Free chapter · Read without an account
TOO YOUNG TO LOVE
by Saddiqah M · NURI
NURI
By Saddiqa
"SUHANA Ummi?" Ya tambayi Ummi da mamaki sosai rubuce akan fuskarsa.
"Yes Suhana Mu'azzam, ita nake nufi. Ba rape din kawai ba I want the blood she will bleed after the raping incident....." Kallonsa ya dauke akan Ummi, yayi imanin Ummi ta fishi rashin tausayi nesa ba kusa ba, rainonta ne shi din just like Fu'ad. Sai dai akwai banbanci tsakaninsu da Fu'ad da sam halinsu ya banbanta ta ko'ina.
"Ok Ummi naji I will do it."
"I want it this week."
"To." Ya amsa mata shortly yana fita don ya gaji yana son hutawa yayi aiki da yawa yau dinnan.
Zama Ummi tayi tana cire dankwalin kanta daya bawa doguwar baqar sumarta irin na fulani damar fitowa. Kamar kanta yana shirin kullewa akan rashin nasararta akan Boddo.
FU'AD'S POV
Wani irin gudu Fu'ad yake kamar zai tashi sama burinsa kawai shine yaje gidansu Fa'iz. Bai dade ba sakamakon gudun da yayi ya karasa gidan. Wani irin wrong parking yayi ya fito da sauri kai baka ce shine wannan mutumin da komai nashi yake yi anutse ba owner of NoveBuild ltd ba.
Da sauri yayi part din Ammi ya shiga wannan karan duk sonsa da sallama ya manta baiyi ba wani irin zumudi nason ganin Fa'iz kawai ke dibansa.
A zaune kan wata ottoman sofa ya taras da Fa'iz gefensa Ammi da Abbi sun sakashi tsakiya sai qasa Addarsa SAFA da qanwarsa guda daya wato SUHANA.
Duk kallon Fu'ad daya shigo yanzu suka yi while Fu'ad ya tsaya kawai yana kallon pal dinsa da wani irin mixed emotions na kewa da murnar yaji sauqi.
Miqewa da sauri Fa'iz yayi yana kallonsa shima da kalar nashi mixed emotions din kamin ya nufi Fu'ad din kai tsaye ya rugumeshi. For a moment Fu'ad ji yayi kamar wani barin jikinsa ne ya rungumeshi.
"Pal." Fa'iz ya fada yana sakin Fu'ad. Murmushi Fu'ad yayi yana riqo hannunsa suka nufi cikin parlourn suka zauna a qasa kamar yadda Safa da Suhan suka yi. Gaida Ammi da Abbi Fu'ad yayi kamin ya gaida Safa.
"Fu'ad ya mukaji da farin ciki kuma?" Abbi ya tambayi Fu'ad wanda yayi murmushi yana kallon qasa yace "Alhamdulillah Abba duk tsanani yana tare da sauqi." Ammi dai kallonsu take yi duka tana wannan murmushin nata mai kyau wanda yake kashe Ummi.
"Hamma Fu'ad ina yini." Suhan ta gaidar dashi tana miqewa taje ta kawo masa drinks.
"Ammi how comes Pal ya dawo daidai?"
Kai Ammi ta girgiza tana cewa "i really don't know how. Nasan dai ina tare dashi yana bacci nace Suhana ta hado masa fruit salad don shi kadai yake iya sha sai ya farka daga barci a zabure yana gumi sosai, he then calls my name abinda for 3 months bai taba yi ba..." Muryar Ammi ya fara rawa that makes Abbi riqo hannunta kadan in a convincing manner.
Shiru Fu'ad yayi yana son figuring abinda ya faru, the scene just look like a Witchcraft, but from who? Dole ya ture wannan tunanin daga ranshi ya barshi kawai as jarabawa ce Allah ya musu amman alhamdulillah.
Sun dade a waren zaune a waren, sai can mijin Safa yazo ya tafi da ita kamin suka yi dinner tare waren 10:30 Ammi ta ankarar da Fu'ad dare yayi. Wristwatch din hannunsa ya kalla qirar kamfanin omega kamin ya girgiza kansa kawai yace "Ammi zan zauna anan na wuce gobe in Allah ya kaimu." Kai kawai ta gyada tana kallonsa.
Ya kalli Fa'iz yana cewa "pal let's go." Sallama sukayi wa iyayen sannan suka miqe zuwa part din Fa'iz.
Anan suka raba dare suna hirar da suka dade ba suyi ba sakamakon basa tare. Suna zaune akan sofa dake bedroom din Fa'iz din kowanne sanye da pyjamas daya mugun masa kyau.
