Free chapter · Read without an account
SHE HAS NO ROOT
by Saddiqah M · NURI
NURI
By Saddiqa
NURI'S POV.......
Kaman yadda Mami tace suje su gaida Inna haka suka shirya yau after Asr prayer. Nuri wear wani black flower material mai touches din soft pink daya mugun yi mata kyau sosai. She's kind of Beautiful that makes you pause and take a look.
Basu da wani option daya wuce bin umarnin Mami that's why kawai zasu je su gaida Innar.
Yau da suka je basu tarar da Aunty Zakia ba. Sannan gidan yau a tsaftace yake da alama Inna da kanta ta gyara ta gaji da kazantar Aunty Zakiar. Binsu ta riqayin da kallo kaman bata sansu ba tana qanqace idanu.
"O'o su waye nake gani kamar dai yaran Audullahi..."
"Mune Inna." Nuri ta fada calmly while Afif sai dauke kansa yayi yana cewa "Abdullahi bawan Allah.." Kai tsaye da Inna yake sannan itama Innar ta gane da itan yake don haka sai cewa tayi "nunamin kana da ilimin da zaka gyaran abu Afifu, duk shekarun Audu bai taba yimin irin haka ba. Maza kama kanka."
Qasa yayi da kansa bai sake magana ba sanin halin Inna sarai. "Me ya kawoku nan tukunna ma dai. Kunga ban dora abincin daren ba tukunna shima..."
"Gaidaki muka zo yi..." Nuri tayi saurin katse surutun Innar. Sai a lokacin ta matsa musu daga hanya suka shiga ciki. Da kanta ta shimfida musu wata matacciyar tabarma. Nuri ta zare flat shoe dinta baqi ta zauna, Afif ya qarewa tabarmar kallo sannan ya sake qarewa shigar jikinshi kallo. Yana sanye cikin wani black trouser da shirt long sleeve da sukayi masa kyau suka haska farinshi don shi fari ne yayo Mami dake fara.
Wata kujera daya gani ya jawo ya zauna, Inna ta galla masa harara tana cewa "aikin wofi ma kenan."
"Ina yini Inna."
"Lafiya Nuriyya."
Sai duk suka yi shiru, Afif ya gyara zamansa sosai kamin ya gaida Innar "barka da Yamma Inna"
Baki ta wage tana sakace goron daya maqale mata a baki tace "nidai iyaka sanina Audi baizo daga dangin sarauta ba bare kuma aje kan uwarku da bamu san ASALINTA ba!"
Wannan shine babban dalilin da yasa yaran basa son zuwa waren kakartasu. She keeps in insulting there mother ko yaushe agabansu ita da yaranta Zakia da Salama. Uwa dai ko ya take uwa ce hakan yasa Afif miqewa yana karkade jikinsa ya kalli Nuri yace "sai kin taho Adda." Don ba iya jura zai yi ba, shi ba kamar Nuri dake da haquri bane, yana da zafi sosai.
"Sai anjima Inna dama munzo fada mki ne wani satin Afif zai wuce Germany ya samu gurbin karatu acan." Nuri ta fada tana miqewa.
Da sauri Inna ta miqe tana cewa "wanne karatu zaije yi a qasar waje bayan wanda yake yi anan. Ko har zaku fara cin amanar Audu daga ganin bayanan ku fara yawace yawace ne?"
Babu wanda ya kulata acikinsu suka nufi hanyar fita kai tsaye. Idan suka cigaba da zama anan rayuka ne kawai zasu baci.
Ko a hanya babu wanda yayi magana acikinsu har suka qarasa gida. A kitchen suka tarar da Mami tana shirya musu dinner don Maghrib ya kusanto.
"Me zan gani haka, har kunyi me?"
Cikiciki Afif ya amsa da "har mun gaisheta Mami." Kallonsa tayi tsaf ta fahimci wani abin ya faru ne amman sai ta basar ta balla masa harara tana cewa "sarkin zuciya naga sai bata rai kake."
Hannunsa ya hade ware daya yana cewa "Mami don Allah yau daya ki fada mana dalilin da yasa Inna ke kiranki marar asali we want to know. Abin yana min zafi a zuciya, na dena zuwa inda take don wallahi wataran zan iya Margaret......" Talle masa qeya Mami tayi tana "this is irresponsible Afif. Innar kake fadawa haka ranka baci zaiyi sannan ku wuce ku bani wuri..."
