Free chapter · Read without an account

73

by Halima Zakariyya Haruna · LULLUƁIN BIRI

Fullo kanta gaba ɗaya ya ɗaure, ta kasa fahimtar komai. Tarin tambayoyi ne kawai suke ta cacar baki a cikin ƙwaƙwalwarta, ɗaya na biyo bayan ɗaya, amma babu amsar ko guda da take da ita.

Ina suka kai ni? Wanne gida ne wannan? Su waye waɗannan mutanen?

Can ƙwaƙwalwarta ta fara bata wani tunani mai ban tsoro.
Ko dai an siyar da ita?

Kenan Abbanta bai mutu ba? Dama basaja ya yi musu? Ya siyar da ita kamar yadda ta taɓa ji a tarihi ya siyar da wasu daga cikin ƴan uwanta?
Ta lumshe idanuwanta da ƙarfi, sannan ta sake buɗe su.

A'a!
Zuciyarta ta ambata da ƙarfi, tana girgiza kanta.
Ba zai yiwu ba. Hakan ba zai taɓa yiwuwa ba.

Ta ci gaba da faman girgiza kai a hankali, duk da yadda take jin kan kamar zai tarwatse.
Tsoron da ke tare da ita ya ɗan kau. Saboda ko babu komai, cikin mutanen da suke tafe tare da ita har da Kaka.

Sai dai tarin tsoron da ke fal ranta ba zai barta gaba ɗaya ba, har sai ta yi kwalli da Umminta tukunna.
A haka take ji ana ta tafiya da ita. Da alama tarin zaurukan cikin gidan suke ta wucewa. Su wuce wannan corridor, su sake shiga wani. Wasu ƙofofin a buɗe, wasu a rufe. Kuma ta ko ina ana jin motsin mutane, da alama gidan na jama'a ne.

"Ku yi a hankali fa, jikin yarinyar ba shi da ƙarfi."

Ta ji wata murya daga bayanta ta faɗa.
Ita kuwa mamakin yadda ake ta nan-nan da ita take yi. Sai ka ce waɗanda suka ɗauko ɗanyan ƙwai, suke tsoron kada ya fashe. Tana dai ta ganin abubuwan mamaki da al'ajabi.

Suna shigowa babban tsakar gidan gaba ɗaya, sai ta ji muryar wata tsohuwa tana cewa,"Ɗauko ruwan tofin nan a bata. Malam ya ce tana shigowa ta fara shan sa."

Ta buɗe idanuwanta tangararau, domin duk da cewa a buɗe suke, ita haka take jin su tamkar a rufe suke; ba komai take iya gani da kyau ba.
A daidai lokacin ne suka shiga wani babban parlo. Tana saka ƙafarta ta ji an kafa mata kofi a baki, ana ce mata ta tsugunna. Ta fara kurɓar ruwan rubutun da bismillah, tana kallon tsohuwar da ke riƙe da kofin a bakinta ta saman idonta.

Sai da ta shanye shi tass, tukunna aka ɗagata ta miƙe tsaye. Ai fa nan ta ja ta tirje.
Ta ƙi gaba, kuma ba ta yi baya ba. Kawai ta ƙi motsawa, kamar yadda ta ga waɗanda ke riƙe da ita suke son ta ɗaga ƙafa su wuce zuwa cikin parlon.

Idanuwanta a buɗe suke sosai, tarwai take kallon wawakeken parlon na alfarma. Zata iya cewa ko Fadar Shugaban Ƙasa albarka.
Zuciyarta ce ke tayata zantawa. Babban parlo ba yau ta saba ganinsa ba. Na gidan su Turaki ma ya ishi a gina wadataccen gida a cikinsa. Haka ma idan ta ce na masarauta, babban parlon Fulani tsab za a iya gina gida biyu a cikinsa.

To amma shi wannan tafkeken parlon da take gani! Gari ne guda.
Ba haufi zai isa a gina a fitar wa da dukkan mutanen ciki sama da talatin, ɗakunansu. Ba wai ɗaki ɗaya ba. A'a. Ciki da falo da banɗaki, har da ɗakin girki, kowa zai samu.

