Free chapter · Read without an account

HALAL REJECTION I

by Saddiqah M · NURI

NURI


By Saddiqa 






Immediately after Maghrib Afif ya shirya ya tafi islamiyyan daren da yake zuwa while Nuri ta zauna a dakinta tana yin tilawarta as usual. 

Bata dade da farawa ba akayi knocking kofar gidan. Da farko bata ji ba sai daga baya sannan, miqewa tayi tana ajiye Qur'anin dake hannunta. Tana fita parlour ta tarar Mami ta rigata fita bude kofar don haka kawai sai ta koma ta zauna tana cigaba a inda ta tsaya. 

Ba wani jimawa Mami ta shigo dakin tana cewa "Nuriyya kije ana nemanki"


Wani ware wannan idanun nata masu haske tayi tana cewa "a ina?"


"A waje mana."



"Mami mistake ne hala bani Nuriyyan ba."



Wani banzan kallo Mami tayi mata tana cewa "don't let me repeat myself Nuriyya. Na baki minti biyar, don Allah ki qara minti daya akai kiga yadda zanyi dake agidan nan." Mami na kaiwa nan ta juya ta fita.



Da yake kuka sam bai da wahala awurin Nuri tuni ta fara hawaye aranta tana tunanin waye wannan. Ganin tunanin babu inda zai kai ta yasa ta miqe don tasan muddin ta qara minti daya akan yadda Mami ta bata zata gane kurenta kamar yadda tace. Mami bata da fada sam sai dai ta mugun iya tafi da yaranta sosai. Ta san Nuri sam ba zata saba lokacin data bata ba. Hakan yasa tace idan ta qara zata hukuntata, tayi hakan ne kuma don karta kawo mata wani excuse.



Miqewa tayi tana share hawayenta tace "ko waye ban yafe ba.." da wani kalar muryar shagwaba ta fadi hakan kamar wata yarinya.



Kallon jikinta tayi already hijab ne ajikinta tunda tayi sallah bata cire ba sai kawai ta fita a haka don shigarta baiyi muni ba. Hasalima hijab din kyau yayi mata sosai kasancewar kalarsa wine sosai ya fito da baiwar kyau da Allah ya mata.



Flat shoe dinta baqi kawai ta dauka ta sawa kafarta ta fita tana tura baki. Kana ganin yadda take yi kadan Kiris take jira ta fara wani kukan.



Tana fita kofar gidan ta tsaya tana son ganin waye tunda bata ga kowa ba. Daga nesa kadan dasu ta hangi babur qirar lifan. Tana tsaye bata motsa ba taga mutumin ya qaraso, da yake babu wani hasken arziqi a waren bata gane waye ba har sai daya qaraso wajenta sannan ta gane.



It was Khaleel, her stalker. A time din Nuri ji tayi dama ta iya masifa tayi masa ko zai rabu da ita. 


"Amincin Allah ya tabbata ga zuciyar da bata nufar kowa da sharri sai alkhairi."



Dauke kanta daga kallonsa tayi, instead of ta amsa mishi sallamar da Hausa kaman yadda yayi mata sai ta amsa da "Aameen Wa'alaikumus Salam."



"Barka da dare Nuri." Kamar ta share shi sai akayi sa'a sam bata iya wulaqanci ba.



"Barka da dre Khaleel, ina...."



Da sauri ya hade hannunsa duka biyun a ware daya yana cewa "for Allah's sake Nuri, karki bani uzuri. For this time only, yau daya Nuri don Allah ki tsaya kiji abinda na zo dashi don Allah."



Ba zata iya ka hadata da Allah taqi yin abu ba don haka ta gyara tsaiwarta tana cewa "kayi sauri akwai abinda nakeyi acikin."


"Thank you Nuri." Sai yayi shiru kamin ya dora da "Nuri I'm in love, I fall for you. Ba wasa nake ba Nuri. I want to marry you."



Da sauri Nuri ta katsheshi tana cewa "Allah sarki Khaleel ka makara. An riga an bada ni. Wannan shine main reason da yasa naqi kulaka ba wani abu ba."



Wani irin bugawa zuciyar Khaleel tayi da sauri yace "don Allah idan kin fada ne saboda na dena takura mki kiyi haquri wallahi zan jiraki, I will wait for you har zuwa sanda kika shirya karbata."



"Kayi haquri Khaleel."



Rasa abin cewa yayi don haka yayi shiru. Ganin baida abin cewa sai ta katse masa tunani da "bara na tafi Khaleel. Nagode da soyayya. Allah y zaba maka wadda ta fini alkhairi."



"Kece alkhairina Nuri. Nayi imani bazan samu wata wadda ta hada qualities irin naki ba."




Juya tayi tana cewa "sai anjima Khaleel."



