Free chapter · Read without an account

25. ...yar aiki ce...🖊️ Kamar anyi ruwa an

by Noor · RU'UYAA (The dreams we never lived)

 ɗauke bayan tafiyar Romo daga wurin...ƙila kowa ya shiga shock da abinda ya faɗa....


'' kun gani ko..Allah ya wadan naka ya lalace!" Hajiya Momma ce ta faɗi hakan

Hajiya Ruƙayyah ta taya ta da faɗin '' ai kam dai,bawai bana son yaro bane...amma gaba ɗaya hallayarsa abun tambaya ce!"


'' Gaskiya Alhaji ya kamata ka ƙara sa ke...yaro yana nema ya gagareka...'' Inji Hajiya Wareesha


'' nidai fatana wannan lokacin bazai dinga kwasowa mutane abun magana ba''

'' once a trouble maker always a trouble maker!" Farzan ya miƙe daga wurin zamanshi bayan ya faɗi hakan...

'' kuyi mashi uzuri...rayuwa babu uwa akwai wahala sosai!" Hajiya Hafsah ta faɗa daga ƙarshe...Hajiya Momma na hura hanci tace '' Koda Fateemah aw Cora ɗin tana nan ai ba wani abun kirki zata aiwatar ba? Kai haɗa zuri'a da irin wa'yannan mutane dai masifa ne wallahi!"

Miƙewa Hajjo tayi cikin shiru tabar wurin sauran manyan matan suka cigaba da magana akan wacce suke kira Cora ko Fateemah duk sunanta ne,kamar basuga cewa Hajjo tabar wurin ba,suma mazan suka bar wurin kusan a tare...amma Cora bai yi kama da sunan musulmai bako?

Sai lokacin da suka bar wurin na lura cewa yan matan kamar zasu kashe ni da kallon da suke min...nayi ƙasa da kaina...Khalil ma yayi shiru kafin ya miƙe yabar wurin...

'' Mtchewww! aikin banza...this guy is a bad luck! daga dawowar shi har gida yayi tsami!" Jawaad da bai cika magana ba idan ana cin abinci ya faɗa tareda dukan table ɗin kafin yabar wurin


suma sauran suka zare jiki ɗaya bayan ɗaya sai da ya rage yan matan da mu masu aiki harda Diyaam Seraphina tayo kan DIYAAM '' Tass!" Ta ɗauketa da marin daya amsa ƙara a gaba ɗaya dining ɗin ƙirjinta na sama da ƙasa

Ɗan kwalin Diyaam ya faɗi doguwar sumarta baƙa ta warware ta rufe rabin fuskarta.. hannun ta dafe da kuncinta...


sakin baki nayi idona na kallon tsakanin su biyun... sauran suka sadda kansu,yan matan suke kallon mu kamar zasu kashe mu '' ba saida nace kada inga ƙafar ki a parlorn nan ba?"

Murya na rawa Diyaam tace '' K...kit...haƙ..hamm..'' damƙo gashin Diyaam Seraphina tayi

Heedayah tace '' ki haɗa min da shegiyar nan mai idon Mayu!" Kallonq Seraphina tayi kafin tace '' ki bari in gama da wannan annobar...''

Idon Diyaam suka fito.. jijiyoyin goshinta sukayi ruɗu ruɗu hannunta riƙe dana Seraphina '' Bana ce kada ki sake kiranshi da Hamma ba? Dan ubanki yaushe ya zama Hamman ki?''

''.kiyi haƙuri dan Allah!" Diyaam ta faɗa tana kuka sosai.. idonta kamar jini..da ƙarfi Seraphina ta tureta ta faɗi goshinta ya haɗu da table take wurin yayi ja kasancewar ta fara...


Tana huci ta juyo kaina..sauran yan matan suka miƙe kamar cin mutuncina yafi ƙayatarwa sama da Diyaam


'' Ji nayi ya I.B ya kira ki budurwar ya Rome?" Matsawa na shiga yi tana matso Ni...'' hala baki ji bane da kyau kike tambayarta?" 

Jameelah ta ɗauki gorar ruwa ta harbo sashena..da sauri na duƙe gorar ta sauka akan Seraphina...


'' Ahhh!!!!" Ta saki ƙara...ta juyo tana kallon Jameelah da fushi...

'' what the hell!"

'' oh bake nayi niyar jifa ba!" 

'' amma ni kika sama!"

'' Duh! Ba laifina bane idan kin shigo tsakani....'' a fusace itama Seraphina ta ɗauki gorar ta jefawa Jameelah..ta sameta a goshi

'' yanzu kema kin san yanda ake ji ai!" 

