Free chapter · Read without an account
9-10
*KINCI DUBU.....*
*Oum Hairan*
*page 9-10*
Yanayin wasannin da yake da ita yasa ta bashi haɗin kai duk da cewa zuciyarta babu daɗi tayi bakin kokarinta na ganin bata tauyeshi ba shima ya samu yanda yake so sannan ya ƙyaleta ta tashi ta shiga bathroom ta tsarkake Jikinta tana fitowa Wayarsa ta fara Ring suka kai dubansu tare “My Atika" taga an rubuta wani bsƙin ciki ya tokare mata maƙogwaro ta dai maze ta ɗauki kayanta ta fice daga dakin tana kallon yanda yake kallon wayar, tana fita ya daga cikin Sauri tace da Atika Kinsan sai yanzu ina gida ko?" cikin Muryar kissa tace “Amma kaima saboda kana gida sai ka manta Dani kamar ba me shirin zama Matarka ba" iska yd furzar yace “Banason shiga lokacin me lokaci ne kin sani Jiddah tana da hakuri da kawaici to bai ka mata a daketa kuma a Hanata kuka ba kuma ma banda rigima irin taki naga ba kirana kike ba saidai na kiraki to yau wani sabon salo ne ya tashi?" sosai Atika take jin haushin Jiddah da irin yabon da IB yake yi mata shi kullum bashi da magana sai Jiddah kaza Jiddah kaza yasan matarsa ta cika goma Meyasa ya taho neman aure? ƙit ta kashe Wayarta yabi wayar da kallo yana Murmushi ya tashi ya shiga bayi shima yayi wanka ya shirya ya fito bai tadda Jiddah a parlour ba ganin ƙofar parlourn a buɗe yasan tana waje ya fita kai tsaye Gonar kifinta ya nufa tana tsaye tana zubawa kifayenta abinci ya tsaya a bayanta yace “Ba gayyata?" ɗagowa tayi ta kallesa da Idsnunta dake shigar dashi nutsuwarsa ya ɗan janye don kallon nata babu rahama a cikinsa.
Karɓar robar abincin kifin yayi yace “Inason zanje na gaida su Abba munyi waya dashi yace yana gari" ba tare da ta ɗago ta kalleshi ba tace “Allah ya tsare" yanda tayi masa maganar a gwasale duk sai yaji babu daɗi har ya juya zai tafi yaji bazai iya ba ya dawo yace “Tun Jiya kike banzatar dani Jiddah na rasa ne Kikeso nace Miki ki yarda Dani" juyowa tayi ta kalleshi sosai tayi wani gajeren Murmushi tace “Na zaci ka gams faɗar abinda zaka faɗa ne Shiyasa na maida hankalina kan abinda yafi min muhimmaci" da sauri ya kalleta yace “Kiwon kifin tafini muhimmanci?" Lumshe Idsnunta tayi tace “Kamar hakanne Ibrahim, idan na gaza kula dakai a baya da har yasa kakejin na cancanci abinda ka faɗamin Jiya saboda yara biyu kacal bayan Ni Nasan ina cikin matan da Allah bazai kamasu da tauye haƙƙin miji ba, to Meye yayi saura banda na maida hankalina wajen kula da dukiyata maimakon kula dakai tunda kai Allah ya azurtaka da samo wacce zata baka lokaci yanda kake buƙata".........
_Kar sunan labarin ya firgita ku Amare Kuzo ayi daku zaku ƙaru domin wataran kune iyayen gidan_
*💃🏼
*For more Info....*
*****
@all
*OUM HAIRAN*