FreeArewaPen original
SEVEN CITIES ONE SECRETHausa Novel Romance Mystery Suspense Adventure Secret Betrayal Danger International Romance Family Secret
- 1views
- 3chapters
- 0audios
- words
- 0likes
Share:
The story
Synopsis
No synopsis yet.
About the author
❤️🔥LOVE LEET HEATE ❤️🔥 Sun hadu ne da ƙiyayya… amma ƙaddara ta zaɓi soyayya. Dana ba ta taɓa tunanin za ta iya ƙaunar mutumin da zuciyarta ta rantse za ta ƙi ba. Shi kuwa mahabub, mutum ne mai tsauri, girman kai da sirrin da bai taɓa bari kowa ya shiga cikinsa ba. Haduwars...
Sample · Seven cities one secret
CHAPTER ONE & TWO Daren Istanbul ya kasance cikin duhu da sanyi, ruwan sama yana saukowa a hankali yayin da wani mutum yake gudu a cikin tsohuwar unguwar da babu mutane sosai. A hannunsa akwai ƙaramin akwatin ƙarfe wanda yake riƙe da shi kamar abin da rayuwarsa ta dogara da shi.Ya dinga waiwayawa yana kallon bayansa. Mutanen da suke binsa suna ƙara matsowa kusa, amma bai tsaya ba. Ya shiga wani tsohon gida wanda ya yi kama da wanda aka daɗe ba a zauna a ciki ba. Da zarar ya shiga sai ya rufe ƙofar ya jingina da ita yana sauke numfashi.Ya san ba zai iya ɓoye akwatin na dogon lokaci ba. Ya ɗaga wani tsohon carpet da ke tsakiyar ɗakin sannan ya buɗe wani ɓangare na ƙasan ɗakin ya saka akwatin a ciki. Kafin ya rufe wurin sai ya buɗe akwatin na ɗan lokaci.A ciki akwai wata tsohuwar takarda da aka nade da baƙin zare da kuma ƙaramin ƙarfe mai siffar lamba 7.Ya kalli lambar na wasu seconds sannan ya rufe akwatin.Wata murya ta fito daga wajen ƙofar.“Ka san ba za ka iya ɓoye shi har abada ba.”Mutumin ya lumshe idanunsa. Tsoro ya bayyana a fuskarsa amma bai amsa ba sai ya ce a hankali“Ku same ta kafin su same ta.”A wannan lokacin ƙofar ta fara girgiza da ƙarfi. Ya koma baya yana kallon ta yayin da aka sake buga ƙofar har ta karye.Duhu ya mamaye gidan.Shekaru goma sha biyu bayan haka.Amara Noor ta tsaya a gaban wani tsohon gini a Istanbul tana riƙe da wata tsohuwar hoto a hannunta. Ginin ya kasance mai nisa da wuraren da masu yawon buɗe ido suke zuwa kuma ko da yake ba shi da wani abu mai ban mamaki a kallon farko Amara ta ji wani irin yanayi da ba ta iya bayyanawa.Ta zo Istanbul ne saboda aikinta. Aikinta ya shafi tsofaffin hotuna da bayanan tarihi kuma hoton da ke hannunta shi ne dalilin da ya kawo ta wannan wuri.Ta kalli hoton sannan ta kalli ginin.Wani abu a zuciyarta ya gaya mata cewa wannan ba bincike ne na yau da kullum ba.Tun tana ƙarama tana yawan yin mafarki iri ɗaya. Wani mutum yana tsaye a cikin duhu yana riƙe da akwatin ƙarfe sannan yana kallonta yana cewa mata kalmomi guda biyu“Ki nemo bakwai.”Amara ba ta taɓa fahimtar ma'anar hakan ba.Amma a wuyanta akwai wata ƙaramar alamar 7 wadda ta kasance tun tana ƙarama.Ta ɗaga kai tana kallon tsohon ginin sannan ta shiga.Ba ta san cewa amsar da ta dade tana nema tana nan a cikin wannan ginin ba.Kuma ba ta san cewa wani mutum mai suna Kael Rahman ya riga ya fara neman ta ba.CHAPTER TWOCikin ginin akwai wani irin shiru da ya sa Amara ta ji kamar lokaci ya tsaya. Ta riƙe jakar da ke kafadarta ta fara tafiya a hankali tana kallon tsoffin bango da hotunan da suka rage a ciki.Kafin ta zo wurin wani tsoho ne ya aika mata da hoton da ke hannunta. Ya gaya mata kada ta je wurin ita kaɗai amma Amara ba ta saurare shi ba. Ta yi imanin cewa abin da take nema yana da alaƙa da tarihin danginta kuma ba za ta bari ...
Contents
Table of contents
Preview every chapter, see what is free, and continue reading when you join ArewaPen.