Haka take ta bin wajen da kallo, daga wannan gefe zuwa wancan.
Ba wai saboda yawan mutanen wurin kaɗai ba, ko kuma girmansa da ya ba ta mamaki.

A'a! Sai saboda abin da ta gani.
Haɗuwar parlon, tsarin kayan alatun cikinsa, fitilun da ke haska ɗakin, kayan ado da aka tsara cikin tsarin taknoloji, da irin daular da ke cikinsa, komai yana nuna tamkar mutanen da ke rayuwa a wajen ba su taɓa sanin wani abu da ake kira talauci ba.

Arziƙi ne aka zuba na gaban kwatance, wanda sai ido ya gani kawai.
Hakan kuwa yasa zuciyarta ta ƙara buguwa. Ta takure ƙafafunta. Tana jin suna luntsumewa cikin tattausan carpet ɗin da ke ƙarƙashinsu. Duk shige da ficenta a gidan su Turaki da take ganin sun fi kowa kuɗi da jin daɗin rayuwa, ba ta taɓa taka irin wannan carpet ɗin mai musulmin taushi ba.

Sanyin AC ya dinga ratsa jikinta, amma maimakon ya sanyaya mata zuciya, sai take jin yana ƙara mata wani irin zafi a ƙashin bayanta.
Ita fa gaskiya, zahiri babu kokwanto. Turaki da Yayanta sun siyar da ita ne.

To me ta yi musu a rayuwa? Babu shiri kuwa ta fashe da kuka.

"Don Allah..."

Muryarta ta karye.

"Ku yi haƙuri..."

Mutanen da ke kusa da ita suka yi shiru. Ta kalli ɗaya, sannan ɗayar.

"Kar ku cutar da ni..."

Wata mata fara ƙal, tsabar farinta har ɗaukar ido ƙyallin fatarta yake yi, ta sha gwala-gwalai a jikinta. Ta yi saurin tasowa tana faɗin,"Subhanallah, a'a! Wa ya ce za mu cutar da ke?"

Fullo ba ta saurare ta ba. Don kuka ya ƙwace mata magana.

"Don Allah... Ina so na rayu da Ummina da Kakata. Ku barni na koma wurinsu."

Ta haɗiye sauran maganar. Saboda saukar da idanunta suka yi akan wata mace da ke tsaye a can gefe.
Ita ɗaya kamar tana tsoron mutanen wajen. Da alama ita ɗin ba mai son magana da hayaniya ba ce. Irin mutanen da idan za a zauna a yi ta hira, sai dai kawai su yi murmushi, kafin su tanka yana da wahala.

Ummi!

Ummi take gani tsaye tana kallonta, idonta cike da ƙwalla, murmushi kwance a saman kyakkyawar fuskarta.
Tana sanye da wata haɗaɗɗiyar lafaya ja wadda ta yi mata matuƙar kyau. Karon farko kenan da Fullo ta ga mahaifiyarta kamar balarabiyar gaske, yadda take jin mutane na faɗa a kan kyawun Ummin da Allah ya yi mata. 

"Ummi..."

Kalmar ta fito daga bakinta cikin rawar murya.
Fuskar Ummin ta washe da annuri. Ta yi mata kallo mai tattare da ɗumbin soyayyar uwa zuwa ga ƴarta.

So take ta buɗe mata hannu ta taho jikinta, ta rungumeta. Amma babu dama. Akwai wannan kunyar ta al'adar Fulani da ke tsakaninsu da ƴaƴansu.
Amma tabbas tana buƙatar ta rungumi ƴarta a jikinta.

Ba ƙaramin daɗi ta ji ba da take ganinta lafiya a yanzu.
Saɓanin kwanakin da suka wuce, waɗanda zata iya cewa ba don cuta ba mutuwa ba ce, sai ta iya cewa har ta cire rai da ƴarta.

Saboda sosai ta yi matuƙar girgiza a lokacin da Malam Usman mai ruƙiyya ke faɗa musu cewa, wasu abubuwan da yawa ba Fullo da kanta ba ce ke aiwatarwa. Akwai taimakon aljanun da ke tare da ita, kuma su ne ke ba ta kariya a mafi yawan haɗurran da take jefa kanta a ciki, ko wani mummunan abu idan ya tunkare ta.

