyar shi tafi ƙwaɗaita ma shi daya shiga ya tsaya, sai kuma ya  juyo slowly yana facing wannan matashin, cikin sassauƙan sauti ya ce.
    "Fahad yana a ciki har yanzu."
     Murmushin tabbatarwa Fahad ya sakar ma shi sannan ya ɗora da faɗin.
   "Ka shiga kanka tsaye zai ji sauƙin raɗaɗin da yake ji idan yayi tozali da kai."
  Sai da ya rintse idanuwan shi sannan ya kama handle ɗin one time yana jin zuciyar shi na tsalle a ƙirjin shi.
     Bai bawa kan shi damar yin tunanin komi ba ya wuce kan shi tsaye domin fuskantar abin da ya kawo shi ƙasar....


****
MALAM
Huwaila ce zaune akan tabarma hannunta riƙe da wani sirirn abu marar gwaɓi kamar zare, a zahiri abin ta ke kallo yayinda a baɗini tunaninda na wajen yaron maƙotansu da ya shigo gidan babu jimawa, kunnuwanta kuma na zaƙwaɗin jiyo tashin muryoyi, sai de kuma shiru bata ji komi ba.
    Malam ne ya shigo gidan babu ko sallama, kasancewar idan ba idon wani ke wajen ba babu ruwansu da abin da ya shafi addini.
     Fuskar shi daya ari bargon malinta ƙarfi da yaji ɗauke da farar da Huwaila kaɗai tasan sanadin yinta, sai da ya tabbatar da babu kowa a kurkusa sannan ya isa wajenta yana zura hannu cikin aljihun rigarsa ya fito da wata kwarba yana faɗin.
   "Maza taso kiga yanda tabarrakin shugaba ya bani sa'a a yau."
   Da sauri Huwaila ta tashi tana sake damƙe zaren cikin hanunta tabi bayan shi don jin abin da yazo da shi.
    Farar kwalba ya fito da ita tare da ɗagata saitin fuskarta yana murmushin samun nasara ya ce.
    "Haƙiƙa yau zan faranta ran Shugaba domin kuwa ina saka ran kasancewa mutum na farko da yayi nasarar cika aiki a yau, yanzu haka idan kika kunna redio zaki ji cecekucen mutane akan aikin dana aikata, yayinda nayi nasarar saka kururuwar kuka tare da dasa tsoro a zukatan iyayen yara da sauran jama'a."
   Kallon ƙwayukan idanuwan da ke cikin kwalbar ta ke wani yanki daga zuciyarta na son razana, yayin da ɗayan sashen yafi ƙarfinta, hannu takai tare da shafa jikin kwalbar don tabbatarwa, sai malam ya karkaɗa ta da ƙarfi, nan take abubuwan ciki suka girgiza har jinin nijinsu na gogayya da bangon kwalbar.

    "Tabbas Shugaba zai yi fara'a da kai a yau, zaka kasance daga cikin waɗanda za'a karrama zan so inbi baganka ako ina sai de da alama wannan karon ba lallai ne inyi nasara ba sabod....."
   Bata ƙarasa faɗa ba suka ji anfaɗo gidan da ƙarfi yayinda wasu muryoyi ke fitar da sautin kuka wata wasu kuma na.....✍🏻

Tofa jama'a kuci gaba da kasancewa tare da ni domin jin yanda zata kaya a cikin wannan zazzafan labarin me taken ƊAURIN ZUCI
 
Zance na gaski likes da comment naku sun yi min kaɗan ku sake sake hannu wajen nuna min jin daɗinku ni kuma insaki hannu wajen typing babu ƙaƙƙautawa.

#hausanovel
#Maryamstar
#daurinzuci.


MARYAM STAR CE⭐.

Want the next chapter?

ui.create_a_free_arewapen_account_to_save_progress_unlock_paid_chapters_fol