Free chapter · Read without an account

05

by Umaimah Ado Gaya · SARƘAƘIYA

Chapter 5 page 9

MEXICO

Tun kusan mako guda kenan, M.d ya fara lura da wasu sauye-sauye a jikin Fukhee. Da farko ya ɗauka gajiyar karatu ce kawai, domin a kwanakin baya sun shafe lokaci mai tsawo suna nazari tare da shirye-shiryen wasu ayyukan jami'a da yake shirin sanyata. Amma da kwanaki suka ja, sai ya fahimci abin ya fi ƙarfin gajiya.

Kasalar jikinta ta ƙaru sosai. Wani lokaci idan suna tsaka da karatu, sai ta jingina da kujera tana lumshe ido kamar wadda ƙarfin jikinta ya ƙare. Idan ya matsa mata ta huta, sai ta yi murmushi kawai ta ce ba komai ba ne.

Sai dai ba komai ba ɗin ya fara zama komai.

Rashin cin abinci ya biyo baya. Duk irin abincin da ta fi so, yanzu sai ta ɗan ɗanɗana kaɗan ta ture farantin. Wani lokaci kuma amai kan taso mata ba tare da wani dalili ba. Haka kuma tana yawan jin tashin zuciya da zazzaɓi mai sauƙi wanda ke dawowa musamman da dare.

Abin da ya fi tayar wa M.d hankali shi ne yadda idanuwanta suka fara rasa haskensu. Fuskarta mai walƙiya ta yi fayau, fatarta kuma ta soma canza launi kaɗan-kaɗan.

"Fukhee..."

Ya kira sunanta a hankali yayin da yake zaune kusa da ita a falon gidan. Ita kuwa tana kwance a kan kujera, hannunta ɗaya a goshinta.

Ta buɗe ido da ƙyar.

"Lafiya?"

Ta yi murmushin da bai kai cikin idanuwanta ba.

"Alhamdulillah."

M.d ya girgiza kai.

"Wannan 'Alhamdulillah' ɗin ba ya gamsar da ni."

Ta yi dariyar ƙoƙarin ɓoye damuwa.

"Kana damuwa da komai ne."

"Saboda ina da abin da nake son karewa."

Ta yi shiru, zuciyarta na bugawa da sauri.

Ya kamo hannunta cikin tafin hannunsa.

"Wallahi, ban ji daɗin yadda kika canza cikin kwanakin nan ba."

Ta sauke numfashi.

"Watakila gajiyar karatu ce."

"Gajiya ba ta sa mutum ya riƙa amai kullum fa."

Ta yi shiru.

"Gajiya ba ta hana cin abinci."

Har yanzu ba ta ce komai ba.

"Gajiya ba ta sa mutum ya yi zazzaɓi kullum ba."

Sai ta sauke idanu.

A hankali ta ce,

"Ba na son asibiti."

M.d ya ɗan yi murmushi.

"Na sani."

"Ba na son allurai."

"Na sani."

"Ba na son ƙamshin magunguna."

"Na sani."

Ta ɗago ta kalle shi.

"To me ya sa kake son ka kai ni?"

Ya ɗan matsa kusa da ita.

"Saboda ba zan taɓa yafewa kaina ba idan na yi sakaci da lafiyarki."

Maganar ta sauka kai tsaye cikin zuciyarta.

Ta jingina kanta a kafaɗarsa ba tare da ta ce komai ba.

Ya shafa kanta a hankali.

"Ki yi haƙuri da ni. Wataƙila ina takura miki..."

Ta girgiza kai.

"A'a."

"Sai dai ina tsoron rasa murmushinki."

Fukhee ta lumshe ido, hawaye kaɗan suna taruwa a cikin idanunta. Ba don ciwo kaɗai take jin nauyi a zuciyarta ba, har da irin ƙaunar da wannan mutumin yake nuna mata a kowace rana.

Bayan ɗan lokaci ta ɗago kai.

"To..."

M.d ya kalle ta.

"Idan na yarda mu je asibiti..."

Ya ɗaga gira.

"...za ka daina yi mini wa'azi na kwana uku?"

Ya bushe da dariya.

"Shi ke nan? Wannan shi ne sharadin?"

Ta ɗaga kafaɗa.

"Eh."

"Na amince."

Ta miƙa masa hannu.

"Deal?"

Ya kama hannunta yana girgizawa.

"Deal."

Sai dai kafin ya saki hannun nata, ya jawo ta kusa da shi.

"M.d..." ta faɗa tana dariya.

"Me kuma?"

"Na ci nasara."

"A kan me?"

"Na sa kika yarda za mu je asibiti."

Ta turo ƙaramin bakinta gaba.

"Ka yi murna da wuri."

"Me ya rage?"

"Ban ce yau ba."

Ya haɗe fuska.

"Fukhee..."

Ta ƙyalƙyale da dariya.

"To shikenan, gobe."

Ya saki ajiyar zuciya mai nauyi.

"Alhamdulillah."

Dukansu suka yi dariya.

Ba su san cewa wannan dariyar za ta zama ɗaya daga cikin lokutan farin cikin da za su daɗe suna tunawa ba.
    
     Washegari tun da sassafe M.d ya gama shiryawa cikin kayan aikinsa na yau da kullum. Da ya fito falo, ya tarar da Fukhee zaune a gefen dining table tana ƙoƙarin shan shayin da ya haɗa mata. Sai dai daga kallonta kaɗai za ka fahimci ba ta da ƙarfin cin komai.

Da ƙyar ta ɗaga kofin ta kai bakinta. Da ta kurɓi kaɗan, sai ta ɗora kofin a hankali ta lumshe ido, tana dafe ƙirjinta.

M.d ya zuba mata ido.

"Babe..."

Ta buɗe idanunta.

"Uhmm?"

"Kar ki tilasta wa kanki idan ba za ki iya ba."

Ta yi murmushi mai rauni.

"Ina ƙoƙari ne."

Ya ja kujera ya zauna kusa da ita.

"Bari na kawo miki ruwa."