A irin kallon da Fullo ke jifan Ummi da shi, Ummin ta karanci ma'anarsa.
Saboda haka laɓɓanta suka tale da murmushi, tana gyaɗa wa ƴartata kai a hankali, tabbacin Ehh, ni ce ƴata. Ba mafarki kike yi ba. Ba gizo nake miki ba.
Sai kawai Fullo tasa hannu tana rufe bakinta.

A hankali take jujjuya kanta. Don ita fa lamarin kamar almara yake. Abin da take gani ya fi kama da mafarki, mafarkin ma a gidan Aljannah. Adda Asma ta lura da irin firgicin da ya sake kama Fullo. Nan take ta ruƙota jikinta, ba tare da matsa mata da yawa ba.

"Nutsu ki kwantar da hankalinki. A gida kike. A gaban dangi kike tsaye, masu ƙaunarki, masu tausayinki, waɗanda suka shirya tsaya miki a rayuwa. Ke ƴar gata ce gaba da baya."

Fullo ta girgiza kai.

"A'a..."

Ta share fuskarta da bayan hannunta duk cikin ruɗewa.

"Ban san kowa ba anan ai."

Adda Asma ta kalli Ummi, sannan ta dawo da kallonta gareta.

"Mu ɗin jininki ne. Iyayenki da Yayyenki ne duk anan wurin. You are in a safe place."

Fullo ta sake girgiza kai.

"Ni ban san ku ba... Kawai ina ganin Ummina tana yi min murmushin ƴan Aljannah."

Kuka ya sake kubce mata. Adda Asma ta shafa bayanta.

"Ba mafarki kike yi ba. Kuma ba wata duniyar kike ba."

Sai ta juya ta kalli Ummi. Ummi ta kasa jurewa. Ƙwallar da ta cika idonta ta sauko a kumatunta. Adda Asma ta matsar da Fullo gaba.

"Maza je ki ga mahaifiyarki."

Ita wallahi, tun da aka haifeta bata taɓa ganin Ummi ta yi irin wannan azababben kyan ba. Ba wai kawai kyau ba ne, kyan fa ba irin na mutanen duniya ba ne. Shi yasa duk take jin kamar fa a lahira su ce, lahirar ma a gidan aljannah.
Tana kallon Ummi ta buɗe mata hannayenta.

"Zo gare ni Auta."

Muryarta ta karye.

"Zo wurin Umminki."

Da jin haka, Fullo ta ƙwace daga hannun Fanne, ta nufi Ummi da sauri gwargwadon ƙarfin jikinta na marasa lafiya, ta faɗa jikinta.
Ummi ta rungumeta tsam. A wannan lokacin kowacce a cikinsu tana jin wani irin shauƙi da ba zai faɗu ba ne.

Fullo ta ɗan ɗago kai daga ƙirjin Ummi. Murya a sanyaye ta ce.

"Ummi nan ɗin ina ne muka zo?"

Ummi bata iya bata amsa ba, sai murmushin jin da daɗi da farin ciki take yi. Ita fa Allah ta tuba, sai ta iya cewa ta ji daɗin mutuwar Hayyo, da yana raye wataƙila da ba a wannan yanayin.

"A Aljannah mu ke Ummi? Wurin nan yana da kyau sosai. Kuma duk mutanen wurin ma masu tsadaddan kyau ne fa."

Gajeriyar dariya ta kubcewa wasu daga cikin mutanen da ke kusa. Ummi murmushi ta yi, ta shafa kanta.

"Muna duniya Auta. Gidansu Abbanku ne wannan. Kuna da kyakykyawan Asali ashe."

Ta ɗan dakata kafin ta ƙara da murya mai taushi.

"Duk waɗannan da kike gani family ɗinki ne. Iyayenki ne. Ƴan uwanki ne. Mutanen da za ki nuna da alfahari ne, mutanen da ba ki da kunyar nunawa duniya su, mutanen da Allah Ya ɗora musu haƙƙin kula da ke ne. Ki gaida su da ladabi."

Fullo ta fita daga jikin Ummi. Ta kalli mutanen. Wannan karon ba tsoro ne kawai a idanunta ba. Akwai mamaki. Akwai tambayoyi. Akwai kuma wani sabon abu da ba za ta iya ba shi suna ba.
Haka ta durƙusa ta gaishesu gaba ɗaya. Suka amsa mata, suna saka mata ɗumbin albarka da addu'o'i.

