Free chapter · Read without an account

NEW BEGINNINGS

by Saddiqah M · NURI

NURI


By Saddiqa 

NURI'S POV  


Daga ita har Mami we're silent throughout there journey back home. Afif dai kamar shine ran gidan haka, daman shine mai saka su magana ga tsokana da takura and now babu shi yayi musu nisa ba dan kadan ba, Irin nisan nan da sai nan da three to four years zai dawo.


And such is life, kana naka Allah yana nasa, nasan kuma shine daidai. Life goes on without Afif, only Mami and Nuri. Mami is trying da dan kudin warenta take son fara sana'a though bata san wanne sana'ar za tayi ba amman she's searching. While Nuri a other side tayi focusing kan karatu ne. Duk da ba'a koma ba amman ta tanadi lecture notes din 300lvl ta fara dubawa saboda yadda result dinta baiyi wani kyau ba which is unlike her.



Kullum suna gida babu inda suke zuwa kaman yanda babu wanda yake zuwa musu. Mami tayi deciding ta fara saida kayan sanyi, irin su chilled zobo, kunun aya harda ruwan sanyi don kudin warenta zai isa sosai ga suna samun wuta and akwai ma'aikata a area dinsu musamman masu gini saboda sabuwar unguwa ce kullum cikin sababbin gine-gine ake.



Kamar wasa ta fara and Allah ya mugun sama abin albarka yawanci masu aikin gini ma ke siya sai masu shago bana provision ba. Burin Mami ta tara kudi saboda registration din yarinta and Alhamdulillah duk da ba da yawa ta fara ba amman tana samun alkhairi sosai aciki, sai dai akwai saura sosai kamin kudin ya kai yanda take so.




FU'AD'S POV 



He's processing akan new branch da yake so su fara constructing a kano. An samo musu wani qaton plot a new area da ke tasowa yanzu. Bai yi rayuwa a Kano ba amman yasan commercial city ne garin so yasan zai samu a lot of clients da contract from government of Kano. Ko ba wannan ba yana son ya kasance kaf 36 states dake Nigeria ace yana da branch. Yanzu akwai biyu kawai ga na ukun nan tafe and abroad yana da two branches a UAE sai USA.




It was one summer Monday again, kaman yadda take Monday ranar aiki haka yake a waren CEO Fu'ad Jimeta. Yana zaune akan office ottoman sofa dake office dinshi ya daura system akan centre table yana operating opposite to him PA dinsa ne. 


"They're starting the construction of the new site tomorrow." 


Ba tare da ya kalli Ahad (PA) ba yace "Masha Allah. I will be there In Sha Allah."



Kai Ahad ya gyada masa yana ajiye masa new file din daya kunshi komai akan construction site din kamin ya juya ya fita. Ya jima kamin ya dago yana sauke ajiyar zuciya. Yana jin kamar ginin site dincan zai dan zaunar dashi a Nigeria and yana so yaje can USA ma.



File din ya dauka daidai wayarsa na ringing. Amsawa yayi yana kaiwa kunnensa tare da sallama.


"Pal, I donno ko zaka iya convincing Abbi." Fa'iz ya fada daga can side din yana ajiye patient file dake hannunsa kan table dinsa.


"Convincing Abbi pal?"

"Yes."


"Amman the case was closed Pal. Abbi yayi making decision dinsa what again do you want me to do about it?"


"Come on. Just try Pal. Suhan dake da rawar kai wai za'a kai abroad though uncle Farouq was there amman dai I prepare her stay anan."



Shiru Fu'ad yayi, shi kansa da Ammi ta fada masa Suhan is going abroad yaji wani iri, irin like gwara tayi zamanta gaban iyayenta a matsayinta na mace.


He just sighed and says "Zan duba Pal if I can."


"You can ma na sani."


File din hannunsa ya bude yana karanta location din unguwar dake rubuce boldly *ZAWACIKI* 



"We will talk later I hava a surgery now."


"Allah ya bada sa'a" Da haka suka yi sallama Fu'ad ya ajje wayar agefensa yana miqewa tare da file din a hannunsa ya fice.......



SUHAN'S POV.



Right from the day da Abbi yace she's going abroad take nan always moody. Suhan dake nan very lively da ita ta koma silent saboda bata so.