Bai jira amsarta ba ya miƙe ya ɗauko robar ruwa daga firiji. Ya buɗe ya miƙa mata.

Ta karɓa tana kallonsa cikin nutsuwa.

"Nagode."

Ya ɗan yi murmushi.

"Yau kin yi mini godiya sau nawa kenan?"

Ta ɗaga gira.

"Ka fara lissafawa ne?"

"Eh mana."

"To idan haka ne..." Ta ɗan yi dariya. "Nagode karo na ƙarshe."

"Na ƙi karɓa."

"Saboda me?"

"Saboda ina son ki riƙa gode mini har tsufanmu."

Fukhee ta sauke idanu tana murmushi. Kullum sai ya faɗi wata magana da za ta sa zuciyarta ta yi laushi.

Bayan ta ɗan sha ruwan, ta miƙe tsaye. Sai dai tana yin taku biyu, jikinta ya yi mata nauyi. Ta ɗan yi tangal-tangal, kafin ta dafa bayan kujera.

M.d ya yi saurin tasowa.

"Fukhee!"

"Cikin sauri ya kama ta kafin ta zame ƙasa."

"Lafiya?"

Ta ɗan girgiza kai.

"Na ji jiri ne kawai."

Ya dafa goshinta. Har yanzu akwai ɗumin zazzaɓi a jikinta.

Ba tare da ya ƙara gardama ba ya ce,

"Muna iya tafiya yanzu."

Ta buɗe baki za ta yi magana, amma da ta haɗa ido da shi sai ta fasa. Wannan karon ta fahimci ba zai saurare ta ba.

---

Mintuna kaɗan bayan haka, motarsu ta fice daga gidan.

A hanya, M.d ya rage gudun motar fiye da yadda ya saba. Idan hasken titi ya tsaya ja, sai ya waiwayo ya dubi Fukhee.

Ta jingina kanta da kujera tana kallon gine-ginen da suke wucewa ta cikin gilashin mota. Fuskar nan tata mai cike da annuri ta yi shiru fiye da yadda ya saba gani.

Ya ɗan saki ajiyar zuciya.

"Kin yi fushi da ni?"

Ta juyo ta kalle shi.

"Saboda me?"

"Saboda na nace sai mun je asibiti."

Ta yi murmushi.

"Ba fushi nake ba."

"To me kike tunani?"

Ta ɗan yi shiru.

"Daddy na."

M.d ya yi shiru na ɗan lokaci.

"Me kika tuna?"

"Yana yawan cewa..." Ta ɗan haɗiye yawu. "...idan mutum ya ji ba lafiya, kada ya yi wasa da ita."

M.d ya ɗan jinjina kai.

"Ya faɗi gaskiya."

Sai ta yi murmushi mai sanyi.

"Da alama da yana nan, da ku biyu za ku haɗa kai a kaina."

M.d ya yi dariya.

"Ba da alama ba. Da mun riga mun ci nasara."

Ta turo ƙaramin bakinta gaba.

"Kun cika haɗin baki."

"Saboda muna sonki."

Ta kasa ɓoye murmushin da ya suɓuce mata.

Shiru ya ɗan ratsa motar na wasu daƙiƙu.

Can M.d ya ce,

"Amma akwai abu ɗaya."

Ta ɗago gira.

"Me kuma?"

"Duk lokacin da kika warke..."

Ta saurare shi.

"...zan rama duk damuwar da kika ba ni."

Ta haɗe fuska da gangan.

"Da me?"

"Zan sa ki dafa mini jollof rice."

Ta zaro ido.

"Ni?"

"Eh."

"Ka manta abin da ya faru lokacin ƙarshe?"

Ya yi dariya sosai.

"Na tuna."

"Ka ci spoon biyu kacal."

"Saboda na ji tausayin tukunya."

Fukhee ta kai hannu ta daki kafaɗarsa a hankali.

"Kai ko?Wato tukunyar ma ka tausayawa ba ni ba."

Ya yi dariya har idanuwansa suka ƙanƙance.

"Haba, ai kin ce kin iya  girkin yanzu,so kin ga akasin daga tukunya ne."

"To ba sai ka riƙa gyara  mini ba?"

"Alright,Zan riqa gyara miki har ki zama k'wararriyar chef."

Duk da ciwon da take ji, Fukhee ta kasa hana kanta dariya. Wannan mutumin yana da wata baiwa ta musamman; ko a cikin damuwa, yana iya samo mata murmushi.

M.d ya ɗan waiwaya ya kalle ta. Da ya ga tana dariya, sai zuciyarsa ta ɗan kwanta. Sai dai a cikin ransa, addu'a ɗaya ce kawai yake yi.

"Ya Allah... kada wannan murmushin nata ya gushe."

---

Bayan kusan rabin awa, motar ta tsaya a harabar wani babban asibiti da ya shahara wajen kula da marasa lafiya masu buƙatar ƙwararrun likitoci.

M.d ya fito da sauri ya zagayo gefen da Fukhee take. Ya buɗe mata ƙofa, sannan ya miƙa mata hannu.

Ta kalle shi tana murmushi.

"Ni fa ba tsohuwa ba ce."

Ya ɗaga gira.

"Na sani."

"To me ya sa kake riƙe ni kamar zan faɗi?"

Ya ɗan matso kusa da ita.

"Saboda ke amana ce a wurina."

Maganar ta sa ta yi shiru na ɗan lokaci.

A hankali ta saka hannunta cikin nasa.

Ya matse hannun nata cikin kulawa.

Sannan suka nufi ƙofar asibitin tare... ba tare da sun san cewa bayan ƙofar nan akwai wasu kalmomi da za su fara sauya rayuwarsu gaba ɗaya ba.
******

Masarautar Agadas

Gimbiya Hadiza ta zura wa Yarima Iqbal idanunta masu cike da tsantsar fushi. Kalaman da suka fito daga bakinsa sun shiga dodon kunnuwanta, suka ratsa zuciyarta da kwakwalwarta tamkar kaifin takobi. Cikin murya mai cike da izzar mulki da gadon manyanta ta ce,

"A duk tarihin rayuwata a matsayin Gimbiya, babu wani mahaluki da ya taɓa yin fito-na-fito da umarnina sai kai, Iqbal. Hatta mahaifiyarka, Fatima, ba ta taɓa aikata haka ba."