Ita da Ummi da Fanne suka fito daga ɓangaren Hajjah, inda nan ne ɓangaren mahaifiyar Hayyo, suka nufi sashin Daada. Anan ma da suka shiga tun a bakin ƙofa Fullo ta tsaya, wallahi tana ganin komai ne fa kamar ba a duniyar da ta sani ba.
Wannan ɓangaren ma ya cika da jama'a. Lallai Hayyo ɗan dangi ne, dangin ma na ƴan gata da alfarma.

Ummi ta yi mata nuni da wata tsohuwa da ke zaune a kan royal cushion.

"Ga Daada."

Daada tun kafin su ƙaraso, idonta yana kanta. Tana kallonta ta cikin gilashin da yake ƙarawa ganinta ƙarfi. Annuri ya cika fuskarta. Ta ɗago hannu ta yi mata alama na zo nan Jikata.

Fullo ta taka zuwa wajenta a hankali. Har tana jin kamar ƙafafun na ta ba za su iya ƙarasawa da ita ba. Tana isa Daada ta kama hannunta.

"Zo ki zauna kusa da ni."

Ta matsa mata wuri da kanta, Fullo ta zauna kusa da ita sosai, jiki na gugan jiki.
Royal cushion ɗin da Daada ke zaune, babu wani mahaluƙi da ya isa ya zauna akanta bayan ita. Amma sai ga shi ta matsawa Fullo, hakan ya bawa sauran Ƴaƴa da Jikoki tabbacin Fullo ɗin ta zama ta musamman a cikinsu, wanda har hakan sai da yasa wasu jin kishi, wasu kuma sosai suka kasa ɓoye jin haushin su.

Daada da kanta ta dinga gabatar da ita ga kowa. Tana faɗa mata sunayen ƴan uwanta, matan ƙannen Hayyo, ƴaƴan yayyensa da sauran dangin da suke zaune duk a wurin.
Fullo dai a wannan rana ta ga abin da ba ta taɓa tunanin za ta samu ba a rayuwa.

Ta ga tattali. Ta ga gata. Ta ga yadda mutum zai iya zama abin so ga mutane da bai taɓa sanin akwai su ba a duniyarsa.
Kafin su kwanta, Ummi da kanta ta riƙe hannunta ta dinga rakata wajen Iyayenta Maza, Yayun Hayyo da ƙannensa, ta gaishe su ɗaya bayan ɗaya.

Mutuwar iyaye ba abin farin ciki ba ce.
Ko da iyayen sun yi kuskure, ko sun lalata rayuwarsu, ko sun bar maka baƙin tabo a rayuwarka, rasuwarsu ba abin murna ba ce.

Amma a ɓangaren Fullo, akwai wani abu guda da mutuwar Abbanta ta haifar mata wanda har tsawon rayuwarta ba za ta iya mantawa da shi ba.
Mutuwarsa ce ta buɗe mata ƙofar rayuwar da ya binne mata.

Idan da bai mutu ba, wataƙila da ba za ta taɓa sanin waɗannan mutanen ba. Da ba za ta san cewa tana da wasu nagartattun iyayen ba, ba zata san su ɗin suna da kyawun nasaba da asali ba.

A cikin satin mutuwar, haka aka riƙa ɗaukarsu ita da Abdulhamid da sauran Sisters nata da suke uba ɗaya, ana kai su gidajen dangi na kusa da na nesa.
Babu inda aka bari a cikin dangin mahaifinsu da ke Taraba.

Waɗanda suke ƙasar waje ne kawai ba su samu ganin su ido da ido ba, amma su ma sun yi video call.

Sannu a hankali, damuwar mutuwar ta fara rage mata jin nauyi. Ba kuma wai don ta manta da Abbanta ba.

A'a.
Sai dai zuciyarta ta fara samun wani sabon jin daɗi da za ta jingina da shi.
Idan ita da Abdulhamid suka samu kansu su kaɗai, sai su riƙa kallon juna suna tambayar juna tambayar da babu ɗayansu da ke da amsarta.

