Free chapter · Read without an account
18
by MARYAM STAR · ƊAURIN ZUCI
***
𝘿𝘼𝙐𝙍𝙄𝙉 𝙕𝙐𝘾𝙄🔐
𝘽𝙔
𝙈𝘼𝙍𝙔𝘼𝙈 𝙐𝙈𝘼𝙍
Chapter 17
"Huwaila na gamu da Aljanna yau wallahi, shikenan tawa ta ƙare na shiga uku na lalace na haɗu da makarina."
Sai da yaja wani dogon numfashi tare da fesarwa a ɗimauce ba tare da ya bata damar yin magana ba ya kuma cewa.
"Ta ganni kuma ta kalli fuskata ya zamar mana dole mu tattare kayanmu mu gudu Huwaila mu gudu mutafi can da nisa."
Ya faɗa kalamansa da muryarsa na tabbatar da yanayin kaɗuwar da yake ciki.
Dafe ƙirji da hannuwa bibiyu Huwaila ta yi tana zare duka girman idanuwanta bayyananen tashin hankali na zama akan fuskarta.
Ganin ta kasa magana ya saka Malam bangajeta ya nufi wajen drowar ya soma finciko kayan da ke ciki a haukace sai ƙyallin gumi ya ke ta cikin hasken kwan lantarkin daya haske ɗaki, cin karo da abin da yake nema ya yi da sauri ya ɗauka tare da saɓar wata jaka da ke rataye sannan ya dawo gaban Huwaika wacce ta ƙame a tsaye tana kallon shi ta kasa cewa komi.
Jan hannunta yayi da sassarfa ya fice daga gidan garin sauri har yana yada wani abu daya faɗo daga cikin aljihun shi ba tare da ya lura ba....
Washe gari.
Dandazon mutane ne musamman matasa tsaye cirko-cirko a ƙofar gidan Malam, wasu da addanu a hanayensu wasu gatari wasu wuƙaƙe, ga wata iriyar hayaniya dake tashi a wajen har baka iya jin asalin abin da ake faɗa.
Daga can ƙofar gida wata mata ce wacce ke sanye da zanin atamfa wanda a kallon farko zaka tabbatar da ba anutse ta yi ɗaurin ba, ga wata abaya data saka wuyan a jirge kamar tsohuwa, hawaye share-share take faɗin.
"Na rantse da imanin Allah ba zan yarda ba du inda yake du inda ya shiga dole a meno shi abi min haƙƙin ɗana da aka zalunta, na tabba Hadi ba zai faɗi ƙarya ba idan kuma kun musa to a shiga cikin gidan ayi bincike indai da saka hannunsa dole za'a gane."
Wani babban mutum da ke ƙoƙarin kwantar da hatsaniyar ne ya roƙi da jama'ar wajen suyi shiru su nutsu a bi komi a sannu, sannan ya matsa kusa da matar tare da kama yaron dake hannunta sannan ya ce.
"Nutsu da kyau Hadi daina kuka faɗamin abin da ke faruwa bani labari daga farko har ƙarshe."
Share hawaye yaron da aka kura da Hadi yayi cikin sheshekar kuka yace.
"To ba zaka bari a kashe Innata ba idan na faɗa kaga su Iro cuwa sun ce zasu kasheta wai tayiwa Malam ƙage."
Jinjina kai muyumin ya yi sannan ya ce.
"Indai ka faɗa min gaskiya babu wanda zai kashe Innarka amma idan kayi min ƙarya zan bar su Iro cuwa su kashe ku kai da ita."
Tun kafin ya dire aya yaron ya ce.
"Jiya da daddare Inna ta aike ni nida Sahabi gidan Inna Mairo mu amso mata ashana zata kunna wuta tayi mana ɗumame, shine muna hitowa mukagaa Malam ya kirawo mu yace mani wai mu bamujin tsoro muka hito cikin hudun mangariba, se nace mashi Inna ta aike mu wajen Inna Mairo kuma babu nisa zamu amso ashana ayi mamu ɗumamen tuwa.
Sai yace to ni inruga in amso inbar sahabi zai bashi wani abu.
Sena ruga da gudu amma ina zuwa na iske gidan kulle ashe bata nan ta tahi unguwa shina na sake rugowa ina karya kwana sai nayi tuntuɓe kuma se aka ɗauke wuta ina taka ƙahwata a hankali sai na ji kukan Sahabi sai kuma na daina jin kukan ina ƙara matsowa sai na hangi malam na saka wanj abu cikin kwalba ya haska da wayar hannun shi kuma naga jini, yana gamawa ya kashe hasken ya tada ƙurƙurar shi yabar wajen na isa inata lalube amma banga Sahabi ba shine naje na gayawa Inna muka taho tare muka ganshi ƙasa ita da Baba suka ɗauke shi aka tahi asibiti basu dawoba se yau."