Da kallo ya bita yana jin kamar bita har cikin gidan yayi mata magiya. To amman within all this years wanne kalar magiya ne baiyiwa Nuri ba. 




Duk lokacin da yace zai haqura da ita sai yaji kamar ba zai iya ba. Zuciyarsa taqi basa hadin kan rabuwa da son Nuri. Shi kansa bai san ya akayi ya fara sonta ba. Ko yau ma da kyar ya samu ya lallaba zara ta bashi address din gidansu. He loves Nuri for Allah's sake. Baijin da gaske akwai wata, someone like her out there. 



Nuri na shiga gidansu ta rufe kofar ammn ba duka ba don tasan biyayyenta ya kusa dawowa.



Bata tara da Mami a parlour ba kamar yadda da zata fita bata tarar da ita ba. Kai tsaye dakinta ta wuce ta dauki wayarta tana zama agefen katifarta. 



Zara ta kira don ta tabbatar Zara ce zata bawa Khaleel address din gidansu. Bugu biyu Zara ta dauka kamar dai daman tana Jiran kiran.



"Assalamu alaikum best ykk."



"Wa'alaikumus Salam, hold your greetings best ba naso, cut the crap, waye yace ki bawa Khaleel address din gidanmu?"


"Come on best. Khaleel truly loves you, Billah da gaske yake. Just give him a chance mana Nuri. You've never be in love just give it a try kiji yadda yake wallahi da dadi."


"To hell with you Zara, to hell with the love da kike magana akai..."


"Uhmmm kinga ya takurawa rayuwata best, bani yake so ba amman kullum cikin kirana yake yana roqona ni wallahi tausayi ma yake bani."



"Zara mai zai hana ki maye masa gurbina, Zara keda Khaleel zaku fi dacewa akan dani. You're a perfect match for Khaleel."


"Allah dai ya sakamin Nuri. Wallahi sai Allah y sakamin. Ban san bakya sona ba sai. Shikenan kije keda Allah. "



"Ke Allah fa ba abin wasa ne ba kike hadani dashi."



"Nuriyya kisan yadda zakiyi da Khaleel nikam na zare hannuna aciki. Kuma ki gama wulaqantashi a qarshe kizo ki aureshi."



"Wallahi sai dai ke, ni me zanyi da wani Khaleel. My prince charming is coming."




Wani tsaki Zara tayi tana cewa "kinga idan baki da abin fada zan kashe wayar chatting nakeyi da Habibi. Ke naga dutse ce."



"Dutsen uhud ce. Best Billah duk ranar da kika sake min irin abinda kika yimin yau zan baki mamaki."


"Kin dade baki bani mamaki ba best ina jira. Munasira wataqila ma azuciyarki ji kike idan ba Khaleel ba sai rijiya...." 



Wani takaici ne ya qule Nuri, Zara ta iya cusawa mutum haushi. Gashi duk din su basu wani ita fushi ba bare wani yayi fushi da wannan.



"Allah sai dai ke...." Ji tayi zara tayi disconnecting Kiran don tasan ta gama kunna Nuri. Ai kuwa ta kunna ta don Nuri ji tayu dama suna tare ne babu abinda zai hanata rufe zara da duka.



Kiran sallahr Isha ya sakata ta miqe a nutse tana nufar toilet din dake dakinta. Alwala ta dauro ta fito ta nufi waren abin sallarta dake shimfide har sannan ta tayar da sallah. Isha, Shafa'i da wutiri tayi kamin tayi addu'a ta miqe tana nade abin sallar. Wayarta ta dauka tana fita parlour.




Afif ta tarar akan sofa din dake dakin har ya dawo daga masallaci.



"Biyayye inzo ayi karatun yanzu?"



"Ki bari anjima inada abinda ya fiki muhimmaci Adda." Indai tsokana ce Afif gwani ne a wannan fannin.



Yi tayi kaman bata jishi ba ta nufi kitchen kai tsaye. Ta lura so yake ta biye masa ita kuwa ba zata yi ba daman yanzun nan dayar 'yar uwartasa ta kunnata. Ruwan mai sanyi ta dauko a fridge sannan ta fito.



"Adda zo muyi karatun." Yanzun ma dai bata kulashi ba ta miqe ta nufi dakinta ta kwaso littattafan da yake koya mata, kamar dau miskilancin nata ya motsa.



Fitowarta yayi dai dai da Mami ta fito. Zama tayi a qasa kusa da Afif daya zamo qasa ganin Mami ta zauna akan kujera. 



"Wanne zamu yi Adda am?" Duk saboda ya kulata don haka tayi masa banza sai cewa tayi "mu fara Mukhtarul Hadith tunda saura half page a saukeshi."



