Free chapter 路 Read without an account

BROTHER VS BROTHER

by Saddiqah M 路 NURI

NURI


By Saddiqa 


FU'AD'S POV 

As usual bayan ya gama azkar din asuba ya fito daga masallaci ya dawo gida. Part dinsu Ummi ya zarce kai tsaye ya wuce dakinta don yasan by this hour tana dakinta. Da sallama a bakinsa ya shiga dakin ya tarar da ita zaune akan darduma hannunta da carbi, tasan wannan shine lokacin zuwansa shi yasa ta zauna ta kai har haka.


Amsa masa sallamar tayi tana dubansa da kyau. Ta dade da sanin yana kama da Boddo tun yana yaro, to amma yau sai taga kamar yafi ko yaushe. Ta kalleshi sai taga kamar Boddo take gani lokacin da take matashiya. Tana yawan tambayar kanta ya akayi Fu'ad yake kama da Boddo not ita? Tasan ikon Allah ne amman ko yaushe tayi tambayar sai tayi sabo. 



Fuskar Fu'ad din wani haske tayi sosai da asubar nan ga wani annuri da haiba hade da kwarjini mai cika ido. Wannan kwarjinin shi yasa Ummi bata wani dade tana kare masa kallo nason ganin wani babu abu nasa da yake kama da nata..

Agefe da ita ya zauna yana yi mata murmushi kamar yadda take yi masa. Hannunsa ya miqa ya riqo nata yana cewa "Barka da safiya Ummina, kin tashi lafiya?"

Kai ta gyada masa tana zare hannunta daga nasa ta mayar dashi kan wannan fuskar nasa mai cike da kamala tana amsawa, "how's your night beloved?"


Murmushinsa da yake mugun yi masa kyau ya sakewa Ummi, murmushin da mutum hudu kawai suke ganin kalarsa, Ummi, Ammi, Abie sai Fa'iz dinsa. Wannan sune kawai mutanen da suke samun damar ganin irin wannan murmushin, murmushi ne da yake narkar da duk wanda akayiwa.


"Ummi the night was hectic, kinsan wani contract muka samu from the government of Ibadan, kuma ni zanyi designing din kalar bridge din da suke so ayi musu, I spent the night ina tsara musu shi."


"But why son, why are you always workaholic ne? Baka gajiya ne Hayaty?"

Kai ya girgiza mata yana cewa "Ummina akwai dalilin da yasa nayi hakan, maybe this week zanje Kano, muna constructing new branch acan."


Ummi was overwhelmed, wannan yana daga cikin burinta akan Fu'ad yafi kowa and is like wannan burin nata yana cika ko ma tace ya cika kai tsaye. Allah yana saka masa albarka akan duk wani abinda yake yi. Dalili kuwa shine, a duk wani abu da Fu'ad zaiyi sai ya nemi zabin Allah, sai yayi istikhara saboda yafi samun nutsuwar zabar abinda yake daidai.


"Masha Allah, Alhamdulillah. Allah ya sanya albarka a duk wani abu da zaka sa agaba Hayaty."


Yana son irin wannan addu'ar daga mahaifiyarsa, and sai yayi sa'a Ummi ko yaushe cikin yi masa take yi. "Aameen Ummi, Thank you Ummi"


"You're always welcome son. Allah yayi maka albarka" ya amsa da amin kamin ya sake cewa "lemme go and get ready Ummi." Kai ta gyadaasa tana cewa "ok nima bara naje na hada mku breakfast kai da Abienku, where's Azzam?"



Kai Fu'ad ya girgiza yanai cewa "Ummi yaushe Azzam ya koma haka ne? I'm pretty sure ko asuba bai yi ba. Na tashe shi ban san sau adadi ba amman sam yaqi"

"Hmm nima wannan banzan halin nasa yana damuna Fu'ad. Bansan yaushe ya koma haka ba."

"Zanyi maganinshi Ummi." Da haka ya fita ya wuce wani madaidaicin flat dake jikin nasu wanda yake cike da kayan motsa jiki. Duk bayan asuba idan ya dawo yake yi that's why yake nan da ginannen jiki mai daukar hankali.

