Free chapter · Read without an account

Chapter 9

by Rukayyat · RIKON KA'KA

RIKON KAKA

Written by 

Rukayyat (Rukyelmuaz)

YOTA

Book 1

Chapter 9

Kanta ɗauke da farantin gyada duk da kayan jikinta sun fara bushewa amma zuciyarta cikin bugawa da fargaba ta ke tsoron da ke cikin zuciyarta ya bayya har a saman fuskarta da gangar jikinta.

Duk wani yaro da ta ci garo da shi a hanya sai ta tambaya "Kai Inno na nan?" wasu su ce basu sani ba wasu ma basa ba ta amsa duk da bugawar zuciyarta haka ta daure ta shiga gida.

Ginin ƙasa ne da ga soron gidan ta tsaya tana zura kai tana leƙen cikin gidan da ta leƙa ta ga babu kowa a tsakar gidan saita dawo baya ta ɗau lokaci tana haka.

Ta sa ke leƙawa tana ƙoƙarin dawowa baya ta ji farantin gyaɗa ya tokare da bayan wani abu a raza ne ta waigo don ganin meye a bayanta haka ido ta ware don wanda ta gani batayi tsamma nin ganin shi ba.

Matashi ne wanda bai wuce irin shekara ashirin ba ko ashirin da biyu black beauty ne baƙin shi ba mai duhu bane sosai yana da dogon hanci sai kuma gefen goshin shi yana da tabo baƙi sosai ance rowa ce wai in akayi ma mahaifiyar mutum rowa tana da ciki shine ya ke fito ma yaron a jiki

"Uban me kike yi a nan da kike leƙa mana gida, ko sata kika fara ne?."

'Ni Yaya Jamilu?" Ta nuna kanta da hannunta ɗaya da yake sake ba tare da ta riƙe farantin gyaɗa da shi ba.

"A'ah ni don uban ki ko ina wasa da ke ne da kike dawo min da tambaya"

"A'a wallahi Yayan mu daga talla nike."

"Daga talla kike shine kike leƙen gida kamar sabuwar ɓarauniya."

"Ni?" ta sake tambayar shi cikin fushi ya kai ma ta duka tayi sauri ta duƙe ƙasa tana dariya ta shiga gida, bayan ta yabi yana dariya shi ma.

Gida ne ginin ƙasa ɗaki biyu ne a ciki sai ɗan ƙaramin rumbu da ke nesa da ɗakunan sai kitchen da kewaye ba wani girma gidan gare shi ba don babu wani faɗi bare girman tsakar gida.

Shigowar su ta yi dai_dai da fitowar Inno daga kewaye riƙe da buta a hannunta kallon Mairo ta ke kallon tuhuma. Da ga kallon jikinki fuskar matar zaka gane ce wa wannan mahaifiyar Mairo ce.

Inno mace ce da bata wuce irin shekaru Arba'in da Biyar ba kallo ɗaya zakayi ma ta ka gano tsantsar kamar da ke tsakanin ta da Mairo.
Sanye ta ke da wata doguwar rigar atamfa blue da design black a jiki.

"Mairo wasan ruwa kika yi da wayon ki da tunaninki?" Inno ta yi maganar ta na sa ke kurama jikin Mairo ido duk da kayan sun fara bushewa amma kallo ɗaya zakayi musu ka gane da ga cikin ruwa ta fito.

"Allah Inno ƴar larabawa ce ta yi wasan ruwa ba ni ba"

"Ahhhhh kina tare da Haisu ta ya zakiyi aikin hankali ai ba zakiyi ba"

"Inno mai kika dafa?" "Abinda kika bani ajiya tun safe kika fita yanzu ga shi ana shirin kiran sallah duk kina can shirme ke da ita Haisu ɗin ko??????