Kai ya gyada yana cewa "your wish is my command." Nan ma Nuri tayi banza dashi. Mami dai kallonsu take cike da so da kauna tana godewa Allah daya bata su.



Littatafai uku ya koya mata, Mukhtarul Hadith, Risala sai Bugyatul Muslimeen. A qarshe ne daya gama sai ya kalli Mami yana cewa "Mami kamar Adda tun tana yarinya kun bayar da ita ko?"



Da kallo Mami ta bishi, kallo irin na ban gane ba. Nuri kam kura masa ido tayi tana son gane inda ya dosa.



"Eh naga duk sanda wani yake sonta haka take ce masa, da na zata fada take amman duk wanda zan hadu dashi haka yake cewa. Dazu ma da na dawo na tarar da wani yake tambayana wai dagaske an bayar da ita."



Da ace ya kalli kalar kallon da Nuri take yi masa da tuni yayi shiru. Sai dai shi kansa yana sane yake fadar hakan kamar dai ya gaji da halin nata ne.



"Nidai Mami idan tayi kwantai wallahi a masallaci zan bada sadakarta..." Mami taso tayi dariya amman ta mugun dakewa, yadda Afif yake maganar kamar wani baban Nuri.



Bai ankara ba sai ji yayi Nuri ta kwada masa remote dake kan centre table. Ta sake kai wani attempt Mami ta katseta tana cewa "if you dare touch him again ranki zai bala'in baci Nuriyya."



Kasa tayi da kanta tana jin mai rabata da Afif yau sai Allah.



"Bansan baki da hankali ba Nuriyya sai yau. Ko da yake ban sani ba ko akwai wani wanda kika bawa kan naki da kike cewa an badake. Uban waye ya bada ke Nuriyya."




Hannu ta fara yarfewa tuni har hawayenta masu arha sun fara bin fuskarta. "Mami wallahi...."



"Shut the hell Nuriyya. You're very stupid."



Kuka ta fara yi yanzu kam da gaske. Rankwashinta Mami tayi tana cewa "me nayi mki zaki saka ni agaba da kuka. Daga fadar gaskiya. Ke ba za'a fada mki gaskiya ba kenan. Ya Allah, imagine wai an bada ke, uban waye ya bada ke ina tambyarki."



Da farko Afif fadan da Mami take yi mata yayi masa daidai. Sai dai by now sai ya fara da na sanin fadawa Mami dayi. Baiso yaga Nuri tana kuka sam. Do. Haka sai cewa yayi "uhmmm Mami kinga ma Adda ai yarinya ce kuma fa kamar da gaskiyarta gwara tana cewa haka tunda makaranta take yi."



Wani cable Mami ta jawo tana shirin zabgawa Afif, da sauri ya miqe aguje ya fada dakinsa. Mami ta bishi da kallo tana cewa "da ka tsaya ai, kai me 'yar uwa ba za'a yi mata fada ba ko? Hadaku zanyi na zane tsaf, na lura gani kuke kamar kunfi qarfin duka. To baku fi ba, na zaneku tsaf ba komai ne a wurina ba don gidanku."



Sai ta dawo kan Nuri "sannu Nuriyya, wadda ke da iko da kanta."



Kai Nuri ta girgiza da sauri tana cewa "Mami kiyi haquri bazan sake fada ba, Allah."




"Kima sake Nuriyya. Bance ki dena ba, ki cigaba kinji. Inaga jiqaki zanyi a ruwa in sha." Sai Mami ta riqe kunnen Nuri tana cewa "listen attentively, duk ranar da kika sake fadin haka ma ko waye I will beat the hell out of you. Ni bance ki fasa ba. Don Allah ki sake. Tashi ki bani ware."



Miqewa Nuri tayi da sauri kai tsaye ta wuce dakinta tana kuka sosai zaka rantse zaneta Mami tayi.




Kai kawai Mami ta girgiza aranta tana tunanin sai yaushe Nuri zata san ta girma in next month zata yi 19 amman look at her. Ta lura kallon yarinya takewa kanta har yanzu. Kawai look at yadda take kuka kamar wata baby. Tayi imanin duk wanda ya auri Nuri zai sha fama dan gaske. Shagwababbiya ce lamba daya wadda kuka sam baya bata wahala. Abu kawai take nema bata gani ba kuka take yi masa. Bugewa kadan tayi kuka takeyi, atimes kallon banza kayiwa Nuri zata iya yi maka kuka. Sakaliya ce lamba daya, kuma bawai haka aka raineta ba, a'a sam kawai a haka halittarta yake....



   
To be continued......




#like
#comment
#share

Want the next chapter?

Create a free ArewaPen account to save progress, unlock paid chapters, follow this author, and keep reading across web and the Android app.