Free chapter 路 Read without an account
GERMANY CALLING.....
by Saddiqah M 路 NURI
NURI
By Saddiqa
FU'AD'S POV.......
Da wannan nustuwar dake mugun dacewa da kamalarsa ya shiga wurin Ummi cikin Ralph Lauren men's suit farare kala da suka mugun yi masa kyau, ko nace yayi musu kyau don shi yake ma kaya kyau馃槈, the scent of Creed Aventus clinging to him and filling every space he passed through.
Bai samu ganin Ummi ba kasancewar tana bathroom da alama wanka take yi. Ya duba agogon Rolex dake daure a hannunsa yaga lokacin kaman yana qure masa hakan yasa ya juya ya fita yana barin text wa Ummi informing her ya tafi he was late zasu zauna meeting ne, akwai sababbin tsare-tsaren da zaiyi sannan yana so ya bude sabon branch din NoveBuild a wani state din a Nigeria apart from Lagos and Abuja, just as he was planning to open another branch in USA.
Yana fita driver dinsa da guards dinsa suka take masa baya har zuwa parking lot din da yake shaqe da wasu mahaukatan expensive luxury cars. Wani black Royce Rolls aka bude mishi bai bata lokaci ba ya shige yana receiving call from his PA. 15 minutes ya kaisu hadadden branch din NoveBuild dake nan Maitama. Kalar yadda aka tsara ginin da yadda yake nan well organized komai in order zaka dauka kana kasar waje ne.
Yadan jima a motar bayan sunyi parking a space din nashi ne kawai a matsayinsa na CEO. Yana fita kai tsaye suka take masa baya, bayan shigansu asalin building din bai wuce kai tsaye ba sai daya ya tsaya ya gaisa da duka workers dinsa da suke gaidashi saboda dadewar da yayi baya nan.
Ko office dinsa bai wuce ba suka zarxe conference room dinsa dake can executive chamber na building din. Anan ne suka shafe almost an hour and a half suna meeting. Finally sun tsayar cewa zasu gina new NoveBuild construction company a KANO STATE.
Agajiye ya fito daga meeting din ya wuce luxurious office dinshi dakenan kaman office din shugaban kasarku馃槈馃榾 akan sofa da aka qawata office din dashi ya zauna yana cire tie din dake wuyansa don ya gaji daman ya cire suit din already ya bar kanshi da ta ciki kawai.
Zama yayi yana sake duba files din da PA dinsa ya biyoshi dashi yana jin Kano din ya dace suje su bude new company don ya lura garin was a blessed city (idan akwai wanda yake neman aiki acikinku ma ya kawo CV dinsa馃槈).
Rufe file din yayi yana kallon PA dinsa yace "the work rests on you. Find a plot for us there. It should be a quiet area. I will be there myself throughout the construction of the company."
"Ok sir."
"You can go."
Fitar PA din ya bashi daman resting sosai yana rufe idonsa yana son brain dinshi ya huta kadan kamin yaje ya cigaba da tulin aikin daya tarar yana jiransa......
NURI'S POV
Tafiyar Afif yazo musu unexpected, babu wani shiri sosai da suka yi. Hakan yasa yanzu da abin ya taho suka fi maida hankali sosai. Mami da Afif din fita suka yi yau suka wuce kasuwa while Nuri na gida zata yi musu girki.
Day before yesterday Zara da Mummy suka zo suka kawowa Afif kusan main abubuwan da zai buqata na tafiya. Shi sam kamar baya murna haka sune suke kidansu suke rawarsu. Tun kamin ya tafi sun fara kewarsa, ba ya Nuri.
Basu dawo da wuri ranar ba don sai da Mami ta kaishi wurin Inna yayi mata sallama ranar asabar jibi kenan zai wuce Munich, Germany.
Afif bai yadda da gaske tafiyar zaiyi ya barsu ba sai da ranar asabar din tayi. Tun bayan asuba Mami ke kansa tana cewa ya shirya. Shida bai da nauyin shiri ranar sai gashi yana shiryawa kaman wadda baida kuzari. Sai daya gama shiryawa tsaf cikin trouser da shirt duka baqi sannan ya samu ya zauna agefen Mami. Mami dai sam ba tayi masa magana ba don tana lura da take-takensa. Hannunsa ya jawo suka fito parlour Nuri dake Jiran fitowarsu ta miqe Mami tace taje ciki ta jawo masa trolley dinsa.
Mami da kanta ta riqa bashi abinci abaki cike da kauna da kewarsa dake cunkushe aranta. Nuri na gefe tana kallonsu admiringly ta naji kamar duniya duk babu ya Maminsu.
Ba wani cin arziqi yayi ba yace ya qoshi, Mami ta matsa sai ya qara garin bashi a bakin ya ture hannun Mami abincin ya zube masa ajiki. Duka mara zafi Mami tayi masa tana cewa "you're very silly Afif, what's this like a toddler?, go get up and change."