'' Guys calm down!"

'' taya zanyi calming down wannan ugly duckling ɗin na ƙoƙarin shiga tsakanina da Ya Rome..bayan ni yake so!" Tayi maganar tana kallona

'' excuse me...wane irin ke yake so? Huriyya take hararar Seraphina kamar idonta zai faɗi

'' wasn't it obvious?'' Seraphina ta bata amsa

'' delude yourself girl!" 

Faɗa ya koma tsakaninsu akan wake ƙoƙarin ƙwace Romo daga wa...ganin hankalin su baya kan mu na isa wurin Diyaam na taimaka mata ta miƙe salin alun muka bar dining

hawayen da suka zuba daga idonta sun isa cika murfin hira koma abinda yafi hakan girma...katin ma'aikatan tayi swiping elevator ta buɗe muka shiga ciki..nesa na tsaya da ita ..ƙila bata so asan munsan juna...ina satar Kallon ta daga lokaci zuwa lokaci yarinyar fara ce sosai...yanzu ta dena kuka kanta a ƙasa...

Sautin buɗewar elevator yasa ta ɗago ta fita ina biye da ita kuma ban san dalilin bibiyarta ɗin ba...ƙofar ɗakinta muka tsaya ta buɗe ƙofar na samu kaina da juyawa zan tafi '' Abeedah...'' ta kira sunan muryarta da taushi..Juyowa nayi ina rarrabar ido..ta nuna ɗakin '' mu shiga ciki...'' tayi gaba ina biye da ita abun ya ɗaure min kwanya...idan ita yar aikice meyasa take da ɗaki a cikin babban gida? 

Meyasa kuma Seraphina tayi mata yanda tayi mata...gefen gadonta ta zauna ta nuna min kusa da ita...nake jin ɗar ɗar..kafin daga ƙarshe na zauna ɗin


ƙaramin locker dake gefenta ta buɗe ta ɗauko magani tana lura da ciwon data ji '' kawo in yimiki...'' na karɓa daga hannunta...bayan shuɗewar lokaci tace '' ashe kina ɗaya daga cikin sabbabin ma'aikatan da aka ɗauko...'' gyaɗa kaina kawai nayi..ban manta yanda ta share niba ɗazu da nayi mata magana

'' oh...nima aiki nake a nan gidan..nasan kina tunanin yanda akai nake da ɗaki anan a maimakon sashen ma'aikata ko?" Jinjina kaina nayi tareda ajiye almakashi bayan na samata plaster a ciwon

'' Hamma Roman ne ya kawo ni shekarun baya...ya ganni ne a gefen hanya bani da inda zani...ni na zaɓi in zama mai aiki a nan a maimakon in zauna ana ciyar dani kyauta...'' nayi mamakin jin wannan.. kuma na rasa abun faɗa gane hakan tace 

'' kin tafi makaranta jiya? Yasu Anaam da Jadeedah?" Murmushi nayi kafin na bata labarin abinda ya faru a jiya ɗin duk da ba wani abu mai yawa ne ya faru ɗin ba...

Mun daɗe muna hira kafin na tashi na wuce sashen ma'aikata inda ake magana akaina...da gaskiya ta..abinda Khalil ya faɗa baƙin jini ya ƙara min..ina tafiya ana bina da baƙin ido kamar zasu sa in faɗi...



Washegari da safe ban samu damar zuwa dining ba saboda wannan Hajiya Momma data tsare ni a ɗakinta da wanki kuma fa akwai laundry room wai ita bata so ana sama ta kaya a mashin kuma bata ga wanda ya dace data ba wannan aikin ba sai ni koda na gama ƙarfe sha ɗaya bazan iya zuwa makaranta ba...haushi kamar in cinna mata wuta..dataga alamun na ƙufula wani shegen murmushi ne maƙale a fuskarta..nakai bakin ƙofa na juyo na kalleta nace '' aljannu na suna tashi su daki wanda ya ɓata min rai...ko su haukatar da mutum... Hajiya gwaggo kibi a hankali...'' expression ɗin dake fuskarta was priceless


Da sauri na fita daga ɗakin ina dariya... kitchen na tafi na iske sun haɗa wani abu a tray kamar biscuit da juice..da sauran abubuwa..kusan plate biyar ne... Hansa'u ceta shigo ta kwashi guda uku saura biyu Leonardo yace in bita dasu zuwa Movie room...