One hour kawai yayi yana motsa jikinsa kamin ya wuce flat dinsu ta wata kofa data hade da nasu hannunsa dauke da qaramin towel yana goge fuskarsa da ta jiqe da gumi sosai. Bedroom dinsa ya wuce yana bin side din Azzam da kallo yana girgiza kai. 

Yana jin kamar ya kamata ya ajiye komai saboda ya saka ma dan uwansa ido, bazai so ya lalace a banza ba. Zai bincika yaga kalar wanda yake mu'amala dasu ya gani. Kasancewar Fu'ad din bai wani yi rayuwarsa anan ba yasa babu wanu shaquwa tsakaninsa da Azzam din, tuna yana secondary school boarding yayi ya gama ya wuce Massachusetts, right from his first degree zuwa na qarshe bai wani dawo gida ba sai dai su kai masa ziyara. Ya gama karatun ya dawo yayi service dinshi anan kamin ya kammala ya samu offer from Bechtel, yayi musu aiki na 4yrs before shima Allah ya buda masa ya gina nasa building company din. Azzam anan duk yayi nasa karatun, Ummi taqi yarda yayi nisa da ita saboda banbanci halaye data gani a tsakaninsu. Azzam tun yana yaro yake da rawar kai sosai unlike Fu'ad da yake nan a nuste.

Bathroom ya wuce ya bata almost 30mins kamin ya fito sanye da far kal din bathrobe, hannunsa daya yana tsane wannan sumar nasa mai cika da baqi da towel. Agaban mirror ya tsaya ya kunna dryer ya fara busar da kansa ya shafeshi da mayuka kala kala don yana mugun tattalin sumar nasa. Yana gamawa ya dawo kan beard dinsa da yake mugun qara masa kyau da kwarjini shima ya gyareshi tsaf, tun ahaka, tun kamin ya kammala shiryawa yayi kyau sosai as komai nashi mai kyau ne.

Jikinsa ya shafe da different signature body lotions dinsa ya feshe jikinsa da body spray dinsa kamin ya wuce closet din dakenan daki guda dauke da different brand clothing, watches, and shoes.

Sanye cikin white long sleeve shirt da trouser all black na kamfanin LV ya fito, qamshin turarensa na pur Oud LV ya cike dakin gaba daya da sanyi da dadin kamshi. He looks handsome sosai and elegant. 

Hannunsa dake sanye da baqin agogon Rolex ya miqa ya dauke wayarsa akan stool dake kusa da mudubi yayi yana juyawa gaba daya ya fice daga dakin gaba daya yana barin qamshinsa.


Dakin Azzam ya fara wucewa ko knocking baiyi ba ya shiga yana sallama da muryarsa a hankali. A kwance ya tarar da Azzam din, da alama ko sallahr asubar har yanzu bai yi ba. Takaici ya kule Fu'ad ya dala masa duka a bayansa yana cewa "useless fellow, wake up Mu'azzam."


Mu'azzam da yake duniyar mafarki mai dadi, mafarki irin na cikar burinsa. He's dreaming yayi mahaukatan kudi yana zaune a office da bai san na waye ba amman from mere indications office din nashi ne, sai ihu yake yiwa ma'aikatansa yadda yaso, very bossy yadda yake so ya zama yana juya kowa da komai. Gefensa wata haddaddiyar 'yan mata mai mugun kyau tana yi masa tausa sai lumshe ido yake. 


Tsabar mafarkin yayi masa dadi agasken ma lumshe idonsa dake rufe yakeyi yana wani killer smile, before kawai yaji duka daga bayansa. A firgice ya farka daga baccin yana qanqace idanunsa da kana kallo kasan rigima ce fal ciki.

Akan babban makiyansa ya sauke idanunsa, wato Fu'ad Aliyyu jimeta. A time din Azzam ji yayi da za'a bashi wuqa babu abinda zai hanashi cakawa Fu'ad din, irin like Fu'ad har a mafarki ma sai ya takurawa rayuwarsa.

"Malam tashi kaje kayi sallah." Da Fu'ad ya lura da kyau zaiga kalar hararar da Azzam yake masa sai dai lokaci yake dubawa a wayarsa hakan yasa bai lura sam dashi ba.

