Free chapter · Read without an account

THE 5-STAR ENCOUNTER

by Saddiqah M · NURI

NURI


By Saddiqa 




NURI'S POV 


"Is ok Nuriyya. Biyayyenki is ok fa." Mami console her don tasan yanzu sai ta sake dorawa kanta wani sabon damuwar. "Mami kowa nesa yake damu." "Allah yana kusa damu Nuri." Shiru tayi don Mami ta gama magana kuma. Allah yana tare da bayinsa dake tsoronsa suke miqa lamarinsu gareshi a ko yaushe. 


Washegari da rana Mummy da Zara suka zo. Zuwansu ya sake sakasu Mami sakin jikinsu har kamar sun manta da warning din Inna don tun kamin 1 suke anan. Zara da Nuri tare suka yi girki while Mummy ta taya Mami aikin zobonta da yanzu kusan kullum sai ta sakeyin sabo saboda karewar da yake yi, ana son sanyi sosai a irin wannan lokacin da yake da zafi.


Suna daki su biyu kwance akan katifar Nuri ko wacce da waya a hannunta suna dannawa. Can Zara ta kalli Nuri tana cewa "Wallahi na gaji Nuriyya." Da sauri Nuri ta kalleta don is unlike Zara, Zara bata fiya kiran Nuri da asalin sunanta ba.


"Me ya faru?" Zaune Zara ta tashi tana miqa mata wayarta dake hannunta tace "ke wallahi na gaji, duk wasu masu sonki a makaranta ta wurina suke biyowa suna takuramin. Ke kina musu kwarjini basa tunkararki sai nice marainiyar wayonsu to wallahi duk number dinki zan basu nagaji ehe."


Wani raurau da idanu Nuri tayi tana marairaicewa sosai yadda Zara zataji tausayinta tace "Ayya best, kiyi haquri don Allah, ki barni naji da Khaleel kawai, shima ya na kare dashi bare ki bawa wasu number na. Don Allah kiyi min rai yadda Allah yayi miki." 


Hade rai Zara tayi tana dauke kallonta akan Nuri, idan Nuri tayi irin wannan kalar tausayin ko mutum baiyi niyya ba sai yayi mata abinda take so.

"Best don Allah...." Miqewa Zara tayi tana daura dankwalinta irin ture kaga tsiyar nan ta dauki wayarta tana yin hanyar fita daga dakin "kiyi ki gama."

Binta Nuri tayi da sauri tana kiran sunanta a haka suka isa parlour suka tarar da Mami da Mummy zaune suna hira abinsu. Da kallo suka bisu ganin yadda suka fito kamar wasu masu yin fada.

"Zara me kika yiwa Nuri ne?"

Wani kalar kallon Nuri Zara tayi kamin ta kalli Mummy dake tambayar tana cewa "Allah ni babu abinda nayi mata, kawai dai na gaji da takuramin din da akeyi akanta." Signal Nuri takewa Zara tayi shiru amman ina Zara parrot bata fahimta ba. "Waye yake takura mki akanta." Mummy asked again.

"Wanda suke sonta mana, ni ba'a sona sai dai nayi hadi, ga mai dalilin aure..." Murmushi Mami tayi while Nuri juyawa kawai tayi ta koma dakinta tana jin haushin Zara da bata iya controlling din bakinta. Tasan akwai tasu da Mami kawai, daman Mami ta mugun saka mata ido kan yadda takewa Khaleel and now Zara zata sake hadata da wasu ta barta taji da wannan din ma mana.



UMMI'S POV


Hankalin Ummi ba qaramin tashi yayi ba sanin yau shine deadline din da Bonefather ya bata. Tana office dinta amman kiran wayar Azzam take tun dazu. Ta kira taji line busy lokacin yana waya da bad, bayan nan tayi ta sake kira yana shiga baya dauka. At that time Ummi ji tayi kamar tayi tsunstuwa ta ganta gaban Azzam. She can't even imagine kalar punishment din da za'ayi mata. Bayan deadline ma bata son Suhana ta tafi ba'a bar mata abin baqin ciki a rayuwarta ba. Zata so taga Suhana din acikin qunci ita da Boddo.





"Mu'az was very useless, bloody whore." Miqewa tayi kawai tana jin zata wuce companyn da yake aiki. Tunda ta fito take walking majestically as the CEO she was. Workers dinta sai gaisheta suke yi amman babu wanda ta kula fuskar nan a hade don sam bata yi musu mutunci ko kadan, wani irin tsoronta suke ji don slight mistake game over zata kori mutum ne ba ruwanta.


Motarta ta shiga tayi driving zuwa companyn da Azzam yake aiki but she was not lucky don baije ba. Tsaki tayi tana cewa "Allah wadaran yaron nan wallahi, marar amfani kawai."