Badan naso ba nabi bayan ta.. yarinyar is self absurd ...ji take kamar tafi kowa kyau da komai a gidan saboda kawai uniforms ɗin ta sun matse ta sun fito da surar jikin ta take ji kamar maxan gidan ba zasu iya haƙura ba harda su Romo da Khalil tana tafe tana juya mazaunai...

abinda ya faru a Movie room ya ƙayatar dani fiye da komai a ranar...

sanda muka shiga wurin da duhu amma ba mazan kaɗai bane yau harda matan...layi layi take bi tana miƙa masu suna ɗauka kowa hankalin shina akan TV nidai ina tsaye daga gefe...

Bayan ta gama dana hannunta tazo ta karɓi nawa na juya Zan bar wurin saboda yanda Mukhtar ya dawo da hankalin shi akaina naji an bada tass

Juyowa nayi da sauri naga Hansa'u riƙe da kuncinta Armani tsaye a gabanta

'' BABBAR BALA'I!!! Ni kika mara?'' Hansa'u tayi maganar kamar zatayi kuka...'' ko zaki rama ne?'' Armani ta tambaya
'' dalla fita kiba mutane wuri shegiya me kama da aljannu..''

Dariya aka saka... Fuuu Hansa'u tazo ta wuce ni tana cika tana batsewa..sanda muka fito kasa haƙura nayi na kwashe da dariya... Juyowa tayi da jajayen ido tayo kaina..na kwasawa da gudu da ita biye dani...ina gudu dariya na cina...ban tsaya ba sai dana kawo gaban wata ƙofa...koda na ɗago bayan na gama kama numfashi ganina nayi gaban ƙofar nan mai XXX..

na juyo naga babu Hansa'u...ni kullum idan ana bina sai na kai wani wuri idan na juya sai inga wa'yanda ke bina ɗin har sun daina...

Miƙewa tsaye nayi da kyau na sake tabbatar da babu wanda ke ganina na matsa gaba na ɗaura hannu na akai zan tura...

'' kina da ajiya a ciki ne?" Maganar ta sauka cikin kunne na a bazata yasa na juyo da ƙarfi losing balance nayi na faɗa jikinshi..yayi tsaye ƙiƙam kamar bishiya hannayen shi cikin aljihu...da sauri naja baya kamar na ɗosanu da wuta ido waje na kalli fuskar shi da take a matuƙar ɗaure...

'' Uhmm...na manta da soso ne a ciki jiya dana gyara wurin...'' ƙaryar ta gamsar dani don haka shima dole ta gamsar dashi ko? amma ko kaɗan babu alamun hakan sai ɗauke idonshi da yayi daga kaina '' bar wurin nan!'' muryarshi ba wasa a ciki yasa na kama gabana

Sai kuma na tsaya '' soson fa?" wai kada ya ɗauka ƙarya nake...bai ko kalle niba naga ya ciro mukulli daga aljihun shi...gwalalo ido nayi kenan shine da ɗakin..kuma na zage ina makaka ƙarya...

Da sauri nabar wurin na tafi ɗakin Diyaam na ganta tana karatun jarabawa..zama nayi muka cigaba tare tana nunamin abinda ban sani ba....tana da ƙoƙari sosai...


Washegari muka tafi makaranta amma ba tare ba...su Jay d suke tambayarta me yasa bata zoba ranar farko.. murmushi kawai tayi bata ce komai ba...nima ban faɗa masu cewa a gida guda muke aiki ba...

Rayuwa ta cigaba da tafiya...har exam time table ɗin mu ya fito..a nan gidan su Khalil kuma dayawa daga mutanen gidan sunyi tafiya...harda Hajjo data tafi Makka...
cikin Alhazozan daga Alhaji Hussein sai Alhaji Mansir suka rage

Yan matan Seraphina, Heedayah Khadeejah da wasu da bansan sunan suba da kuma ya'yan Hajiya Momma kaɗai suka rage...suma samarin tsiraran su kawai ne a gidan duk sun tafi ƙasar waje karatu...


Yau Alhamis ina zagaye ƙaton gidan dan babu aiki da yawa saboda raguwar mutanen gidan... kitchen na shiga na buɗe ƙofar bayan nan da koda yaushe take a rufe.. nayi mamakin ganin dogon swimming pool da bishiyoyi hagu da dama da kujeru farare masu taushi...daga can gaba green grass mai laushi...

