Free chapter · Read without an account
MATAR GIDA PAGE 71
by Maimuna Bala · MATAR GIDA
MATAR GIDA BOOK 2
SHUUKRAN/022
YOTA ASSOCIATION
P71
Da dare misalin ƙarfe takwas likita ya shiga ya duba Unaisa bayan ya gama duba ta ne ya mayar da dubansa gareta ya ce ''kin fara antinatal?" Unaisa ta basa amsa ta ce ''a'a ban fara ba'' gyara tsayuwar sa ya yi kafin ya ce ''wata nawa ne ciki'' a hankali Unaisa ta ce ''four month'' daga haka ya gyada kai alamar gamsuwa da zancenta ''in babu damuwa zamu yi maki rijistar a nan sai ki fara zuwa daga wata me zuwa'' Unaisa ta ce ''babu damuwa na amince'' yan rubuce rubuce likita ya yi cikin wata ƙaranar paper bayan ya gama rubuta abinda zai rubuta ya miƙawa Amirah takardar ya ce ''a siya mata wannan maganin anti biotic ne zai taimaka mata da abinda ke cikin ta'' karaɓar takardar Amirah ta yi tare da faɗin to,bayan fitar likita ne nurse ta shiga ta sawa Unaisa drip,bayan fitar nurse Amirah ta fita zuwa phamercy dake asibiti ta siyawa Unaisa magani cikin kuɗaɗen da Ɗalha ya turo mata ɗazu,washegari karfe goma Unaisa ce zaune kan gado tana cin chips daga gefenta kuma Amirah ce tana vidoe call da Husnah,Amirah na dariya ta ce ''lallai ki ce ba irin namu bane anko dubu hamsin a lallai sai ku manya'' ɗaya bangaren Husnah ta ɗaga atamfa ta nunawa Amirah ta ce ''wannan 25k babu tsada,atamfa ta uni less na kamu'' dariya kawai Amirah ta yi ta ce ''in zai siya mana duka biyu 150k kenan banda kuɗin ɗinki da mayafi tabb wallahi ban ce zai yarda ba amma zan masa Allah ya daura mu bisa ka sa''Husnah ta yi dariya kafin ta ce ''ameen'' daga haka ta daura da ''ya naga kamar kina hospital ba ki da lafiya ne?" ko ciki gareki dan ki kam ba kya gajiya da haihuwa''sai da Amirah ta kalle Unaisa kafin ta ce ''Unaisa ce ba lafiya tun jiya muke asibiti'' taɓe baki Husnah ta yi kafin ta ce ''Allah ya bata lafiya,ciki ne da ita?uhmm ikon Allah rabbi ya bata lafiya ki gaishita'' yunƙurawa Amirah ta yi tare da miƙewa tsaye ta nufi gadon da Unaisa ke zaune tare da faɗin ''bara na bata sai ki gaishita'' da sauri Husnah ta ce ''a'a ba sai kin bata waya ba ki gaishi ta kawai'' Amirah ta yi kamar bata ji abinda Husnah ta faɗa ba ta je har inda Unaisa take ta miƙa mata waya,jikin Unaisa ya yi sanyi jin abinda Husnah ta faɗa,jiki sanyaye Unaisa ta sa hannu ta karɓi waya fuskar Husnah babu yabo babu fallasa ta gaida Unaisa ta yi mata ya jiki Unaisa ta amsa da alhamdulllah ganin irin kallon rainin hankali da Husnah ke mata yasa ta mikawa Amirah wayar da sauri Amirah ta sa hannu ta karɓi waya ''kin san Allah shekaran jiya mun yi waya da Nailah amma bata faɗa min an fitar da anko ba'' cewar Amirah Husnah ta yi dariya ta ce ''aiy mutumiyar take sai a hankali kun fi kusa'' ta kare magana tana dariya ita ma Amirah dariya ta yi ta ce ''da mun gama waya da ke zan kirata'' daga haka sun ɗan taɓa hira kafin daga bisani suka yi sallama,bayan Amirah ta gama waya da Husnah ne ta kira Nailah bugu ɗaya Nailah ta ɗaga kiran nan Amirah ta shiga tsokananta sosai Amirah ke wasa da Nailah,Nailah ƴar kawo Abubakar ce ƙanin Dady (mahaifin Ɗalha) mahaifinta Abubakar ya kasance kanin Dady su biyu rak iyayensu suka haifa tun sanda ya kammala karatunsa na Sakandire ya samu scholarship ƙasar Maroco bayan ya gama deegree ya yi zaman sa a ƙasar har ya samu aiki,bayan ya samu aiki ne Allah ya haɗa sa da matarsa wacce ƴar kasar ce mai suna Nazaaha bayan auren su Allah ya albarkaci su da haihuwar Nailah,bayan