Free chapter · Read without an account
BOOK ONE CHAPTER SEVEN
Rungumar da Aliya tai masa da wasu kalamai da tafaɗa waɗanda basa kaiwa cikin kunnuwansa yakalla.
Ta zare jikinta daga nasa tana dariya tamiƙe tasoma tattara kayan da sukai amfani dasu.
Iska yafesar yana bin bayanta da kallo tazo tawuce.
Day two kenan....
Day three tazo tawuce.
Day four tazo.
Kullum haka garin Allah yake wayewa yana tafiya, Aliya na kashe sa da mamaki tana ƙirƙiro sabbin abubbuwa atsakanin su, tanayi kamar batasan matsayin sa agaretaba.
Tun yana mata shiru har ya soma biye mata, yana sakewa da ita kaɗan bawai dan yamanta bayaba sai dan Aliya bata bashi ƙofar da zai mai data baƙuwa acikin gidan taba.
*JAMILA*
Jamila ta tsaya a bakin ƙofar tana kallon inda motar baƙin ta ɓace. Har yanzu tana jin ɗumin rungumar Raihan a jikinta. Ta sauke idanunta a hankali, tana ƙoƙarin fahimtar abin da ya faru da ita.
"Me ya sa?"
Ta furta a hankali, kamar tana tambayar zuciyarta.
Ta juya ta koma cikin falon. Komai yana nan yadda yake. Manyan kujerun da aka kawata da tsada, fitilun da ke haskakawa, ƙamshin turaren da ya cika gidan.
Amma wani abu ya ɓace.
Ta zauna a kan kujera, ta jingina kanta da bayanta. Hannunta ya kai kan ƙirjinta, inda har yanzu take jin bugun zuciyarta.
Ba rungumar Raihan ce ta firgita ta ba.
Abin da ya firgita ta shi ne yadda ta ji kanta a lokacin.
"Na zaɓi abin da nake so..."
Ta yi shiru.
"To, me ya sa har yanzu nake jin kamar na rasa wani abu?"
Babu wanda ya amsa mata.
Sai shiru.
Shiru mai nauyin da ya fi dukkan kayan alatu dake kewaye da ita.
Ta kwanta a hankali, tana kallon silin ɗakin.
A yau ta fahimci cewa akwai wani irin kaɗaici da ba a iya kawar da shi da kuɗi.
Kuma akwai wasu mutane da ko da ka rufe musu ƙofa, zuciyarka tana ci gaba da barin su su shiga.
Ta juya gefe, ta jawo filo ta rungume.
Amma wannan karon, ba ta sami natsuwar da take nema ba.
Domin a karon farko, ta fara jin tsoron abin da zuciyarta za ta iya tunasar da ita.
Wani lokaci, abin da mutum ya zaɓa da hannunsa shi ne abin da zai fi wahalar rayuwar shi da shi.
Jamila ta ɗauki wayarta daga kan coffee table din dake falon, ta buɗe sunan Samir.
Ta danna kira.
Ɗaya...
Biyu...
Har wayar ta daina ringing, babu wanda ya ɗaga.
Ta sake kira.
A wannan karon, muryar wata mata ta amsa.
"Hello, ma'am. This is Samir's P.A. He's currently in a meeting. I'll let him know you called. He'll call you back once he's done."
"Okay, thank you."
Jamila ta kashe wayar a hankali.
Ta sauke ta a kan cinyarta, tana kallon allon wayar.
Tana jira.
Mintuna suka wuce.
Sa'a ɗaya.
Babu kira.
*
Da yamma ta sake duban wayarta, tana fatan ganin sunansa.Haka ta ci gaba da kiransa, tana samun amsar cewa yana aiki ne, zai kira ta idan ya samu lokaci.
Amma kiran bai zo ba.
Rana ta koma dare.
Dare ya koma safiya.
Har sati guda ya cika.
Sati guda tana jiran muryarsa.
Sati guda tana kallon wayarta.
Sati guda tana kwanciya da tambayoyin da babu wanda zai amsa mata.
Kuma duk da kasancewarta a cikin gidan da ke cike da dukiya, zuciyar Jamila ta fara jin kamar an bar ta ita kaɗai a cikin wani babban wuri marar ƙofa.
Ta rungume filonta, ta lumshe idanunta.
A hankali, hawaye ya zubo mata.
Ba don ba ta da komai ba.
Sai don mutumin da take son ya kasance kusa da ita, shi ne wanda ta fi jin nesa da shi.
Sati guda kenan.
Amma a zuciyar Jamila, kamar wata rayuwa ce ta shuɗe.
*ZAINAB*
Misalin ƙarfe 3:00pm tana zaune yara sukai sallama suka shigo.
Dagudu Ramlat tazo ta rungume ta. Tana cewa
"Oyo-oyo Mami"
"Oyo-oyo Ramly baby ya makarantar"
Zama sukayi. Khadija ta miƙa mata takarda tana cewa
"Mami term ya ƙare anbamu takardan biyan kudin makaranta."
Amsa tayi. Ramlat da Anis ma suka bata nasu. Khalid na zaune agefe yana kallon su.
Jiki asanyaye Zainab tasa hannu ta karɓi takaddan afili tace
"Shikenan anjima sai kuje sashin Auntyn ku ku kaima Abban ku."
Nan take Khalid ya sauke kansa. Yana motsa harshen sa kamar wanda akaima dole. Hakan yasa muryanshi fitowa can ƙasan maƙoshi.
