Free chapter · Read without an account
CODE NAME II: FU'AD ALIYYU JIMETA
by Saddiqah M · NURI
NURI
By Saddiqa
*Nnamdi Azikiwe International Airport, Abuja*
Cike da nutsuwa da haiba yake saukowa daga jirgin. Yana sanye da Ralph Lauren men’s suit all black, wanda ya fito da haskensa na Fulanin asali. Duk wanda ya gansa zai gane cewa jinin Fulani na gudu a jikinsa. Fuskar sa mai daukar ido ta hadu da kyawun gyara da tsari. Kanshi a kasa yake tafiya, amma matashin mutum ne mai ƙarfi da kuzari.
Kamshin turaren _Pure Oud_ na Louis Vuitton ya rinjayi duk wani kamshi a wurin. Ka ji nan take cewa kuɗi ne aka kashe wajen siyansa. Ba shi kadai ba ne yana tare da masu gadi, amma suna nesa da shi domin bai son suna binsa a baya a baya. Ummi ce ta nace sai ya dauke su.
Tun kafin ya isa wurin da motarsa ke jiran sa, suka bude masa motarshi qirar Lamborghini Urus. Ya shiga kai tsaye ya zauna. Shi kadai ne a cikin motar, sai direba. Ya sauke ajiyar zuciya yana kallon garin da ya dauki watanni uku bai nan. He missed this atmosphere, the intense feeling of longing for home that suddenly came over him.
“Let’s head to Guzape,” ya fada da muryar sa mai sanyi da jan hankali.
“Ok sir,” direban ya amsa, ya sauya hanya daga zuwa Maitama.
Ba tare da dalili ba ya ji yana so ya fara ganin dan uwansa kafin ya je gida. Tun da ya tafi ba su yi magana ba. Bai nemeshi ba, wanda ba a al’adar su ba ne. Suna yawan neman junansu, amma wannan karan bai nemeshi ba, ya kira shi ma bai shiga ba. Tunanin wani abu ya sameshi ya sa numfashinsa kusan ya tsaya.
“Speed the car,” ya fada, son ganin dan uwansa kuma abokinsa na ƙaruwa. A ƙofar wani gida mai alfarma direban ya tsaya yana yin horn. Ba'a bata lokaci ba domin an san motar da lambar ta.
Bai jira direba ya bude masa ba. Bayan ya yi parking ya fita da nutsuwa, ya nufi babban ginin.
*Meet DR. FU’AD ALIYYU JIMETA*
CEO and founder of NoveBuild Ltd. Da a waren CJN Aliyyu Umar Jimeta and Zuhra Mamman. He is a civil engineer and entrepreneur from Massachusetts International Technology with MSc in Structural Engineering from TU Delft and a PhD in Earthquake Engineering from ETH Zürich.
He spent four years working with Bechtel, one of the top construction companies in the world. Before founding NoveBuild Ltd, he carried out research on low-cost seismic design, which was published in the Journal of Structural Engineering. He is a registered COREN engineer in Nigeria.
At just 29 years old, he has achieved what many people don’t achieve even at 50. He is a young billionaire who owns a construction company not only in Nigeria, there's another branch in UAE. He is currently working on opening another branch in USA.
Da ya shiga falo, ya taras da Ammi zaune tana tunani mai zurfi. Har sallamarsa ba ta ji ba. Ya dube ta da damuwa. Duk da ba ita ce mahaifiyarsa ba, tana matsayin uwa a gare shi saboda al’adun Fulani. Wannan ne yasa yake jin ta a matsayin uwa kamar Ummi. Qanwa ce ga Umminsa, ko kuma kai tsaye muce usainar Umminsa ce saboda twins suke amman ba identical don sam basa kama.
A ƙasa kusa da ita ya zauna, ba ka ce shi ne wanda ke gudanar da NoveBuild ba.
“Ammi,” ya kirata da sanyi saboda yadda ya ganta.
A firgice ta dawo hayyacinta tana sauke ajiyar zuciya. Sai dai tana kallonsa sai ta ji wani rauni da ba ta taba ji ba a rayuwarta.
Da Hausa mai ɗanɗanon Fulani ta fada, “Fu’ad, yaushe ka dawo?”
Ya kama hannunta mai laushi kamar na yaro, ya tambaya, “Ammi, me ya same ki? Kin yi rashin lafiya? Komai lafiya ne?”
Ta dube shi, tana danne abinda ke ranta, ta ce, “Eh,” a sanyaye.
“Ammi, ina Pal?”
Wannan tambayar ta karya Ammi. Hawaye suka fara zubo mata ba zato ba tsammani. Kamar dai yadda yayi tunani wani abu ma faruwa ko ya faru during his absence.
“Ammi,” ya sake kiranta yana riƙe hannunta.
“Baya da lafiya Fu’ad. FA'IZ yana rashin lafiya mai tsanani.”
Da sauri ya tashi tsaye yana kwantar da kansa.
“Yana asibiti ne?”
“A’a.”
Kai tsaye ya juya ya fita da sauri. Ammi ta miqe ta bishi a baya. Ba ta so ta barshi shi kadai ya ga halin da dan uwansa yake ciki. Da sauri ya nufi dakin Fa’iz. Zuciyarsa cike take da tambaya wani irin ciwo ne za'a bar mutum agida maimakon asibiti?
Da sallama ya shiga part din Fa'iz dake nan a tsaftace sai ƙamshin turaren wuta. Ya hau sama da dan gudu yana neman ɗakin Fa’iz. He was eager to see his one and only brother kuma best friend.
Yana shiga dakin dake nan well furnished ya tarar da Fa’iz zaune gefen bango ya takure kansa. Ya dube shi sosai, bai kama da Fa’iz da ya sani ba. Da sauri ya matsa kusa da Fa'iz.
