Free chapter · Read without an account

CODE NAME I: NURIYYA ABDULLAHI

by Saddiqah M · NURI

NURI

By Saddiqah 📚  

BISMILLAHIR RAHAMIR RAHEEM

_In the name of Allah, the Most Beneficent, the Most Merciful._

Note: wannan qirqirarren labari ne any resemblance to real person is purely coincidental 🙏

“Mami, na shirya zan tafi. Yi mini addu’a,” ta fada tana durƙusawa ƙasa gaban wadda ta kira da Mami.

Mami ta kallota tana murmushi sosai. “Allah ya ba da sa’a, ya tsare ki. Ki kula sosai, kin ji?”

“In Sha Allah.” Ta miĆ™e tana rataya jakar makarantar nata a kafada, sannan ta fita daga parlour É—in gidan nasu. 

A tsakar gida ta haɗu da ƙaninta Afif, wanda ke bin ta da shekara ɗaya kacal. Kai tsaye ma idan ka ganshi za ka ce ya girmeta, kasancewarsa namiji. Shi kansa kuma yana acting as if shine yayan, ita kuma ƙanwarsa.

“Sai ina kuma? Ba kince baku da lectures ba?”

Ta gyada masa kai. “A’a, ba mu da lectures. Sai yanzu wai an yi fixing lecture ɗin Physiology da Anatomy da ba a yi last week ba. Kasan yanzu exams ɗin nan ya taho, kowa so yake ya yi rounding off.”

Kai ya gyada. “Sai kin dawo, Adda. Allah ya tsare.”  
Adda da yake kiranta da shi shine kawai abin da ke tabbatar da ta girmeshi ga mutane.  
“Aameen, AFIF.”

Ta nufi ƙofar gidan kai tsaye. Bayan ta yi addu’a, ta fita. Ta tuna yau ba ta haɗu da Abbansu ba ya fita kasuwa da wuri.

Gidan nasu bai da nisa da titi, don haka tana fita ta samu napep wanda kai tsaye ya kai ta BUK bayan sun daidaita farashi.

Tana shiga hall ɗin da suke da lecture, ta fito da wayarta Huawei Nova 5i ta yi dialing number ɗin ƙawarta. Amma kafin kiran ya shiga, aka kirata daga baya.

Ta juya. Idanunta suka sauka akan ƙawarta Zara. Gaisawa suka yi, sannan suka nufi empty desk suka zauna. Daidai lokacin lecturer ɗin ya shigo, hakan yasa suka nutsu sosai.

Kusan 3 hours ya yi, saboda yayi missing last class. Bayan ya gama, ya sake su suka fita. Tare da Zara suka nufi Ummah Mosque dake makarantar.

“I really don’t know why wasu lecturers din suke haka. Imagine ace sai dab da exams zasu wani matsemu da lectures,” Zara ta fada, tunda suka fito tana mitan gajiya.  
Nuri ta buɗe baki zata amsa, sai aka kira sunanta daga baya…

“NURI!”  
Tare ita da Zara suka juya suna kallon mai kiran.

Khaleel ne. Matashin da tunda ta shigo makarantar yake takurawa rayuwarta. Ta fada masa bata da lokacinsa, amma ya kasa yarda.

Ta É—auke fuskarta daga gare shi. Fuskarta dake nan ba baĆ™i ba, amma ba fararce ba, sannan ta ci gaba da tafiya.  
Zara ta bita da kallo, sannan ta dawo da kallonta kan Khaleel da ya bi Nuri da idanu.

“Zara, ki fadamini, laifin zuciyana ne da yake sonta?”  
Kai Zara ta girgiza masa.  
“To me yasa Nuri ta kasa fahimtana? Na kira wayarta, she isn’t picking. I’ve chatted her via WhatsApp, no response. She’s physically ignoring me, and it’s killing me, Zara.”

Tausayi ya bawa Zara. Khaleel yana kusa da shekara 26, shima É—alibi ne a makarantar, amma ahead of them. Yana final year, yana karantar Pharmacy.

“Ka yi haƙuri Khaleel. Nuri ba ta kyautawa, na sani. Amma kai ma kana takurawa. Ka riƙa bata space. Yawan bibiyar nan shine abin da bata so. And mind you, karatu ta zo yi, ba neman degree a soyayya ba.”

Murmushi da bai shiryawa ba ya yi. “Shikenan, zan yi ƙoƙari na rage takurawa. Amma ki shaida mata zuciyar Khaleel ta dade da mutuwa a kanta tun ranar daya fara ganinta. Ki ce mata love at first sight ke damuna.”

“Is ok, I will inform her.”  
Daga haka suka yi sallama. Zara ta bi bayan Nuri.  
Ko da ta shiga masallacin, Nuri ta riga ta tayar da sallah. Don haka Zara ta fice, ta daura alwala, ta zo tayi joining dinta.

Bayan sun idar, suka fito. Kai tsaye suka wuce wani lecture hall É—in don Anatomy. Shima sai yau din yake gaya musu.