Ta ɗan dakata, tana kallonsa. Yariman ya sunkuyar da kansa, ya dunkule hannayensa cikin juna, yana ƙoƙarin danne wutar fushin da ke ta ƙuna a cikin zuciyarsa.

Ta ci gaba da cewa,

"Aurenka da Fakriyya ba tamkar wajibi ba ne, Iqbal... wajibi ne. Kuma za ka aure ta, ko da amincewarka ko babu."

A karo na farko tun fara tattaunawar, Yarima Iqbal ya ɗago kansa ya kalli kakarsa ido cikin ido. Fuskarsa babu alamar tsoro ko rauni, sai tsantsar ƙuduri. Cikin zurfin muryarsa mai nauyi—wadda babu wani a masarautar da ya taɓa jin irin sautinta daga bakinsa—ya ce,

"Ki yi haƙuri, Amma bana jin zan taɓa auren wannan yarinyar. Ba ta da nutsuwa, ba ta da tarbiyya. Ta yaya zan dab'a wa kaina wuƙa da hannuna, in amince da auren da na san nadama ce za ta biyo baya?"

Ya ɗan yi shiru, yana jan numfashi kafin ya ci gaba.

"Me kike so in gaya wa 'ya'yan da zan haifa idan suka tambaye ni dalilin da ya sa na zaɓa musu uwa mara cancanta? Shin zan ce musu kakata—wadda ba ita ce Allah Ya bai wa alhakin zaɓa mini mata ba—ita ce ta tilasta mini wannan aure? Wannan ba zai dauki hankali ba , Gimbiya."

Ya girgiza kansa a hankali.

"Na yi miki biyayya sau da yawa a baya. Na sadaukar da ra'ayina saboda mutuncinki. Amma a wannan karon... ki yi haƙuri. Gaskiya ba zan iya ba."

Gimbiya Hadiza ta daskare a zaune. Bakinta ya ɗan buɗe, idanunta suka tsaya cak kan yaron da ta shafe shekaru tana fafutukar mallake zuciyarsa da rayuwarsa.

Ta sha wahala wajen tabbatar da cewa ya kasance a ƙarƙashin ikonta. Ta yi amfani da dabaru iri-iri, wasu na alheri, wasu kuma waɗanda ko ita kanta ba ta son tuna su. Yanzu kuwa, bayan komai ya kusa cika, sai ga Iqbal yana shirin rusa ginin da ta kwashe shekaru tana ginawa.

Yayin da take kallon idanunsa, ta hango wata irin wuta da ba ta taɓa gani ba a cikinsu. Wutar ƙin yarda. Wutar tawaye.

Nan take zuciyarta ta buga da ƙarfi.

"Ashe... ya fara zargin wani abu?"

Ko da bai furta komai ba, idanunsa, yadda yake magana, da yanayin motsinsa sun bayyana mata cewa akwai wani babban sirri da ya fara gano wa.

Sai dai... wane sirri ne?

Shin me ya gani?

Me ya ji?

Ko kuwa wani ne ya sanar da shi abin da ta shafe shekaru tana binne wa cikin duhun asiri?

Tambayoyi suka fara yi mata tururuwa, suna caccaka mata zuciya.

Ba tare da ya jira amsa ba, Yarima Iqbal ya miƙe tsaye. Ya gyara alkyabbar da ke jikinsa cikin isa irin ta magajin sarki, sannan cikin ko-in-kula ya ce,

"Ni zan tafi. Ina fatan za ki yi la'akari da uzurina."

Daga haka ya juya, ya fara tafiya cikin natsattsun takunsa masu bayyana asalinsa na jinin sarauta.

Har ya kusan fita, Gimbiya Hadiza ta kasa ko motsawa.

Kamar wadda aka dawo mata da gani bayan shekaru na makanta, ta zaro idanunta tana binsa da kallo. A zuciyarta kuwa tunani ya fara kai-komo.

Wane mataki ya kamata ta ɗauka a kansa?

Ta wace hanya za ta gano iyakar abin da Iqbal ya sani game da sirrikan da ta binne tsawon shekaru?

Domin duk yadda Yariman ya yi ƙoƙarin ɓoye abin da ke cikin zuciyarsa, fuskarsa da idanunsa sun ci amanarsa. Domin ko karin maganar hausawa ne cewa, "Labarin zuciya, a tambayi fuska."

Kofa na rufewa a hankali bayan fitowar Yarima Iqbal ya yi daidai da saukar wani irin shiru mai nauyi a cikin falon Gimbiya Hadiza.

Na wasu daƙiƙu ba ta motsa ba. Idanunta suna kan ƙofar da ya fita tamkar tana sa ran zai dawo ya janye maganganunsa.

Sai dai hakan bai faru ba.

A hankali ta lumshe idanunta, ta sauke dogon numfashi. Da ta sake buɗe su, fushin da ke cikinsu ya ragu, amma ya maye gurbinsa da tsantsar fargaba.

"Ba zai yiwu ba..." Ta furta a hankali. "Iqbal ba zai iya gano komai ba... ba zai yiwu ba."

Sai dai zuciyarta ta ƙi amincewa da abin da bakinta yake faɗi.

Tun daɗewa take lura da sauyin halayensa. Yana yawan yin dogon tunani. Yana tambayar wasu tambayoyi da a da bai taɓa yi ba. Har ma ya fara yawan fita ba tare da sanar da kowa inda zai nufa ba.

A lokacin ta ɗauka girma ne kawai yake ƙara yi.

Yanzu kuwa ta fahimci kuskurenta.

Da sauri ta miƙa hannu ta ɗauki wayarta. Ta latsa wani lamba da ta haddace tun shekaru da dama.

Ba a jima ba aka ɗaga.

"Mama..." muryar namiji ta fito daga ɗaya ɓangaren.

"Ka zo fada yanzu."

"Mama, akwai matsala ne?"

