Free chapter 路 Read without an account

THE BALCONY VOW

by Saddiqah M 路 NURI

NURI




By Saddiqa
 


FU'AD'S POV


Juyawa Ammi tayi ahankali ta sauke idonta akan Fu'ad dake kallon wayarsa. Shi kansa sai yaji kaman bai kyautawa Umminsa ba. Yasan tana matuqar son ganinsa yau din just like he does. Zaije bawai ba zaije ba amman yana son a samo mafita wa Pal dinsa. 


"Fu'ad you have to go back home right this instance. Adda needs you there. Fa'iz is ok and will be ok. Dawowarka kenan Fu'ad."


Da wannan idanun nasa masu mugun haske ya kalli Ammi. Da har kamar zaiyi magana sai ya gyada mata kai kawai yana 茩arasawa kusa da ita ahankali. Kasa ya durqusa agabanta yana cewa "Ammi you're alone yanzu, babu wani mai taimaka miki da kula da...."


Da sauri Ammi ta katseshi saying "no more excuses Fu'ad. Nasan Adda will feel bad, inaji idan nice bazan iya jura ba Fu'ad. My son away from me for 3 months and now Ka dawo kana cewa...."


"Ammi ba wai ba zanje ba I will go for sure. Is just that inason a samu solution for my Fa'iz...." Ya qarashe Yana kallon Fa'iz daya kwanta.



Murmushi Ammi tayi masa "ok kaje to ka dawo zuwa gobe ka huta nasan."


Da ido yabi Ammi hearing her saying ka dawo gobe, Da shine Fa'iz bazai mai haka ba. Amman duk yanzu yasan babu mai fahimtarsa.

Miqewa tsaye yayi yana cewa "as you said Ammi, na tafi. Allah ya bashi lafiya."


"Aameen Fu'ad." Da kallo Ammi tabi bayan Fu'ad har sanda ya fita. Ajiyar zuciya ta sauke ahankali tana dawo da kallonta kan Fa'iz da har bacci ya daukeshi. Shiru tayi many thoughts running in her mind. Kamin ta miqe itama ta fita....


______________


Yana fita duk guards dinshi suka miqe. Tsaki yaja qasa qasa, dole ma ya sallamesu idan zaije office sa riqa zuwa amman bazai lamunci ko yaushe suna tare dashi ba.


Cike da wannan charisma din yake takawa har ya qarasa waren da motarshi ke jiransa, budeshi mishi suka yi ya shiga kai tsaye ya bada umarni su wuce Maitama.

Bai san yayi kewar Ummi na wuce misali ba sai da yaga sun iso gidan. Wani irin urge na son ganin Ummi na taso mishi amman sam idan ka kalleshi baza kace hakan ba.


Bayan fitowarshi kai tsaye ya nufi main building din dake cikin mansion din. Wani irin hadadden gida daya amsa sunansa, kamar baka a qasar. 


Da sallama ya shiga part din Ummi dake nan a gyare komai tsaf sai kamshin turaren wuta ne yake tashi, irin kamshin nan mai tsayawa arai. Da kallo yabi parlourn da kallonsa kawai zaka san dukiya tayi kuka, it was screaming luxury ta ko'ina. 


Upstairs ya nufa kai tsaye da dan sassarfa a takunsa. A parlourn sama ya hadu da Ummi. Tana zaune cikin luxurious outfit din daya mugun dacewa da ita. Ummi ba fara ce ba sannan kai tsaye ba zaka kirata baqa ba unlike Ammi dake nan jajawur kamar ka taba jini ya fito. 


Fuskarta babu yabo babu fallasa tana operating waya ta daura kafa daya akan daya. Yadda tayi kai tsaye kana kallonta kasan she's a no nonsense woman. 


Sallama Fu'ad yayi mata da wannan husky voice din nashi. Hakan yasa ta dago da sauri jin muryarsa. Akansa ta sauke idanunta, sai dai kamar ko yaushe kamannin da yakeyi da Ammi bai bari ta kureshi da kallo ba, because idan tana kallonsa tana jin mugun tsanar Ammi yana qaruwar mata arai ne.


Dauke kallonta akanshi tayi tana cigaba da danna wayarta. Murmushi kadan Fu'ad yayi "Ummi tayi fushi." Y fada aransa kamin cike da wannan nustuwar ya nufi inda take yayi zaman dirshan akan lallausan carpet dake waren yana facing dinta.

Kunneshi ya kama yana marairaice fuska kaman wani yaron goye yace "Ummina I'm really very sorry. Ki yafemin, ban son fushinki dani please Ummiiiiiiii."

Kamar ta basar dashi sai dai ba zata iya ba. Bata hada Fu'ad da komai ba duk da bashi kadai ne danta ba akwai dan uwansa AZZAM.