Tana zaune a parlour hannunta riqe da wayarta don hatta sch ta dena zuwa anyi sorting komai na tafiyarta Abbi yana jiran next week ne kawai.




Shigowar da akayi yasa ta dago kanta and it was Safa addarsu. Kallo daya suhan tayi mata tana dauke kanta tace "Adda sannu."



Ajiye handbag dinta Safa tayi tana cewa "Hana har yanzu dai damuwar Germany ne?"



Baki ta turo tana cewa "nifa Allah Adda kawai bana son tafiya can ne? How can I live babu Ammi acan and zan riqa daukar time banga Hamma F ba"



Kowa yasan waye take kira da Hamma F, Fu'ad ne. Da kallo sosai Safa ta bita, she was not a child, shekararta 32 a duniya tasan rayuwa sosai. Statement din Suhan yasa ta nazarceta sosai and just like Ammi ta fahimci kamar fa Suhan is in love with her brother. Sai dai unlike Ammi ita she's overwhelmed sosai. 



Taji kaman hakan yayi mata hardai shima Fu'ad din zai so ta, tasan qanwarta tayi dacen miji nagari da yake da halin nagarta, husband material. 



Zama tayi a kusa da ita tana cewa "Hana"



Kallonta Suhan tayi tana amsawa. Safa tace "why is it ko yaushe zancenki akan Fu'ad ne?"



Tabe baki tayi tana cewa "oho Adda, I really don't know, is just that tunashi kawai yana making day dina."



Kai Safa ta gyada tana cewa "uhmmm girly, kina jina keep on praying. Kullum ki riqayin addu'a kinji. Allah yayi mki zabi nagari."



Da amin ta amsa ba tare da ta fahimci inda zancenta ya nufa ba don bata da experience sam.



Miqewa Safa tayi tana cewa "bara naje waren Ammi."



"Ta shiga sch yau" 



"Ohhh na manta fa." Dawowa Safa tayi tana zama gefen Suhan dake danna wayarta....




JANNAH'S POV.



"Where is Dr Jannah?" Ya tambya Dr Cynthia dake round din duba patients.


"She will arrive soon Dr."


Gaba yayi yana bada command a shirya patient din da zasu yiwa surgery din. Office dinsa ya koma ya shirya kamin ya fito daidai zuwan Jannah. 


Ba qaramin kokari tayi ba ta hana kanta kallonsa tayi kaman bata lura dashi ba.



"Dr Jannah." Ya kirata da wannan muryar nasa dake sake sawa tana fada mishi kullum.



Juyawa tayi ta kalleshi tana kwabar zuciyarta akan yadda take sake zurma mishi kullum. Zuwa yanzu ta fahimci da gaske she's in love with Dr Fa'iz Ardo. 


"You're late, sannan kinsan da surgery din ko?"


Kai ta gyada ahankali da wannan sanyin take cewa "I'm sorry Dr, I dosed up."


"Get ready." Ya fada yana nufar hanyar elevator Kai tsaye. Da kallo Jannah ta bishi tana jin hawaye yana cika idonta. Ba zata taba gajiya da cewa zuciyarta ba tayi mata adalci ba sam. Ta lura bata ma gabanshi, Ko kallonta ba wani yi yake yi ba. Is hard tana wuri yayi noticing. 



"Yah Rabbi ease whatever trial is along the way."



Da sauri ta shiga office dinta ta shirya kanta cikin kayan surgery kamin ta fito itama. 



Sunyi surgery din successfully though Jannah tana jinta kawai gata nan. Indai zata ga Fa'iz zuciyarta tana qara rikicewa ne. Bata da wani best friend as friends dinta duk sunyi aure and duk sun watsar da ita saboda wannan al'adar wai idan mace tayi aure ba ruwanta da qawayenta da basu da aure, this is not fair.




Bata wani tsaya ba suna gamawa ta wuce nata office din kai tsaye ta zauna kan office chair dake dakin. 



Yanzu kam dagaske take she will resign zata nema aiki a national hospital Abuja. Zata koyawa zuciyarta rayuwa babu Fa'iz. Sannan zata qoqarta ta fitar da daya acikin wanda ke sonta ko hakan zai cire mata Fa'iz aranta. 