Ya faɗi yana shehseka tare da kai duban shi kan ƙafar shi ta haggu yana kallon babbar yatsar shi kamar yanda shima mutumin yakr kallon yanda akaifar ta ɗaɗɗako.
Nan take hatsaniya ta sake tashi akashiga kace nace kowa na faɗar albarkacin bakin shi.
Wasa-wasa magana ta girmama doke sai da aka dangana da kiran police, bayan masu Unguwanni sun hallara nan aka tsaida magana akan za'a shiga cikin gidan Malam a duba ko yana nan dan tun da aka fara hatsaniyar bai leƙo ba.
Folisawa biyu da matasa biyu sai dattijai biyu ne aka wakilta akan su shiga bayan an rafka sallama babu amsa suka kutsa kai cikin gidan.....
Turus suka yi fuskokinsu na washewa da wani irin mamaki tsoro, gami da ɗimauta.
A kusa da wani ɗan ƙaramin abu me kama da ƙarfe wani tabkeke tambari ya bayyana jini na gudana a tsakiyar shi yayinda hayaƙi ke kewaye a saman shi yayinda wata kururuwa haɗi da maganganu da mabanbantan muryoyi da mabanbantan yaruka ke tashi a ciki.
Da baya-baya suka soma juyawa suna ficewa a kiɗime.
Bayan wani lokaci.
Tsaitsaye suke mazansu da matansu a babban filin da aka tara su don tattaunawa akan abin da ke faruwa, yayinda aka miƙa ragamar binciken a hanun hukuma bayan an rufe gidan Malam da kwaɗo kowa na ta'ajjabi akan abin da ya faru tsoro fal rayukansu musamman da suka bada gaskiya suka yi aamanna da shi amma daga baya ya cutar da su ya ha'incesu ya yaudare su, domin dai iya abin da aka gani a cikin gidan Malam ɗin ya isa ya tabbatar musu da ba ƙazafi aka yi mashi ba, sannan kuma barin gidan da yayi ba tare da kowa ya sani ba hakanma wata hujjarce.
A ranar Malam yasha tsinuwa da fatan bala'u a wajen mutanen unguwar Shinkafi, wasu masu karyayyar zuciya har da kukansu akan yaudarar da yayi musu.
******
GIDAN TSAFI.
Zaune ya ke akan kujerar shi ta tsafi, fuskar nan babu alamun fara'a bare sassauci, a kallo ɗaya zaka tabbatar da babu koda kwatankwacin ƙwayar zarra na ɗigon imani a tattarr da shi.
Malam ne da Huwaila ɗaɗɗaure a cikin sarƙa kamar wasu marasa galihu haka aka duƙar da su a gaban Makafa.
Ɗaga idanuwan shi Malam yayi waɗanda suka ture saboda tsabar azaba bakin shi na fitar da jini fuskar shi a kumbure ya ke faɗin.
"Ina barar afuwarka ya shugabana haƙiƙa na yi kuskure da ban tunkari ƙalubalena ba amma zan so ka bani damar da zan gyara kuskurena koda dama ɗaya ce tak ina meyin rantsuwa da kai da ƙarfin tsafin zancika aikina akanta."
Karkaɗa ƙafa kawai Mafaka ke yi yana watsa wutar tsafi da sandar hannun shi kamar maganganun da Malam ke yi basa shiga hudar kunnuwan shi.
Wani baƙin kallo Ƙwaro yayiwa Mafaka ta gefen ido yana raya wasu abubuwa a ƙasan ran shi amma a fili sai ya ɗaga sandar hannun shi ya soma warware tsafin da aka ɗaure Malam da shi sannan ya miƙe yana faɗin.
"Ka je ka tabbatar da ka cika aikinka sati ɗaya kawai kafin cikar lokacin bikin shekara, ita kuma matarka ka barta a nan."
Yana gama gaɗin hakan ya tashi ya juya tare da bin iskar wajen ya ɓace ɓat.
Ran Makafa ya sosu da abin da Ƙwaro ya yi yarasa dalilin da yasaka suke samun saɓani a wannan lokacin gashi abubuwa da dama sun caƙuɗe ma shi yana buƙatar tattaunasu da Ƙwaron domin sh nemo mafita sai a yanzu ya gane tabbas tafiyar shi ba zata tafi daidai ba sai da Ƙwaro a gefen shi kamar yanda suka saba,sai de kuma daya tuna da kallon nan kallon da ya tsaya ya tokare can tsakiyar kan shi wanda hakan ya bawa halittun da ke tare da shi damar addabar rayuwar shi, da ace ba Rimsha bace wata macence daban da zai bawa Ƙwaro ita ya ɗanɗana kamar yanda suka saba amma Rimsha ta fita daban a cikin matan daya sani shi kanshi badan cikar burin shi ba da babu abin da zaisa ya haɗa mata da tsafi saboda yanda ya ke tsananin jinta a ƙasan ransa.