"Me ya sa Abba ya tsiyatar da kansa haka? Me ya sa mutumin da yake da irin wannan gata ya zaɓi rayuwar da bata da kyau? Me yasa ya nisanta kansa daga Family ɗinsa? Har ya zaɓi ƙasƙantacciyar rayuwa irin wadda ya yi."

Ba su da amsar tarin tambayoyin da suke da.
Sai dai wata rana Fullo kan ji a ranta, ina ma Abba zai dawo da ta tambaye shi.

Da ta zaunar da shi a gabanta. Da ta tambaye shi dalilin da ya sa ya zaɓar musu rayuwa mara daɗi. Da ta tambaye shi dalilin da ya sa ya hana su sanin cewa suna da wannan gatan da kyakykyawan asalin.

Sai dai Abba ya tafi. Ya barta da tambayoyin da ba ta san wa za ta yi wa su ba.

Saudi Arabia, Jeddah, Al-Shati District, House No. 08.
13:00.

Raudha ta fito daga bedroom ɗin hannunta riƙe da biro da jotter, yayin da Fullo ke biye da ita a baya, laptop ɗinta a hannunta.

Suka ƙaraso parlon, Raudha na ci gaba da maganar da suka fara a ɗakin.

"Yanzu to ya kika ga lissafin? Tun da dinner ce kawai, ai hakan ya yi ko? Sai dai ban sani ba ko after an kai ki akwai abin da za a ƙara yi. Kin san al'adar tamu da tsirface tsirface. Ƙirƙiran event ba abu ne mai wuya ba a wurinsu Fanne."

Fullo ba ta amsa mata ba.
Ta wuce kai tsaye zuwa gefen da Daada take, ta zauna kusa da ita, sannan ta buɗe laptop ɗin, ta ci gaba da operating ɗinta. University take dubawa. Tun bayan sati biyu da rasuwar Abbanta, ita da Raudha da Amatullahi suka zauna suka yi private WAEC. Su ma jikokin gidan ne, kuma bayan sun gama aka ce kowannensu ya nemo university ɗin da yake son zuwa.

Da farko Fullo ta so ta zauna a Nigeria.
Amma da ta tuna karatun nigeria da take jin labarin ƙalubalen cikinsa, sai ta fasa, tun da Allah yasa tana da gata yanzu, kuma cikin wadata su ke, gwara ta yi karatu mai inganci. Yanzu haka ma bincikenta ya karkata ne kan universities da ke Europe, musamman waɗanda Raudha ta ba su shawarar su duba.

Aure kuwa? Ba ya cikin lissafinta ko kaɗan.
Tun bayan addu'ar arba'in, take ganin yadda aka mayar da hankali kan maganar aurenta, to ita wallahi har tana mantawa cewa tana da wani aure.

Idan basu sani ba, ta ma kusa sa mijinta ya sake ta. Domin har zuciyarta, ba ta ga ta yadda za ta iya zama da Turaki ba. Daada na shan tea ta ɗago kai. Ta kalli Fullo daga sama har ƙasa, sannan ta girgiza kai tana yamutsa fuska kamar wadda ta ga wani abin ƙyama.

"Tirrr! Tirrr! Tirrr da wannan mugun halin na ki irin na Hayyo."

Fullo ta ɗago kai daga laptop ɗin.

"Kai dan Allah Daada!"

Ta shiga dukan ƙafarta a ƙasa, fuska ta ɗan canja.

"Abba na fa ya mutu. Ki daina min irin haka. Duk in kin ambaci sunansa sai ya tashi a ƙabarinsa fa."

Daada ta tsaya tana kallonta sheƙeƙe. Kallon ki shiga hankalinki da ni.

"An faɗa ko ba halin nasa ba ne? Wani ya ce kar ya zama mutumin ƙwarai?"

Ta ajiye cup ɗin tea ɗinta.
"To in faɗa miki, har duniya ta naɗe, Hayyo dai bai da halin kirkin da za a shaide shi da shi. Gwamma ma ki daina nunawa duniya shi ubanki ne. Zai fi kyau ki riƙa barin ana ambatarsa akai-akai ko ake masa addu'ar samun rahamar Ubangiji."