Iska da yanayin wurin na daban ne,kallon ruwan nayi da murmushi a fuska ta kafin nabar wurin na koma ciki na fara zagyena daga first floor... gidan kamar bada gaske ba saboda haɗuwarshi....daga first floor zuwa second floor har zuwa fifth floor...harda ɗakin motsa jiki na shiga na fito na duba sauran wurare a can ƙarshe naga wani ƙaramin matattakala,

Da nahau matattakalar ya kawo ni a roof top dake kewaye da glasses harda wani swimming pool...da kujeru masu taushi da lema kamar dai Beach...gaban wurin na isa ina kallon ƙasa jiri naji yana ɗiba ta da sauri naja baya tare da dafe ƙirji...

Zagaye wurin nayi ya tsaru sosai...zan bar wurin idona ya sauka akan Romo dake saye da rigar sanyin saƙa da baƙin jeans rigar tayi mashi yawa, ƙamshin shi ya mamaye wurin... hannun shi riƙe da plate ɗin katako da ake zuba paint 🎨 sama...ɗayan riƙe da brush...gaban shi allo da paper yana zane...

Matsawa kusa nayi na tsaya daga ɗan nesa kaɗan dashi ina kallon painting ɗin ƙaramin yaro da bazai wuce shekaru biyar ba yana bibiyar bilbilaye a wurin dake kewaye da bishiyoyi da haki mai taushi..komai na wurin green ne,sai wata mata biye da yaron su biyun farin cikinsu a bayyane yake...daga yanayin zanen zaka gane da safe ne wurin ƙarfe tara ko makamancin haka rana ta fito amma bada ƙarfi ba...

Daga ƙasa ya rubuta wani abun da ban san ma'anar shiba **(La cosa che ho perso**) abunda na rasa) 

Painting ɗin yayi min kyau sosai...'' idan kin gama kallo zaki iya tafiya!" Muryar shi ta sauka a kunne na,...Hausar shi idan dai mutum ba saurara yayi da kyau ba,zai ɗauka da yaren Italiya yake magana...abu na chakwakiya 

'' waya ce zanen ka nake kallo? ni aiki nazo yi... zanen ko kyau beyi ba... yaron daga gani bai jin magana...da nice Mamar dana kamashi na zane mashi jiki gobe bazai sake ba....fuskarshi kamar an taɓe alala kan titi kaɗan goge wannan abun..'' na ɗan matso gaba kaɗan amma cikin rashin Sa'a i tripped on absolute nothing, tafin hannayena suka damɓaru akan painting ɗin 


A wani irin slow na fara juyo da kaina ido waje na kalle shi,if looks could kill da ban zo ina baku labari ba,ƙasan idon shi har wani ja yayi tsabar takaici

Da sauri na cire hannu na, zan matsa kuma na sake cin tuntuɓe da akwatin kalolin shi na damɓara hannayena a ƙirjinsa, ya wani irin zabura kafin plate ɗin painting ɗin ya sulɓuce daga hannun shi ya sauka saman yatsun ƙafafunshi dake saye cikin baƙaƙen slippers 

Da sauri yaja baya yana tsalle akan ƙafa guda yana faɗin '' LORD GIVE ME THE PATIENCE '' idon shi kafe a kaina,ni kam nayi tsaye baki sagam ina kallon shi,mutum kamar ba namiji ba

ganin ya dena wannan tsalle tsallen yana takowa inda nake kamar dutse mai aman wuta,yasa na fara ja baya idona kamar zasu faɗo

'' ehhmm..naji kamar ana kirana bari in tafi...'' a gaggauce nabar wurin gabana na faɗuwa kuma babu wanda ke kirana fa...
__

Yau da wuri dukan mu muka gama aiki yasa mun taru a parlor muna kallon fim ɗin indiya kafin wata mai suna Nana ta canja tashar zuwa ta yan Italiya wai tana so ta koya don ta burge Romo...aiko sauran kamar mahaukata suma wai suna so su koya ɗin...aka bi aka ishemu da shegen Yaren mara daɗin sauraro...

amma fim ɗin yayi kyau..kuma naji daɗin kasancewar mu tare ba tare da anyi faɗa da hantara ba... na kuma riƙe kalma ɗaya take..wai ragazze..nifa ina ganin so suke suce ragadada,wannan abun da ake haɗawa da nama ko?

Oho..nidai idan na haɗu da Romo nan gaba zance mashi ragadada ake cewa ba ragazze ba..ehe!


***

RU'UYAA…📖



₦500 ne idan ya kammala zai koma 800

Biya ta wannan account ɗin 9138091955..Salma Aliyu opay

Shaidar biya ta ***

Autumn writes 📖🖋️





Want the next chapter?

Create a free ArewaPen account to save progress, unlock paid chapters, follow this author, and keep reading across web and the Android app.