Da wani rashin kuzari ya koma dakinsa ya sake kaya ya fito without wasting time. Mami ta kamo hannunsa suka fito a parlourn Nuri a bayansu da trolley dinsa.
Suna fita wajen gidansu Zara da Mummy na zuwa. Tare suka wuce airport duka babu wanda yake cewa komai har suka isa.
Babu wani bata lokaci suna isa a time din yayi boarding pass da baiyi online ba and some checks ups from Immigration officers ya wuce departure lounge. Ya kasa sakin hannun Mami da Nuri kaman yadda suma suka kasa barinsu. Babu magana cikinsu sai dai kana ganinsu kasan suna kukan rabuwa da junasu a zuci ne.
Boarding announcement da akayi yasa Mummy yi musu magana. Dole haka nan suka haqura ya kasa yi musu magana sai hawaye kawai ya rungumesu duka yana jin kamar bazai sake ganinsu ba. Shekara hudu zaiyi acan kamin ya dawo. Yanajin tabbas idan yaje can ba zama zaiyi ba. Zai fara neman sana'a ya samu ya tara kudi ko zai samu yana kawo musu ziyara.
Rabuwarsu ya bude sabon Chapter wa Nuri da Mami. Yanzu sauran su biyu, family of four are now 2......
SUHAN'S POV
Tana zaune ta baje akan gadonta tana kallon wani K-Drama da aka gama releasing dinsa May dinnan, Perfect Crown. Ta maida hankali tana kallo gefenta ledar chocolates din da take sha ne tana tarawa. Admiringly take kallon drama din. And her small brain ya fara mata imagining Hamma F da ita acikin scene din da ake.Lol
Tsabar she was carried away har bata san Ammi ta shigo ba sai gani tayi an dauke system din daga gabanta. A firgice ta dago tana bin Ammi da kallo.
"I warned you about watching these red-ear shows and you refused." Baki ta turo mata zata fara mata shagwaba tace "Abbinku yana nemanki a parlournsa yanzu, ya kira wayarki bakya dauka ashe kina nan kina sana'ar."
Ba tace qala ba ta sauka daga gadon tana sanye cikin cream colour palazzo da chiffon top kanta ko dankwali babu sai wannan sassalkar sumar fulanin nata yana a baje da alama ko taje kan nata ba tayi ba.
Zata fita babu dankwali Ammi ta dawo da ita ta dauki white scarf ta sakawa kanta. Tare suka fita da Ammi suka wuce part din Abbi. A can suka tarar da Fa'iz da bai dade da dawowa ba.
"Hamma Fa'iz don Allah tunda ka warke ka cikamin alqawarina kaji."
Harararta yayi yana cewa "wannan shine naki kalar sallamar." Dauke kanta tayi tana yin sallama ta wuceshi tana tura baki gaba. Kai iyayen suka girgiza suna kallonsu.
Agefen Fa'iz din ta zauna tana cewa "Abbi gani." Kallo sosai ya qure Suhan din dashi kamin yayi gyaran murya da kyau yana cewa "ki bude kunnenki da kyau kiji abinda zan fada mki."
Kai ta gyada masa tana yin qasa da kanta "you're leaving for Germany nan da two weeks, In Sha Allah."
Ba Suhan kawai ba hatta Fa'iz da wani sauri suka kalli Abbi, Fa'iz yana cewa "Abbi Germany kuma? Wannan sarkin rawar kan za'a kai Germany?"
"Yes Fa'iz. I want her to focus on her studies."
"Amman she's trying anan din ma fa."
"Look Fa'iz, I have made my decision so it's final. Zata zauna da Uncle Farouq acan nayi masa maganar already da kyar ma ya samo mata admission a TUM don sun rufe, za tayi studying architecture acan din kaman dai yadda take yi anan."
Shiru Fa'iz yayi bai sake cewa komai ba yayi shiru yana jin bayanin da Abbin yake yi musu. Shi dai Fa'iz kawai don su Abbi sun matsa ne amman yadda Suhan ke da rawar kan nan kamar bai kamata akaita abroad karatu ba. Ita kanta Suhan din baso take ba, though can din ma kamar gida ne don Uncle Farouq shine autansu Abbi.
Jiki a sanyaye Suhan ta tashi ta koma dakinta bayan Abbie ya sallamesu. Sai taji ma karatun gaba daya kamar ya fita mata arai. Kallon da bata cigaba ba kenan kawai ta tashi tayi shirin bacci ta kwanta abinta.....