"Na ce ka zo. Yanzu."

Ba tare da ta jira amsarsa ba ta katse kiran.

---

A gefe guda kuwa, Yarima Iqbal yana tafiya cikin harabar fada, amma zuciyarsa cike take da wani irin nauyi.

Bai taɓa tsammanin ranar da zai tsaya ya ƙi bin  umarnin kakarsa za ta zo ba.Har ma yayi fito-na fito da ita.Tun yana ƙarami, Gimbiya Hadiza ita ce komai a rayuwarsa.

Ita ce ta raina shi.Ita ce ta koya masa siyasa.Ita ce ta gina shi ya zama magajin sarauta.Amma kuma...

Ita ce mutum ɗaya da ya fara zargi da ɓoye wani babban sirri da zai iya girgiza masarautar Agadas baki ɗaya.

Ya tsaya cak a tsakiyar lambun fada.

A hankali ya saka hannu cikin aljihunsa, ya ciro tsohuwar hoto da gefenta ya fara shuɗewa saboda tsufa.

Ya kalli hoton na ɗan lokaci.

Sai ya shafa fuskar wata mata da ke cikin hoton da babban yatsansa.

Cikin murya mai cike da kewar da ba a saba ji daga gare shi ba ya ce,

"Na yi miki alƙawari... zan gano gaskiya, ko da kuwa za ta rusa komai."

Daga nesa, wani mutum da ya ɓoye kansa a bayan bishiyoyin lambun fada yana kallonsa.

Da Iqbal ya ci gaba da tafiya, mutumin ya fito a hankali.

Ya zaro wayarsa.

"Ranka ya daɗe..." ya faɗa cikin ƙasa da murya.

"Yariman ya fara motsi. Kuma ina da tabbacin ya kusa gano abin da muka shafe shekaru muna ɓoyewa."

Ya kashe wayar.

A hankali murmushi ya bayyana a fuskarsa.

Murmushin da babu alamar alheri tattare da shi..

Shiru Gimbiya Hadiza ta yi, idanunta ƙafe kan ƙofar da Yarima Iqbal ya bi ya fice. Zuciyarta kuwa babu abin da take yi sai tafarfasa, kamar tukunyar ruwan da aka ɗora kan garwashin wuta.

"Tabbas akwai abin da ya canza a tare da Iqbal... amma mene ne?" ta tambayi kanta cikin ƙunci.

Ta lumshe idanunta na ɗan wani lokaci kafin ta sake buɗe su da sauri.

"Ko kuwa... kamar yadda nake zargi ne? Shin ya gano wani abu daga cikin tarin sirrikan da na shafe shekaru ina binnesu?"

Tambayar ta tsaya mata a rai ba tare da ta samu amsa ba.

Cikin rashin natsuwa ta miƙe tsaye, tana kai-komo a cikin ɗakin, hannayenta a haɗe a bayanta. Kowanne taku da take yi yana ƙara bayyana irin tashin hankalin da take ciki. Tunaninta ya karkata ne kawai kan hanyar da za ta gano ainihin abin da Iqbal ya sani; abin da ya sa ya fara kallonta ido-da-ido ba tare da fargabar matsayinta ba.

A daidai lokacin ne  sallamar Jakadiya ta bayyana daga bakin ƙofa, tana neman izinin shiga.

Kai-komon da Gimbiya Hadiza take yi ya tsaya cak. A hankali ta ja dogon numfashi, sannan ta nufi kujerarta cikin nutsuwa irin ta masu mulki. Ta zauna tare da jingina bayanta, fuskarta ta koma cike da izza da kwarjini, tamkar babu abin da ke damunta.

Sai bayan ta tabbatar da cewa ta sake ɗaukar kamanninta na shugaba mai cikakken iko, sannan ta ce,

"Shigo."

Jakadiya ta shigo da sauri, tana isowa kuwa ta zube ƙasa rubda ciki. Jikinta har rawa yake yi saboda tsananin girmamawa da kuma tsoro. Cikin murya mai cike da kirari ta fara cewa,

"Barka da wannan lokaci, Uwargijiyata. Allah Ya ƙara miki lafiya da ɗaukaka. Ki daɗe, ki yi karko irin na dabino. Waye ya ce da ke ba ke ba? An buga da ke, an bari. Allah Ya ja zamanin Fulanin Sarki. Sarauniyar da ba ta da tamka a wannan nahiya, wadda ba za a sake samun irinta ba. Hutawarki lafiya, 'yar sarki, matar sarki, jikar sarki. Babar Sarauniya Fatime, kaka ga Magajin Sarki..."

Gimbiya Hadiza ta ɗaga hannu kaɗan.

Alamar kaɗai ta isa.

Jakadiya ta yi shiru nan take, ta rufe bakinta tamau, ta kuma ƙara sunkuyar da kanta ƙasa tana jiran umarnin uwargijiyarta.

Gimbiya Hadiza ta gyara zamanta kafin ta ɗora idanunta a kan Jakadiya. Cikin muryar da ke nuna iko da hikima ta ce,

"Jakadiya... gaya mini gaskiya. Kina ganin akwai inda na yi kitso da ƙwarkwata a cikin al'amurana?"

Jakadiya ta ɗan ɗago kai cikin firgici, amma ba ta kuskura ta haɗa ido da ita ba.

"Allah Ya taimake ki, Ya ƙara miki nisan kwana, Uwargijiyata. Ban fahimci abin da kike nufi ba. Allah Ya sa dai ba wata matsala ce ta auku ba."

Gimbiya Hadiza ta fesar da wani dogon numfashi. Daga bisani ta ce cikin sanyin murya mai cike da tunani,

"Kamar yadda kika sani, bayan na aika aka kira Yarima Iqbal, ya zo gare ni. Amma maganganunsa a yau ba irin na da ba ne. Ba wai kawai ya yi watsi da umarnina ba... har ma ya yi mini magana kamar wanda ya san wani abu da nake ɓoye wa."

Ta ɗan yi shiru, idanunta suna ƙanƙancewa.