Dagowa tayi ta kalleshi tana son harararsa amman ba tayi ba "daka zauna acan ai Fu'ad."


"No way Ummi, I missed you." Y qarashe yana kamo hannun Ummi da yaji jan lalle don Ummi irin 'yan gayun nan ne masu son kwalliya sosai.


"In as much as kasan yanda nayi kewarka Hayaty da you wouldn't have said that..."


"Ohhhh come on Ummi it's a bygone. Ya wuce let's face the reality...." Zaiyi magana kenan aka kirashi daga baya "Hamma F." Da sauri ya juya yana kallon matashin da yake haurowa, a shekaru bazai haura 26yrs ba.


"Azzam" kallonsa Azzam yayi yana karasowa ya miqa masa hannunsa sukayi musabaha kamin ya zauna agefensa. 


"Long time Hamma F. Ka guje mu." Wani murmushi Fu'ad yayi masa mai mugun sanyi wanda ya fito da zallar madarar kyan da Allah ya bashi. 


Azzam ya dauke kansa yana kallon Ummi dake kallonsa. Wani irin deep kallo da yake dauke da ma'anoni.


"Ummi lemme go and shower. Kince you cook my favourite right."

Kai Ummi ta gyada masa tana cewa "yes yes Hayaty. I'm waiting for you." Miqewa yayi yana kallon Azzam yace "see you later Azzam." 

"Ok." Fita Fu'ad yayi kai tsaye ya nufi part dinsu shida Azzam. Wani katon part daya kusan girman na Ummi. Anyi furnishing part din duka da taste din Fu'ad ne. Komai yana kan tsarin Fu'ad. 

Dakinsa da yake makeke ya shiga yana zare suit dinsa ya bar fara kal din long sleeve din kawai. Da kallo yabi dakin da kallo. Komai yana nan very neat sai tashin kamshi yake. Ko baya nan ana gyara masa dakinsa that's why ko yaushe yake nan a gyare tsaf. Duk da baya nan dakin nasa kamshin turarensa mai mugun kama wuri yake. Agefen Italian king size bed dinsa ya zauna yana ajje suit dinsa. Ya sauke idonsa akan hotonsu shida Fa'iz dake nan agefen bed side drawer a ajje. 


Dakin na Fu'ad ne, amman nasu ne duka. Komai nasu tare yake kaman wasu 'yan biyu. Da kallo ya qure Fa'iz sosai yana sake ganin tsananin kamar da suke. Sai yake jin wani sabon kewar Fa'iz na damunsa, yasan maybe da tuni suna tare. Yadda ya shaqu da Fa'iz bai shaqu da Azzam da yake dan uwansa uwa daya uba daya ba.


Miqewa yayi yana zare agogon patek phillipe dake hannunsa ya ajiye anan gefen wayarsa kai tsaye ya nufi bathroom..........


________________



AZZAM'S POV


Wani irin kallo Azzam yabi Fu'ad dashi na zallar kishi da hassada kamin ya dawo da idonsa kan Ummi dake cigaba da danna wayarta.


"Ummi ashe yau Hayatynki yake dawowa ban sani ba..." Ba tare da ta kalleshi ba tace "uhmmm yau yake dawowa. Sani kuma ba dole sai kayi ba Azzam."


"Yana da kyau na sani Ummi, dan uwana ne..." Wani kallo Ummi tayi masa mai ma'anoni daban daban.


"Naga kamar baka damu da dan uwan naka ba....." Sai tayi shiru kawai tana ajiye wayar agefe ta maida hankalinta akansa.


"Ka nutsu Azzam. Duk abinda kake yi ka dena. Fu'ad ya dawo yanzu. Bana son wannan rashin jituwar dake tsakaninku. Ka girmamashi Azzam."


"Damn it, Ummi ko yaushe na girmamashi kawai kike cewa."



Zamanta Ummi ta gyara tana kallon Azzam tace "mene yasa kake da taurin kai ne Azzam, He's your elder brother..."


"Kina fifitashi akaina Ummi." 


"Hakan ya dace nayi Azzam, ya fika hankali da nutsuwa....." Murmushi Azzam din yayi yana miqewa tsaye yace "is ok. Hakan ma yayi.." da kallo Ummi ta bishi har ya fita. Babu wanda bata so acikinsu sai dai Fu'ad fa daban yake awarenta.



_______________



FU'AD'S POV 



Sanye yake cikin baqin trouser da rigarsa na kamfanin Calvin Klein. Ba wai kwalliya yayi ba amman yayi kyau as komai kyau yakewa Fu'ad. Duk abinda Fu'ad zai saka sai ya yi masa kyau, hatta kayan bacci kuwa. Yana da wani irin kyau ne mai sanyi marar hayaniya. Banda kamshin Pur oud na Louise Vuitton babu abinda ke tashi adakin. Sanye yake da baqin loafers na kamfanin Hermes daya mugun haska qafarsa dake nan kaman bai taba taka kasa ba.


