Free chapter · Read without an account
THE PROMISE OF SORROWS
by Saddiqah M · NURI
NURI
By Saddiqa.
Ya tabbata a komai Boddo (Ammi) ce a gabanta. Su din ‘yan biyu ne da sam basa kama. Ummi sunanta Zuhra yayin da Ammi sunanta Zahra, amman suna kiranta da Boddo, mai kyau, kasancewarta kyakkyawa sosai. Tun suna yara kyan Boddo yake damun Ummi. A tunanin Ummi tunda sun kasance ‘yan biyu, twins and all, ya kamata kyansu ya kasance iri daya, ko kuma tunda itace babba tafi Ammi kyau.
Tun suna yara kowa Ammi yake so, it’s not like people didn’t love her. A’a, Ammi ta fita hankali da nutsuwa sosai. Kowa zancensa Boddo ne, ba Zuhra ba. Bata taba nunawa Ammi komai ba, ko a fuska, sai dai gradually that resentment started building into a real hatred for Ammi. Tun tana son dannewa har hakan ya fi karfinta, ya zamana kaf duniya babu wadda ta tsana sama da ‘yar uwarta Boddo.
Yanzun ma da Fu’ad yace zai zauna tare da Fa’iz yayi mata kama da hatta dan cikinta yafi son Boddo da abinda ya shafeta ne akanta, wanda sam ba haka abin yake ba. Ba wannan ba ma, babban abinda yafi tsayawa Ummi a rai shine yadda Fu’ad da Fa’iz suke kamar da ko ita da Boddo basa yi. Ta so ace danta yafi kyau, sai ya kasance kyan nasu yazo daya. Tunda kamarsu daya babu wanda zai fi wani kyau tako ina. A abu daya ne taji dadi, daya kasance Fu’ad ya mugun ninka Fa’iz kudi na wuce misali kasancewarsa tsohon ma’aikaci a Bechtel kamin ya gina NoveBuild.
Bawai Fa’iz bai da kudi bane, a’a shima yana da nashi kudin sosai ma, sai dai not on Fu’ad’s level. Ko yanzu da Fa’iz bai da lafiya bai dameta ba sam, duk da tana zuwa dubashi akai-akai ma kuwa, kuma ko ba taje dubashi ba zata kira Ammi a waya.
Ummi tun farko irin mutanen nan ne masu son ace a komai sune a gaba, the type that always wants to be first, masu son kansu na wuce misali. Amman kasancewar Boddo ya dakile mata wannan damar. Ammi ta fita a kyau, ta fita a hankali, ta fita farin jini, she was just popular like that. Abubuwan da Ammi ta fita suna da yawa, hatta da miji Ammi ta fita, don kuwa mijin Ammi ya ninka nata mijin a kudi da komai kasancewarsa tsohon ambassador sannan dan kasuwa.
Da kallo tabi wayar nata. "Fu’ad choose Boddo and her son over me." Abin nan ya kasa barin ranta, ya tsaye mata sosai. Da ace Fu’ad ya san halin daya saka Umminsa da ba haka ba. Kasancewarsa da mai biyayya, he was meant to be obedient.
Sam Fu’ad babu ta inda ya debo halin Ummi, ya fita kyan hali nesa ba kusa ba, gashi yazo sam a kammani ma bai debo Ummi ba. Yafi kama da Boddo dai da Ummi ta tsana. Har akwai lokacin da idan ta kalli Fu’ad sai taji dama ta barwa Boddo shi saboda yadda duk idan ta kalleshi sai taga fuskar Boddo a tare dashi. Amman idan ta barwa Boddo Fu’ad ita bata da wani nasara knn, she’d have lost completely. Boddo zata cigaba da zama a samanta, Boddo zata cigaba da zama mai nasara akanta.
Duk wannan abun ita kadai take damun ranta akai. Don kuwa yadda Ammi ta dauki Ummi kamar uwa tunda ance babbar ya uwa, the older one is supposed to be like a mother. Bata duba tare aka haifesu na dan mintina kawai, Ummi ta rigata zuwa duniya ba.
"Me zanyi na baqantawa Boddo rai, how do I hurt Boddo’s heart? Me zanyi da zai qunsawa Boddo baqin ciki, make her miserable? Ina so Boddo ta kasance cikin baqin ciki har ranar da zata mutu. Zan so zuciyar Boddo ya buga da baqin ciki. Allah yasa kada Fa’iz yaji sauqi. Allah yasa ya dawwama a mahaukaci." Ta fada da dukkan zuciyarta tana jin she’ll go to any length as long as it will breaks Ammi’s heart.
Ammi ta tare mata abubuwa da dama ciki harda masoyinta da take masifar so. Bata ga dalilin da zaisa taso Ammi da abinda ya shafeta ba. Duk da ba zata taba bari Ammi ta gane ba, amman she swore she’d make Ammi’s life bitter, tayi alqawarin baqin ciki ne zaiyi silar mutuwar Boddo!!!