Mairo bata sake ce wa komi ba ta shige ɗaki ta aje farantin gyaɗa ko me ta tuna sai ta fito da gudu tana kiran sunan Inno da ƙarfi kamar suna nesa da juna."Inno Inno, kinsan me?" Bata jira amsa ba ta ci gaba da magana. "Yayan Haisu ya zo daga Abuja na san gobe zai tafi a bamu kayan wasa kowa da nashi kayan ƴan binni.

"To" Kawai inno ta ce don ta ɗauka kiran arziƙi ne Mairo ke yi ma ta.

"Amma Mairo wallahi bakida hankali shine kike min wannan kiran duk don saboda wannan labarin, to shikenan naji yazo lafiya ko?"

"Shikenan ni na ma koma cikin ɗaki" Mairo ta ce da hanzari ta shige cikin ɗakin, ɗaki ne ciki ɗaya sai gado da wata ƙaramar kujera duk ta tsufa yadin duk ya koɗe. 

Inno taƙi fidda kujerar saboda ta ce tarihin Baban su Mairo ne a kai ya ke cin abinci ta kasa rabuwa da aguguwa da dama a cewar ta su na tuna ma ta da tsohon mijinta.

"Mairo kinga ki iya maraicin ki ba komi bane don ƴar larabawa ta yi kema zaki ce sai kin yi baki da kowa sai Allah sai ni sai ɗan uwan ki gashinan, don Allah ki rage ɗaukar magana ni wallahi tsoron yarinyar nike ji aguguwan ta ba irin na masu hankali ba ne."

"Yo ai dama dole kiji tsoron ta Inno tunda kunyi karo bakiji da daɗi ba" Jamilu ya faɗa yana fitowa daga ɗakin shi yana wata dariya wacce ke nuna tsantsar mugunta a cikin ta.

"Kai Jamilu dole inji tsoro shiyasa kullin gyaɗar hamshi ke rabamu kullum sai na ƙulla ma ta"

"Hahahaha Ƙyal ƙyal Ƙyal Ƙyal Ƙyal Ƙyal" Haka ya ke ta jera dariya ganin dariyar bazata ƙare ba yasa Inno miƙewa ta shige ta barshi agun dariya yake har da zama akan benci ya na rike ciki.

Jin dariyar taki ƙarewa ya saka Mairo fitowa wacce duk firan da sukeyi tana jin su da sauri ta zo gurin shi.

"Yaya Jamilu don Allah ka faɗamin wai me yasa Inno ke tsoron ƴar larabawa"

"Nawa zaki biya don wannan labarin mai tsada ne"

"Zan baka gyaɗa kwano ɗaya"

"To shikenan" Kin san lokacin da ƴar larabawa ta faɗo da ke da ga saman bishiya har kika goce a hannu aka miki ɗauri?"

"Ehhhh mana na sa ni lokacin na ci daɗi har naman kaji Kaka Hasatu ta ke kawomin kullum"

"To shine Inno da taƙalar rigima ƴar larabawa ta zo gurin ki ta hanata shiga ta tsaida ta a soro."

"Inno ɗin ta hana ƴar larabawa shigowa to me ye na hanata shigowa ai ba da gangan ta yi ba ko"?

"Matsala ta da ke ba ki iya cin ribar zance ba wallahi"

"To kayi hakuri faɗamin"

"Bayan Inno ta tsaida ta a soro ta zare ma ta ido ta ce duk ranar da kika sake turomin Mairo daga bishiya sai na yanka ki na ba karnuka sun cinye kasu'suwan ki"

"Tunda Inno ta fara ma ta faɗa bata ce komi ba saima kallon gefe daban da ta ke yi ina zaune a soro ina kallon ikon Allah har Inno ta gama faɗa ta kora ta gida bata ce komi ba"

"Washe gari da safe Inno ta dawo sayen gyaɗa kawai taji an jefa ma ta wani abu a saman hijabinta yana ya wo ta saki buhun gyaɗa tana ihu, a saman layi yara suka rufarma buhun gyaɗar suna warwaso harda ƴar larabawa ɗin a cikin masu warwason gyaɗar fa."