Kana kallonsu zaka san kai tsaye akwai shaquwa mai qarfi a tsakaninsu, yadda suka mai da hankali suna tattauna abu mai muhimmanci ya mantar da Fu'ad sanar da Ummi da yayi niyyar yi duk da itama Ummi kanta ya dauki zafi she even forgets with him.
Da asuba tare da Abbi suka wuce masallaci wanda basu dawo ba sai da gari yayi haske. Shima sai da suka dan yi strolling kamin suka koma gidan kai tsaye suka nufi waren Ammi.
Tana zaune akan darduma ta idar Suhan agefenta.
"Ammi ashe Hamma F ya dawo ban sani ba?"
Ammi bata kalleta ba ta amsa da "ba dole sai kin sani ba Suhan."
Wani kallon shagwaba tayiwa Ammi tana cewa "Ammi amman yayana ne fa just like Hamma Fa'iz."
Kallonta Ammi tayi with deep thoughts, Suhan tana son baro musu aiki ne. Besides she's too young for this she's just 16yrs.
"Suhana." Ammi ta kirata tana kure kallonta akanta tana son tabbatar da zarginta akanta.
"Kina isana da zance akan Fu'ad Suhan, baki iya yin zaman 20mins sai kinyi zancensa ne wai?"
A yarinta da kuma zallar shiririta da sangarta irin na 'yan auta Suhan sai cewa tayi "wallahi Ammi zuciyata ce kullum take cikin tunanin Hamma F ban san me yasa ba. Ko Hamma Fa'iz bana jin haka kansa, I don't know why."
Da Suhan nada lura da ta lura da wani gumi da yake tsatssafowa Ammi sai dai shiriritarta bazai bari hakan ba. Kamin Ammi ta bata amsa sai gasu sun shigo.
Sallamar Fu'ad ya ratsa dakin da wannan husky voice din shin mai saukar da nutsuwa.
Bugawa zuciyar Suhan tayi da sauri har saida ta dafe kirjinta is like abinda take ji yana shirin fin karfinta. Ta fara tunanin ko tana da wani ciwo ne bata sani ba.
Agaban Ammi suka tsugunna suna gaisheta. Danne komai Ammi tayi tana amsawa da murmushin data dorawa kanta.
Fu'ad ya kalli Ammi yana cewa "Ammi are you ok." Kai ta gyada masa da sauri tana kallon Suhan dake satar kallon Fu'ad din.
"Baki iya gaisuwa ba Suhana?" Da sauri ta girgiza kai muryarta har yana rawa tace "good morning brothers" a tare duk suka amsa mata.
Da sauri ta miqe tsaye tunawa da tayi ashe fa wai ta fara zuwa jami'a. She's studying architecture a Nile university tana a first level ne.
Da sauri ta wuce Fa'iz yana cewa "wannan yarinyar taki Ammi I don't know ko za tayi hankali."
Hararar Fa'iz Ammi tayi tana cewa "tunda kayi hankali Fa'iz ai kowama zaiyi." Miqewa yayi yana shafa sumar kanshi dake nan sak irin na Pal dinsa ya juya yana cewa "Ammi kina son kiyi zancen quruciyata Allah."
Murmushi Fu'ad yayi yana cewa "Ammi I'm leaving."
"Da wuri haka without taking your breakfast Fu'ad?"
"Ammi zanje company na kwana biyu banje ba kuma ina son fara zuwa gida."
"Ok Allah ya bada sa'a." Ya amsa da Aameen zasu fita Ammi ta tambayi Fa'iz ko Abbi ya dawo ya amsa mata da eh ya tafi raka Fu'ad.
Miqewa Ammi tayi kai tsaye ta nufi part din Abbi. Sanda ta shiga ta tarar yana bathroom dole ta haqura da maganar da take so suyi ta fito don shiryawa Abbi breakfast don bata taba bari yaci girkin maids dinta. Musamman take yi masa girki da kanta.
Cikin wani Dubai Abaya Suhan ta shirya wadda ta mugun yi mata kyau ta fito da zallar yarintarta. School bag dinta ta dauka da wayarta ta fita don yin breakfast ta tarar Ammi ta kammala. Kanta a kasa ta karasa ganin kalar kallon da Ammin ke binta dashi.
"Ke fashion parade kike zuwa makarantar ne?" Ammi ta tambaya ganin kalar kyan da Suhan din tayi kamar wata wadda zata je gasar kwalliya. Kai ta girgiza da sauri tana cewa "Ammi makaranta zanje."
"Ohhh I see, yayi miki kyau. This should be the last time da zanga kinyi makeup irin haka kawai don zaki je school?"