NURI'S POV.
Hutun session su Nuri suke yi, they were on break from school, hakan yasa har bayan yanzu one month and a half basu koma ba. Zuwa yanzu sun saba da rashin Abba duk kuwa da cewa yana maqale a ransu. Ba zasu manta dashi ba.
Nuri ta farfado sosai daga yanayin da suka shiga na rashin Abba, duk da cewa sanyinta ya ninka na da sosai, she’d gotten colder too. While Mami is suffering in silence, Afif ya samu wani scholarship offer da Abba ya cike masa tun kamin bacewarsa. Ya samu gurbin karatu a Technical University of Munich, Germany. Zai karanta Aerospace engineering kamar yadda yake so.
Rnr da suka tura masa message din ta email dinsa bai nunawa kowa ba, kasancewar ya yankewa ransa cewa ba zai je ba. Don ba zai iya tafiya ya bar Mami da Nuri su kadai ba, duk kuwa da yana son karatun.
It was Saturday again, hatta Afif yau yana gida bai je shagon dinkinsu da yake zuwa ba. Suna zaune a parlour ne dukkansu su ukun. Afif yana danna waya while Nuri tana goge kayan sakawarsu da iron saboda akwai wuta.
"Nuriyya ya kamata kuje ku gaida Inna, kwana biyu bata leqo ba."
Kallon Mami Nuri tayi tana cigaba da yin gugarta tace "amma Mami...."
"No buts Nuriyya, just do as I said. Inna kakarki ce, ba a canzawa tuwo suna."
Kai Nuri ta gyada tana cewa "shikenan ki fadawa wannan sarkin taurin kan, kin san halinsa."
Kallon Afif da yake danna waya Mami tayi, sam hankalinsa baya kansu, bai ma san me suke cewa ba.
"Afif."
Da sauri ya kalli Mami yana cewa "na’am Mami."
"Cewa nayi in Allah ya kaimu gobe kuje ku gaida Inna, kwana biyu bata leqo ba."
Wani iri yayi da fuskarsa yana cewa "she doesn’t even like us Mami me yasa zamu je?"
"Kul, I don’t want to hear that again, even as a joke."
Kai ya gyada kawai yana jin zai je ne kawai don Mami, ba don komai ba.
Nuri dai bata sake cewa komai ba, gugarta kawai takeyi. Mami sai kallonta takeyi. Idan ta kalli Nuri sai ta kalli Afif, sam babu wanda ya lura da ita.
Bata san mene yasa take jin a ranta kamar akwai wani abu da zai raba su ba anan gaba. Tana addu’a Allah ya taqaita musu jarabawarsu nan gaba, ease whatever trial is coming.
Yadda ta fahimta sam Nuriyya ba mai dauriya ce ba, she’s never been patient. Abu kadan ne yake canza mata tunani. Ko acikin mata raunin Nuri daban yake, Nuri breaks differently.
"Biyayye wai kuwa har yanzu basu baka admission bane?"
Yi yayi kamar baiji Nuri ba, yana sake yin qasa da kansa.
Mami ta kalleshi tana cewa "amman dai you can hear her talking to you, right Afif?"
"Na’am Mami, me kika ce?" Kallo mai kama da harara Mami tayiwa Afif, don tayi imanin yaji Nuri yana sane. Tana mugun gane duk wani motsi da yaranta suke, kamar tana karantar zuciyarsu ne.
"Ko dai ka samu kake boyewa wani, Kmr you’re hiding something from us?" Mami ta tambyeshi, Nuri na qoqarin kashe socket don ta gama gugar ta kalli Afif da yayi saurin ware idonsa dake nan sak irin na Nuri, yace "a’a fa Mami."
"Karya kake Afif, stop lying." Mami ta fada kai tsaye tana miqa masa hannunta tace "miqo wayar nan."
Wani kallo yayi wa Nuri, irin kallon dake nufin duk kece kika jawomin. Ta dauke kanta tana yin murmurshinta mai mugun kyau da sanyi.
Kamar mara laka ajiki haka ya taka ya kaiwa Mami wayar, yana jin yau da ace ya girmi Nuri babu abinda zai hana ya hukuntata.
Amsa Mami tayi kai tsaye ta shiga email dinsa. Bata sha wahala ba kasancewar email din da TUM suka turo masa shine a farko. Kai tsaye ta shiga ta karanta.
Wani harara ta dago ta zabga masa tana cewa "since 2 weeks da suka wuce Afif, you’ve been hiding this from us. Da Nuriyya bata tambayeka ba, da shikenan zaka shashantar damu kenan?"
Qasa yayi da kansa yana sauraren Mami.
"Meye dalilinka na kin fada mana? Next week ya kamata ka tafi Afif."
Kansa har yanzu yana kasa, yana so Mami ta gama fadan sannan ya fada mata nasa dalilin.
