Free chapter · Read without an account

10

by Bilkisu Ibrahim Musa · SANTSI


..........««GUSAU»»

         Sosai yanda aka shirya karɓar lefe ya ƙayatar. Dan sai ka ma ɗauka bikin ya fara ne. Lefe kuwa ya cancanci a kira shi da lefen ƴar gata. Set ɗin akwatina goma cif, ga danƙareriyar mota ta miliyoyin kuɗi. Domin maganar 100m akeyi bata yaku bayi ba. 
          Komai ya gudana cikin tsari da girma irin na masu kuɗi. Anan gidan su Ibtisam ma tarbar ta girma akama dangin angon, tare da tukuyci mai tsokar gaske.
       Bayan wucewar su aka buɗe kaya. Babu batun dalla-dalla, sai dai gani da ido ace sambarka. Ibtisam dai na sashen su. Sai su Munerah ƙawayenta da ƙannenta da suka ɗauka video suka kawo mata ta gani. Ɗan murmurshi kawai tayi batare da tace komai ba. Hakan yasa baka isa gane yanayin da take a ciki ba. 
         Tuni videos ɗin wannan lefe sun fara yawo a media. Aure fa ake magana na ƴaƴan manya. Mutane sai sambarka. Mata na fatan ALLAH ya maida su a damshinta. Ba a IG kaɗai da su Munerah suka ɗora ba. Tuni videon ya fara yawo har a wasu shafukan na tiktok dama groups na WhatsApp zuwa Facebook. Al'amarin sai dai wanda ya gani. Amma dai ƴan media sun kafa harsashin jiran ganin bikin da angon kansa, dan daga lefen kasan za'a zuba harka a wannan aure...

        ....★Washe garin da aka kawo lefe Ms. Adaora tazo da tailor ɗinsu na company. Kai tsaye Rufaidah sashen su Ibtisam ta kai su. Dan yanzu komai ya dawo hannunta. Hajiya Lubnah tana da nata uzirorin. Yau kam Afia da Muhseenah duk suna gida. Ƴammata masu kama da Ibtisam sosai. Sai dai sun fita surutu da ɗan rawan kai. Sannan sun fita jiki, idan ma ba ka kalla fuska ba da yanayin nutsuwar sai ka ɗauka sun girmeta.
         Tailor ya basu iPad ɗinsa dake ɗauke da bridal designs na ƴan gata irinta domin zaɓi. Duk da dai da farko Ms. Adaora taso ace sunyi zaman ne tare da ango shi kansa. Amma tunda anyi haka zasu fara tattaunawa da ita sai shima su nemesa. Idan ya kama suje inda yake su samesa shima kuma shike nan.
         Da taimakon su Afia suka zaɓi komai. Hatta da wanda zasuyi pre-wedding photos nan da kwana biyar. Bayan sun kammala yarinyar tailor dake tare da su ta gwada Ibtisam yanda ya kamata. Daga nan Ms. Adaora ta amshi details ɗin angon shima akan zatai magana da shi..

               ★______________★
                      ««KANO»»