JANNAH'S POV
She's typing her resignation letter tun bayan da tayi dinner. Ta rubuta ta goge yayi kusan sau shida. Wani ma sai tazo zata yi sending sai ta fasa. Gaba daya kaman ta ruda kanta ne. Tana son samarwa kanta mafita ne kawai, zuciyarta baiyi mata adalci ba sam, of all wanda ke sonta babu wanda ya mata aciki sai ta dauko mata wanda take ganin kamar yafi qarfinta. She just slammed the laptop and pushed it away completely tana jin tashi tsaye. Tana sanye cikin pyjamas blue black da suka haska fatarta dake da haske kadan ta daura blue Chantilly cap qamshin turarenta na Lattafa yana tashi ajikinta.
Balcony din dakinta ta nufa kai tsaye ta tsaya tana kallon harabar gidan nasu. Yadda iskar damina yake kadawa kawai ya fara saukar mata da nutsuwa tana jin kamar tana dawowa hayyacinta.
"I will not resign, who is Fa'iz that I should resign because of him? I must maintain my dignity.... I am a woman of my pride.... there's no man that will drive me crazy...." Irin wayannan calming words din kawai take bama kanta. Ka ganta sai kace kan ba kalau ba. Daman gata nan gaba daya shekarun nata sun girmi jikinta. No one da zaice tayi 25 ma bare aje ga 29 sai dai idan ta idonta kawai za'a san babba ce.
Komawa tayi dakin nata ta dauki wayarta ta fita zuwa parlourn gidan da yake nan cike da 'yan uwanta suna zaune suna kallo suna hira.
Sallama tayi tana binsu da kallo ganin gaba daya hankalinsu yana kan film din da suke kallo. Agefe da autar gidan nasu mai suna Sara ta zauna. Ita ba fan din kallo bace don haka ta maida hankalinta gaba daya akan wayarta.
"Ya Jannah wai kije?" Dago kanta tayi tana kallon qaninta na kusan hudu dake magana.
"Inji wa?"
"Abba."
Miqewa tayi tana cewa "ok let me get my veil." Sama ta koma ta dauko mayafi ta yafa akan kayan bacci dake jikinta ta fita a part din nasu.
Abbanta da Mammansu ta tarar zaune a parlour hala suna wani magana ne. Sallama tayi tana shiga ciki. Duk suka zuba mata ido suna amsa sallamar nata.
A qasa ta zauna tana cewa "Abba barka da dare."
"Barka Jannah ya aiki?"
"Alhamdulillah." Sai ta kalli Mamma tana mata alama da hannu ko tayi laifi ne. Kai ta girgiza mata.
"Jannah yau kwana nawa da maganar mu ne?" Sai da gabanta ya fadi. Tayi saurin yin qasa da kanta tana son samowa kanta mafita.
"Am..am..Abba...dama...."
"Stop this your pretence Jannah. You're not a child. Freedom din da na baki kaman yayi yawa. I've sent you abroad and you spent almost 10 years studying, kin dawo nan kika ce aiki zaki fara na samo mki shima."
Kamar wata yarinya haka tayi da fuskarta duk saboda tana so Abbanta ya saurareta ya fahimceta kuma.
"Abba zan...zan"
"Jannah shekaru basa Jira, mace ce ke. Kina 29yrs amman shiru ko jikaki zamuyi mu sha."
Da sauri ta girgiza kanta. "Then acikin wanda suke zuwa ki turo wanda kike so...."
"Abba bana son kowa ni..." The way tayi maganar kamar sara qanwarta haka.
Duk kallonta iyayen suka yi, Mamma tace "Jannah."
Kallon Mamma tayi tana amsawa.
"Are you sure you're okay, of all the men coming for your hand you don't want even one?"
Kai ta gyada Mamma zata sake magana Abba yace "is okay jeki, na baki nan da two weeks ki tsayar da wanda yayi mki aciki ki turomin shi if not I will choose myself."
Kai ta gyada da sauri tana share gumin da taji tana hadawa a fuskar. "You can go."
Da sauri ta miqe tana cewa "goodnight Abba and Mamma." Kamin ta juya ta fita.
Sam bata saurari qannenta dake mata magana ba ta wuce sama da sauri. Dakinta ta fada ta kulle tana wurgi da veil din data yafa.
"Yah Rabbi make it easy for me."
Zama tayi kan gadonta tana ajiye wayarta tayi shiru tana ajiye idonta a spot daya ta tafi tunani. So take ta tuna wayanda ke son nata taga wanda zata iya zaba amman zuciyarta Fa'iz kawai take hasko mata. Ko ta ture zancensa agefe sai ya sake dawowa.
Kanta ta dafe tana jin kamar abin yana shirin fin qarfinta. Bata taba tunanin zata taba son namijin da bai sota ba, baima san tana yi ba.
Miqewa tayi da sauri ta fada bathroom ta dauro alwala tazo ta tayar da nafila tana roqon Allah ya sauqaqa mata. Idan Fa'iz alkhairinta ne Allah ya karkato da zuciyarsa idan ba alkhairi bane Allah ya sauya mata da wanda ya fishi.....
To be continued......
#like
#comment
#share