Haka taron ya tashi babu armashi ya sallami kowa bayan an cike gaban table ɗin shi da sassan jikunnan mutane kamar yanda aka saba, ya ɗan jima a gidan Tsafin yana tunanuka barkatai kafin daga bisani bayan ya gana da dodo ya tafi domin cika sauran abubuwan da suka rage ma shi.
*****
"Sannu Kaka lallaɓa ka haɗiye in sha Allah zaka samu sauƙin wannan cutar da kaina na yofa maka ayatush shifa kuma ba normal ruwa bane harda ruwan zamzam na garwaya maka."
Tafaɗi tana ƙoƙarin tada shi zaune bayan ta saƙala hannunta ta bayan shi ta ɗan ɗaga kan shi kaɗan.
Wani yamusashen fari tas ɗin tsoho ne wanda cuta ta gama cinye garkuwar jikin shi shida tsumma basu da maraba, amma ga mamakina sai naji yana faɗin bayan ya shanye ruwan tofin da ta yi ma shi.
"Allah yayi maki albarka Allah yayi riƙo da hannayenki Allah ya baki nasara akan abin da kika saka a gaba, Allah ya nuna min lokacin cikar burunki kafin inbar duniyar nan."
Ya faɗa wasu ruwa masu kama da hawaye na gangaro daga idanuwan shi.
Nisawa ta yi damuwa na ƙoƙarin bayyana a kan kyakkyawar fara tas ɗin fuskarta amma ta hana hakan faruwa, ta danne damuwar da ƙarfin zuciyarta.
A hankali kuma cikin taushin murya ta ce.
"Kaka Ladan dan Allah yau ɗay, yau ɗaya ina so ka ƙara banj haske ko zan samu tsayayyar makama da zata sada ni da hanyar cikar burina."
Ta yi maganar muryarta cike da roƙo.
Sai da yayi tari na sakanni sannan ya nisa yana sakin numfashi sama-sama irin na wanda cuta ta gama cinye rayuwar shi sannan yace da muryar shi da ke rawa.
"Karki damu Maryama Allah yana tare da ke a dukkan komi kuma yana sane da ke da burinki shi zai taimaka maki ya kuma baki haske sannan yayi miki jagora, abin da nike so da ke karkiyi sake koda wane lokaci cikin ko wanne hali karki yi sake da addu'a da ibada, kici gaba kamar yanda nasan kina yi ki ɗore da ibada hakan kawai zai zama tsanin da zai haudake katangar nasara."
Sake riƙe hannun shi da yayi taushi luguf a cikin nata ta yi, cike da gasgata kanta ta ce.
"Na yi maka alƙawari Kaka kamar yanda ka raineni ka tarbiyantar da ni ba zan taɓa sauyawa ba du wuya du tsanani ba zan taɓa yin sake da addini da ibada ba."
Wani busashen murmushi ya saki yana kallon farar fuskarta cike da alfahari sannan ya jefa mata tambayar data saka ta kalleshi da alamun tuhuma akan fuskarta.
"Mi yasa baki da tsoro, mi yasa kika fiye nuna jarumtakarki a fili da ace ya cutar da ke fa?."
Sau uku tana buɗe baki amma sai ta gagara furta koda kalma hakan ya saka ta rufe manyan idanuwanta tare buɗe su ta kalli wani sashe daga ɗakin sannan ta ce .
"Ya aka yi ka sani, taya zakaga abin da ya faru a wajen gida bayan kai ɗin kana kwance kana jinya a nan?."
Ta jefa ma shi tambayar still bata kalli sashen da yake ba.
Shiru yayi bai ce komi ba sai ma sakin numfashi daya soma yi alamar barci, wanda hakan yasakata ta kalle shi tsananin tausayinsa na sake dabaibaye zuciyarta kaɗaici da maraici na lulluɓe ta gamu da tausayin rayuwar da suke ita da shi.
******
G.R.A
Daddy ne zaune akan gefen bed hannun shi riƙe da wata takarda wacce ke ɗauke da zanen wasu yara su biyu, suna kama sosai amma kuma akwai banbanci a kamanin nasu, babbar ba zata wuce ahekaru shida ba yayinda ƙaramar ba zata rufe uku ba, su dukansu fararene tas duda hoton yaɗan kwana biyu amma hakan bazai hana ka gane yanda ƙaramar tafi babbar haske ba domin kuwa ita fara ce sol irin hasken larabawa me shiga cikin ido.....✍🏻
MARYAM STAR