Kai tsaye part din Ummi ya nufa hannunsa dauke da wayarsa. Calmly haka yake taka kasar sai dai cike da kuzari da wannan giant jikinsan da kana gani kasan yana gyming.


A dinning table ya tarar da Ummi tana shirya komai duk da ashirye suke sai dai tana son komai ya kasance yadda Fu'ad yake so.


Wurinta ya nufa yana cewa "Ummina." Kallonsa tayi tana murmushi sosai "yes Hayaty."

Zama yayi a kujerar dake facing din Ummi yana ajje wayarsa akan dinning table din. Fura mai sanyi ta fara miqa masa a cup don tasan shine babban abinda yafi so duk abin sha. Ya amsa yana cewa ya gode. Serving dinshi sauran dishes din tayi duk da tasan ko yana so bawai da yawa zai zage yaci ba. Chinese rice ne da salad sai pepper chicken da yaji veggies sai dayan plate din ta saka masa abincin gargajiya da tasan shi kadai yake so wato alkubus da miyar taushe.


Furar ya shanye tas kamin ya tattaba sauran yaci kadan bada yawa ba. Ummi dai kallonsa take cike da so da kauna. Irin wannan kaunar mara algus.


Yana ajiye spoon dinsa ya jawo tissue yana goge lips dinshi suka yi ido hudu da Ummi dake kallonsa admiringly irin like wannan dana ne proudly dinnan. Murmushinsa mai taushi ya mata yana cewa "Ummi."

Mayar masa da murmushin Ummi tayi tana cewa "yes son har ka koshi. Rashin son abincinka gaba yake dada yi Hayaty."


Shagwabe mata fuska yayi yana cewa "Ummi na ci fa. Ko so kike cikina ya fashe ne?" Da sauri ta girgiza masa kai tana cewa "a'a" 


Da kansa ya taya Ummi sukayi arranging wurin duk da cewa akwai maids din da sukeyi kamin suka koma parlour suka zauna.

"Ummi ina Abie? Rabon da muyi waya dashi tun day before yesterday wayarsa bai shiga."


"Ya tafi Lagos wai za suyi wani taro maybe ma sai next week zai dawo."


"Allah ya dawo dashi lafiya." Ta amsa da Aameen. Duk wannan abinda yake Fa'iz yana ranshi. Ba wani hira suka yi sosai ba Ummi tace yaje ya huta tasan ba wani hutun arziqi yake ba don he's a workaholic. Da murmushi ya miqe yana fita daga part din gaba daya.

Wayarsa ne yayi ringing hakan yasa ya dakata a tsakiyar katuwar harabar gidan yayi picking call din ganin Abbansa daya gama zancensa ynzun ne yake Kira.


Daga can saman balcony din part dinsu Azzam ne a tsaye yana kallon Fu'ad. Wani irin kallo da kai tsaye zamu iya kiransa dana zallar kiyayya. He despise Fu'ad so much. He hate him with passion. Fifita son Fu'ad da Ummi take shine abinda ya fara sakawa yaji ya tsani Fu'ad sosai. And da yazo Fu'ad ya fishi nasibi sosai a komai.



Fu'ad irin mutanen nan dake nan suna da sa'a a komai. Fu'ad yafi shi farin jinin mutane kowa son Fu'ad yake both maza da mata. Ga yazo yana gama uni ya samu offer din aiki a Bechtel. Now that he owns NoveBuild yana jin kamar shi bai zo duniyar da sa'a ba.



Irin like duka dream life dinsa ita Fu'ad yake kanyi. Duk irin abubuwan daya tsara na rayuwa su Fu'ad yake kan samu. Yana son ya zama mai kudi na sosai, Fu'ad ya zama. Yana son ya zama famous a duniya, Fu'ad is now famous. Yana son kowa ya soshi, amman kowa Fu'ad yake so. Fu'ad ya fishi kyau nesa ba kusa ba, abubuwan da Fu'ad ya fishi idan zaiyi counting ba zasu kirgu ba sam. Is like Azzam sak halinshi irin na Ummi ne. Halinsu daya na son suga sune a saman kowa.




"I promise sai na rabaka da komai Fu'ad, duk wannan abinda kake ji dashi. Zaka dawo zero behind decimal point. Sai na rabaka da duk abinda Ka mallaka. Hatta kyan da kake taqama dashi na rantse sai na rabaka dashi......" 



(Is like Azzam yana manta cewa Fu'ad yayansa ne uwa daya uba daya, this guy here ya gado Ummi har kaman ya fita fa.... oh ni dai yayi min gsky I'm in his team馃)  



#like
#comment
#share

Want the next chapter?

Create a free ArewaPen account to save progress, unlock paid chapters, follow this author, and keep reading across web and the Android app.