"Na shafe shekaru ina jan ragamar wannan masarauta cikin hikima. Ban taɓa bari wani ya gano sirrina ba. Amma yau... zuciyata tana gaya mini cewa Iqbal ya fara hango wani ɓangare na abin da na ɓoye."

Ta karkata kanta kaɗan tana kallon Jakadiya.

"Saboda haka ina son ki sa ido a kansa. Kada ya fahimci cewa ana bibiyarsa. Ki gano inda yake zuwa, waɗanda yake haɗuwa da su, da kuma duk abin da yake bincike."

Jakadiya ta haɗiye yawu kafin ta ce cikin rawar murya,

"An gama, Uwargijiyata. Da ikon Allah zan gano komai, ko da kuwa yana ɓoye ne a ƙarƙashin ƙasa."

Murmushi mai cike da maƙarƙashiya ya bayyana a fuskar Gimbiya Hadiza.

"Ki tuna, Jakadiya... akwai sirrikan da idan suka tonu, ba mutum ɗaya kaɗai suke hallaka ba. Masarautu ma suna rushewa saboda su."

Kalaman nata suka sanya zuciyar Jakadiya yin wani irin bugawa. Ta ƙara russunawa ƙasa, tana jin tsoron cewa sirrin da uwargijiyarta ke magana a kansa ya fi ƙarfin duk abin da ta taɓa zato..

Chapter 5 page 10

VILLA CAPITAL STATE

Mr. President ya zuba wa Personal Assistant (PA) ɗinsa ido cikin nutsuwa yayin da yake karanta masa jadawalin ayyukan da suke gabansa na ranar. Sai da PA ya kammala rattaba komai dalla-dalla kafin shugaban ƙasar ya gyara zamansa, ya jingina bayansa da kujerar fata mai girma, sannan cikin murya mai cike da kwarjini ya ce,

"Please, go and call the Chief of Staff."

PA ya ɗan sunkuyar da kansa cikin girmamawa.

"Okay, Sir."

Da wannan ya juya ya fice daga ofishin, ya nufi ofishin Chief of Staff.

Da PA ya fita ya rage sai shi kaɗai, Mr. President ya lumshe idanunsa na ɗan lokaci. A hankali ya ɗaga hannayensa cikin addu'a.

"Ya Allah, Ka shiryar da ni zuwa abin da zai amfani wannan ƙasa da al'ummarta. Ka ba ni ikon yin adalci, Ka kuma ba ni ƙarfin aiwatar da abin da yake daidai."

Bayan wasu mintuna kaɗan, ƙofar ofishin ta buɗe.

Chief of Staff ya shigo tare da PA. Ya yi sallama cikin ladabi, ya gaishe da shugaban ƙasar, sannan bayan ya samu izini ya zauna a kujerar da ke fuskantar teburin shugaban ƙasar.

Na ɗan lokaci Mr. President ya ci gaba da kallonsa cikin tunani kafin ya sauke numfashi.

"Chief..." ya fara da murya mai natsuwa. "Tun ranar da na hau wannan kujera nake ta nazarin abubuwan da suka addabi ƙasarmu. Matsalolin suna da yawa, kuma na san ba zan iya magance su gaba ɗaya lokaci ɗaya ba."

Ya ɗan yi shiru kafin ya ci gaba.

"Amma ina son mu fara da abin da kowa yake gani da idonsa—hanyoyinmu. Ina magana ne kan manyan hanyoyin ƙasa gaba ɗaya, na Tarayya da kuma waɗanda jihohi ke kula da su. Idan hanyoyi suka gyaru, kasuwanci zai bunƙasa, zirga-zirga za ta sauƙaƙa, rayuwar jama'a ma za ta inganta."

Ya haɗe hannayensa kan tebur.

"Ina so ka shirya mana taro da dukkan gwamnonin jihohi. Ba wai domin mu ɗora musu nauyi ba, a'a, domin mu gina haɗin gwiwa. Bayan haka za mu tantance birane uku da suka fi buƙatar gyaran hanyoyi domin su zama matakin farko na wannan shiri."

Chief of Staff ya gyara zamansa, ya ɗan yi shiru yana nazarin maganar shugaban ƙasar kafin ya ce,

"Sir, wannan kyakkyawan tunani ne, kuma babu shakka zai amfani ƙasa. Sai dai ina da wata shawara."

Mr. President ya ɗaga kai.

"Go ahead."

Chief ya ci gaba,

"A ganina, zai fi dacewa mu fara ne da hanyoyin da ke ƙarƙashin gwamnatin tarayya, domin ikon aiwatar da su yana hannunmu kai tsaye. Idan muka nuna wa jama'a sakamako cikin gaggawa, hakan zai ƙara mana karɓuwa da amincewa."

Ya ɗan yi shiru kafin ya ƙara da cewa,

"Bayan mun fara samun nasara a bangaren hanyoyin tarayya, sai mu zauna da gwamnonin jihohi. A lokacin za mu tsara tsarin haɗin gwiwa, mu ji irin gudummawar da kowace jiha za ta bayar, sannan gwamnatin tarayya ta cike gibin da ya rage. Hakan zai sa aikin ya kasance na haɗin kai, ba na umarni kawai ba."

Mr. President ya yi shiru na ɗan lokaci, yana nazarin shawarar Chief of Staff ɗinsa. Daga bisani ya ɗan jinjina kai a hankali, alamar cewa kalaman sun shiga zuciyarsa.

Mr. President ya ci gaba da kallon Chief of Staff na wasu daƙiƙu, kamar yana auna nauyin shawarar da ya gabatar. Daga ƙarshe ya ɗan yi murmushi, ya jinjina kai.

"Chief... wannan shawara taka ta nuna min dalilin da ya sa na zaɓe ka ka riƙe wannan muƙami. Kana kallon abin ta fuskar doka da kuma ta fuskar aiwatarwa. I like that."

Chief of Staff ya ɗan sunkuyar da kansa cikin girmamawa.

"Thank you, Sir."

Mr. President ya miƙa hannu ya ɗauki alƙalami, ya rubuta wasu bayanai a cikin ƙaramin littafinsa kafin ya ɗago.