“Nuri, akan Khaleel plz, ki sauko haka nan…”  
“Assalamu alaikum, Abba,” Nuri ta katse ta, tana amsa kiran da abbanta ya mata.

“Wa’alaikumus Salam, NURIYYA.”  
“Ina yini, Abba? Duk yau bamu gaisa ba.”

“Kirana akayi a kasuwa. An kawo kayan da muke jira. Ya makarantar, ashe kince ba lectures jiya ko?”  
“A’a, Abba. Ka ganni ma a makarantar. Sun mana fixing lectures har biyu.”

“To Allah ya ba da sa’a, Nuriyya. Ki kula da kanki sosai. Allah ya albarkaci rayuwarki, ke da ƙaninki. Allah ya kula mini da ku.”

Cak Nuri ta tsaya. Zuciyarta na bugawa saboda addu’ar Abba. Ba sabon abu bane, kusan haka yake faɗa koyaushe, amma yau ya yi mata daban. Ta kalli ƙofar hall ɗin, kamar tana jiran Abba ya shigo. Kafin ta amsa, Abba ya katse kiran kamar akwai wanda ke jiransa.

Zara ta bita da kallo. “Lafiya Nuri?”  
Kai ta gyada mata kawai, tana riƙe hannunta. Suka shiga hall ɗin, don already sun ƙaraso.

Kusan rabin lecture É—in hankalin Nuri bai nan. Zuciyarta na bugawa, tana son ganin Abba.  

Da suka fito, bayan Asr ne. Ko Zara ba ta jira ba. Nuri ta fita kai tsaye ta wuce gida.

Da sallama ta shiga gidan nasu.  
Mami dake shanya kayan Abbansu a igiya ta amsa. “Maraba da Hasken gidanmu.”
Nuri ta murmusa mata, ta Ć™araso ta rungumeta. “Mami, sannu da gida. Kawo na miki, ki huta.”  
“A’a, kin kwaso rana, Nuriyya. Je ki ajje jakar. Ga ruwa can na sa miki a flask. Ki zo ki yi wanka kiyi sallah, sai ki ci abinci.”

“To Mami. Ina biyayyena?”  
“Na aikeshi. Amma nasan maybe yana hanya.”

Kafin Mami ta gama magana, sai ga sallamar Afif tare da Abbansu.  
“Dan halak,” Nuri ta fada.  
Harar wasa ya mata. “Hala zancena kike?”

“Abbansu, har ka dawo?” Mami ta katse musu.  
“E, mun kammala. Sai gobe idan Allah ya kai mu.”  
“Sannu da dawowa, Abba.”  
“Sannunki, Nuriyya.”

Kusan tare duk suka wuce parlour. Kowa ya yi nasa dakin. Alhamdulillah, kowa yana da daki.  

Ba masu kuÉ—i ba ne, amma suna da rufin asiri sosai.

_1 hour later_  
Zaune suke bayan cin abinci. Iyaye a sama, yaran a ƙasa. Nuri da Afif suna nasu hirar, haka ma Abba da Mami suna nasu.

“Yawwa Afif, na yi magana da wurin koyon dinki. In Sha Allah this week za ka fara zuwa.”  
“To Abba, nagode.” Afif ya amsa yana gyada kai.  
“Waye ma zai bawa biyayye dinki tab, da an ga kwamacala kuwa?”  

Dariya suka yi duka. Hira mai cike da ƙauna. Ahalin da kansu kawai suke da su.

Bayan Maghrib, Afif ya wuce makarantar Maghrib da yake zuwa. Idan ya dawo, shi ne yake koyawa Nuri, domin sun riga sun yi sauka.

Abba ya dawo a interval É—in Maghrib da Isha, abin da bai saba yi ba.  
Nuri zaune a parlour tana bitar Qur’ani. Ta bi Abba da kallo bayan ta amsa sallamarsa.  
“Na tafi, Nuriyya!”  
“A dawo lafiya, Abba.”  
“Aameen,” ya amsa, ya fita. Nuri ta bishi da kallo tana jin kaman bugub zuciyarta yana sauyawa, hakan sai ya tuna mata da dazu a school. Sai ta samu kanta da bin hanyar da Abba yabi da kallo kamar tana ganinsa yana fita a sannan ne. 

*THE ORDER FOR ABBA*

Fitarshi yayi daidai da zuwan wata mota. Bai ma lura ba, sai wani farin kyalle kawai yaji an jefa masa a hanci. Ya É—ago kansa, amma jikinsa ya sake. Kafin ya fadi, wani ya tareshi. Suka É—auke shi, suka tura shi cikin baĆ™ar motar.  

Daidai lokacin Afif ke dawowa daga makarantar Maghrib…✍🏼

To be continued.....

like
comment &
share

Want the next chapter?

Create a free ArewaPen account to save progress, unlock paid chapters, follow this author, and keep reading across web and the Android app.