Zuwan Fu'ad kusa da Fa'iz ya fito da wata irin kama ta sosai da suke da juna. Kama data fi qarfin ace iyayensu ne kawai 'yan uwan juna. Yadda suke kama yafi ace su din twins ne irin identical dinnan da komai nasu yake iri daya. The only difference is that Fu'ad yafi Fa'iz haske amman bayan wannan babu wani abu daya banbanta Fa'iz da Fu'ad.
Yana qarasawa kusa Fa’iz ya ture shi, yana girgiza kai tare da matsawa baya kadan.
“Pal what’s this? Mene yake damunka?”
Ya juya ya tambayi Ammi, “Ammi, why is he behaving like this? Mene ya faru yayin da nake waje?”
Ammi ta matso a hankali. Tana kallonsu da idanunta da suke kama da na su. Ta tsuguna kusa da Fu’ad tana kallon Fa’iz, kuma ganin haka na ƙara karya mata zuciya.
“It started with a fever, Fu’ad. Just a fever brought him to this state. The doctors said it came from a severe convulsion that affected his brain. Now he behaves like a child. He is fighting Alzheimer’s…” ta fada tana danne kukanta.
Fu’ad ya zauna shiru yana kallonsa. Wani irin kallo mai cike da ƙauna da tausayawa. Now Fa’iz was no longer the Fa’iz he knew, the consultant doctor, the handsome and charming brother. Now he was different, but still his brother with all the good qualities he loved.
“Alzheimer’s…” Fu’ad ya fada yana tunawa da lokacin da Fa’iz ke bayani wa wani guardian din mara lafiya a asibitinsa na Maitama
“Alzheimer's is common among old people. It’s rare to see someone young fighting dementia or Alzheimer’s. It causes memory loss and loss of social control. The person starts acting like a child, needing help with basic tasks, becoming emotionally impulsive, and not understanding consequences.”
Zuciyar Fu'ad na bugawa da sauri yake tuna sanda Fa'iz yake cigaba da yiwa mutumin bayani cewa, “Alzheimer’s has no cure yet. We can only manage the symptoms with medication and therapy.”
“Ammi, who is taking care of him? I mean, who is handling his therapy?”
“A therapist from Cleveland Clinic USA, in collaboration with his clinic.”
Fu’ad ya tashi ya kusanci Fa’iz. Fa’iz ya dago, ya kalle shi amma bai gane shi ba. Ya ture hannunsa yana ƙoƙarin tashi, amma bai iya ba. Fu’ad ya ɗaga shi da sauri ya kai shi gadon sa.
“Something is not normal, Ammi. A fever alone does not cause Alzheimer’s. I’m not a doctor, but living with Fa’iz makes me think like one. A one-day fever cannot bring this.”
Ammi ta tashi tana kuka, “Fuad, Fa’iz forgets easily. The doctor said that’s the main symptom of Alzheimer’s, memory loss. Fa’iz has forgotten everyone… even you and I.”
Tausayin Ammi ya sake cika zuciyarsa fiye da dazu, ya rasa me zaiyi ya tausashe ta. He just found himself hugging Ammi. Sai dai a cikin rungumar akwai wani abu da bai taba ji ba ga Ummi, wani irin attraction sosai yake ji towards her. He patted Ammi’s back quietly, not knowing what to say to a mother clinging to the only hope she had.
Ringing din wayarsa qirar Samsung Z fold7 ya jawo hankalinsu, Ammi ta bar shi ta nufi Fa’iz. Ummi ce ke kira. Ta san ya dawo, kuma shirun da taji ya sa ta kira.
“Assalamu alaikum, Ummi,” ya fada.
“Where did you went from the airport, Fu’ad?” Ummi ta tambaya kai tsaye ba tare da ta amsa mishi sallamasa ba.
“Ummi, Fa'iz has been sick for three months and you didn’t tell me.”
Ummi ta yi shiru. Ta san ta yi laifi, amma Boddo (Ammi) ce tace kar a faɗa masa domin ya kammala abin da ya je yi.
“I’m sorry, Hayaty.”
“I’ll come back, Ummi, but not now. Bloody needs me here. I should be with him.”
“But I want to see you, Hayaty. It’s been three months.”
Shi kansa yana son ganinta. Ita ce mahaifiyarsa wadda ba ta raba ƙaunar sa da wani. Idan ya ce ita ce rayuwarsa, bai yi ƙarya ba.
Ya juya ya kalli Fa’iz dake ture hannun Ammi yana magana ƙasa ƙasa.
“Hayaty, you're quiet. I’m waiting for you, I prepared your favorite meal.”
Kallon Ammi dake goge hawayenta Fu'ad yayi besides her is Fa'iz, his only brother suffering from Alzheimer's. Thoughts kept running through Fu’ad’s mind. Ammi was struggling alone for her only son. Why wasn’t Ummi there for her?
Should he leave Ammi alone with Fa’iz even though there was a caregiver? It felt like too much for her, duk da cewa daddy yana nan
But the truth was, it was Dr. Fa’iz Aliyyu Ardo they were talking about. After Ummi, no one loved Fu’ad more than Fa’iz. Fu’ad believed Fa’iz would give his life for him. And now they had hidden his illness from him.
Now that he was back, was it right to leave him alone? Fa’iz had been fighting Alzheimer’s for three months without him.
“Ummi, I can’t leave Fa’iz alone. Fa’iz needs me,” ya fada a hankali.
Ummi ta tashi da sauri tana kallon wayar, ta tabbatar Fu’ad din ne yake cewa ba zai zo yanzu ba. Fu’ad chose his brother over her.
To be continued…
#like
#comment
#share