Na dawo daga sayen rake kawai na hango Inno na ƙoƙarin cire hijabin jikinta sai ƙyarma ta ke yanda kika san ɗan mazari Allah kamar zata sume, "Kin san dai Inno da tsoron ƙadangare, ba sai na baki labari ba." Na isa gurin da gudu naga ƙadangare ne kebin hijabinta yana neman hanyar sauka nayi ma za na cire ma ta shi na yarda.

Muna tsaye Inno na maida numfashi wani yaro ya ce.

"Ƴar larabawa kika ce in muka saka ma ta kadangaren zata ruga mu bita muna ihu muna cewa a cire ma ta ƙadangare muna dariya."

Kafin ta ba yaron amsa ina jin haka naje zan ɗauki buhun gyaɗa aiko na riƙeta na ɗauke ta da mari wai kin san yarinyar nan dani zatayi rigima ƙafa nasa na taɗiye ta tafaɗi ƙasa zan cire belt in zane ta Inno ta ce In ƙyaleta to tun da ga nan Inno ke tsoron ta

Duk in a kayi gyaɗa saita kulla mata todishiyar baki"

"Amma Yaya naji ka ce ka mari Haisu to me tayi maka ai wallahi baka kyauta ba haba shiyasa dama ƴar larabawa ta ce bata son ka, bazata kawo ma kayan binni ba" Ta kai ƙarshen maganar tana miƙewa ta shige cikin ɗaki ranta duk ya ɓaci.

Kallon mamaki ya ke bin ta da shi to ya fahimci in aka bata zabi tsakanin shi da ƴar larabawa za ta iya zaɓar rayuwa da ƴar larabawa ta rabu da shi.

*********

Tunda ya shiga cikin ɗaki ya kasa bacci saboda yunwar da ya ke ji fitowa ya yi daga cikin ɗaki ya fita waje ya je in da ya aje motar shi ya buɗe ya shiga wani sauran biscuits ne ya ɗauka ya dawo cikin gida ya shiga ɗaki kwance ya ke yana cin biscuits ɗin amma ba wai don da ɗi ba sai don yunwa da ke shirin tsinka hanjin cikin shi ta raba su guri biyu yana ci ya na yatsina fuska alamar ba don daɗi ya ke ci ba. Yana gamawa ana sake kiran wayar shi WhatsApp call ganin mai kiran ne yasa ya ɗauka da murmushi cikin girmamawa.

"Hello uncle barka da rana"
"Barka son ya ka ke"
"Lafiya lau uncle"
"Daddyn ku ya ce ka zo Batsari?"
"Ehhhh na zo ina ɗaki kwance yanzu haka ma"
"Alright ina ƙanwarka"
"Tana bacci a kai ma ta ne?"
"No need kafin ka koma za'a ma ta register na Jss kunyi magana da daddy kafin kazo kuwa"
"A'a amma mommy ta faɗa min"
"Ok zan tura maka kuɗi akwai birthday gifts ka saya ma ta aguguwan da ya kamata tunda ka riga ka taho ba dama in ce Jannat ta yi siyayyar don saita fika sanin abinda ya da ce tunda ita mace ce"

"Shikenan uncle babu damuwa"

"In sun ta shi bacci ka haɗa ni da ita, wayar Kakarku taƙi shiga lafiya?"

"Ka san wayar ta ƴan gayu ce kilan mai mulkin gidan ta jefa ta wani gurin"

"Shikenan zan kira anjima in na samu time, ka kula da kanka in ta tashi baccin ka haɗa ni da ita ko na manta ina son in yi ma ta murnar ƙarin shekara don maybe ita bama ta san ta ƙara girma ba"

"Ok"

Shine abinda kawai ya ce aka kashe wayar daga ɗaya ɓangaren wata dariya ma Uncle ya ba shi wai ta ƙara shekara ita wannan ai shekarun hauka ta ke ƙarawa ba na hankali ba ta ya ma zata san ta ƙara shekara ita da kullum cikin hauka da neman ta shin hankali ta ke wannan da wa ta wahalar kashin kuɗin da uncle zai yi da gidan gyaran hali ya kaita kilan a gyara ta ko wa ya samu kwanciyar hankali.

