Free chapter · Read without an account

seven cities one secret

by NasirBoss · SEVEN CITIES ONE SECRETHausa Novel Romance Mystery Suspense Adventure Secret Betrayal Danger International Romance Family Secret

CHAPTER THREE & FOUR

Cikin ginin akwai wani irin shiru da ya sa Amara ta ji kamar lokaci ya tsaya. Takan ji karar takalmanta ne kawai yayin da take tafiya a hankali cikin dogon corridor ɗin. Bangon ya kasance cike da tsofaffin hotuna da zanuka wadanda suka yi duhu saboda shekaru. Wasu daga cikin gilasan da ke kan tagogin sun fashe amma iska mai sanyi tana shiga cikin ginin tana motsa tsoffin labule.

Amara ta riƙe jakarta sosai. Hoton da ta zo da shi tana cikin hannunta kuma duk lokacin da ta sake kallonsa sai wani abu a zuciyarta ya ƙara gaya mata cewa ba ta zo wannan wurin ne saboda aikinta kawai ba.

Akwai wani abu da yake jiran ta a nan.

Ta tsaya kusa da wani tsohon hoto da aka rataye a bango. Hoton ya nuna wasu mutane da ba ta san su ba suna tsaye a gaban wannan gidan shekaru da yawa da suka wuce. Ta duba fuskokinsu ɗaya bayan ɗaya amma babu wacce ta saba da ita.

Sai dai wata mace da ke gefen hoton.

Amara ta matsa kusa.

Fuskar matar ba ta fito sosai ba saboda tsohon hoton ne amma akwai wani abu a jikinta da ya sa Amara ta ji wani irin ciwo a kirjinta.

Ta taɓa hoton da yatsanta sannan ta janye hannunta.

“Me ya sa nake jin kamar na san wannan wuri?”

Ta tambayi kanta amma babu wanda ya amsa.

Ta ci gaba da tafiya.

Kafin ta zo Istanbul wani tsoho ne ya aika mata da hoton da ke hannunta. Ba ta taɓa ganinsa ba kafin wannan rana amma ya san abubuwan da Amara kanta ba ta sani ba. Ya gaya mata cewa idan tana son gano gaskiyar rayuwarta ta je wannan ginin.

Amma ya kuma gaya mata abu guda wanda ya sa ta yi tunani tun lokacin da ta bar otal

“Kada ki je wurin ke kaɗai.”

Amara ba ta saurare shi ba.

Ba don ba ta ji tsoro ba ne. A gaskiya tun lokacin da ta fara neman tarihin rayuwarta akwai abubuwa da yawa da suka faru da suka kamata su sa ta daina. Amma duk lokacin da ta yi ƙoƙarin komawa baya sai mafarkinta ya dawo.

Mafarki ɗaya ne.

Duhu.

Wani mutum yana tsaye a gabanta.

A hannunsa akwai ƙaramin akwatin ƙarfe.

Fuskarsa ba ta bayyana.

Sai ya miƙa mata akwatin yana cewa

“Ki nemo bakwai.”

A wasu lokuta Amara tana farkawa cikin dare tana zufa. A wasu lokutan kuma tana tashi tana jin kamar muryar mutumin tana nan kusa da ita.

Ta yi ƙoƙarin tambayar mahaifiyarta game da mafarkin amma mahaifiyarta ba ta taɓa ba ta amsa mai ma'ana ba. A duk lokacin da ta ambaci wannan mafarkin sai fuskar mahaifiyarta ta canza.

Kamar tana tsoron wani abu.

Amara ta kalli hannunta sannan ta ɗaga gashin kanta kaɗan. A gefen wuyanta akwai ƙaramar alamar 7.

An haife ta da wannan alamar.

Aƙalla haka aka gaya mata.

Ba ta san dalilin da ya sa take da ita ba.

Ta sake kallon bangon.

Sai wani abu ya ja hankalinta.

Wani tsohon zanen da ke rataye shi kaɗai.

Ta matsa kusa da shi.

Zanen yana nuna wani tsohon gida mai kama da wannan ginin. A ƙarƙashin hoton akwai rubutu wanda kusan ya goge. Amara ta share ƙurar da ke kansa da yatsanta.

Babu abin da ta fahimta.

Ta kama gefen zanen tana shirin komawa sai ta ji wani ɗan ƙaramin sauti.

Ta tsaya.

Ta sake taɓa wurin.

A wannan karon ta fahimci cewa akwai wani abu a bayan zanen.

Ta sauke shi daga bango a hankali.

A bayan zanen akwai wata alama.

7.

Zuciyarta ta buga da ƙarfi.