         A wannan gaɓar rayuwar Ummul-khair ta fara samun ɗan nutsuwa. Ina nufin nutsuwa a ɓangaren talla, abubuwa sun fara yi mata sauƙi. Kamar yanda Baba Sambo yace ta dinga yi hakan take yi. Hatta da awarar safe data ɗauka take kaita makarantar allon da yace ta raba, tana zuwa ta sanar masa kuɗin kuma zai ɗauka ya bada tamkar ba nemansu yake da wahala ba. Hakama na rana, dama bata zuwa tallar dare sai yayunta. Wannan damar data samu ya sata komawa islamiyya sosai.
          Umma bata ce mata komai ba, dama ita matsalarta aƙi saida mata kayan sana'arta ne ko a ballagazar mata da kuɗi. Amma in har zaki sayar, ka kawo mata kuɗinta cur duk uwar ma da zakayi je kaita yi rayuwarka ce. Ba Ummah kaɗai ba, wannan halayya ce ta duk matan gidan ma. Shiyyasa ko yaran sun dawo talla da wahala ka gansu suna tayasu wani aikin gida kuma. A'a nan fa ɗaya, duk wata wahala ta cikin gida da girka sana'ar tasu zuwa wake-wake babu ɗan dake taya uwarsa. Talla dai akace kuma sunayi. Suna dawowa wahalarsu ta ƙare, kowa sai ya nema wajen zuwa kuma.
           Kamar kullum yau ma Ummul-khair ta ɗauki botikin awarar safe. Sai dai tana fita ƙofar gida taci karo da malam Awwal. Cike da farin ciki da ɗoki take kallon sa. Sai kuma ta risina tana gaishe shi. Shi ma yana murmurshi da kulawa ya amsa idonsa akan awarar data ɗakko. Sai kuma ya kauda kallon nasa zuwa fuskarta. 
          “Talla zaki je?”.
     Kanta ta jinjina masa, har lokacin dai da murmurshin. Tana matuƙar ƙaunar Malam Awwal, duk da ƙuruciyarta tana jinsa kamar Babanta a ranta, duk da kuwa shekarunsa basu kai na ya haifeta ba. Hasalima ko aure bai taɓa yi ba.
        Takardun dake cikin brown envelope babba ya fido batare da ya sake magana akan tallar tata ba. Ya miƙa mata yana faɗin, “Sakamakon jarabawarku ne ya fito. Kin yi ƙoƙari sosai, Ummul-khair. Zaki tafi sakandare da izinin UBANGIJI”.
      Tuni farin cikin ta ya sake yalwatuwa akan fuskarta. Dan yana mata bayani ne dai-dai da fahimtar ta. Ta ajiye botikin awarar a ƙasa. Da sauri ta karɓi takardun, ta juya ta kwasa da gudu cikin gida... tana kiran       
      “Umma! Umma!”.
Idanu Malam Awwal ya ɗan waro yana binta da kallo. Sai kuma yayi ƙaramar dariya yana mai jinjina halin ƙuruciyarta. Baifa gama mata bayani ba ta amshi takardu ta afa da gudu. Ya girgiza kai tare da kaiwa zaune a dakalin ƙofar gidan yana janye botikin awarar tata gefe kasancewar a hanya ta ajiye ta ma..

       ....★★....