"Mami kawo na qarasa mki aikin."
"Jeki Nuriyya na kusa gamawa, kin bar wayarki agida anata kiranki."
Kowa dakinshi ya nufa Nuri da sauri ta dauki wayarta tana dubawa sai dai missed call din Khaleel data ganI yasa ta maida wayar. Kamin ta ajiye wayar saiga kiran Zara yana shigowa.
Agefen katifarta ta zauna tana picking call din. Sallama suka yiwa junansu kamin suka gaisa yadda suka saba.
"Friendy yau duk na jiki shiru baki hau online ba, babu text babu kira."
"I'm kind of busy Zara kinsan Afif by next week zai wuce Germany. Wai muna tayashi siyan abun da yake necessary ne."
"Afif dinne zai wuce Germany ammn ba sanarwa...."
Dafe kanta Nuri tayi da sauri tana cewa "ya Salam I'm sorry best, na manta ban gaya mki ba. Wannan scholarship din da Abba ya nema masa ne suka bashi. Muma bamu sani ba sai recently wai bai son zuwa shisa bai nunawa kowa ba..."
"Amman is a good opportunity kar yayi wasa dashi."
"That's exactly what Mami told him."
"Is ok. Thinking zanzo gobe that's why na kira na fada mki."
"Really?"
"Yeah."
"Ok Allah y kaimu goben ki gaidasu Mummy."
"Zasuji Friendy my regards to all."
"In Sha Allah see ya.." sallama suka yi Nuri ta ajiye wayar ta fada toilet don yin alwala ganin lokaci yayi tasan yanzu za'ayi kiran sallah.
Kamin ta fito Azan yayi kiran sallah don haka tana fitowa ta tayar da sallahrta. Bayan ta idar ta hau yin muraji'a as she normally does.
Around 9pm after sunyi having dinner dinsu ne Nuri ta kalli Mami da kyau tana cewa "uhmmm Mami ina da tambya."
Kallonta Mami tayi ganin yadda ta kureta da kallo yasa tace "lafiya wannan kallon haka Nuriyya."
Kai ta girgiza tana murmushi tace "Allah Mami muna kama dake sosai kawai you're fair ni kuma I'm dark."
Hararar wasa Mami ta mata tana cewa "wannan shine tambayar Nuriyya?"
Da sauri ta girgiza kai tana cewa "a'a."
"Kinsan halinta ne ai Mami, komai sai tasa shirme.." Afif dake danna wayarsa ya fadi yana kallonsu.
"Addan naka kake kira da tana shirme.." Mami ta fada tana masa kallo mai kama da harara.
Wannan sumar nashi mai santsi da laushi irin na fulani ya shafa yana cewa "I'm sorry..."
Nuri tayi murmushi kawai tana kallon Mami tace "Mami I'm tired of hearing Inna insulting you....Mami don Allah why is she addressing you with harsh words."
Shiru Mami tayi yayinda Afif yabi Mami da kallo kaman dai Nuri ta shiga zuciyarsa ne. Kallonsu takeyi daya bayan daya tana kallon qaguwa da sonjin wace ita da suke yi.
"I'm nobody....." Ta fada tana breaking maganar. Ita kanta ba wani abu take tunawa akanta ba mai yawa kasancewar yarinta.
"I can only remember few things..."
"Yes Mami, we wanna here that few things." Afif ya fada yana gyara zamansa a kusa da ita.
"We're from Maiduguri ni da Ummana. Daga lokacin da na fara wayo don ina yarinya. Zan iya tuna maganganun mutane dai suna cewa kakannina sun tura Ummana karatu ta dawo musu da ciki, ta haife musu ni....
Dukda ina yarinya I was stigmatized, called with many names wai babu tabbacin ma ina da uba. Da yarinta akaina sosai amman abun yana damuna tunda ina ganin yadda uba yake playing role a waren yaran da nake tare dasu.
Amman kakannina jajirtattu ne. Ban rasa komai ba. Sune suka kula dani suka sakani a primary school har zuwa sanda na girma nayi secondary school. Ummana tana sana'a sosai dake kawo mata kudi as matan Maiduguri akwai neman na kansu. Alokacin ne kuma masifar boko haram ya fara. Tun muna ji a nesa damu har ya kawo garinmu.
