Free chapter · Read without an account
Page 14
by Ummu~Fadeela · JUYIN LAMARI
*JUYIN LAMARI*
By
*Ummu Fadeela*
Page 14.
*Arewapen @ummufadeela01*
Ta tsugunnar da kanta kasa. Jikinta yana rawa tare da muryarta tace.
"Zan iya bada Ta...reeq maaa" ta fada da kyar muryarta tana rabe sunan.
Hallitar ta kuma kecewa da dariya har dakin ya girgiza tace. "Dangana ba'a canza mana alkawari. Alex muke so, kuma shi zaki bamu. Ki shirya rabuwa dashi anytime soon, and kada ki kuma kuskuren kai mana shi asibiti idan muna aiki a kansa. If not zaki iya rasa komai, I mean komai harda matsayinki".
Daga haka ya bace bat tamkar bai taba wanzuwa a dakin ba. Dangana ta zaro idanu ta mike tana share zufar dake tsatstsafowa daga jikinta. Duk da sanyin AC da ya gauraye dakin, hakan bai hanata jin wani irin zafi yana ketowa ta cikin jikinta ba.
Ta goya hannunta a bayanta tana zagaye dakin da tunani kala-kala.
"Alex muke so, kuma shi zaki bamu". Muryar tayi mata amsa kuwwa cikin kunne tamkar yanzu ake sanar mata.
"Ina ba zai yiwu ba. Ba zan rasa shi ba. I can't, ba zan iya rasa Boy dina ba. He's my everything, and I can't loose my post. Ba zan lamunci rasa matsayina ba koda ace zanyi yawo tsirara"
Ta dinga sambatu ita kadai. Kamar wacce ta tuna abu ta fita daga dakin a sukwane.
A main palo ta fito. Ta tsaya tana kallon hanyar da ta raba bangarorin gidan. Ta kai kallonta kan makeken agogon dake manne a falon. 'karfe 1:30 cuff na dare. Batare da dogon tunani ba, ta shiga walk way din ta kama stair case ta haura bangaren Alex.
Lokacin da ta shigo falon shiru sai sanyin AC da kamshin turare dake tashi. Still ta kuma bude wata ƙofar. Hadadden bedroom nashi mai kama da aljannar duniya ta shiga. Yana kwance saman makeken gadon, ya lulluba da fari sol din duvet yana bacci peacefully. Ta zauna gefen gadon kusa da kanshi. Tagumi tayi tana kallonsa zuciyarta tana bugawa da sauri sauri tamkar zai faso kirjinta ya fito.
Alex ya bude idanunsa a kanta. Cikin magagin bacci murya kasa kasa yace. "Mother!"
"Shhhshtt" ta fada tana dora yatsarta daya a kan lebenta. Ta dan matso kadan tana shafa gashin kansa gently tace. "Kayi addu'a kafin kwanciya?" Ya gyada kai yana lumshe idanunsa domin wani irin azababben ciwon kai ya kwanta dashi, dakyar bacci ya daukesa yana yi yana farkawa.
Dangana tace, "Ohk, oya tashi muyi wani addu'ar" dan bata fuska yayi yace "Mother" bata bari ya cigaba da magana ba ta kama kafadarsa ya zauna a tsakiyar gadon. Dangana ta rufe idanunta ta dunkule hannunta duka biyu cikin na juna, shima yayi hakan. Tsawon lokaci tana jero addu'oin kariya a cikin sunan yesu kafin su shafa, ya koma ya kwanta ta rufeshi da duvet din. Karfin AC ta rage taja mishi kofa ta koma bangarenta.
Washegari daya kasance asabar. Misalin karfe 9:30 na safe Alex ya sauko main parlour. Sanye yake da riga armless sai wando three quarter farare tas, fara sol din kafarsa sanye da silifas mai taushi na kamfanin gucci suma farare sol. Jikinsa yana tashin kamshin turaren . Fuskarsa babu fara'a ko kadan ya kai zaune kan daya daga cikin luxurious sofas dake falon ya harde kafarsa.