Dole ta juya ta koma office dinta tana cigaba da trying number dinsa ammn har yanzu baya picking. Bata tabajin haushin Azzam din ba sama da yau. Like sai taji sam baida wani amfani a rayuwarta. She was like tayi data sanin haifansa da tayi. He was totally unlike Fu'ad, Fu'ad ko meeting yake yaga kiran Ummi zai dauka ko ba zasuyi waya mai tsayi ba zaice yana meeting idan ya fito zai kirata. That's why Fu'ad na daban ne acikin ranta. Tsaki kawia take jerawa akai akai tana sake kiran Azzam din.




SUHAN'S POV 



Tana kitchen tana taya Ammi girki, she is slicing onion ammn fuskar nan nata kana gani kasan sam ba son aikin take yi ba. She's that kind of mutanen da sam basa son girki, da tayi girki gwara mata tayi aikin gida duk yawansa. Ga Ammi ta horeta sosai kan aikin gida har girkin, ta iya varieties of dishes amman sam ba tayi sai Ammi ta takura mata. 



Ammi na son yaranta su iya komai kar su zama komai sai anyi musu. Kallonta yanzu ma Ammi tayi tana girgiza kai ganin yadda take wani turo baki cike da shagwaba. Hannu Ammi ta kai ahankali ta buge bakin nata tana cewa "are you pouting lips to me or what?"



Da sauri ta girgiza kanta tana gyarawa tace "Ammi albasa ne fa...akwai yaji."


"Haka zaki gyara idan kika je gidanki waye zai yi miki?"


Wannan gidanki da Ammi tace yasa Suhan yin murmushi kadan tana cewa "Ammi zaiyi mana..."

Baki Ammi ta bude tana jin zallar rashin kunyan Suhan din tace "wayeshi?"


Dauke kai Suhana tayi aranta tana son fadawa Ammi Hamma F mana amman tasan bugeta Ammi za tayi at long last. Hakan yasa tace "mai rabo mana Ammi....." 



Bata qarasa fadin mai rabon ba taji duka mara zafi a bayanta. Ajiye wuqar tayi ahankali tana yin baya fuskarta da murmushi kadan tace "o'o Ammi da zafi fa.."

"Zafin nake so kiji ai." 

Shagwabe fuska sosai tayi tana kallon Ammi da tayi kamar bata ganin abinda take yi. "Je ki sake wanka madam, we're going out, your vissa is ready, you're leaving this country the day after tomorrow."

Kai kawai Suhana ta gyada tana juyawa ahankali ta fita a kitchen din. Dakinta ta wuce tana jin dama akwai abinda za tayi da zaisa a fasa tafiyar nan. Sai data fara fito da wani atampha na super Holland da akayima plane A-line kamin ta wuce bathroom...


Ba wani kwalliya tayi mai yawa ba don ko kwalli bata saka ba duk sonta da kwalliya kuwa. Haka ta sauko da daurin kanta plane ta yafa Chantilly a kafadarta kafarta sanye da flat shoe na Zara baqi kalar mayafinta. 


A shirye ta tarar da Ammi don abaya ash kawai ammin ta saka da mini v shaped hijab daya mata kyau kamar ba ita ta haifi yara uku manya ba.


"Gyaran yafin mayafin nan." Ammi ta fada mata tana miqewa hannunta riqe da key din motarta. Da sauri ta gyara mayafin nata suna jerewa tare suka fita......



JANNAH'S POV 


"Ki gama abinda kikeyi kizo nan ki sameni muyi wani magana kinji." Kai Jannah ta dagawa Mamma tana kokarin rufe system din da take kallon wani K-Drama, kallo sam ba halinta bane amman rashin abinyi yasa ta fara and now gashi ya fara shiga jikinta. Sai dai indirectly the more tana kallon K-Dramas the more tana sake falling for Fa'iz. She's imagining herself with Fa'iz madly in love. 


Miqewa tayi tana daura dankwalin atamfar dake jikinta ta fita. Dakin Mamma ta nufa dake can edge na hallway din. Da sallama ta shiga ta tarar da Mamma a zaune tana hada wasu paper bag don Mamma business din atampha da laces take agida duk mai so zatayi masa packing ta aika masa.


Agefe da ita ta zauna tana cewa "Mamma."


"Yes Yayarsu, har kin gama ne?" 


"Kiranki is more important than abinda nake yi mamma."

Murmushi Mamma tayi tana cewa "Allah yayi mki jagora a rayuwa Jannah."


"Aameen."


"Kinga dama aike ne zanyi, kije gidan gwaggonku Aisha ki kai mata wannan." Mamma ta qarashe tana nuna nata packs din laces din data ajiye agefe.


"Tom Mamma dama munyi da wannan mai Khumras din zamu hadu ta bani saqona."

"Ok karki dade kinji."