"I’m talking Afif."
Wani kallon abin tausayi ya dorawa fuskarsa, like he wanted her to feel sorry for him.
"Don’t look at me like that." Mami tayi saurin fada, don bata son suna yi mata irin wannan kallon, yana sa tayi musu abinda suke so ne.
Dariya Nuri taji tana zuwar mata, don haka ta toshe bakinta da sauri.
Wani kallo Afif yayi mata a shagwabe yana cewa "Mami kinga Adda ko?"
Kallon Nuri Mami tayi tana cewa "stop it Nuriyya, this isn’t funny. Afif here is playing with the chance Allah gave him."
Kai Nuri ta gyada tana danne dariyar da yake zuwa mata.
"Afif I need to know why you didn’t tell us."
Yana turo baki kaman qaramin yaro yace "Mami Abba baya nan..."
"Afif not now, ba yanzu ba, don’t bring that up." Mami ta katsehsi tana son dauke kanta daga kallonsa. Zuwa yanzu ta fara haqura da Abba. Jikinta yana bata kaman this might be the end of the story tsakaninsu da Abba.
Nuri tayi kasa da kanta sosai saboda yau ce rana ta farko da taji raunin Mami ya bayyana a fili sosai.
"Afif zaka je Munich, you’re going to study there Afif. Wannan shine burin Abbanku Afif."
"Burin Abbanku" ba iya Afif wannan kalmar ta tsayawa arai ba, harda Nuri.
Idan har wannan shine burin Abba, to tabbas zai je Munich, zai yi karatu a TUM. Zai tabbatar ya cikawa Abba wannan burin.
"Zakaje ko Afif? For Abba’s sake?"
Da sauri ya gyada kai yana cewa "eh Mami, zanje In Sha Allah."
Rungumeshi Mami tayi tana cewa "nagode Afif, Allah yayi maka albarka." Ya amsa da amin.
"Mamiii" Nuri ta kirata da muryar yarinta sosai.
Duk kallonta suka yi, ganin yadda ta shagwabe fuska yasa duk sukayi dariya, don sun san kishin Afif ne ya motsa mata.
"Mami kin rungumeshi, kin saka masa albarka, ni baki yi min ba."
Gwalo Afif yayi mata yana cewa "kishiyata." Rankwashinsa Mami tayi tana cewa "gidanku Afif."
Murmushi Nuri tayi, Mami tace "oya come here Nuriyya."
Da sauri ta miqe ta qarasa waren Mami ta rungumeta tana cewa "Allah ya albarkaci rayuwarki." Tare suka amsa da Aameen, Afif ya qaraso ya rungumesu duka ta baya.
"Zaku ballani ne?" Mami ta tambaya tana zare jikinta daga nasu.
"Mami yaron nan me nauyi kalleshi fa." Nuri ta fada tana kallon Afif dake bayanta. Baki ya tabe yana dauke kai yace "tabarkalla Masha Allah, kedai da mayya ce da tuni kin cinyeni."
"Yo kai, idan ni mayya ce ai kurwarka ba dadi za tayi ba."
"Zaku fara ko?" Mami ta katsesu.
Miqewa Afif yayi yana nufar dakinsa yace "gwara ma na tafi in rabu da this snoop, my witch."
Harar bayanshi Nuri tayi da idonta kaman zai fadi tana cewa "nima gwara ka tafi, na dawo daga ni sai Mami."
Kallon Nuri Mami tayi ba tace komai ba. Bata san dalilin da yasa taji maganar tasu wani iri ba. Idan wani abin ya faru fa? Zuciyarta ya fara raya mata.
Da sauri ta kawar da tunanin a ranta. Zata qarfafa musu gwiwa ne dukkansu, ba wai sace musu ba.
Ta fara tunanin yadda zasuyi da rayuwar ne kuma. Suna da kayan abinci enough wanda zai kai musu 6 months nan gaba. Ita kanta akwai kudi a hannunta wanda take amfani dashi wajen kula da gidan, sannan Afif ma duk kudin dinkinsa akansu yake tafiya.
Yanzu babu Afif, by next week zai tafi Munich. Zasu dawo daga ita sai Nuri. Me yasa take jin kamar suna shirin rabuwa ne daya bayan daya? Abba ya bace, Afif zaiyi nesa dasu har sai ya gama karatunsa nan da shekara uku zuwa hudu.
Ba wannan ba. Damuwarta shine yadda zasuyi da registration din Nuri. Tasan nan da wani month din zasu koma makaranta. Idan ta tuna bata da wani hanya da zata biyawa Nuri kudin makaranta, ta kanji kamar tayi kuka.
Ba zata so karatun yaranta ya salwanta ba sam, she can’t let their education fall apart, saboda suna da burin suyi karatu mai zurfi ita da Abba. Me yasa take ji kamar wannan burin nasu ba zai cika ba?
To be continued....
#like
#comment
#share