Fullo ta yi shiru ƙwalla na cika idonta. Daada ta sake shan tea, sannan ta ci gaba.
"Banda iskanci ke kenan ba ki da aiki sai faman ɓata fuska. Ki ta tura wa mutane laɓɓa gaba kamar ganda. To wallahi ki kiyaye ni tun ban ɓata miki ba."

Ta zabga mata harara sosai.

"Ana tausaya miki, amma kina yi wa mutane iya shegen da kika ga dama. To ni ubanki zan ci. Ba kowanne iskanci na ke ɗauka ba."

Ta yi ta faɗa, tana harar Fullo kamar idanuwanta za su zazzago, tukunna ta juya ga Raudha.

"Ke kuma ina jinki? Kin gama lissafin abin da na saka ki?"

Gaban Raudha ya faɗi. Nan da nan ta shiga zare idanu kafin ta ce,"Ki yi haƙuri Daada. Wallahi na manta, amma zan yi yanzu."

Daada ta buɗe baki cikin mamaki.

"Kin manta? In saka ki aikin tun yammacin jiya, ki ce min ba ki yi ba? To uban me kike rubutawa yanzu?"

Raudha ta sunkuyar da kai tana kallon jotter ɗinta.

"Daada, bari na..."

"Bari na me?"

Raudha ta yi shiru. Daada ta ja tsaki.

"Ni fa ba na son mutum ya ke sa ni magana biyu. Ki gama min abin nan kafin na sake tambayarki wallahi."

Fullo kuwa duk da cewa tana kallon screen ɗin laptop, sai da gefen bakinta ya ɗan motsa. Raudha ta hango hakan kuma ta ƙulu.

"Ke kuma me kike wa murmushi?"

Fullo bata tanka mata ba dai. Illa danne dariyarta da tayi.
Cikin ɓacin rai Daada ta ci gaba da yiwa Raudha faɗa sosai. Babu fa wanda yake son faɗan tsohuwar nan har ga Allah.

"Daada ai kin san can dangin mijin Fullo sun ce za a yi events kafin ta tare. Shi ya sa dama na ke lissafin abubuwan da za mu yi. Ƙanwar mijin tana ta yi min waya tana tambaya ko mun gama shirya abubuwan da muke so, kuma duk ban yi ba. Ita kuma ina ta tambayarta, ta ƙi ce min komai. Ki yi mata magana don Allah."

Ta faɗa duk a ɗarɗarce, saboda irin kallon da Daada ke jifanta da shi da makafin idanuwanta.
Daada ta gyaɗa kai. Sai ta juyo ta fuskanci Fullo.

"Ke ɗauko min sandata."

Sanin halin Daada yasa Fullo miƙewa babu shiri. Ta wuce bedroom, cikin ƴan seconds sai ga ta dawo, tana miƙawa Daada sandar daga baya-baya. Daada ta karɓa. Ba tare da wani ɓata lokaci ba, ta saita kafaɗar Raudha ta muƙa mata.

Tuni zafin dukan ya ratsa Raudha, idonta ya ciko da ruwa. Daada ta fara mata sabuwar masifa.

"Uwaki da ubaki ke da lissafin bikin! Wato har wani shirin bikinta ku ke yi saboda ba kwa ƙaunarta ko?"

Ta ƙara ɗaga muryarta.

"To tana da ni Kakarta! Ni ce nan gatanta. Don haka ban ga wanda zai ɗaukar min jika ya kai ta inda ba a ƙaunarta ba."

Ta ɗan dakata, sannan ta ci gaba cikin ɓacin rai sosai.

"Ko za ki ce baki da labarin Kakar yaron bata sonta? Har tana faɗin wai ya sakar min jika! To dama ko bata sa shi ya saketa ba, ai dole ne ma ya saketa, tunda dama Jikata ba sonsa take yi ba."

Ta girgiza kai cike da takaici.

"Ni ina ma na taɓa jin ma an yi gantalallen aure irin wannan? Allah dai ya gafartawa Hayyo kawai."

Ta yi shiru kaɗan, kafin ta ci gaba da sababi. "To in har ba so ake rai ya dinga ɓaci ba, kar in ƙara ji an tada maganar auren nan. Suma can da suke na su basu da hankali ne, zan kira waya na kora musu kashedi."