Ta kalli alamar sannan ta kalli wuyanta.

“Ba zai yiwu ba.”

Ta kusan janye hannu amma sai wani tunani ya zo mata.

Ta danna alamar.

Sai wani ƙaramin sauti ya fito daga bangon.

Amara ta ja baya.

Wani ɓangare na bangon ya motsa a hankali.

A bayansa akwai wani ƙaramin wuri mai duhu.

Ta kunna flashlight ɗin wayarta sannan ta haska ciki.

Akwai ƙaramin akwatin ƙarfe.

Amara ta kasa motsi na wasu seconds.

Akwatin ya yi kama da wanda take gani a mafarkinta.

Ta ɗauke shi a hankali.

Yana da nauyi fiye da yadda ta zata.

Ta zauna a ƙasa sannan ta ajiye akwatin a gabanta. Hannunta yana rawa lokacin da ta fara neman yadda za ta buɗe shi.

Babu makulli.

Sai dai akwai wata alama a saman akwatin.

Da'ira ce mai zagaye da wasu siffofi bakwai da suke kama da maɓallai. A tsakiyar da'irar akwai ƙaramin ido.

Amara ta dinga kallon alamar.

Wani irin sanyi ya ratsa jikinta.

Ta san wannan alamar ba ta taɓa ganinta ba.

Amma zuciyarta tana jin kamar ta san ta.

Ta buɗe akwatin.

A ciki akwai wani ƙaramin takarda da aka nade da baƙin zare. Akwai kuma wata tsohuwar hoto.

Ta fara ɗaukar hoton.

Da zarar idanunta suka sauka a kan matar da ke cikin hoton sai jikinta ya yi sanyi.

Mahaifiyarta ce.

Matar tana zaune tana riƙe da jariri a hannunta.

Amara ta kasa magana.

Ta kalli jaririn.

Sai ta sake kallon mahaifiyarta.

Ta san wannan hoton bai kamata ya kasance a cikin wannan ginin ba.

Ba wai kawai saboda mahaifiyarta tana cikin hoton ba.

Sai saboda hoton ya kasance kamar an ɓoye shi ne saboda wani dalili.

Ta juya hoton.

A bayansa akwai wasu kalmomi.

SEVEN CITIES. ONE SECRET.

Amara ta karanta su sau biyu.

Sai ta ga wani ƙaramin rubutu a ƙasan hoton.

Rubutun ya yi ƙanƙanta sosai amma ta iya karantawa.

Ba kowane sirri ne ake binne shi domin a manta da shi ba. Wasu ana binne su ne domin kada wanda ya same su.

Ta ji wani irin tsoro.

Ta kalli ƙofar ɗakin.

Shiru.

Sai ta ji wani sauti daga corridor.

Ta yi saurin kashe flashlight ɗin.

Ta zauna cikin duhu tana sauraro.

Takun mutum.

Ɗaya.

Biyu.

Sai shiru.

Amara ta riƙe numfashinta.

Takun ya sake dawowa.

Wani mutum yana tafiya a wajen ɗakin.

Ta matso kusa da bango tana ƙoƙarin kada ta motsa.

Bayan wasu seconds sai takun ya yi nisa.

Ta sake kunna wayarta.

A wannan lokacin wayarta ta fara ringing.

Lambar ba ta cikin wayarta.

Ta kalli screen ɗin na wasu seconds.

Sai ta ɗaga.

“Hello?”

Shiru.

“Waye?”

Sai wata murya ta fito a hankali.

“Kin samu akwatin.”

Amara ta tsaya.

“Waye kai?”

“Ba wannan ne abin da ya kamata ki tambaya ba.”

“Me kake so?”

“Ki bar wurin.”

Amara ta ƙara riƙe akwatin.

“Me ya sa?”

“Saboda idan kika tsaya a Istanbul har zuwa ƙarfe goma sha biyu za su same ki.”

Kiran ya yanke.

Amara ta kalli agogon da ke wayarta.

11:17.

Ta fara tattara kayanta.

Sai wani abu ya hana ta motsi.

Ta sake kallon hoton.

A wuyan mahaifiyarta akwai ƙaramin abu da ba ta taɓa lura da shi ba.

7.

Hannunta ya fara rawa.

Ta matso da hoton kusa da hasken wayarta.

“Me ya sa?”

Ta juya hoton.

A wannan karon ta lura cewa akwai wani rubutu da ke bayan hoton wanda ya ɓoye a ƙarƙashin tsohon tabon ruwa.

Ta share wurin a hankali.

Kalmomi suka bayyana.

KAEL YA SAN GASKIYAR.

Amara ta karanta sunan sau ɗaya.