"Ka tashi nace." Takaici ma yasa Azzam ya kasa magana sai miqewa kawai da yayi ya fada bathroom aransa yana cewa "kuma wallahi ka jawo bazanyi sallar ba." (O'o Azzam 馃榿)

Daga murya sosai Fu'ad yayi yadda Azzam zai jishi yace "bayan kayi sallar ka shirya and meet me in my office kazo da CV dinka Mu'azzam." Yana gama fadin haka ya fice don a yadda yake mugun son komai ayi shi a tsari bazai dauki Azzam haka kawai ba tare da anyi masa Interview ba duk da kasancewarsa dan uwansa don kowa da yake aiki a NoveBuild has passed through that stage, don haka Azzam baifi kowa ba.


Flat din Ummi ya wuce ya tarar da ita tare da Abie suna breakfast is like yau Ummi zata fita don tana sanye cikin wani appliqu茅 lace mai mugun tsada daya dace da ita yayi mata kyau. Jewellery din da ta saka duka gold ne kama daga sarqa, bangles da zobe. Kana kallonta dai kaga hamshaqiya.


Da kallo suka bi Fu'ad din daya shigo da sallama, tare suka amsa masa sallamar suna yi masa murmushi admiringly. Sai da ya sake gaishesu kamin ya zauna Ummi tayi serving dinshi ya fara cin nasa abincin cike da wannan nustuwar nashi.

Basu wani dade ba duk suka miqe kusan a tare suka fita, sai Fu'ad ya raka kowanne various car dinsa kamin ya koma flat dinsu ya qarasa shirya kansa ya fito sanye da suit din kayansa ya wuce shima nashi RR din suka bar gidan.


AZZAM'S POV

Yafi 20mins a bathroom din bayan shigarsa kawai yana saqa yadda zai maida Fu'ad qasansa shi ya koma samansa. Yau yayi dana sanin rashin mai da hankali yayi kudi da yake yi. Kawai shi taqamarsa Abie da Ummi suna da kudi don haka no need shi yayi. Don da kallon dan wahala yake yiwa Fu'ad ganin yadda yake struggling wajen gina kansa. Ashe akwai lokacin da zaizo yayi sha'awar Fu'ad din, ashe akwai lokacin da zaiji dama shine yake da kudin Fu'ad din, instead of ya maida hankali shima ya nemi nashi ah no, shifa kawai na Fu'ad yake so, ai Fu'ad ya tara mishi.

Sai da ya gama tsarinshi yadda yake so kamin ya fara wankan da ya bata kusan 30mins shi a dole komai irin na Fu'ad. Bayan ya fito ya shirya kansa cikin Ralph Lauren suit farare da sam ba suyi mishi kyau ba, shi daban kayan daban. Amman a wurinsa ya gama haduwa 馃榿 ya balbale kansa da turaren Creed Aventus ya fito ko breakfast baya jin zaiyi ya wuce flat din Ummi.

Sai daya karewa part din nata kallo kamin ya wuce upstairs ya tabbatar bata nan sannan ya shiga bedroom dinta. Closet dinta ya shiga kai tsaye ya wuce wurin da take ajiye gold jewelleries dinta ya kwashe fin rabi ya fito yana adjusting kansa kamar baiyi komai ba. Bai da matsalar komai don babu CCTV a gidan ko daya saboda Ummi tace bata so, rashin yarda ne wai ita kuma ta yarda da kowa alhalin tayi hakane saboda kanta.

Fita yayi ya fada motarsa ya bar gidan yana jin sarqaqoqin daya dauka zasu ninka 10M din da yake nema don haka yayi dialing number din bad.

Bai dauka a Kiran farko ba sai da ya sake kiransa sannan ya amsa mai kiran.


"Ko yaushe baka kusa bad..."


"I'm busy ne man yane ta samu?"


"Yes kusan haka mu hadu kawai kaji yadda za'a yi."


"Wai waye wannan kake so ayiwa illa haka, wai kuwa kasan acid ma kuwa Mu'az?"


"Ban sani ba bad, na san kawai yana da mugun hadari ajikin dan adam, yana zagwanyar da jikin duk wanda ya shafa. Bad ina son kayi amfani da concentrated one sosai wadda tafi hadari sosai."


"Waye shi da za'a yiwa aiki da ita?"


"FU'AD ALIYYU JIMETA!!!!"



To be continued.....



#like
#comment
#share

Want the next chapter?

Create a free ArewaPen account to save progress, unlock paid chapters, follow this author, and keep reading across web and the Android app.