Haisu da Kaka basu ta shi bacci ba sai da aka fara kiran sallar la'asar lokacin har ya tafi masallaci yana dawowa ya iske Kaka ta, tashi a cikin falon ya zauna, Kaka ta kalle shi. "Kai ka ci abinci kuwa?"
"Kin bani ne kin bar kyakkyawan matashi yunwa zata yi ajalin shi kina bacci shine yanzu zaki tambaya"

"Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un yi hakuri kaji wallahi bacci ne ya ɗauke ni"

Bai ƙara ce wa komi ba sai kallon Kaka da ya ke yanda duk ta wani ruɗe akan baici abinci ba ya na jin daɗin yanda ta ke kula da su, ya kan shiga farin ciki a duk lokacin da ya ke tare da ita yana jin ina ma tare suke rayuwa a wuri ɗaya murmushi ya yi ya shafa sajen fuskar shi.

Da hanzari ta miƙe ta nufi kitchen ta zubo mishi abinci shinkafa ce fara da miyar jajjage sai kifi tana shiga ɗakin ƙamshin miyar ya shiga hancin Julaibib ya wani lumshe ido a duniya yana son girkin Kaka duk da ce wa ba girkin zamani ba ne amma zai iya ce wa ya fijin daɗin girkinta akan na zamani babu wani tarka can aguguwa a ciki simple girkin gargajiya tana bashi abincin ta fita domin ta ɗauro alwala ta yi sallah.

Yana cikin abincin Haisu ta fito kanta babu kallabi tana murza ido sai turo baki ta ke bama ta lura da shi ba amma tun fitowar ta, ya kalle ta ya ci gaba da cin abinci.

"Kaka ina kike" shirun da ta ji anyi ya sa ta buɗe idonta gaba ki ɗaya suka sauka akan Julaibib da ke zaune yana cin abinci sai wani yanga ya ke kamar anyi mishi dole turo baki ta yi gaba sai kuma ta ƙura ma abincin hannunshi ido tana haɗiye yawu jin shiru ba ta sake magana ba ya sa ya ɗago idonshi ya kalle ta ya ga abincin da ya ke ci ta ke kallo.

"Kin fara maita ne bansani ba"

Murguɗa baki ta yi tana wani kallon shi a banza ce "Abincin ai na gidan mu ba na gidanku ba" Tayi maganar tana zaro mishi manyan idanunta bai ce ma ta komi ba ita ma bata sake magana ba kuma ba ta daina kallon shi ba.

"Ke yau she kika ta shi baccin"

"Kaka an cinye abinci?"

Haisu ta yi maganar tana kallon in da Kaka ke tsaye sai raba idanu ta ke tana jiran amsar da Kaka zata ba ta.

"Da rigima kika ta shi yaushe za'a cinye abinci kuma ke da cin abincin ma sai kin yi niyya kike ci shine zaki zo kina min rigima."

Shiru tayi tana kallon abincin da Julaibib ke ci duk haushin shi ta ke ji ya zo zai cinye mu su abincin gida.

"Wallahi in na ƙware sai na miki dukan tsiya kinji na faɗa miki kallon uban me kike min?"

Murguɗa baki ta yi da gudu ta koma cikin ɗaki ta bar falon.

Dariya Kaka ta yi wannan rigimar ta Haisu na bata ciwon kai wani lokacin amma ya zatayi ba'a takurawa maraya.


Want the next chapter?

Create a free ArewaPen account to save progress, unlock paid chapters, follow this author, and keep reading across web and the Android app.