       “Kai jimin wani iskanci. Ummul-khair wane irin kira ne haka?, zaki ƙarar mana da sunan uwa ne? Ubanwa ya biyo ki?”.
      Cikin ɗan rage rawar jikin da take, sai dai murnar bata gushe ba ta ce, “Yaya Hajna ba wanda ya biyo ni. Kalli Malam Awwal ne ya kawo min sakamakon jarabawar da mukayi ta gama firamare. Kuma yace naci zanje sakandare”.
      Wata banzar harara Hajna ta watsa mata. Sai kuma taja tsaki da faɗin, “Ikon ALLAH, iska dai na wahal da mai kayan kara. Ke wai halan kina ma da aljanun son zuwa makaranta ne? Aiko aiki ya sameki. Ga ƴan bokon nan taf gari babu aikin yi sai zaman gulma da hamma a bakin layi. Idan sukaga motar masu kuɗi har zirarar da yawu suke. Yarinya ki nema kuɗi kawai, wannan karance-karancen babu inda zai kai ki sai wahalar da kai mtsowww”.
         Cikin tura baki Ummul-khair ta ce, “Toni ina ruwana. Nidai kawai ina so”.
       Daga haka ta wuceta zuwa inda Umma ke fitowa daga bayinsu mai murfin labulen buhu. 
     “Shegiya, jeki kiyita so mana”.
  Hajna ta faɗa a ƙufule tana shigewa cikin ɗakinsu. Akwai abinda taso sake faɗa, sai dai kiran daya shigo wayar ta data saƙe cikin zani ya katseta. Waya ce babba touch screen. Sabuwa ce fil kwana uku kenan da mallakarta, sai dai babu wanda ya sani a gidan nasu tana ta ɓoyewa. Ganin mai kiranta ne ya sata ɗagawa da sauri karta katse. 
         “Hello Hajjaju, ina wuni?”.
    Ta faɗa ƙasa-ƙasa tana kallon ƙofa alamar bata son wani ya jita, sai kuma ta ɗan yi shiru alamar sauraren wancan ɓangaren. Sai kuma cikin gyaɗa kai ta ce, “Karki damu zan zo, amma sai da yamma na saida abincin rana. Kin san halin Umman mu dai. Yanzu kuma zanyi wanki ne kayana duk sunyi dauɗa”.
        Shiru ta sake yi. Sai kuma ta gyara tsaiwa tana sake leƙa hanyar shogowa. Ganin babu dai wanda ya taho ta ce, “Yo Hajjaju idan kin ce zaki biya min ɗin mizai hana. Sai na samo almajirin da zai yi ni kuma ki saurareni gani nan zuwa yanzun nan”.
        Ta sake yin shiru. 
    “A to shike nan sai nazo”.
Daga haka ta sauke wayar ta sake maidata a cikin zaninta ta gyara rigarta. Mayafi ta ɗauka akan murfin wardrobe ɗin su da duk ya karye ta fito.
       A ƙofar gida Hajar ta iske Umma da Zaitoona da Ummul-khair wajen Malam Awwal. Sai dai Umma nata masifa akan ita bata yarda ba yanzu da batun makarantar Ummul-khair. Tunda dai tayi wancan ya isa. Shi ko sai roƙon Umma ɗin yake tamkar shine zai yi karatun ba ƴarta ba. Zaitoona kuwa tayi shiru damuwa shimfiɗe a fuskarta. Ga Ummul-khair na kuka. 
         Cikin taɓe baki Hajna ta ce, “Umma ina zuwa”.
      “Gidan Ubanwa kuma zaki ke kuma Hajna? Abinci fa nake shirin kammalawa kina ganin har goma ta kawo jiki”.
      “Kai Umma yanzu fa zan dawo. Nan gidan Hajjaju zanje amso saƙo”.
     Daga haka tai gaba abinta bata jira amsar Umma dake a ƙufule ba. Dan haushin Malam Awwal ne ke sake tunzurata da kukan da Ummul-khair ke rusawa kamar ubanta aka aiko ya mutu ne...........✍️


    Hummmmmm… tirƙa tirƙa kenan. 😂🔥


Masu karatu, barkanmu da sake ganin yau ɗin fa.

 Wannan pages ɗin da kuka karanta sune ƊANƊANO daga sabon littafin Bilyn Abdull mai suna SANTSI.

Labarin SANTSI ya taɓo abubuwa masu yawan gaske da suke cikin rayuwarmu ta yau da kullum.

Ya taɓo ɓangarori daban-daban na rayuwa da suke mana illa ba tare da mun fahimta ba, ko kuma mun fahimta ɗin amma mun kasa gyarawa.

TARBIYYAR YARANMU, wadda muka kasa gane cewa tana fara taɓarɓarewa daga hannayenmu, musamman mu iyaye mata, kafin duniya ta ci gaba da jan ragamar su.

Kowace rayuwa tana da ƘALUBALE.

Ba a gidan TALAKA kawai ba.
Ba a gidan masu ARZIKI kawai ba.
Ba a gidan masu ilimin ADDINI kawai ba.
Ba a gidan masu ilimin BOKO kawai ba.

A ko’ina rayayye zai iya fita. Haka ma matacce zai iya fita.

Kowane ƊAN ADAM yana da alheri, yana da sharri. Ɗabi’arka ce ke bayyana ka ga sauran mutane har ake iya gane WANENE KAI?