"To, za mu fara da hanyoyin gwamnatin tarayya. Amma ba na son aikin da zai zama na anfani da kuɗin gwamnati ba tare da an ga sakamako ba. A wannan gwamnati babu abin da zai kasance kamar da."

Ya ɗan yi shiru.

"Ina son a kafa Kwamitin Kula da Ayyukan Hanyoyi na Ƙasa. Kwamitin zai ƙunshi Ma'aikatar Ayyuka, Ma'aikatar Kuɗi, Hukumar Procurement, da jami'an tsaro. Za su riƙa duba duk wani aiki tun daga bayar da kwangila har zuwa ranar kammalawa."

Chief ya zaro ƙaramin littafinsa yana rubuta duk umarnin.

"Noted, Sir."

Mr. President ya ƙara da cewa,

"Sannan ina son a fara binciken manyan hanyoyin da suka fi lalacewa a faɗin ƙasar nan. Kada a kawo mini rahoto daga cikin ofis kawai. Ina son Injiniyoyi su fita su duba da idanunsu, su ɗauki hotuna da bidiyo, su kawo cikakken rahoto cikin makonni biyu."

"Yes, Sir."

"Bayan haka..." Mr. President ya ɗan matsa gaba.

"Ina son tsarin bayar da kwangila ya kasance a buɗe. Duk kamfanin da zai ci kwangila dole ya nuna ƙwarewarsa, ya nuna irin ayyukan da ya taɓa yi, sannan ya tabbatar yana da ƙarfin kammala aikin cikin lokacin da aka ba shi."

Chief ya ɗaga kai.

"Sir, hakan zai rage zargin son rai da kuma hana kamfanonin bogi samun kwangila."

"Exactly!" Mr. President ya amsa cikin sauri.

"Kuma ina son a saka wani sashe a cikin kwangilar da zai ba gwamnati damar soke kwangila nan take idan aka tabbatar da sakaci ko almundahana. Duk wanda ya ci amanar al'ummar Najeriya, ko da wanene, ba zai tsira ba."

Kalaman shugaban ƙasar suka sa ofishin ya yi shiru na ɗan lokaci.

Chief of Staff ya lura cewa wannan ba shugaban ƙasa ne mai son yin surutu ba. Mutum ne mai son a ga sakamako.

Ya rufe littafinsa, sannan ya ce,

"Sir, zan fara aiki kan duk umarnin nan tun daga yau. Zuwa ƙarshen mako za ku samu jadawalin taron gwamnoni, sannan cikin kwanaki goma sha huɗu za mu gabatar da rahoton hanyoyin da suka fi buƙatar gyara."

Mr. President ya miƙe tsaye daga kujerarsa, ya taka zuwa bakin tagar ofishinsa. Ya zuba idanu zuwa harabar Villa, inda motocin gwamnati ke kai da kamo.

Cikin ƙaramar murya ya ce,

"Mutane sun zaɓe ni ne saboda suna son canji. Kuma in sha Allah, canjin nan ba zai tsaya a takarda ba... za su gan shi da idanunsu."

   Bayan Chief of Staff ya fice daga ofishin Mr. President, bai nufi ofishinsa kai tsaye ba. Ya tsaya na wasu daƙiƙu a bakin doguwar hanyar da ta haɗa ofisoshin manyan jami'an Villa. A zuciyarsa kalaman shugaban ƙasar ne suke ta yawo.

"Lokaci ya yi da za a bambanta gwamnati da gwamnati..." ya faɗa a ransa.

Ya fitar da wayarsa.

"Get me the Honourable Minister of Works on the secure line... yanzu."

Cikin ƙasa da minti biyu aka haɗa kiran.

"Good morning, Honourable Minister."

"...Good morning, Sir."

"Mr. President yana son ganawa da kai cikin awa ɗaya. Ka zo da cikakken bayanin duk manyan ayyukan hanyoyin gwamnatin tarayya—waɗanda ake yi yanzu, waɗanda aka dakatar, da kuma waɗanda aka biya kuɗinsu amma ba a kammala su ba."

Sai ɗayan ɓangaren ya yi shiru na ɗan lokaci.

"...Sir... cikin awa ɗaya?"

Chief of Staff ya amsa cikin murya mai cike da ƙarfi.

"Yes. One hour. Mr. President doesn't like excuses."

Ya katse wayar.

---

A lokaci guda...

Federal Ministry of Works

Ofishin Ministan Ayyuka ya kaure da tashin hankali.

Yana gama wayar, Ministan ya miƙe tsaye daga kujerarsa.

"Ina Permanent Secretary?"

"...Yana cikin meeting, Sir."

"Ka katse meeting ɗin nan take. Ku tara dukkanin Director-General, Directors da Chief Engineers. Ina son cikakken bayanin dukkan kwangilolin hanyoyi cikin mintuna talatin."

Ma'aikatan ofishin suka fara kai da kawo.

Aka fara buɗe manyan fayiloli,tare da kunna kwamfutoci.Ana neman rahotannin da tsahon wata da watanni ba a taɓa dubawa ba.

Wasu jami'ai kuwa suka fara kallon juna cikin damuwa.

Domin sun san cewa idan sabon shugaban ƙasa yana neman bayanai cikin gaggawa, to akwai yiwuwar ba zai yi wasa da sakaci ba.

---

A wani sashe na ginin...

Wani babban Darakta ya ja wani ɗan kwangila gefe.

Ya rage murya.

"Ka kira Chairman ɗinku. Ka faɗa masa ya zo Abuja cikin gaggawa. Ina jin wannan gwamnatin ba irin wadda muka saba da ita ba ce."

Mutumin ya haɗiye yawu.

"Kana nufin za su sake duba tsofaffin kwangilolin nan?"

Daraktan ya kalle shi.

"Ba wai za su sake dubawa ba... ina jin za su bincike su ne daga tushe."

Kalaman suka sa zuciyar mutumin bugawa da ƙarfi.