“Ni ba zan je ba.”
Zainab ta kalle shi.
“Me ya sa?”
Ya yi shiru.
“Na tambaye ka, me ya sa?”
Khalid ya ɗago idanuwansa dake ɗaukeda fushin yaro wanda bai san yadda zai bayyana ciwonsa ba.
murya acun kushe yace“Kin manta wancan ranar da muka je wurin sa yai mana magana kamar wasu bare ba ƴaƴan saba"
Kadija da ke gefensa ta yi shiru. Zainab ta ji zuciyarta ta tsinke.
Ramlat da Anis da bawani fahimtar abinda ke faruwa sukayiba suka juya suna nasu hirar a tsakanin su.
“Banaso ku koya guje wa mahaifinku saboda abin da yake faruwa tsakanina da shi.”
Khalid ya share hawayen dasuka ciko idanunsa da sauri.
“Amma shi ma ya guje mu.”
Zainab tai shiru domin abinda Khalid yafadi gaskiya ne, Ahmed yana cikin gidan amma yabarta cikin kaɗaici, yabar yaran suna jin kamar sun rasa uba bayan yana raye.
Ta ja numfashi. Da dukkan abinda yai mata saura awannan lokacin tace
"Khalid su iyaye ba'a fushi dasu akan duk wani abu da sukai ma ƴaƴansu arayuwa.
Abaya babu irin kulawar da bai nuna mukuba kun sani ayanzu daya sauya uzuri yakamata kui masa ba fushi da shiba.
Aduk lokacin da zakui sallah inason kui ma mahaifin ku addu'a"
Shiru sukayi babu wanda ya amsa, wanda alamu suka nuna maganar ta bata gamshe suba.
Zainab tagir giza kai ta kallesu suduka"kuwwa yatashi yaje yacire kayansa yazo yaci abinci"
Batai maganar sallah ba sabida acan makarantar sukeyi, jiki asanyaye suka mike suka je suka cire kayan su.
*
Da yamma bayan sallahn ishai taji ƙaran motar Ahmed yadawo. Seda tabari yaɗan ɗau lokaci tacema Khadija taɗauki takardun takaima Abban su kuma kada tayarda taji tayi wani abu ba dai-dai ba.
Khadijah tamiƙe jiki asanyaye tafita tanufi sashin Aunty da tun shigowar ta gidan bata taɓa shigaba.
Knocking tayi a kazo aka bude mata kofa. Batare da tai kuskuren kallon fuskar matarda suke mata kallon uwaba abaya amma yanzu tazame musu annobar dake barazanar tarwatsa su.
A zaune taga Abbansu yana danna wayarsa hankali kwance batareda wani damuwa atare dashi ba. Rayuwa kenan komai bayada tabbass!
Ta duƙa agabansa. Kanta aƙasa ta gaidashi ya amsa da
"Yawwa. Lafiya?!"
Wani mulmulallen abu mai ɗaci ta haɗiye. Ta runtse idanunta tana ƙoƙarin danne duk wani abu da takeji tace
"Takardan biyan kudin makaranta Na kawo maka."
"Ajiye anan ki tafi."
A jiyewan tayi tafito tadawo.
_*_
Yabi bayan Khadija da ido wani mulmulallen abu mai ɗaci na kaiwa da komowa a ƙirjinsa.
A kwanakin nan jinshi yake yi kamar bashiba. Kamar anɗauke wani abu mai muhimmanci agaresa andasa sabo.
Ga wani abu dake cikin kansa acan nesa daya kasa cimmasa balle yasan komeye.
Duk lokacin daze wuce ƙofar sashin Zainab se yaji zuciyar shi ta doka kamar zata faso allon ƙirjinsa ta tarwatse.
Sau da dama ya kanyi ƙoƙarin zuwa inda take amma wani abu mai ƙarfi dayafi magnet na janyesa daga gare ta har mada ƴaƴansa da zuciyar sa ke gaya masa yayanke duk wata alaƙa atsakanin su.
Musamman yanzu da Khadija tazo gabansa tana magana jiyai kamar tana watsa mai ruwan zafi. Samm bayason ganinta. Numfashin shi har wani sarƙewa takeyi saboda yanda yaƙi miƙewa ya aiwatar da umarnin zuciyar shi agareta.
Zaliha dake zaune a kujerar dake gefensa tamiƙe tadawo gefensa ta zauna ƙamshin tiraren nan nata mai nauyi na ƙara danne duk wani abu dake taso mai.
Takarya murya tana kallonsa da lumsassun idanun ta tace"lokaci yayi da zaka sauke nauyin Zainab da yaranta akanka"
Taɗan numfasa tana kallon cikin idanuwansa dake kallonta babu ko ƙiftawa. Sai ta cigaba da magana
"Katashi yanzunnan kaje ka gaya mata kayan ke duk wata alaƙa dasu. Tarungumi ƴaƴanta su rayu a'inda suke kada taƙara tun karoka da matsalar su."
"To My love duk abinda kikace haka za'ayi. Farin cikin ki shine nawa. Faɗa naki cikawa nawa."
"To! My honey tashi katafi."
Taƙarke maganar tana kashe shi da wani shu'umin murmushi.
Da azimansa yamiƙe yafita zuciyar shi na azalzalansa da son cika umarnin ta agareshi.