Ta ja dogon tsaki. Tsakin da ya yi ƙarfi har su Fullo suka toshe kunnuwansu.
Ta doka sandarta a kan table ɗin da ke gabanta, fuskarta na bayyana tsurar ɓacin rai. Ta hau surfa ruwan bala'i tamkar za ta haɗiye gidan gaba ɗaya.

"Ita Kakar tasa wace ita da za ta ce Jikanta ya fi ƙarfin jikata, ba zai zauna da ita a matsayin matarsa ba? To me take ji da shi? Kuɗi ko mulki ko kuwa sarauta?"

Ta ɗaga gira tana huci. Domin irin fusatattun matan nan ne. Wanda idan suka fara bala'i sai dai a bar musu wuri kawai, idan sun gaji sa daina. Sai dai kuma fa akwai ƙwatarwa kai haƙƙi.

"Idan tana ɗagawa cewa suna da Gombe a hannunsu, to muma haka muke da Taraba a tafin hannunmu, tun daga sama har ƙasa kuwa."

Fuskarta ta ƙara ɗaukar zafi. Su Fullo na jin kamar su miƙe su bar mata wajen. Raudha na ta danasanin ta so da maganar.

"Ita wai ƴar wofi, har wani kashedi take turo min kar in sake Jikata ta tare a gidan Jikanta saboda yana auran ƴar sarki!"

Ta bugi hannunta a kan kujera.

"To idan ban sa an ƙwace sarautar ta su ba Allah ya tsine! Babu ƙulla-ƙullar da ba zan iya yi ba akan a tsigesu daga kujerar sarautar na su, sai inga ta tsiya. Banda ma dai ƙaddara! Ina Jikata, ina Jikanta? Ai wallahi sam babu haɗi."

Ta ɗaga kai cikin alfahari.

"Jikata ta fi ƙarfin wannan mummunan jikan nata. Dogon banza da shi, Fullo fa matar Larabawa ce, Matar manya. Ba matar mutumin da zuwansa Saudiyya ma bai fi ƙirgen yatsun hannuna ba."

Ta girgiza kai tana sake jan tsaki, sannan ta ƙara da cewa,",Daga jin ma yadda take hayagaga a kan sarautar ta su, kasan ci aka yi aka yi, aka rage musu."

Ta yi shiru tana girgiza ƙafa ɗaya a kan ɗaya. Ta kuma jan tsaki, ta kurɓi tea ɗin da ke gabanta, sannan ta zubar da shi a cikin wata ƙaton kwanon silver mai kama da sink.
Ta kama haɓa tana jijjiga kai, alamun takaici ya isheta. Ta ɗora manyan idanuwanta a kan Fullo ta ce,"To ni dai ba zan yafewa ubanki ba, da ya sa aka raina mu haka. Banda ya jawo mana raini, har ina wannan figaggiyar tsohuwar kamar kazar mayu ta samu zarrar yo min aiken raini irin haka, wai in raba jikata da jikanta saboda jikanta ya fi ƙarfin Jikata? Kuma yana auren ƴar uwarsa wadda tafi ƙarfin ta haɗa kishi da Ƴar aiki. Har tana ƙara faɗa min mu kuka da kanmu, idan har muka bari aka yi tariyar auren nan."

Ta yi shiru tana cizon yatsa kafin ta nuna kanta.

"Har ni ake yowa wannan baƙin aiken rashin kunyar, kuma ban ɗau matakin komai ba? Ni uwar Galadiman Wurkum, Kakar soja, Uwar macen da ta fi kowacce mace kuɗi a nahiyar Africa... Yo ni kam yaushe na yi wannan saken? Dama har haka tsufan ya lalatar da ni? Ko da ya ke, duk Hayyo ne ya jawo min ba kowa ba."

Cikin ƙarin ɓacin rai ta sake buga sandarta a kan table, har glass ɗin ya tsage.

"To billahillazi idan ban sa jikan nata ya yi fatali da gimbiyar waje ba, ya zauna da Jikata kaɗai ba shegiya na ke. Hassana sunana na fita fitina da rigima wallahi. Bata san wacece ni ba, ta binciki tarihi ta ji ba a taɓan ƴaƴa da jikoki a zauna lafiya. Kuma wallahi bani da kyau, ni kaina ina shakkar kaina."