"In Sha Allah."


Miqewa Jannah tayi ta koma dakinta ta dan sake gyarawa don babu abinda shigarta tayi ta dauki car key dinta ta koma waren Mamma ta amsa saqon tana mata sallama ta fice.


Ahankali take driving akan titin kaman bata so, ta dade sosai bata fita ba tun ranar da tayi resigning almost two weeks kenan rabon data fita. Ko zasu fita za tace musu sai sun dawo ne kawai bata son fita. Aganinta babu abinda fitar zai yi mata har dai ba haduwa za tayi da Fa'iz Aliyyu Ardo ba. Yanzun ma don babu yadda za tayi da Mamma ne, dole ne taje mata aikenta that's why ko musu ba tayi ba.


Gidan Aunty Aisha yana da dan nisa amman haka nan take wani irin driving kaman titin gidan su ne. Ta dade sosai kamin ta isa gidan nata tayi parking a qofar gidan don ba wani babba ne da zata shigar da motarta ba, parking space na mota biyu ne kawai and itama ba dadewa za tayi ba. Kashe motar tayi tana daukar package din aiken ta fita.


Ta jima tana knocking din gidan kamin aka bude mata, yarinyar Aunty Aishan da kanta ta bude mata. Idanu ta ware tana kallon Jannah da mamaki sosai tana cewa "laaa Yah Jannah kece?" Murmushi Jannah tayi mata tana riqo hannun yarinyar suka gaisa suna shiga cikin gidan tace "eh nice Ikram, how're you doing?"

"Alhamdulillah, kin dade baki zo ba daman Umma tayi fushi." 

Murmushi Jannah tayi tana cewa "zata sauko yau ta ganni." Don Aunty Aishan qanwar Mamma ce and tana mugun son zumunci sosai musamman da Jannah ma don ita ba kowa ya saba da ita ba saboda dadewa karatun da tayi abroad. Tare suka jera da Ikram suka shiga cikin parlourn da suka tarar da Aunty Aisha zaune a qasa tana bawa qaramin danta abinci.

Da kallo ta bi Jannah jin sallamarsu, da dan mamaki ta ware idanunta tana cewa "wa nake gani haka kamar Jannah?"

Murmushi Jannah tayi tana zama a gefe da ita ta miqa hannunta zata dauki Aiman ya maqale mamansa don yana da kiwa. "Aunty barka da yamma."


"Barkanki Jannah, ysu Yaya? Yau Allah yayi kenan?"


Murmushin sai Jannah ta sake yi tana cewa "eh Aunty saqo wai na kawo Miki." Ta fada tana miqa mata package din hannunta. Amsa tayi tana cewa "Yawwa nagode don yanzu ma mai saqon tace min zata aiko a amsa bayan da mukayi waya da Yaya tace kin taho."

Kai kawai Jannah ta gyada mata tana gyara zamanta, Ikram ta kawo mata snacks da drink masu sanyi ta ajiye agabanta. Lemon kawai Jannah ta dauka tana amsa kiran da yake shigo mata wayarta. Miqewa tayi tana gyara yafen mayafinta Aunty Aisha ta bita da kallo tana cewa "ban gane ba, Jannah naga kin miqe."


"Wai Khumras na siya a waren wata shine mukayi zamu hadu na amsa amman karki damu Aunty zanzo na wunin miki."

Hararar wasa kawai tayi mata tana cewa "kamar gaske, Allah ya tsare hanya ki gaida yayan."

"Za taji In Sha Allah, Allah ya bamu alkhairi." Fitowa tayi Ikram tana rakota har kofar gida, kudi ta bawa yarinyar tana cewa su sai chocolate ita da qannenta, ta amsa tana godiya suka yi sallama ta koma gida.


Unlike before yanzu gudu Jannah keyi sosai amman very carefull don kamin taje 5-star restaurant din da zasu hadu ta amshi saqonta matar ta kirata kusan sau biyar wai tayi sauri tana jiranta. Tana zuwa tayi parking a compound din wurin ta kashe motarta da dan sauri haka ta qarasa ciki. 


Da sallama akan harshenta ta shiga don tasan babu wanda zaiji ma bare a amsa mata. Side din damanta da taga matar tayi ta qarasa tana jan kujera ta zauna tana cewa "I'm sorry Husna na barki kina jira."

Kai Husna ta girgiza tana cewa "ba komai don ina sauri nema shi yasa ga saqonki naso kawo miki gida wallahi kawai biki muke yi ne bani time shi yasa."


"Babu komai ai." Jannah ta miqa hannunta zata amsa tana dago kanta idonta ya fada cikin na Fa'iz!!!!



To be continued....


#like
#comment
#share

Want the next chapter?

Create a free ArewaPen account to save progress, unlock paid chapters, follow this author, and keep reading across web and the Android app.