Da gudu daya daga cikin professional chef's dake shirya dinning area ta zo hadi da durkusawa, kanta a kasa domin kwarjininsa bazai barta kallon cikin idanunsa ba idan ana mishi magana tace. "Barka da fitowa uban masu gida..... Ya tabe fuska, cikin husky voice yace. "Hot tea, no sugar, no milk, only honey 2tea spoon."
"Yanzu za a kawo yallabai" cewar chef din tana mikewa a hanzarce ta fada babban kitchen dake main falo din. Relaxing yayi a kan sofa din yana karkada kafarsa. Alex kyakkyawan matashi ne fari sol dake tsakanin shekaru 30 zuwa 32.
A kan tea tray ta dora cup din dake ta tururi yana tashin kamshin kayan shayi masu dadi. A dan gefe kuma pure zuma ne a cikin container mai murfi. Sai tea spoon dake cikin karamin bowl ta shigo dashi, ta dora bisa table dake gefen kujerar kafin ta matso dashi duka gabansa. "The tea is ready sir" Ta fada tana dan rankwafawa kadan.
Bai ce komai ba tsawon minti biyu itama bata matsa daga wajan ba gudun kada tayi laifi. A hankali ya dago daga kwanciyar da yayi. Yatsar hannunsa ya mata pointing hanya dashi alamar 'you can leave' ya bude zumar ya zuba tea spoon biyu a cikin black tea din yana gaurayawa. Bude kofar palon akayi. Wani dattijo ya shigo. A kallo daya zaka fahimci hamshakin mai kudi ne daga yanayin suturar jikinsa.
Alex ya ajiye tea cup dake hannunsa ya mike, daidai isowar mutumin kusa dashi.
Ya rungumesa tsam tamkar yaro yace, "Welcome Dad"
Dattijon ya rikesa mai kyau shima yana shafa bayansa yace, "how you feeling now Abba, mamarka tace you're sick har anyi admitting dinka hospital. Na kasa zama na nemi jirgi na dawo in ganka." Ya sake sa yana kallon fuskarsa. Alex yace. "Iam much better Daddy. It's just a headache amma yayi sauki yanzu"
Dad ya rike hannunsa suka zauna a kan kujerar da ya tashi. Ya dauki tea cup din ya debo a spoon kamar dan goye ya mikawa Alex a baki. Haka ya dinga bashi sai da ya shanye shayin tass dama ba wani yawa ne dashi ba. Yana kallonsa sosai yace, "Abba!"
Alex ya dago kansa suka hada idanu da uban. "Abba ka daina dorawa kanka damuwa. Ka sani there is always a reason for everything daka ga ya faru a rayuwa. Damuwa da bakin ciki da masifa da sauran bad habits da kake yi would not be a solution, sai dai ya kara dagula maka lissafi ohk. Ka dinga sassautawa kanka kayi farin ciki my son"
Alex ya lumshe kyawawan idanunsa ya bude, a take suka fara kadawa suna canza kala. Ya gyada kai yace, "Yes dad" Daddy ya rike hannun Alex gam yana jin tamkar ya karbi ciwon dake jikinsa ya mayar kansa.
Da steps bibbiyu Dangana ta gama saukowa daga stairs din tamkar zata kifa ta karaso wajansu. "To me ka ajiye mini yaro kake karanta masa iyeee? Kana karanta masa yadda zai bijire mini ya dawo wajanka ne? To ba zai taba yiwuwa ba, Alex is my son, he's my only son. Kuma ni kadai na isar masa komai a nan cikin duniya."
Ta karishe maganar tana huci kamar wata zakanya. Dad ya mike tsaye ya bude idanunsa sosai yana kallonta. Alex ya dafe kansa da dukkan hannayensa. Ma'aikatan dake shawagi a falon suna aikace-aikace duk suka bar palon cikin sauri. Dad ya nunata da yatsa strictly yace "Dangana are you shouting at me?"