The day I will never forget was the day da suka tashi garinmu duka suka kashe na kashewa suka tafi dana tafiya. Acikin wanda suka kashe harda Ummana da Kakana namiji. Kakata Innayo ta boyeni a inda ba zasu ganni ba amman ni naga sanda aka kashe Ummana da kakana. Na gansu cikin jini ransu yana fita.....
Innayo ce ta fito dani bayan sun tafi muka yanki jeji muna tafiya. Tun muna yi da kuzarinmu har ya muka yi la'asar. Bansan kwana nawa mukayi muna tafiya a daji ba, qafafunmu babu takalmi, kishirwa da yunwa kaman zasu kashemu. kwananmu biyu kamin muka samu wani ruwa daya taru da alama ruwan sama ne rashin hanya yasa ya kwanta don ya fara qafewa, wannan ruwan shi muka sha muka koshi duk da yadda yake kana gani kasan ba lallai mai kyau bane.
Wahala ya kashemin Innayo itama a wannan tafiyar. I was now alone wandering a dajin Maiduguri with no one to help me bayan Allah.
Life was tough back then, miserable but Alhamdulillah. Tare da wasu 'yan garin namu dai akarshe na hadu muka iso camp din refugees dake nan Kano. Anan nayi rayuwana, ni kadai tunda suna tsangwamana. Sai dai akwai wata mata da Allah ya hada jinina da ita Baba talatu wadda tausayina yasa ta tsayamin akan al'amurana. I was depressed, na koma silent ba ruwana da kowa, bana shiga cikin mutane, only Baba talatu and I.
Na hadu da Abbanku ne a asibiti naje kai Baba talatu shi kuma ya kai Innarsa. A time din babu wanda yayi noticing kowa sai dai zaman jinya da mukayi daki daya da Innarsa yasa ya ganeni. Bayan an sallamemu bansan yadda akayi ya gane inda muke ba na dai gansa. Tun bana kulashi har na fara kulashi and that was the beginning of our love story.
Innarsa bata sona ne saboda tana da wadda take so ya aura. Shi kuma Abbanku ya nace saini. Tayi bincike akaina tagane 'yar gudun hijira ce, and I'm very sure 'yan camp dinmu ne suka fada mata wani part na labarina that lingered to her brain har zuwa yanzu. Ta tsaneni for that reason don Abba yace mata bazai iya auren wadda take so ba, har ya hadata da wanda da take tsoro. Akayi aurenmu na tare muke zaune da ita da dadi ba dadi. Kafin budi ya samu muka canza gida before this one da muke ciki. Nima zanso nasan waye mahaifina. Zanso na ganshi koda a hoto ne. Sunanshi kawai na sani *GIDADO ARDO*."
Parlourn was silent for a moment. Sam basu taba kawowa wannan shine labarin Mami ba. A refugee, stigmatization, and leave to live alone without parents and grandparents. Ji suka yi kamar nasu jarabawar da sauki. Abbansu kawai suka rasa, Mami fa?
Ita bama tasan waye Abban nata ba, ta taso cikin tsangwama, boko haram incidences, living in a refugees camp with no one.
Nuri sarkin kuka tuni ta fara kuka ta rungume Mami. Afif ne shi a komai sai ya nuna namiji ne shi. Fuskarshi ja kawai yayi while ya barwa zuciyarshi komai yana son kada su sake tadawa Mami tsohon abinda take binnewa.
"Mami we're sorry mun tuna mki past dinki." Ya fada yana riqe hannunta.
Qanqame hannunsa tayi tana murmushi mai tafe da hawaye tace "this is my destiny, ina roqon Allah y kula daku kada ya doro muku qaddara irin nawa na rayuwa ku kadai."
Rungume Mami shima Afif yayi kaman yadda Nuri tayi. Patting back dinsu Mami keyi tana cewa "is ok ban fada mku don kuyi kuka ba fa."
"Mami we're sorry." Suka fada a tare. Ta dade kamin ta shawo kansu suka nutsu ta nuna musu wannan qaddararta ne yanzu su kadai take da a duniya Abbansu ma babu.
Afif zai sake mata maganar ya haqura da karatu a TUM tace sam bai isa ba sai yayi. Dole ya haqura tace dashi ma zasuje kasuwa gobe su sai masa abinda ya rage da zai buqata da kudin hannunta wanda shi kadai yayi mata saura, they're slowly getting out of money.
By next week Afif zai barsu wanne kalar rayuwa zasu sakeyi? Shi kansa Afif wanne kalar rayuwa zaije Munich yayi?
To be continued.......
#like
#comment
#share