Kael.

Ta sake karantawa.

Kael.

Wannan shi ne karo na farko da ta ga wannan sunan.

Ba ta san shi ba.

Ba ta san inda yake ba.

Amma wani abu a cikin zuciyarta ya gaya mata cewa mutumin nan yana da alaƙa da duk abin da take nema.

Ta saka hoton da akwatin cikin jakarta.

Da ta tashi sai ta ji ƙarar ƙofar ginin.

An buɗe ƙofar ƙasa.

Wani ya shigo.

Amara ta kashe wayarta.

Ta tsaya cikin duhu tana sauraro.

Muryar wani mutum ta fito daga ƙasa.

“Ta shiga ciki.”

Wani ya amsa

“Ku duba kowane ɗaki.”

Amara ta lumshe idanunta.

Sun zo.

Ba ta san su waye ba amma ta san ba mutanen kirki ba ne.

Ta kalli wata ƙaramar ƙofa da ke gefen ɗakin. Ta buɗe ta a hankali ta shiga wani ƙaramin corridor da ke bayan bangon.

Ta rufe ƙofar.

Mutanen sun fara hawa matakala.

Amara ta fara tafiya cikin duhu tana ƙoƙarin kada takalmanta su yi sauti.

Ta isa wani ƙaramin taga wanda yake kallon bayan ginin.

Tsayin yana da yawa.

Amma ba ta da wani zaɓi.

Ta buɗe taga.

Kafin ta fita sai ta ji murya a bayan ƙofar.

“Duba wannan ɗakin.”

Ta sauka daga taga ta riƙe gefen bangon.

A wannan lokacin wata mota ta tsaya a gefen titi.

Ba ta san ko wanene ke cikinta ba.

Amma a cikin motar wani mutum yana kallon ginin.

Kael Rahman.

Ya zauna cikin nutsuwa yana kallon hasken taga.

Mutumin da ke kusa da shi ya ce

“Mun same ta.”

Kael bai amsa ba.

Ya kalli hoton Amara da yake hannunsa.

Sai ya ce a hankali

“Kada ku taɓa ta.”

“Amma idan ta gano—”

“Na ce kada ku taɓa ta.”

Muryarsa ta sa mutumin ya yi shiru.

Kael ya sake kallon ginin.

Ya san Amara ba ta san komai ba tukuna.

Ba ta san abin da alamar 7 take nufi ba.

Ba ta san dalilin da ya sa aka ɓoye asalin haihuwarta ba.

Ba ta san cewa hoton mahaifiyarta da ta samu yau zai kai ta zuwa wasu garuruwa shida ba.

Kuma mafi muhimmanci ba ta san cewa ita kanta tana cikin sirrin.

Amara kuwa tana tafiya cikin duhun titin Istanbul tana riƙe da jakarta.

Ta tsaya ta waiwaya.

Ginin ya tsaya a bayanta kamar babu abin da ya faru.

Sai dai yanzu ta san wani abu guda.

Rayuwarta ba ta kasance kamar yadda aka gaya mata ba.

Akwai mutane da suka san gaskiyarta.

Akwai mutane da suke tsoron ta gano ta.

Kuma akwai wani mutum mai suna Kael wanda aka rubuta sunansa a bayan hoton mahaifiyarta.

Ta ɗaga hannu ta taɓa alamar 7 da ke wuyanta.

A karo na farko a rayuwarta sai ta fara tunanin ko wannan alamar ba kawai alama ba ce.

Ko wata hanya ce.

Hanyar da za ta kai ta zuwa gaskiyar da aka ɓoye shekaru goma sha biyu.

Amma kafin ta isa ƙarshen titin sai wayarta ta sake yin ringing.

Lambar ba ta da suna.

Ta ɗaga.

A wannan karon muryar da ta ji ta sa zuciyarta ta tsaya.

“Amara Noor.”

Ta yi shiru.

“Kin fara neman bakwai.”

Sai muryar ta yi ɗan shiru kafin ta ce

“Amma ba ki san abin da zai faru idan kika same su duka ba.”

Kiran ya yanke.

Amara ta tsaya a tsakiyar titi.

A hannunta akwai akwatin ƙarfe.

A jikinta akwai alamar 7.

A zuciyarta kuma akwai tambaya guda ɗaya wadda ta fi dukkan tambayoyin da ta taɓa yi nauyi.

Su waye suka ɓoye gaskiyar haihuwarta kuma me ya sa suke tsoron ta gano ta?




miss Nasir ♥️✍️

Want the next chapter?

Create a free ArewaPen account to save progress, unlock paid chapters, follow this author, and keep reading across web and the Android app.