Mutum KIRKI, idan alherinsa ya rinjayi sharrinsa.

Ko…

Mutumin BANZA, idan sharrinsa ya rinjayi alherinsa.

Ainihin RAYUWA ba daga inda muka fito ba ne. Ba daga yadda muka fara ba ne. Ina muke shirin zuwa? A nan babban ƙalubalen yake.

Domin idan muka yi gaggawa ko son zuciya, tabbas za mu iya taka SANTSI.

Shi kuma ɗiba yake ya zubar… ko kuma ka tsallake shi da NASARARKA.

Rayuwa ba ta raba WAHALA DA JIN DAƊI a hanya ɗaya.

Wasu suna da komai amma zuciyoyinsu sun cika da tsoro.

Wasu ba su da komai amma suna riƙe da fata.

Kuma dukansu mata ne.


★ Ga Umar (Ahkam) nan mun fara ganinsa tun yana yaro. Yanzu ya girma dole. Yana ina? Wacece mahaifiyarsa? Me mahaifinsa Isma’il yake ɓoyewa da yake tsoron bayyanawa su Ammah? Ya shafi rayuwar Ahkam ne? Ko kuwa shi kaɗai mahaifinsa?.


★ Ga Ummul-khair nan mun gani, mai burin ILIMI. Amma inda ta fito da yadda take rayuwa ne SANTSIN da take kai. Shin Ummah za ta bari ta samu cikar burinta kuwa?.


★ Ga Deenah, mace ’yar gata, mai ilimi, mai mijin da yake sonta, tana da halaye masu kyau, ’yar gayu ce, ta tashi cikin dukiya, tana rayuwa a cikinta. Amma zama da kishiya ya zama mata BARAZANA tun a farkon tafiyarsa. Shin za ta haƙura ta amshi kishiya, ko za ta iya hana Farouk?.


★ Ga Hajna, yayar Ummul-khair. Wani ɗan haske ya fara haska mana wani muhimmin abu da yake ɓoye a duniyarta. Wacece Hajjaju? Wace rawa za ta taka a rayuwar Hajna?.


★ Ga Ibtisam, amarya mun gan ta a Gusau. ’Yar masu kuɗi. Mai ilimi. Mai sanyin hali. Wanene mijin da za ta aura?.


★ Sambo.
★ Malam Awwal.
★ Zaitoona da sauran ahalin gidan Ummul-khair.

Wace rawa za su taka mana?

Bafa su kaɗai suke nan ba.
Akwai sauran rina a kaba. 😭🔥

SANTSI wata duniya ce mai cike da CAKWAKIYA, mai zaman kanta.
Duk yadda zan muku lissafin abin da yake cikinta, ba lallai ku gane ba… har sai mun shiga cikin labarin tare.
Amma ku sani…

Akwai:
★ TARBIYYA.
★ CAKWAKIYA.
★ SOYAYYA.
★ ƘALUBALE.
★ KITUMURMURA.
★ ƘADDARA.
★ ZAMBA CIKIN AMINCI.
★ KWAƊAYI.
★ SAKACI.
★ ABIN TAUSAYI.
★ MAMAKI.
★ AL’AJABI.
★ BAN HAUSHI.
★ MUHIMMANCIN AIKI DA ILIMI, BA TAKARDAR SHAHADA KAWAI BA.

Duk suna cikin littafin SANTSI.

Labarin da ya zo muku da salo na musamman.

ƁANGARORI DABAN-DABAN NA RAYUWA.

Amma fa… wannan da kuka karanta har yanzu ƊANƊANO NE. 👀

Abin da ke gaba ne zai fara buɗe mana ƙofofin wannan duniyar.

Kar ku bari a baku labari.

SANTSI.
SANTSI.
SANTSI.

Shine taken.🔥


FREE PAGES SUN KAMMALA😘🙏.


 

Want the next chapter?

ui.create_a_free_arewapen_account_to_save_progress_unlock_paid_chapters_fol