haihuwar Nailah mahaifiyarta ta ce baza ta sake haihuwa ba,kawo Abubakar ya goye bayan hakan,a can ta taso ta yi karatunta da komai yanzu haka wanda zata aura ɗan kasan Maroco ne daga dangin mahaifiyarta da fari Nazaaha ta ce a can kasan Maroco za a yi shagalin biki baki ɗaya amma Dady ya ce sam bai yarda ba wannan dalilin yasa za a daura aure a Nigeria da bikin kamun amarya, sauran shagulgula biki mahaifarta zata yi a can ƙasar Maroco Amirah da Nailah sun dauki a ƙallah mintina ashirin suna waya daga bisani Amirah ta faɗa wa Nailah Unaisa ba lafiya yanzu haka suna asibiti ɗan jim Nailah ta yi kafin ta ce ''ki gaishita'' tana shirin kashe waya Amirah ta ce ''tare muke ga ta nan ku gaisa'' Amirah ta faɗa tana da miƙewa Unaisa waya,Unaisa dake kwance ta miƙa hannu ta ƙarɓi wayar ta kafe Nailah da ido sai wani cin magani take kamar wacce aka yiwa dole haka ta gaida Unaisa,Unaisa dake fama da kanta bata bi ta kan Nailah ba ta miƙawa Amirah waya tare da gyara kwanciya tana rufe ido cikin zuciyarta tana faɗin baza ta sake karɓar waya ta yi magana da wata ko wani ba abinda ta fahimta shine kusan gaba ɗaya ƴan uwan Ɗalha suna kaunar Amirah ta kuma fahimci Amirah ta gama kama ƴan uwan Ɗalha ta kuma iya zama da su a iya fahimtar Unaisa yan uwan Ɗalha sun mayar da ita ɗaya daga cikin su kamar ƴar uwarsu haka suke hulɗa da ita,ta kuma fahimci son da ƴan uwan Ɗalha kewa Amirah ya sa basu sonta a fahimtarta suna ta ya Amirah kishi ne,ita kuma Amirah gaba ɗaya babu kishi gabanta rayuwarta kawai take babu ruwan ta da kowa fatanta ta zauna da kowa lafiya,wata doguwar ajiyar zuciya Unaisa ta sauke cikin zuciyarta ta ce insha Allahu nima zaku soni kamar yadda kuke son Amirah,ba zan taɓa gajiya ba da yardar Allah Ɗalha zai huce da na gama da Ɗalha zan dawo kan ku kamar yadda kuka karɓi Amirah nima zaku ƙarɓi ni
Kwanakin Unaisa huɗu a asibiti a ka sallame ta sosai ta samu lafiya,a kwanakin huɗu da tayi a asibiti kusan kullum Anty Aisha na zuwa dubanta Mama dai sau biyu ta zo,ko sau ɗaya Ɗalha bai zo asibiti ya duba Unaisa ba sai dai duk abinda suke buƙata yana aika masu,duk sanda Amirah ta masa magana zuwa asibiti sai ya kawo mata uzurin aiyuka sun masa yawa a ofis,sosai Aina'u ta yi ƙokarin wajen kula da yara cikin kwanakin huɗu da Amirah ta yi a asibiti,ita ma Unaisa bata ji dadin abinda Ɗalha ya mata ba musamman in ta tuna irin ciwon da ta yi,duk sanda ta zauna ita kadai sai ta yi ta tunani gani take kamar baza ta iya cigaba da zama da Ɗalha ba,wani sa'ilin kuma sai ta ce laifin ta ne ita ta janyuwa kanta komai,can ƙarƙashin zuciyarta ta fara tunanin neman saki daga wajen Ɗalha gani take hakan zai fiye mata sauƙi,ta sawa zuciyarta da ta koma gida zata je gidan Mama ta yiwa Mama bayanin komai zata fadawa Mama yadda zaman ta Ɗalha ya koma sannan zata nemi shawarar Mama kafin ta nime saki,duba da irin rashin lafiyar da ta yi a iya fahimtar Unaisa ko babu aure tsakaninta da Ɗalha ko bai santa ba,ko da ita ba musulma ba ce bai dace ya barta a halin ciwo ya nuna mata halin ko in kula ba,bari ita matarsa ta sunnah ga kuma cikinsa jikinta,wannan tunanin yasa take jin lallai baza ta iya zama da shi ba,Anty Aisha ce da Unaisa daga gefensu kuma Amirah ce waya kare kunnenta,da Ɗalha take waya tun kafin azahar ta kirasa ta ce masa an sallame su amma bai zo ba yanzu karfe uku,kallo ɗaya zaka yiwa Amirah ka fahimci ranta a ɓaci yake bayan ta gama wayar ne ta mayar da dubanta ga Anty Aisha ta ce ''ba