Ba tare da tayi shawara da kowa ba tayi typing later ta tura masa a email dinsa ta miqe ta tattare komai nata daga office din ta fita ba tayiwa kowa sallama ba ta fita premises din asibitin dake da girma sosai. Da kallo ta bi asibitin tana sallama dashi a ranta ta shiga motarta ta bar asibitin...





FU'AD'S POV.



Da kanshi yayi driving back home. Ya jima cikin motar azaune kawai doing nothing har Azzam ya dawo daga nashi aikin da yake claiming yana yi. Da kallo Fu'ad yabi Azzam din bayan ya fito, sai yake ganin kamar bai yadda da aikin da yake ba and he decided wannan karon ko baya so zai dawo aiki a NoveBuild duk da baya so, zai hadashi da Abie.




Azzam din yi yayi kamar bai ganshi ba ya dauke kai. Daga haduwa dashi har ya sawa ransa yau bad day ce a wurinsa don Fu'ad was a bad luck to him. Bin bayansa Fu'ad yayi zuwa part dinsu. Jin Fu'ad a bayansa sai ya fara wani irin taku shi bai yadda ba wai irin salon tafiyar Fu'ad yake yi and sai yake jin yau fa ya kai tunda founder and CEO din NoveBuild ke take mishi baya.



Sam wanda yake yi don shi din bai ma san yanayi ba don hankalinsa yana kan wayarsa da yake duba text din Fa'iz a haka har suka isa part din nasu. Azzam zai yi side dinsa Fu'ad ya dakatar dashi saying "zo nan Azzam."



Wani irin cije lips Azzam yayi yana hadiye wani yawun baqin ciki jin yadda Fu'ad ya kirashi with full authority kana ji kasan gaba yake dashi ko ba iya wa ba kasan a duniya ma ya fishi a komai.



Juyowa yayi yana sauke idonsa kan Fu'ad. Nan wannan kyan nasa ya bugeshi, da sauri ya dauke kansa yana komawa baya kadan ya zauna kan sofa dake parlourn behaving a good brother.


"Hamma F."


"Azzam zaka dawo aiki a NoveBuild, ban yadda da wannan companyn da kake aiki ba." Ya fada masa kai tsaye da wani irin order a muryarsa.



"Amman Allah ya tsine maka rayuwa Fu'ad." Azzam ya fada aranshi. Yanajin over his dead body yayi aiki a companyn daya tsana ya kuma tsani wanda ya mallaki companyn tun ba yanzu ba. Tun yana yaro, tunda ya fahimci Ummi tafi son Fu'ad akanshi.


"Kaji zanyiwa Abba magana."



"Don't start please Hamma. An gama magana please don't come up with this again. I prefer working anan don Allah." Da kallo yake bin Azzam din sai yake ganin wani irin abu daga idonsa da yasa ya dauke kansa yana yin gaba yace "my decision is final Azzam. You will work a NoveBuild." Ya qarasa fada yana yin side dinsa.



Iska Azzam ya kaiwa naushi yana jin Fu'ad bai taba bashi haushi irin na yau ba. Yadda yake masa magana as the boss he is a NoveBuild. Yaji kenan haka zai riqa yi masa a NoveBuild din. Wani tsaki yayi yana jin babu abinda zai saka yayi aiki a NoveBuild ko mutuwa zaiyi. Har zai zauna sai wani tunani yazo masa kansa. Da sauri ya miqe yana bin side din Fu'ad da kallo.



Kansa ya gyada yana murmushi. Irin murmushin nan da ake kira da na mugunta. Yes, ya yadda zaiyi aiki a NoveBuild, bama aiki ba shi zai koma CEO a NoveBuild. Zaiyi aiki a NoveBuild while Fu'ad yana nan babu abinda zai iya aikatawa. Yana jin it was high time yayi ruining wannan kyan na Fu'ad!




Ya kamata ya fara raba Fu'ad da kyansa yadda zai riqajin bai son fita sai ya dorashi akan kujerarsa a NoveBuild!!!!




To be continued.......



#like
#share
#comment



Want the next chapter?

Create a free ArewaPen account to save progress, unlock paid chapters, follow this author, and keep reading across web and the Android app.