Tace, "eh. Nayi maka ihu, nace nayi ihun Mr Olamide Malabu."
Dad ya firgita ya zaro idanu, Alex ya mike da hanzari ya wuce part nashi.
Dad was short of words. Yayi kokarin nuna ta da yatsa a hankali yace. "Olamide Malabu?" Ta kwace maganar da hanzari tace. "Eh, Olamide Malabu, me ya rage na mutunci a tsakaninmu yanzu. Ko kadan babu, komai ya kare azzalumi mai cin amana. And don't forget Iam now a DEPUTY GOVERNOR of the mighty Lagos State, kuma governor din gobe."
Daddy yayi murmushi mai ciwo yace. "A wajene kike mataimakiyar gwamna Dangana. Amma a cikin gidan you're still Mrs Olamide Malabu, a karkashin ikona kike dole ki yi mini biyayya."
Da sassarfa ya bar wajan Dangana ta bishi da sauri tana masifa. Ganin ya shige bangaren amaryarsa Hauwa, taja tsaki tace, "bunch of cheater's" ta shige part nata.
Daddy ya zauna dabas bisa jerin kujerun da suka kawata falon. Ya dafe kansa da hannu yana mamakin halin Dangana. Yau shekaru ashirin kenan da faruwar komai, amma ta kasa cirewa a ranta. Ta kasa sakin ranta tayi rayuwa cikin salama duk da mukamin mataimakiyar gwamna da Allah ya bata. "Ya Allah " ya fada yana huro huci daga bakinsa.
Hauwa da ake kira da Mom ta iso wajan. Ta zauna a gefensa kadan tace, "barka da dawowa yallabai." Ya dago ya kalleta yace, "Barka dai Hauwa, mun sameku lafiya?"
Mommy tayi tsaki tace, "Lafiyar dai ba sosai ba, dama jira nake yi ka dawo ka shata mana layi tsakanina da Dangana..." Da sauri ya daga mata hannu kafin ta gama maganar.
"Yanzu tsakani da Allah Hauwa kuna kyauta mini. Ke da nake tunanin zan samu sassauci a wajanki amma babu. Shigowata ke nan fa, all the way from America. Ko ruwa ban samu ba sai tashin hankali? Dame kuke so inji ne."
Mommy ta tabe baki tace, "Ai duk wanda bai ji bari ba, yaji hoho." Da sauri yace, "Auren Ahlul kitabi ba laifi bane, ubangiji na ya halatta mini auren mace kirista a matsayina na musulmi."
Mommy tace, "Ana barin halal ko don kunya da tunanin me gobe zata haifar. Gashi nan ai tayi nasarar raba maka kan yayanka. Wasu suna Sallah, wasu suna tafiya coci bautar Yesu."
"Hauwwaaa" ya fada a fusace. Mikewa tayi ta shige kitchen tana fadin "Ai bani na kar zomon ba, daga fadar gaskiya?"
Alex ya shiga dakinsa yana jin kansa yana juyawa wani irin yanayi yake ji yana yamutsa jininsa. Ya tura hannayensa cikin gashin kansa yana yamutsawa. A hankali ya taka jikin wani luxury mini fridge dake ɗakin ya bude. Kwalabe ne jere reras a ciki. Ya zaro manya manya guda biyu ya koma bakin gadonsa. Zaro ido nayi ganin kwalbar giya ce. Ya bude ya fara tuttula shi a cikinsa, sai da ya shanye tas yayi jifa da kwalbar. Kwanciya yayi rigingine a kan allon bayansa, fuskarsa tana kallon pop ya watsa duka hannayensa a kan gadon.
Ya lumshe rinannun idanunsa can kasan makoshi yace, "they can't change, never change".