A shagwabe tace "nifa Ammi Allah ba wani kwalliya nayi ba look at my face fa."
"I'm blind Suhan." Qasa tayi da kanta kamin ta juya ta koma sama ta goge janbaki da lining din da tayiwa idonta ta bar kwalli kawai. Suhan nada kyau ne sosai and Ammi was protective over her sanin yarinyarta har yanzu babu wani hankali a tare da ita. Shirme yayi mata yawa sosai gata tana da girman jiki sam ba zaka ce she's 16 ba.
Tana sauka qasa Ammi tace "better for you girl, oya maza zo kiyi breakfast ki wuce."
A shagwabe ta qarasa waren Ammi din. Kana kallon Suhan zaka san 'yar gata ce from both parents and brothers don cikin Fa'iz da Fu'ad babu wanda baiyi mata abinda take so har dai yana kan daidai. Ammi da kanta tayi serving dinta, bata wani ci da yawa ba ta tashi da sauri tayiwa Ammi sallama. Da kallo Ammi ta bita haka kawai taji kaman tana tausayin yarinyar nata. "Yah Rabbi don't make it what I'm thinking, Yah Rabbi please..." Muryarta ne yayi breaking sosai daidai Abbi yana saukowa ya sauke idonsa kan Ammi dake nan zaune cikin adon kace da akayiwa dinkin T bubu yayi mata kyau as kalarsa ya mugun haska wannan farar fatar nata.
Da kanta taja masa kujera ya zauna yana cewa "nagode fulani." Murmushi tayi masa tana serving dinsa tace "kayi kyau Yallabai."
"Ban kaiki ba Fulani, kullum kara kyau kike kamar bake kika haifi Safa, Fa'iz da Suhana ba, meye sirrin ne?" Ya tambaya yana kifta mata ido. A kusa dashi ta zauna tana murmushi tace "kaji Yallabai."
"Boddo shine ya dace dake, kyakkyawa." Murmushi suka yi dukkansu kamin suka yi bismillah suka fara cin abincin a tare. Bayan sun gama ne Abbi ya miqe yana cewa "I'm going fulanina."
Miqewa Ammi tayi tana yi masa wani irin kallo tace "Yallabai da wuri haka?"
Agogon hannunsa ya kalla yana cewa "ko akwai wani abu ne?" Shiru Ammi tayi tana so dai suyi magana amman taga kamar akwai abinda zaiyi don haka ta barshi kawai idan ya dawo sai suyi maganar.
"Idan ka dawo za muyi magana ranka y dade."
Kai Abbi ya girgiza yana riqo hannun Ammi suka qarasa well furnished parlourn nasu suka zauna yace "akwai magana a bakinki Fulani. Don haka say it kinji."
Kai ta girgiza tana cewa "a'a Yallabai mu bari ka dawo karna shiga lokacinka."
"Lokacina naki ne ranki ya dade."
Murmushi tayi tana jin son mijinta duk da cewa sun girma amman har yanzu yadda yake sonta bai ragu ba kai tsaye ma qaruwa son da yake mata yake kullum.
"Yallabai Suhana ce." Sai tayi shiru ba tare da ta qarasa ba. Abbi yadan damqe hannun Ammi dake cikin nasa yana kallonta yace "me Suhan din tayi Amminsu?"
Rawa muryarta yayi lokaci daya tana jin wani rauni yana rufeta tace "Abbinsu tana shirin jawowa kanta abinda ba zai taba faruwa ba..."
Bai gane ba sam don haka ya girgiza kansa yana cewa "ban gane ba Fulani."
Ajiyar zuciya Ammi ta sauke tana cewa "tana son FU'AD ne ba tare data sani ba."
Da sauri ya saki hannun Ammi yana dan ja da baya kadan yace "Fu'ad kika ce Fulani?"
Kai Ammi ta gyada da sauri tana cewa "daidai kaji Yallabai, Fu'ad."
"Subhanallah, me yake shirin faruwa Fulani? How comes?"
Kai Ammi ta girgiza "I don't know your highness, is just that ko yaushe cikin begensa take. Ban lura ba sai kwanan nan."
Miqewa Abbi yayi yana cewa "tayi qanqanta da fara so Fulani, a ajiye batun waye Fu'ad a rayuwarta ma. She's too young to love a yanzu. Ina tunanin I will send her abroad kawai. She will quite studying a Nile. Zan nemar mata Technical University of Munich, Farouq is there zata zauna tare dasu acan. Let she be far from him, zata manta da sonsa In Sha Allah......"
To be continued.......
#like
#comment
#share