Domin ya san akwai kwangilolin da aka karɓi biliyoyin kuɗi shekaru da suka gabata, amma abin da aka yi a ƙasa bai kai rabin abin da ke cikin takardu ba.

A karon farko cikin shekaru masu yawa...

Tsoro ya fara shiga zukatan masu anfani da dukiyar gwamnati.
*****

MEXICO

Da shiga cikin harabar asibitin, sanyin na'urar sanyaya iska ya daki fuskokinsu. Wurin ya kasance cikin tsari da tsafta. Ma'aikatan jinya suna kai-komo cikin natsuwa, wasu na tura marasa lafiya a kan kujerun guragu, wasu kuma na rakiyar 'yan uwansu zuwa sassa daban-daban.

M.d ya matsa zuwa sashen karɓar baƙi (Reception), inda ya yi wa jami'ar da ke bakin aiki bayani a taƙaice kan halin da Fukhee ke ciki.

Bayan ta karɓi bayanansu, ta buɗe musu fayil sannan ta nuna musu inda za su zauna suna jiran kira.

Fukhee ta zauna a hankali tana jingina bayanta da kujera. Kallo ɗaya M.d ya yi mata, zuciyarsa ta sake cunkushewa. Tun fitowarsu daga gida bai lura ba, amma yanzu da hasken cikin asibitin ya bugi fuskarta, ya hango yadda farin idanunta suka fara ɗaukar ɗan launin rawaya.

Ya ɗan matso kusa da ita.

"Babe..."

Ta ɗago kanta.

"Kin taɓa lura idanunki sun canza launi?"

Da sauri ta girgiza kai.

"A'a."

Ya yi shiru. Bai so ya ƙara tayar mata da hankali ba, don haka ya ɗauke zancen.

Bayan kusan mintuna goma sha biyar, wata nurse mai fara'a ta fito tana kiran sunan Fukhee.

"Mrs. Fukhaihat..."

M.d ya taimaka mata ta miƙe, sannan suka bi bayan nurse ɗin har zuwa ofishin likita.

---

Likitan, wani dattijo mai kimanin shekaru hamsin da haihuwa, ya tarbe su da murmushi.

"Good morning."

"Good morning, Doctor," M.d ya amsa yana musabaha da shi.

Likitan ya nuna musu kujeru.

"Please, have a seat."

Da suka zauna, ya buɗe fayil ɗin Fukhee ya ɗauki biro.

"To, wa zai fara bani tarihin matsalar?"

M.d ya kalli Fukhee.

"Za ki iya?"

Ta gyada kai.

A hankali ta fara bayanin abin da take ji tun farkon alamomin.

Likitan bai katse ta ba. Yana rubuce-rubuce ne kawai yayin da yake saurarenta da kyau.

Da ta gama, ya ɗago kansa.

"Kin ce kina yawan amai. Sau nawa a rana?"

"Wani lokaci sau biyu... wani lokacin sau uku."

"Kin daina cin abinci?"

"Eh... bana jin yunwa sosai."

"Zazzaɓin fa?"

"Yana zuwa musamman da yamma."

Likitan ya yi rubutu.

"Sannan kina jin ciwo a wani ɓangare na cikinki?"

Fukhee ta ɗan yi tunani, sannan ta ɗora hannunta a gefen dama na saman cikinta.

"A nan nake ji kamar wani nauyi da ɗan ciwo."

Likitan ya gyada kai.

"Fitsarinki fa?"

Ta ɗan yi shiru kafin ta ce,

"Na lura ya yi duhu fiye da da."

M.d ya yi mamaki.

"Me ya sa ba ki taɓa gaya mini ba?"

Ta kalle shi.

"Ban ga muhimmancinsa ba."

Ya sauke ajiyar zuciya cikin damuwa.

Likitan ya ci gaba.

"Kin taɓa yin Hepatitis?"

"A'a."

"Kin taɓa samun ƙarin jini (Blood transfusion)?"

"A'a."

"Akwai wani a danginku da ya taɓa fama da ciwon hanta?"

Tambayar ta sa Fukhee yin shiru.

Ta haɗe hannayenta cikin juna.

Muryarta ta yi ƙasa sosai.

"Mahaifiyata..."

M.d ya juya ya kalle ta. Wannan shi ne karo na farko da ta taɓa ambatar hakan a gabansa.

Likitan ya ɗaga kai daga rubutun da yake yi.

"Mahaifiyarki ta rasu ne saboda matsalar hanta?"

Fukhee ta gyada kai a hankali.

Likitan bai ƙara tambaya ba. Ya rubuta wannan bayanin, domin ya san tarihin iyali na iya taimakawa wajen gano musabbabin wasu cututtuka.

Ya miƙe daga kujerarsa.

"To, yanzu zan duba ki."

Ya fara auna zafin jikinta, bugun zuciya da hawan jininta. Daga nan ya matsa kusa da ita ya duba idanunta da harshenta, sannan ya latsa cikinta a hankali.

Da ya kai hannunsa gefen dama na saman cikinta, Fukhee ta ɗan saki ƙara.

"Ahh..."

Nan take ya janye hannunsa.

"Yi haƙuri."

Ya koma ya zauna yana haɗa bayanan da ya samu a zuciyarsa.

Akwai abubuwa da dama da za su iya haifar da irin waɗannan alamomi. Ba zai yi gaggawar yanke hukunci ba kafin ya ga sakamakon gwaje-gwaje.

Ya ɗago ya kalli M.d da Fukhee.

"Zan rubuta wasu gwaje-gwaje. Da zarar sakamakonsu ya fito, za mu fi fahimtar inda matsalar take."

M.d ya gyara zamansa.

"Wane irin gwaje-gwaje ne, Doctor?"

Likitan ya fara rubutawa.

"Za mu yi gwajin jini domin mu duba yadda hanta da ƙoda ke aiki. Za mu kuma yi gwajin Hepatitis, sannan a yi mata Ultrasound na cikinta."

Ya ɗan yi shiru kafin ya ƙara da cewa,

"Ba na son ku firgita. Akwai cututtuka da dama da kan haifar da irin waɗannan alamomi. Saboda haka ba zan iya cewa ga abin da yake damunta ba sai mun ga sakamakon gwajin."