zai samu damar zuwa ba aike ya riƙe shi bara na fita na samo mana adaidaita'' daga haka ta fita reception ɗin,a kwanaki hudu da Anty Aisha ke zuwa asibiti wajen Unaisa ta fahimci kamar da akwai matsala tsakanin Unaisa da Ɗalha amma ko sau ɗaya bata taɓa tambayar Unaisa ba,bayan komawarsu gida su Sudais sun shiga murnar ganin Amirah har da Unaisa sosai yara sun yi farin ciki dawowar mahaifiyarsu Anty Aisha da Unaisa suka wuce ɓanagaren Unaisa, bayan shigar su bangaren ko ina tsaf kasancewar kusan kullum Aina'un tana gyara ɓangaren,ɗaki Unaisa ta wuce Anty Aisha na biye ita bayan shigarsu kwanciya ta yi kan gado tana mayar da numfashi tafiyar da ta yi daga gate zuwa ɓangarenta ta ji ta gaji sosai,kayayyakin da suka dawo da su daga asibiti Anty Aisha ta gyara masu zama,zaune take cikin ɗakin Unaisa yayin da Unaisa na kwance tana tunani Anty Aisha ta kafe Unaisa da ido tana tuna abubuwan da suka faru a asibiti ko ba a faɗa ba tabbas da akwai abinda ke faruwa tsakanin Ɗalha da Unaisa tana son tambayar Unaisa amma sai taga rashi dacewar hakan,har da Unaisa ta samu sauki sai taga bai dace ta yi mata tambayar yanzu ba hakan yasa bata cewa Unaisa komai,ba ita ta bar gidan ba sai da ta yi sallar magrib,karfe takwas na dare Unaisa ce zaune cikin ɗaki tana shan magunguna da aka bata a asibiti,bayan ta gama sha ne ta hau gado ta kwanta shiru,tana nan kwance Ɗalha ya shigo ɗakin bakinsa dauke da sallama bata amsa sallamarsa ba ta kafe sa da ido,yana tsaye daga wajen kofa ya ce ''har kun dawo?" a hankali Unaisa ta ce ''eh'' ''to ya jikin?" ya tambaye Unaisa a takaice ta basa amsa ta ce ''da sauƙi alhamdulillah'' ya ce ''masha Allah Allah ya ƙara lafiya'' ta amsa da ameen daga haka ya fita tare da ja mata kofa,da ido Unaisa ta bisa bayan fitarsa ya taɓe baki,wayarta ta dauko tare da kunna data ta shiga whatsapp,group ɗin matan gida taga an tura saƙo cewar jibi akwai taro gidan wata ƴar kungiya an faɗa sunanta tare da address ɗin gidanta duk an tura cikin group,taging message Unaisa ta yi inda ta rubuta baza ta samo damar tafiya taron ba dalili bata da lafiya kwanaki huɗu ta yi a asibiti,ta kuma rubuta a bata account number na wacce za a yi taro a gidanta sai ta tura mata kuɗi daga haka ta tura saƙon,bayan ta tura Hajiya Bilƙisu ta bata amsa inda ta ce _ba za ki samu damar zuwa ba ko mijinki ya hanaki zuwa?_ Unaisa ta karanta maganar Hajiya amma ba ta yi replying ba,bayan wasu ƴan sakanni wata ta rubuta _Unaisa yaushi ki ka fara bautar miji?_ nan ma Unaisa bata yi reply ba,wata ta sake rubuta _ikon Allah ashe a cikinmu akwai masu jin tsoron mazajensu_ Unaisa bata amsa ba Unaisa tana shirin fita daga group wata ta rubuta _yanzu yadda muke ƙwatarwa kanmu ƴanci wajen mazajenmu miji bai isa ya juya mu ba bai isa yasa mu yi ba, ke da muke kallon kin waye kin san abinda ki ke ki ce za ki tsaya miji ya tanƙwasaki a lallai kin bani kunya ina mijin ne wanda ki ke gayawa bakar magana iya son ranki shine yau ya hanaki fita kuma kika yarda a lallai kina da abinda mamaki na samu labarin kin dawo da mota wai ni kam Unaisa kin tabbata za ki iya zama cikin mu? sai nake ganin ki fita daga kungiyar kawai dan hakan zai fi maki sauki_ ganin message ɗin yan kungiya zai ɗaga mata hankali kawai ta kashe data daga haka ta tashi ta shiga bathroom ta yi wanka ta wanke baki,bayan fitarta daga bathroom ta shirya kanta cikin nigthwear daga haka ta kashe wutar ɗakin ta kwanta tare da rufe jikinta da bargo
SHUUKRAN