Ta yi ƙwafa tare da miƙewa.

"Na rantse Allah ne ya rufawa Hayyo asiri, ba mu ƙara gamuwa ba, da wallahi tallahi ya gane kuransa da wannan wulaƙancin da ya ja mana. Akan jikarmu zata tare a gidan aurenta, a kira waya ana mana gargaɗi. Kashhh!"

Ta yi shiru na ɗan lokaci, sannan ta ƙara da kakkausar murya,"Amma babu komai. Idona idonta sai ta san ta yi min rashin kunya. Ni ai ba sa'arta ba ce ta sani sarai... Sai ta san ta sa shegiyar matar tasa ta kira Jikata ta zazzageta. Zan nuna mata na fita ɗanyen kai. Kowa ai shegen kansa ne. Jikan nata da take ta haƙilo a kansa, zan nuna mata mu ne rayuwarsa. Ba dai an ce yana matuƙar ƙaunarki ba? To aradun Allah sai ya sake ki, sai dai ya mutu! In ya mutu ita ke da asara ba mu ba."

Zata bar wajen, sai ta kalli Fullo ta ga tana kuka. Ai ko ta ɗaga sandarta ta fara dukan Fullo da ita tana cewa,"Saboda na ce sai ya sake ki ne shi ne zaki saka mun kuka? Da ike baki da hankali ba ki da wayo, ya yi fatali da ke tsawon kwanakin nan masu uban yawa, amma saboda dusar awara ke cikin kanki, har kina tunanin ma za ki zauna da shi. Ba kuka ba ki haɗiyi zuciya ki bi ubanki, amma wannan aure sai ya mutu a yau-yau ɗin nan. Ba zan yarda ki je inda za a riƙa miki kallon raini da ƙasƙanci ba, duk da cewa ubanki ya jawo miki."

A hankali Fullo ta ce,"Ni fa ba haka ba ne..."

Daada ta taɓe baki. "Ki yi kukan jini ba na ruwa ba. Indai jikan wannan figaggiyar tsohuwar ne, na raba ku, ba ke ba shi! Ya sake ki, ki samu mijin kerewa sa'a wanda ya ci uwar ubansa."

Ta kama hanyar ɗakinta tana ta jaraba, ta buɗe ƙofa zata shiga, sai ta waigo ta kalli Raudha ta ce,"Ɗau waya ki kira min Jagarɗo."

Sai kuma ta fasa shiga ɗakin. Ta dawo ta zauna, ranta a ɓace, tana kallon Fullo da take ta kuka. Banda tana tausayin kar ta ɓaɓɓallata, da ta ƙara mummuƙa mata sandar har ta shiga hankalinta.

Raudha ta miƙo mata wayar tana cewa,"Ga shi Daada."

Ta karɓa ta kara a kunne tare da saka glass ɗinta, kamar ganinsa zata yi. Bayan sun gaisa, sai ta ce da shi,"Ka na jina?"

Daga ɗayan ɓangaren Jagarɗo ya ce,"Ina ji Daada."

"To ka saka Kakinka na soja, ku ɗauki hanyar Gombe yanzu nan. Ka shiga har cikin gidan Alƙali wa yake oho, ka kamo ɗansa da yake auren Fullo, ka sa masa ankwa, sannan ka ba shi biro da takarda ka ce ya sakar min jikata. In yaƙi, ka yi barrack da shi, da figaggiyar Kakarsa da ta yo min aiken rashin kunya da rashin mutunci."

Jagarɗo ya ce,"Amma Daada..."

Cikin fusata ta katse shi.

"Idan raina ya ɓaci rayuka dubu za su ɓaci. Umarni na baka, kuma idan kana son ganin daidai ka aiwatar da abin da na ce."

Tana faɗin haka ta kashe wayarta. Ta kalli Fullo, ta doka mata tsawa,"Ɗago da kanki, ki ba ni lambar mijin na ki."

Fullo ta ɗago kanta, hawaye duk ya wanke mata fuska. Cikin muryar kuka ta ce,"Ban san lambarsa ba."

Want the next chapter?

Create a free ArewaPen account to save progress, unlock paid chapters, follow this author, and keep reading across web and the Android app.