M.d ya gyada kai cikin girmamawa.

"Mun gode, Doctor."

Likitan ya miƙa musu takardar gwaje-gwajen.

"Da zarar kun gama, ku dawo da sakamakon. Daga nan za mu san mataki na gaba."

M.d ya karɓi takardar gwaje-gwajen daga hannun likitan, ya yi masa godiya, sannan ya taimaka wa Fukhee ta miƙe daga kujerar da take zaune.

Da suka fito daga ofishin, nurse ɗin da ta shigo da su tun farko ta yi musu maraba da murmushi.

"Please, follow me."

Suka bi bayanta zuwa sashen da ake ɗaukar jini domin gwaje-gwaje.

Fukhee ta tsaya a bakin ƙofar tana kallon alluran da ke jere a cikin wata ƙaramin tire. Kafin ta ankara, sai ta kama hannun M.d da ƙarfi.

Ya sauke idanunsa kan hannun nata, sannan ya yi murmushi.

"Har yanzu kina tsoron allura kenan?"

Ta turo baki gaba kamar ƙaramar yarinya.

"Ba na son ta."

"Am sorry dear,ki nutsu a yi miki insha Allah ba za tayi zafi ba,and idan aka gama mai kike so na samo miki?"

Sai da ta ɗan yi tunani,sannan tace "Za ka siya mini ice cream."

Ya ɗaga gira.

"Ice cream?"

"Eh."

"Duk da likita bai ce za ki ci ba?"

Ta haɗe fuska.

"To shikenan, kar ka saya."

Ya yi dariya.

"Na shiga uku. Ashe ana yi mini barazana ne."

Nurse ɗin ta yi murmushi tana kallonsu.

"You two are adorable."

Fukhee ta sunkuyar da kai cikin kunya, yayin da M.d ya amsa da murmushi.

---

Bayan ta zauna, nurse ta ɗaura mata abin matse hannu a sama.

Da ta hango allurar, Fukhee ta yi saurin lumshe ido.

M.d ya matsa kusa da ita.

"Kalle ni."

Ta girgiza kai.

"Kawai ka bari ta gama."

"A'a."

Ya miƙa mata hannunsa.

"Ki riƙe ni."

Ba tare da gardama ba, ta kama hannunsa da dukkan ƙarfinta.

Nurse ta ɗan yi dariya.

"Ready?"

Fukhee ta ƙara matse hannun M.d.

"Bismillah..." ya faɗa cikin sanyin murya.

Allurar ta shiga.

Fukhee ta ɗan kwaɓe fuska, amma ba ta motsa ba.

Bayan ƴan daƙiƙu kaɗan, nurse ta cire allurar.

"Finished."

Fukhee ta buɗe ido a hankali.

"Shi kenan?"

Nurse ta gyada kai.

"Shi kenan."

Ta sauke numfashi.

"Na yi tunanin za ta fi haka."

M.d ya kasa hana kansa dariya.

"Jaruma."

Ta harare shi.

"Kar ka raina ni."

---

Daga nan nurse ta raka su zuwa sashen da ake yin Ultrasound.

An nemi M.d ya tsaya a waje yayin da aka shigar da Fukhee ciki.

Da ƙofar ta rufe, sai karon farko tun shigowarsu asibitin, M.d ya ji kamar zuciyarsa ta yi nauyi.

Ya zauna a kan kujerar da ke bakin ƙofar.

Takardar gwaje-gwajen tana hannunsa, amma bai san sau nawa ya buɗe ya sake rufe ta ba ba tare da ya karanta komai ba.

Lokaci ya fara tafiya a hankali.

Kowane minti yana masa kamar awa guda.

Ya ɗaga kansa yana kallon ƙofar ɗakin Ultrasound.

Shiru.

Sai ƙarar na'urar sanyaya iska kaɗai ake ji.

Ya lumshe ido.

"Ya Allah..." ya furta a cikin zuciyarsa.

"Idan akwai wani ciwo, Ka ba ni ikon ɗaukarsa. Amma kada Ka sa ta sha wahala."

---

A cikin ɗakin Ultrasound kuwa...

Fukhee tana kwance a kan gadon dubawa.

Likitar da ke gudanar da gwajin ta shafa gel mai sanyi a saman cikinta.

"Zai ɗan yi sanyi," ta faɗa cikin kulawa.

Fukhee ta gyada kai.

Na'urar ta fara yawo a hankali a saman cikinta.

Likitar ta mayar da hankalinta gaba ɗaya kan allon na'urar.

Da farko fuskarta a sake take.

Sai dai bayan wasu daƙiƙu...

Murmushinta ya ɓace.

Ta ƙara matsowa kusa da allon.

Ta sake juyar da na'urar zuwa wani ɓangaren.

Ta yi shiru.

Fukhee ta lura da canjin fuskarta.

Ta haɗiye yawu.

"Doctor..."

Likitar ba ta amsa ba.

Sai ta ci gaba da duba allon cikin nutsuwa, tana ɗaukar wasu hotuna.

Zuciyar Fukhee ta fara bugawa da sauri.

"Doctor..."

Ta sake kira, wannan karon muryarta cike da fargaba.

Likitar ta ɗago kanta, ta yi mata murmushi mai laushi.

"Ki kwantar da hankalinki."

"Komai lafiya ne?"

Likitar ta ɗan yi shiru na ɗan lokaci kafin ta ce,

"Likitan da ya aiko ki shi ne zai yi bayanin sakamakon. Ni aikina shi ne in gudanar da gwajin."

Ta faɗi hakan cikin girmamawa, amma zuciyar Fukhee ta kasa samun natsuwa.

Ta fahimci akwai wani abu da likitar ta gani...

Sai dai ba ta da ikon faɗa mata.

A hankali ta lumshe idanunta.

A karon farko tun da suka iso asibitin...

Tsoro ya fara samun guri a cikin zuciyarta.

Want the next chapter?

ui.create_a_free_arewapen_account_to_save_progress_unlock_paid_chapters_fol